Showing 9001 words to 12000 words out of 41935 words
suna Kawu Inuwa ɗan bala'i ne na gaske, yana da faɗa sosai domin duk faɗan Umma tana tsoran sa, shine ke bin Gambon Hassan da Hussaini duk da ita Gambon Allah yayi mata rasuwa, shima Al-Hasan ɗin wato mahaifin su Siyama shima ya rasu, yanzu daga Kawu Inuwa ɗin sai Baba Husaini ɗin.
ya ce "Ka natsu tukunna Bala yanzu ta lafiyar ka ake yi". Ganin Bala yaƙi tsayawa ne yasa suka kira likita, nan ya sanar musu cewar babu abun da ke damun sa, kawai karya ce a hannun kawai, kuma an ɗaure. Shima ɗayan karaya ce hannu da ƙafaɗa shima an ɗaure. Sai da aka zuba musu abinci sukaci ƙadan kafin aka ƙara musu allura likitan yace zuwa gobe in sha Allah za'a sallamesu, sai suje su cigaba da jinyar hannunsu a gida. Sai da barci ya ɗauke su kafin kawu Inuwa da sauran suka koma gida aka bar Umma da Siyama da Fati.
Umma ta kalli Siyama ta ce "Jiya bayan fitar su Yayanki ina kika je? Umma tayi tambayar ne badan tasan komai ba, domin ita bata ko kalli shirin ba kasancewar babu wuta. Siyama ta ɗago daga chatting ɗin da take yi da Aida ta kalli Umma. Umma cikin faɗa ta ce "Ina miki magana kina danna waya tsabar raini ko Siyama" Ai da sauri ta kashe wayar tana dawo da hankalin ta ga Umma. Umma ta sake faɗin "Ina kika je baki dawo bar har wannan abun ya faru tun safe? Siyama ta kalli Fati taga itama ita take kallo sai kawai ta ce "Gurin taron nima naje". Umma da dama tasan dole gurin taje, domin yadda Siyama ta ƙwallafa wannan gasar a ranta tasan ko masu shiga gasar ƙare kenan. Umma ta ce "Amma ai Yayanki ya hana ki ko, kuma nima na hana ki, amma kin nuna mana cewar bamu isa ba ko? Siyama kibi duniya a hankali, yanzu gashi kina kallo yadda ake mutuwa cikin rashin shiri, yanzu da nice na mutu ina fishi da ke Siyama yaya zaki ji! Lokaci ɗaya gaban siyama ya faɗi jin kalmar mutuwa, ga kuma tunowa da yanzu fa da gaske Anty Zainab ta rasu ko. Umma ta ci gaba da cewa "Ki duba yadda yake fadi tashi akan mu, shi kansa ba wani samun kirki yake yi ba, amma haka yake kokari damu, yanzu ko wannan ba zaki duba ba ki riƙe maraicin kiba Siyama, yanzu ba kya tsoron wani abu ya dameki a hanya da kika tafi har gurin ke ɗaya bayan Uwar da ta haife ki tace karki je?. Daidai lokacin Siyama taji ƙarar shigowar message a wayarta hakan yasa ta kalli wayar ba tare da Umma ta kula ba, shigar kuɗi ne cikin account ɗin ta wanda tun ɗazu take jin shigar su. Haka dai Umma tai mata faɗa sosai wanda Fati dake kusa da ita tasha kuka ita kuwa rabin hankalin ta naga wayar ta ne. Haka dai Bayan farkawar su Nasiru Umma da Fati suka tafi gida. Har lokacin yaya Bala bai ko yi wa Siyama magana ba, yakan dai saci kallonta lokacin da take chatting yana ganin irin dariyar da take yi ko tayi murmushi. Sosai ya shiga tunanin meye laifin sa a riƙon da yayiwa Siyama, sannan tayaya har ta shiga team har ta samu damar halartar gasar batare da ta bar wata alama ko ɗaya da zai gane ba, ta yaya duk irin tsaron da ya saka mata, sosai wannan tunanin ke masa yawo akai.
Chatting suke yi a group ɗin su wanda ake sanar da ita dole sai tazo gurin aikin su wato shagonsu damin sa hannun akan komai nata, kuma ta warewa team nasu, kuma ga wasu manyan mutane dake son ganin ta. Ta ce duk Aida ta wakilceta amma Oga Fita yace, awa ɗaya aka bata ta shirya tazo, kuma ta tabbatar ta sha wanka domin ba ƙananan mutane bane zasu zanta da ita. Haka tace to zata zo.tana ɗago kai taga Yaya Bala yana kallon ta hawaye na zubo masa ta kumatu, ta kashe datar tana kallon sa, taje kusa da shi tana share hawayen ta kamo hannunsa, lokaci ɗaya ya dawo daga tunanin da yake ya riƙe mata hannun yana faɗin "Zainab baki mutu ba ko, kin dawo gare ni ko. Yana faɗa ya haɗa ido da Siyama ya sakar mata hannu ya juya kai gefe. Sai a lokacin Siyama ta ce "Dan Allah yaya kayi haƙu" Da sauri ya daga mata hannunsa mara ciwon ya juya baya. Siyama ta fashe da kuka tana toshe baki. Ta kalli Nasiru ta ce "Dan Allah yaya Nasiru" shima ya dakatar da ita. Ta juya ta fita daga ɗakin ta shiga Gurin likitan ta ce "Yanzu babu wani abu da ake binmu ko? likitan ya ce ba komai, sai maganin da zaki siya idan sun koma gida su dinga sha, amma sai zaku tafi za'a rubuta muku. Ta ce "Suma rubuta tun yanzu. Ai kuwa take ta fidda kuɗin maganin dama ita ce ta biya na komai, sannan ta kama hanyar gida. Ganin tana tafiya ana kallonta ne yasa ta samu wani guri a gefen asibitin ta tsaya ta kira Aida ta ce tazo da Mota yanzu ta dauke ta, bayan tai mata kwatancen gurin da take. Ai kuwa bata daɗe sosai ba sai ga ta nan da Mota, tana zuwa ta buɗe mata gidan gaba ta shiga. Aida ta kalleta ta ce "Ina muka nufa? Siyama ta kwantar da kanta a kujerar matotar tana tuna faɗan da Umma tai mata, ta ce "Muje gidan ki" Aida ta juyo ta kalleta bata ce komai ba har suka isa gidan Aida ɗin da ta kama take zaune ita da ƙanwarta da ƙanin ta Jamila da jamilu. Kana shiga gidan Aida kasan ka shigo gidan Model, hotunan ta ne ta ko'ina a cikin palon, haka cikin ɗakinta, hotuna dai irin na Model wasu doguwar riga wasu iya kayan barci.
Ganin Siyamar ta kwanta a kan gado ne yasa Aida faɗin "Amma kinsan awa ɗaya Oga Fita ya baki ko? Siyama ta ce "Ban san kayan da zan sa ba, kuma ni barci naje ji wallahi na gaji tun jiya ban huta ba, kawai kije a maimako na please. Siyama ta faɗa Domin tasan tabbas Aida ita ce komai nata, zata iya rantse wa da Allah akan cewar duk wani abu nata Aida ta fita sanin sa, haka zaluka wasu abubuwan ma duk Aida ɗin ce ke mata su, haka ko a team ɗin su idan kaji Aida na faɗa to an taɓa Siyam ne. Aida ta ce "To dama waye zai tsaya jiran ki yaji kunya, ai daga yau zuwa sati daya duk na tana di kayan da zaki dinga sakawa, ai ke sai dai a barki da halinki, Malama ki tashi ki shiga wanka ko wankan ma sai na miki ne? Ta faɗa tana sauko da wata akwati mai kama da Zakara. Take ta buɗe shi ta ɗauko wata doguwar riga jaa, mai adon duwatsu sai ɗaukar ido take yi, gefe ɗaya kuma ga taƙalmi da jaka duk irin ruwan riga, ga wata sarƙa mai tafiya da imanin wanda yasan darajar sa, kana ganin kayan kasan a haka suke zuwa a cikin wannan akwatin. Siyam na ganin haka ta shige toilet ta faɗa wanka tana tuno yadda suka yi da yaya Bala ɗazu. Koda ta fito ta tarar da matar da take musu kwalliya tana jiranta, ai kuwa nan aka fara mata, tana gamawa ta saka kayan sannan Aida tai musu hotuna, nan take suka dora a Fage ɗin su. Sai da suka gama sannan suka fita izuwa gurin aikin su. Ita dai Siyama duk rabin hankalin ta na ga asibiti, ga shi bata sani ba ko anyi jana izar anty Zainab ko sai yaya Bala ya tashi, ko dai ɗazu da ƙanin babansu ya tafi aka je akayi, sai take ganin kamar bai dace ta bar gida yanzu ba, amma wata zuciyar take sanar da ita cewar ai yanzu zata dawo. A haka suka ƙaraso Team ɗin nasu....📝
(Muna tare daku kuwa masoya? Kuzo mubi Siyama a hankali muga ina take son zuwa)
Love all
One love
Comments
And shering
Love my fan's
By S-Reza write ✍️
[7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
_By S-Reza ✍️_
*FCW*
*My WhatsApp channel*
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*PAGE 4️⃣*
Shiru Siyama tayi a cikin motar tana kallon shigar da tayi. A hankali Aida ta ce "Lafiya dai ko?" Siyama ta sauke ajiyar zuciya ta kawar da kai gefe, ita da kanta tasan shigar da tayi sam bai dace da itaba. Ta ce "Lafiya ina ɗan wani tunani ne" Ka she motar Aida tayi ta juyo ta kalleta da kyau kafin ta fara bata baki har dai Siyama ta sauƙo. Duk da hakan wata zuciyar na sanar da ita bata kyauta ba, amma ta danne suka shiga cikin group din da tun daga bakin get zaka fara cikin karo da manyan motoci na Medels ɗin dake gurin da kuma mutanen da aka ce suna san ganin ta.
***
*Yaya Bala*
Cikin tsananin ɓacin ran da ya sarƙe masa zuciya yake tuƙa motar kamar zai tashi sama, Anty Zainab kuwa sai kuka take duk ta rikice da ganin wannan sabon al'amarin. Sosai wata zuciyar tata ke ƙoƙarin ƙin yarda da cewar Siyamarsu ce haka. Shi kuwa Nasiru gaba ɗaya ma shi halin da Yaya Bala ɗin ya shiga ne yafi tashar masa da hankali gashi sai gudu yake yaƙi yayi magana da kowa. Daidai lokacin aka kirasa a waya ai kuwa take ya kai hannu da niyyar ɗauka kuma gashi sun iso kan jakshon, bai ma san sun iso ba hakan yaba wata babbar motar damar hawa kansu, lokaci ɗaya motar ta komatse ta baya, yayin da itama babbar motar ta dungura gefe ɗaya. Lokacin da mutane suka iso gurin Nasiru ne kawai ke motsi, kafin minti biyar har motar agaji ta iso aka kaisu asibiti mafi kusa da gurin. Take likitoci suka tabbatar da mutuwar macen cikin su, sannan suka naimi da a sanar da wani nasu. Cikin ikon Allah kuma waya biyu aka samu ta Yaya Bala da Nasiru, sai dai wayar Nasiru ta fashe hakan yasa aka duba number da ya kira karshe. Number yaran wajan aikin su ne wanda ya kira lokacin da suke tafiyar, koda aka kira aka sanar dasu shine suka zo gurin. Shine suma suka kira number mamar su suka sanar da ita. Koda Umma ta ƙaraso sai ta cika asibitin da kuka, tana kiran sunan yaran nata, sosai ta fita a haiyacinta sai faɗin dama ta hana su zuwa wannan gurin amma suka ce sai sunje yanzu ga abun da ya sake su, sosai take ta zaro magana harma bata san tana yi ba. Sai da likitoci suka tabbatar mata da cewar suna lafiya kafin ta ɗan rage kukan, amma duk da haka bata daina faɗa ba. Ganin halin da take ciki ne yasa likitan bai mata maganar macen da ta mutu ba, sai ma tabbayarta ko zata kira mahaifinsu ko kuma wani Namijin. Jin haka yasa ta bada number Kawu Inuwa wanda aka kirasa shima yazo cikin daren. Nan likitan ya sanar da shi cewar a kwai mace ɗaya a cikin su kuma Allah yayi mata rasuwa. Haka suka je ya ganta sannan ya dawo ya sanarwa da Umma wacce jin haka yasa ta ƙara dawowa da sabon faɗa. "Sai da nace masa kar ya je da ita amma yace yaji ya gani, yanzu dan Allah mai zai cewa iyayenta, wannan wacce irin masifa ce, wannan abun na arna da gaba ɗaya ma saɓon Allah ne, abun da babu wani ɗan musulmi kuma ɗan kirki da ya fito daga gidan mutunci zai bar ƴarsa tayi, shine har kuke ɗaukar iyalai kuje kallo to ga abun da ya jawo muku, ni dai sam ban ji daɗin wannan abun ba, Allah ma dai ya tarwatsa taron mutanen da suka ƙirƙiro wannan kafurcin Allah ya isa ban yafe ba. Sosai Umma take kuka tana face majina, sosai mutuwar Anty Zainab ya taɓa ta, samun sirika irin Zainab a wannan lokacin sai an tona, yarin ya ce mai kawai ci ga na tsuwa, duk da irin faɗan da Umma keda ita amma hakan baisa kana yawan jin kansu ba, gasu a gida ɗaya.
Haka ƙanin Kawu Inuwa ya fita da gawar Anty zaibab ɗin, basu Kaita gida ba sai suka wuce da ita babban masallacin domin tayi kwanan kaso a gurin. Acikin daren aka fara sanar da dangin ta da sauran abokon zama. Tun a daren likitan ya tabbatar da cewar karaya kawai suka samu ɗaya guri biyu ɗaya kuma guri ɗaya, sai kuma ɗan buguwa da suka samu amma ina sha Allah zuwa safiya zasu farka. Yana cikin barci yake mafarkin matarsa na cikin matsanancin hali, lokaci ɗaya ya buɗe ido da sauri yana bin gurin da aka kwantar da shi da kallo, ganin Umma da Kawu Inuwa ne yasa shi tambayar ina matarsa. Tun da yaga sun fara ce masa ya kwantar da hankalin da ya tabbatar da cewar ba lafiya ba, yana ƙoƙarin rufe ido ya haɗa ido da Siyama, wacce take zaune ta kusa da hannun sa mai karayar. Kallon ta yayi yaga komai na dawo masa. Haka dai bai ƙara cewa komai ba har suka ci abincin da aka kawo musu, sannan barci ya ƙara ɗauke sa bayan an masa allura. Lokacin da ya ƙara buɗe ido sai ya sauƙe a kanta ita kaɗai zaune a ɗakin tana kallon waya tana dariya. Sosai ya dade yana kallonta yana ƙoƙarin haɗa fuskar wannan ta gaban nasa da kuma wacce yaji jiya ana kira da Siyam Olosha. Sosai ya tabbatar da basu da wani banbanci sai dai wannan da take zaune a gaban sa yanzu hijabi ne a jikin ta waccer kuwa marabanta da tsirara babu nisa. A hankali yake lumshe ido yana budewa yana tunanin Allah yasa matarsa lafiya take. Yana cikin haka likitan ya shigo hakan yasa ya lumshe ido kamar mai barci. Yana ji likitan yana mata magana amma bata ji ba. Har sai da ya sanar da ita Nasiru ya tashi kuma abinci zasu ci kafin anjima. Likitan na fita ta shima ya sake buɗe ido.Yana farkawa itama tana satar kallonsa, ganin yana kallonta ne yasa ta fara masa sannu tana tambayar ina ke masa ciwo. Shi kuwa wani irin haushin ta da yake jine yasa ya juya mata baya yana ɗaga mata hannu yana kawar da kai gefe, sai yaga ta fashe da kuka tana wa Nasiru magana sai kuma yaji tabar dakin da gudu.
Bangaren su kawo Inuwa kuwa washegari aka shirya gawar Anty Zainab ƴan uwanta sukai mata addu'a harda Umma da itama ta zauna a gurin, nan dai ƴan uwanta su kai mata rakiya izuwa gidan ta na gaskiya. Lokacin da Kawu Inuwa ke sanar masa da rasuwar matar tasa sai kawai ya saki murmushi haɗi da hawaye duk lokaci ɗaya, dama ya ji a jikinsa hakan yasa ya kasa yin wani yunguri, amma zuciyarsa wani irin zafi take masa ga shi abun takaici har yanzu babu wanda ya gano cewar Siyama tun da ta fita bata dawo ba. Shi yanzu abun da yafi basa tsoro ma itace Umma, yanzu tana sanin wannan abun shi zata baiwa laifi. Lokaci ɗaya Yaya Bala ya fashe da wani irin kuka wanda yasa Nasiru ma da ke kusa da shi fashewa da kuka. Sosai yaya Bala ke kukan rashin matarsa abar son sa wacce take zaɓar farin cikin sa fiye da nata. Wata zuciyar kuma na nuno masa Siyam a filin taron sarauniyar kyau ta ƙasa! Sosai yake jin ya muzan ta, ya gama zama babban banza kuma ƙaton daƙiƙen da ƙaramar yarinya ta mayar kwandon shara, hannunsa ya kalla ya gani a ɗaure ya cici yatsa. Sosai su kawo Inuwa suke bashi haƙuri har dai ya samu ya ɗan daina kukan. Likita na shigowa Yaya Bala ya ce a sallame shi ya warke, likitan yace yayi hakuri zuwa gobe, amma yaya Bala ya daka masa wata tsawar da tasa likitan rikicewa. Ya ce "Ok ok ok kwantar da hankalinka bari yanzu nasa a rubuta maku takardar sallama. Suna zaune Yaya Bala ya dafe kai, Nasiru kuma ya shiga Toilet yana uzuri sai ga likitan tare da wata noss a bayan sa. Yana zuwa ya miƙawa kawo Inuwa takardar shedar biyan kuɗin su da kuma magunguna da aka sayo musu sai kuma ta sallama. Kawu Inuwa ya amsa yana tambayar na maye? Likitan ya masa ƙarin bayani. Haka dai ba tare da sun fahimci komai ba suka tattara izuwa gida bayan kawo Inuwa ya tare musu mai ɗan sahu.
Yaya Bala yace a saukesa a ƙofar gidan su Zainab kasancewar babu nisa da gidansu. Babu yadda kawo Inuwa bai yi da shi ba amma ina haka ya sauƙa hannu a saƙale bai ko bi ta kan mutanen da ke ƙofar gidan ba ya shige cikin gidan. Koda ya shiga ya tarar da mutane da yawa a ciki hakan yasa ya fara gaisuwa yana hawaye, yana zuwa gurin mahaifiyar Zainab kuwa ya fashe da kuka kamar mace, sosai yake kuka har ya dawo da sabon kuka a gidan. Ƙanwar ta mai suna Zilai da dama tun tuni basa shiri da Yaya Bala domin yarinyar irin marasa kunyar nan ce, shi kuma yaya Bala baya son raini gashi da saurin kai hannu yasa basa shiri da ita, domin kuwa ya sha kwaɗe ta idan tayi rashin kunya a gaban sa. Zilai ta fashe da kuka tana faɗin "Wayyoo Anty Zainab ta tafi ta barmu kun kashe mana ita, to wallahi ba zamu yarda ba, ai ance ba ita kaɗai ce a motar ba amma ita ka dai zata mutu... "Wata ƴar uwarsu ce ta buge mata baki tana harararta. Ohoo shi baima san tana