Showing 36001 words to 39000 words out of 41935 words

Chapter 13 - TSINUWAR UWA Book Complete Document by S-Reza .txt

S Reza   

29 Nov 2024

2665

kansa yace ya fasa. Cikin masifa da rufewar ido ta ce "Sai naga uban da zai sa na aure sa ɗin, kafita min daga daki ai dukkanin ku muna fukai ne, ai ba haka muka yi daku ba. Kawu Inuwa da ya cika da mamaki ya ce "Siyama nine munafikin? Ai kuwa ta hayayyaƙo masa ta ce "Eh kaine ai ba haka muka yi ba, kai kazo kana ta nuna mata ƙwadayin ka a kan kuɗi duk ka ɓata komai ni ka bar min ɗaki. A zuciya Kawu Inuwa ya ce "Shi kenan girma ya fadi akan kuɗi! Afili kuma ya ce "Shi kenan Siyama na tafi Nagode" Ko kallonsa bata yi ba har ya bar ɗakin. Ganin ya fita yasa Nasiru dawowa ɗakin domin lokacin da ya shigo shi kuma fita yayi.


Lokaci ɗaya taji wani irin tsanar Yaya Bala da kuma tsoron Umma da taji yana fita a ranta, barin ma idan ta tuna da cewar tana da kuɗi. Sai kuma shi waccan yaron dolon da take jin wallahi zata iya kashe shi idan suka haɗu. Sosai take yin da ta sanin shiga da Ibrahim cikin rayuwarta ganin duk sabo da shi burin ta ke neman tarwatsewa. Kai dole nema taje gidan nasu taci kutumar ubansa shida kakar tasa, to ana so dole ne, su basu ga yanayin yaron nasu ba mai zubin doleye sakalai wai shi zata sura to ta kai ina tayi yaya da shi. Haka ta sha kukanta kafin ta miƙe ko wanka bata yi ba, ta ɗauki mayafi da niyyar zuwa gidan su Ibrahim.


Binta da Fati ne suka kai Umma sashen ta, wanda har kanta ya fara mata ciwo, magani suka ɓallo mata tasha sannan ta kwanta tana tunanin abun da ya faru, ko tace yake faruwa. Sosai ta ɗorawa Yaya Bala laifin komai da kuma aikin sa, anan take ta yanke shawarar wallahi dole sai Siyama ta auri Ibrahim sai dai idan ita ba uwarta bace, sannan dole Bala yabar wannan aikin nasa, kawai gidan su nada za'a saka a kasuwa sai ya ja jari da kuɗin, sannan a biyawa Nasiru kudin makaranta sannan a koma asibiti da shi. Haka dai Umma ta gama sake-saken ta har tayi Sa'a barci yayi gaba da ita. Sunzo sai tin ɗakin yaya Bala Binta ta tsaya ta ce da Fati "Bari na duba Yaya ko lafiya" kafin ta bata amsa ta tura ƙofar ta shiga tana sanɗa. Ganin haka yasa Fati tafiya ta barta domin ta gano takun Binta ɗin, ita dai tace ga fili ga mai doki indai Yaya Bala ne.


******
*YAYA BALA*
Sosai ya shiga ruɗu jin irin rashin Kunyar da Siyama ke yi, bai san lokacin da ya ɗauketa da mari ba, har sai da hannunsa mai ciwon yayi kara wanda hakan yasa ya ƙara fama ciwon nasa, sosai yake masa zafi dan kamar ruwa ne yaji yana ɗan fita ta cikin ɗaurin da a kai masa. Haka ya ɗaure ba tare da kowa ya lura ba har dai ya dinga bawa Umma hakuri yasa su Fati suka tafi da ita bangaren ta, bayan Baba Hassan da wannan tsohuwar sun tafi ne shima ya tashi da ƙyar ya nufi ɗakinsa yana ji kamar hannun nasa baya jikin sa. Sosai yake shan a zaba haka yasa ya shiga warware nadin da a kai masa. Ganin jini ya fara nuna a lama ne yasa ya fara cire kayan jikinsa kasancewar farare ne. Sosai yayi da ya sanin dukan ta gashi ya dawo da ciwon sa sabo, tsabar azaba ji yake kamar ya fashe da kuka, dan har wani hawayen azaba ke fitowa daga idonsa. Sai da ya rage daga shi sai gajeren wando ɗan ciki, kafin ya shiga warware ciwon yana tunanin ƙara dai ya samo mai ɗaurin gargajiya ya ɗaura shi zai fi. Sosai ya warware naɗin ai kuwa ga jini ya ɗan fito alamar dai ya fame sosai. Yana son ya tashi ya shiga Toilet ya ɗebo ruwa amma ya kasa sai sauƙe ajiyar zuciya yake yi. Haka dai ya miƙe tsaye kenan yaji an turo ƙofar dakin an shigo ba tare da sallama ba. Kallonta yayi cike da mamaki yake binta da kallo ganin ta shigo masa ɗaki babu sallama ga shi ta doso gurinsa a rikice tana neman kamo masa hannu. Wata tsawa ya daka mata wacce yaji ta har cikin ciwon nasa, wanda yasa sai da ya koma zaunen da yake da. Binta kuwa ta tsorata da tsawar amma hakan bai hanata ƙarasawa gurin tana kamo hannunsa ba ta ce...📝




Wannan littafin na kuɗi ne duk mai son karantawa sai ta biya a sakata a group. Duk wacce take son karantawa zata iya fara biya tun yanzu naga kaman hakan zaifi. Complete ɗinsa ɗari biyar 500₦ a tura ta wannan lambar 8100785178 opay Adam Salisu. A turo da shedar biya ta wannan lambar 08100785178. Na kusa gama free page. Babu laillai babu dole, idan kinga zaki iya kizo ayi tafiyar dake, idan kuma kinga ba zaki iya ba ki bimu da addu'a, nasan ina tare da ƴan amanar S Reza masu bina duk rintsi. Daga page 11 za'a daina ganin posting har sai mutum ya biya zai samu.


Love all
One love
Comments
Ana shering
Love my fan's
By S-Reza write
[7/16, 3:54 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*








_By S-Reza_




_FWAS_






*Page 1️⃣1️⃣*
Binta ta ce "Yaya dama karaya kayi ne? Ai ina ce targaɗe ne, kawo na gyara maka na iya" ta faɗa tana ruƙo hannun nasa. Yaya Bala kuwa sai yanzu ya tuna da cewar Mommy fa ta iya gyaran karaya da targaɗe to amma bai san ita Binta yau she ta koya ba. Ya ce "Tashi ki fita daga ɗakin nan yanzu?" Ta ce "Yaya ɗaurin da a kai maka ɗin ne bai yi ba ina zuwa ka gani, karka tashi kaji yanzu zan dawo" Tana faɗa tana miƙe wa da sauri ta bar ɗakin ta nufi ɗakin su, shi dai ya bita da kallo bai ce komai ba. Bata yi sallama ba ta shiga duba jakarta ta kwaso wasu kwalabai gudu uku ita dai Fati tana ta raka ta da ido. Haka ta koma ta same sa a gurin da ta barshi. Toilet ta shiga ta fara dube-dube sai ta ɗauko wata singlet ɗin sa ta ce "Yaya kana son wannan rigar? Ya kalli rigar da kyau ya ce "Meye kike yi haka a ina kika koyo gyaran karaya?" Ta ce "Yaya kenan kai dai tsaya ka ganewa idon ka. Sai ta shiga duba inda zata ga tsunma, ganin bata samu bane ta cire hular kanta shi dai ya bita da kallo yana ta mamaki. Gashin ta yake kallo ganin sa baki ƙirin kuma a wanke gashi babu laifi yana da tsayi kasancewar babu kitso akan, har wani ƙamshi ke fita daga cikin gashin, lokaci ɗaya ya tuno da Anty Zainab itama haka take da gashi har ma yafi wannan tsayi, sannan takan buɗe gashin kan nata idan suna su biyu, domin yana son mace mai gashi sosai kuma bai cika son yaga mace na yin kitso ba, yafi son ganin gashi a haka. Kallonsa ya kai gurin da hoton ta yake ita kaɗai sanye da doguwar riga ta saka glas ta riƙe gife da gefen glas ɗin da hannu biyu tana murmushi. Kallon gurin da yake kallo tayi sai ta sauke ajiyar zuciya a zuciya ta ce "Lallai a kwai Binta kina da aiki". Yana ta kallon hoton har ta jona ruwa ya ɗan yi zafi ƙadan, kafin ta cire ganin har lokacin yana kallon hoton harda hawaye ne, yasa ta tsoma hular tata a cikin ruwan ta ɗan matse kafin ta danna masa da ɗan karfi wanda yasa da sauri ya dawo da kallonsa gareta. Tayi ɗan murmushi ta ce "Yaya bari kaga aikin ƴar gado". Haka ta wanke masa jinin ta ɗan danddana hannun da ruwan zafi kafin ta ja masa hannun, ganin yadda yake yi ne ta ke yi da gaiyya amma ya dake, haka ta shafa masa wannan mayukan da ta ɗebo, sannan ta yi amfani da igiyar da ya ware ɗazu ta wanke ta ɗaure masa. Tana gamawa ta ce "In sha Allah sati ɗaya za'a warware ɗaurin. Ya ce "Idan kuwa kaka ɓata min hannu zan koya miki hankali, je ki kawo min abinci".Tayi dariya ta ce "Yaya bani da hankali dama?" Ya ce "Nace ki kawo min abinci ko? Ta ce "Ni dai Allah yaya ka daina ce min bani da hankali, to me nake yi na rashin hankali?" Ta faɗa harda bubbuga ƙafa a ƙasa ita a dole zata yi shaƙwaɓa. Yaya Bala da mamaki yake kallonta har abun yaso basa dariya amma ya dake. A ransa yana mamakin Binta yana tunanin Allah yasa dai ba sonsa take ba, domin kwana biyu gaba daya ya lura da ita. Ya haɗe rai ya ce "Yau she na fara wasa da ke Binta? Kin raina ni ko? Ya faɗa yana tamke fuska. Ita kuwa Binta ta ƙara maraireciwa ta ce "To yaya haka kawai sai kace min mahaukaciya, yanzu fa na gama maka gyara ko na gode baka ce ba, kuma baka biya kuɗin gyara ba shine zaka ce min mahaukaciya. Yaya Bala tsabar mamaki bai san dariya ta kufce masa ba. Shi yaushe ya ce mata mahaukaciya. Ganin harda kukanta yasa ya ce "Ok tom naji ke ba mahaukaciya ba ce, kuma na gode sosai, sannan nawa ne kuɗin aikin. Jin haka yasa Binta sakin dariya da karfi harda riƙe ciki ta ce "Yaya kaga nasa kayi dariya, kuma kuɗin aiki na dubu goma ne amma ka ajiye min a gurinka ka tara min idan ciwon bai gyaru ba na sake gyarawa shima sai ka ajiye min har na tara da yawa. Tana faɗa ta bar ɗakin tana dariya. Waro ido yayi yana kallonta amma har ta bar ɗakin. Dariya yayi yana kallon hannunsa da har ya daina masa zugi sai wani sanyi yake masa da alamar man da ta shafa a gurin ne. Rabonsa da ya samu kansa a cikin farin ciki haka tun kafin rasuwar Anty Zainab. Kwantawa yayi yana jira ta kawo masa abincin.


****
*IBRAHIM*
Lokacin da ya dawo daga aikin Hajja ta tare shi da zancen da Haladu yayi mata na karbar kuɗin da Siyama ta ce ya rubuto zata basa tayi masa. Amma Ibrahim ya ce shi sam ba dan kuɗi yake sonta ba, kuma duk abun da ya taɓa bata ya bata domin Allah da kuma son da yake mata ne. Shima ya shiga tambayar Hajja ɗin akan taje gidan su Siyama ɗin. Tsabar haushi da takaici yasa Hajja faɗin. "To bari kaji wallahi babu inda zanje, idan kuma kana son naje to sai kaje ka ƙarbo mana wannan kuɗin, haba Ibrahim kai idan baka buƙata ai mu muna da buƙata, yarinyar nan tace bata sonka to dole ne kayi hakuri kowa yaje yayi rayuwarsa mana. Ibrahim da baya son jin kalmar wai Siyama bata son sa kuwa wani irin ɓacin rai ne ke taso masa yana jin zai iya cewa komai ga Hajja idan ya tsaya sauraronta, hakan yasa ya barta a gurin tana cigaba da faɗa. Washegari kuwa sai ga Haladu yazo da takarda ya rubuto abubuwan da yaga sun dace, aka duba kuɗi totall nera dubu talatin da biyu harda ɗari biyu da ashirin. Hajja da kuwa bayan Nana ta sanar da ita yawan kuɗin ne yasa ta riƙe baki tana faɗin "Kuma gaba ɗaya zata bayar? Haladu ya ce "Ai Hajja wannan ma iya wanda na sani ne, ina so shima ya fadi sauran kinga ko dubu hamsin da wani abu aka kai ya ya isa yaja jari ya manta da ita. Haka suka runtuma zuwa ɗakin Ibrahim da yau yace bashi da lafiya ba zai je aiki ba. Kwance suka samesa yana kallon sama duk ya rame, domin tun da abun ya faru baya wani cin abinci da yawa. Zama Haladu yayi ya ce "Ta shi malam duba ka gani meye ban saka ba, harda tsiren da kake sintirin saya mata duk ran juma'a na ɗari uku-uku na saka kuma shima iya wanda na gani ne, ai kwara a ramawa kura aniyar ta, kai da nine kai wallahi har wanda ban bata Bama sai na saka. Haladu ya faɗa yana miƙa masa takardar. Ibrahim ya ce "Wai meye ne duk kunzo zaku dame ni, ni barci nake ji dan Allah ku fita min" Haladu ya tura masa takardar gabansa yana faɗin, kai ɗin banza nasha wahalar rubutun kace na fita. Dole ya mike ya amshi takardar yana dubawa. Ibrahim na gama kalla ya yaga ta yana sakin tsaki. Ya ce "Ni wallahi matsala ta dai kai Haladu kwaɗayi da shegen son kuɗi, kai a tunaninka kuɗi ko wani abu zai sa na rabu da Siyama ne, nifa wallahi sai dai ko mutuwa nayi, amma muddin an barni a raye to babu mai iya rabani da siyamata, kuma maganar kuɗi ni ba domin ta biyani nayi ba, siyama ba zata iya biyena abun da nayi mata ba har sai ta yarda zata aure ni. Hajja da ta gama ƙuluwa tace "Haladu ku rabu dashi ai bari ba shegiya bace da ubanta, yunwa da damuwa ba ƙannen ubansa babe, ta shi ka tafi sannunka da ƙoƙari kaji mun gode. Haka Haladu ya tafi yana mamakin anya kuwa abakinsa bai samu tabin hankali ba, duk da cewar dama kamar dai yana da ɗan matsala. Haka suka manta da shi har dare, ganin bai fito bane yasa Hajja ƙara leƙasa, ta ganshi zaune ya dafe kai. Ta karasa ciki taga yana kuka yasa waya a gaba alamar dai Siyama yake kira. Lokaci ɗaya Hajja ta tausaya masa, ta zauna tana lallashin sa, tasa Nana ta kawo masa abinci amma sam yaki ci, sai sunan Siyama yake kira, sosai fa Hajja da Nana suka tsorata, har dare yaki cin abinci, karshe ma ya fara amai yana tari. Da safe ta kira masa mai dan shagon gurin magani yayi masa allura bayan an bashi baƙin shayi ya sha. Shima a shagon Haladu aka karbo, ko kuɗin maganin ma shine ya dauki nauyin biya. Haka jikin nasa ya ƙara sauki har washe gari da ya tashi da wani irin ciwon zuciya wai shi dole sai yaga Siyama, gashi baya iya tafiya, kuma sai riƙe zuciya yake yi, hakan yasa Hajja ta zari hijjabi sai gidan su.


Lokacin da ta dawo daga gidan su Siyama da kuka ta shigo domin kuwa taga duk abun da yake faruwa a gaban ta. Yanzu kam ta tabbatar sai dai Ibrahim ya mutu idan a kan Siyama ɗin ne. Lokacin da ya ga Hajja na kuka sai ya ƙara ruɗewa yana tambayar meye ya samu Siyama ɗin, Bama meye ya samu Ita Hajja ɗin da taje gidan ba a'a shi dai siyamarsa. Sosai Hajja ke kuka tama rasa ta ina zata fara yi musa bayani. Nana ta ce "Hajja ko Siyama ɗin ta mutu ne?" Lokaci ɗaya Ibrahim ya miƙe zaune yana sakarwa Nana mari tass a bakinta! Ta riƙe bakin tana kallonsa shima ya na kallonta kowa yaƙi yin magana sai hannu ɗaya da ya riƙe zuciyar sa. Nana ta ja dogon tsaki ta tashi ta bar ɗakin tana faɗin "Allah yasa ma ta mutu mota ta take tsinanniyar kowa ya huta, ƴar banza mai girman kai" Ibrahim ya bita da kallo yana ƙara cigaba da tari yana kallon Hajja da take ta kuka, a ransa yana jin zai iya ɓalla Nana a gidan tabbas kuwa. Ya ce "Wai Hajja ba zaki min magana bane, kinzo kin sani a gaba sai kuka kike baki ce min komai ba, kina so sai zuciyata ta fashe ne kafin ki sanar dani. Itama cikin Irin ihun da yayi ta ce "Dan ubanka zuciyar taka ta fashe ko yanzu wawa mara hankali kawai kaje kana hauka akan yarinyar da bata ragawa kowa ba har iyayenta, wacce babu wanda ya isa da ita, to ni wallahi ma ko tace zata aure ka ba zan yarda ba, me za'ayi da irin marasa tarbiyya da rashin ganin girman iyayensa, yarinyar da a gabana uwarta na faɗa tana faɗa, to wallahi kamaji bada niba. Tana rufe baki Siyama ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin "Eh fadi ki ƙara tsohuwar muna fuka ashe gulma ya kai ki gidan namu.


Kwallon-kallo aka tsaya ana yi tsakanin Siyama da Hajja da IB. Da sauri ya miƙe tsaye yana kallonta kamar dai gizo take masa. Ganin kowa yayi shiru ne yasa Ibrahim ɗin faɗin "Siyamata kece da gaske ko dai gizo ne?" Ya faɗa yana ƙoƙarin kamo hannunta. Ita dai Hajja tayi mutuwar tsaye domin tsoro take ji, yanzu-yanzu ta gama da iyayenta ma bare ita, hakan yasa ta takure agefe ta kasa cewa komai. "Da sauri ta ture hannunsa tana faɗin "Kai wawa soko ɗan dolo-dolo, saurareni kaji, gargaɗi nazo nayi muku kai da wannan tsohon magulmaciyar taka. Ta faɗa tana nuna Hajja da hannu kamar zata tsokale mata ido. Taci gaba da faɗin... Na rantse da girman Allah idan baku fita daga sabgata ba zan sa a kulle wannan soloɓiyon jikan naki, kuma ƙullewar da bazaki sake ganinsa ba. Kai kuma ɗan dolo, ba kana yin abu kamar wawa ba, kana yi kamar baka da zuciya ba, to wallahi muddin ka ƙara nuna ka sanni na rantse sai na aikata abun da na faɗa maka. Daga yau ko nace daga yanzu idan na fita daga gidan nan to babu ni babu ku, karku ƙara nuna kun taɓa ganina, idan ma wani ya kiraku daga gidan mu kace kai yanzu ka daina sona, koma waye kana dai jina ko? Ta karasa tana daka masa tsawa kuma tana kama kunne alamar gargaɗi. Ibrahim da yaji ciwon zuciyar da ke damunsa ya tafi dalilin ganin Siyama ya ce "Siyama kome zaki min sai dai kiyi amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login