Showing 12001 words to 15000 words out of 41935 words
yi ba.
jin abun yaƙi ƙarewa ne yasa baban su Zainab ɗin shigowa cikin gidan ya fita da Yaya Bala. Ganin halin da Bala ɗin ke ciki ne yasa Alhaji Sani wato baban su Zainab fara basa baki hardar yaci nasarar shigar da shi ɗan sahun suka tafi. Koda suka isa gida Umma ce sai matar kawo Inuwa suna kiranta da Mama da matar Husaini suna ce mata Momy, sai wasu daga cikin ƴan uwa. Koda Umma ta gansu tayi mamaki domin ta yi zaton sai gobe ko jibi zasu dawo. Basu jima da dawowa ba sai mutanen gurin aikin su yaya Bala ɗin nan sun yo Mota guda sun zo gidan. Yana aiki da wani karamin kamfani ne irin masu shirya guraren taro ko wani gida idan anyi ko dai filen gabatar da wani taron a nan cikin garin Abuja. Kasancewar aikin ba kullum ake samu bane yasa wani lokaci sukan shiga halin babu, godiyar Allah ma da yasa gidan da suke ciki nasa ne ba na haya ba, domin aikin nasu babu laifi idan aiki ya samu ana samu hakan yasa lokacin da yaji kuɗi a hannunsa sai ya sayi wannan suka dawo wanda suke ciki muka ya saka ƴan haya. Duk da gidan ƙarami ne amma Alhamdu lillah ya ishe su bata tare da takura ba. Bangare biyu ne gidan daya wanda Umma ke ciki, ɗakuna biyu ne sai Toilet daya a gefen ɗakunan babu kicin agurin. Bangaren da suke ciki kuma a kwai ɗakuna hudu da kicin sai kuma kowani ɗakuna guda uku a kwai Toilet a ciki. Ɗaki daya na Nasiru sai ɗaya na Siyama da Fati, biyun kuma shida matarsa, sai kicin guda ɗaya. Idan sun yi baƙi sai su turasu bangaren Umma, haka suke rayuwarsu babu hangen Dala.
Ganin haka yasa Umma sa Fati ta shiga kicin tayi girki sabo da baƙin, hakan yasa ƴar gidan matar kawo Hassan mai suna Binta tashi ta raka ta suka fara girkin.Baƙin basu jima ba suka tashi suka tafi bayan sun bar masa abu dubiya da suka ruƙo masa. Bayan sauran sun fita ne ɗaya daga ciki ya dawo da alamar dai a bokiksa ne yazo ya fara masa tambayar da yasan sai ya gaji da amsawa. "Wai da gaske ne yarinyar da tazo ta biyu a gasar jiya ƙanwar ka ce? Yaya Bala ya ce "Eh" mutumin yace "Sunanta fa wai Siyam Olosha? Yaya Bala da ya gama kaiwa iya wuya ya ce "Eh itace " ya faɗa da ƙarfi har sai da hankalin su Umma ya dawo gare su. Shi kuwa mutumin yayi sum-sum ya bar palon. Umma kuwa da tun da suka shigo take son taji ko dai Siyama taje gidan su Anty zaibab ɗin ne ganin bata gansu tare ba ta ce "Lafiya dai kake ihu ga mutumin da yazo duba ka? Yaya Bala ya tashi ya shige cikin ɗakin yana jin hawaye na son zubo masa. Umma ta dawo da kallonta ga Nasiru da shima hannunsa ke maƙale da ƙafaɗa ta ce "Wai ina kuka baro Siyama ɗin ne, ko dai ta tsaya gidan su Zainab ne? Nasiru ya kalli Umma da yasan wallahi babu ruwan ta da wannan ciwon tana jin abun da ya faru shi kenan hankalin kowa ya tashi kenan. Ya ce "Eh tana gidan sai an jima zata dawo koma ta kwana a gurin" Umma ta ce "To ai ta kyauta dama haka ya kamata ace wani yaje gidan nasu. Nasiru ganin haka shima ya miƙe da gyar ya shige ɗaki ya bar palon.
Suna cikin Girkin Binta ta ce da Fati "Wai ina Anty Siyama ne naga ban ganta a gida ba? Fati ta ce "To mun barta a asibiti dai ban sani ba ko kayan ta tsaya kwasuwa. Binta ta ce "Alasarki Anty Zainab wallahi ko ni da ba gidan nan a zaune ba nayi kewar matar tana da kirki sosai ga son mutane. Fati da har ruwan hawaye ya fara taruwa mata ta ce "Da yanzu da ni za'a tafi, Umma tazo tayi faɗa akan baza'a je dani ba, har fa na ke ta kuka ashe dai Allah ya tsara komai ne. Binta ta ce "Alasarki Kinga amfanin bin maganar iyaye ko, yanzu da kin ƙi yarda kin bisu, Kinga ko baki mutu ba ai zaki sha wahala" Fati ta share hawaye ta ce "Ana ganin kamar Umma tana da faɗa har ake ganin hakan yasa bata sakewa sosai da yaran ta, kuma abun da take yi ɗin shine daidai, ni kam daga yanzu duk abinda Umma ta hana ni wallahi ba zan ƙara yi ba. Suna cikin haka wayar Binta ta hau ƙara tana dagawa ba tare da sallama ba wata ƙawarta ta ce "Ke shegiya shiga Whatsapp ki raba mana wannan gardamar ni nace wannan wannan kozin ɗin taki ce Siyama amma su Laila sun ce ƙarya ne. Binta da bata fahimta ba ta ce "Ban gane ba? Ta ce "ki shiga zaki gani ai muna jiran ki"
Ana faɗa aka kashe wayar. Fati ta ce "Wannan Farida ce ko? Binta ta amsa da "Yaya kika gane" t
Ta faɗa tana buɗe datar ta. Fati ta ce "Wannan saurin zagin nata mana, wallahi bana son mutum mai saurin zagi, yanzu fa ji wannan wayar da kukayi ta zage ki har sau biyu kamar wata kafura. Binta ta ɗan yi murmushi ta na faɗin ai Farida da zagi kamar jikar maguzawa. Daidai lokacin Binta ta fara kallon video ɗin da ya gama budewa. Ganin wata kamar Siyama yayarta yasa ta jawo Fati tana faɗin ke duba min nan dan Allah kamar fa Anty Siyama ko? Fati ta amsa tana kallo. Lokaci ɗaya Fati ta ce "Wannan ai ba Siyama ba ce" ai kuwa Binta da farin ciki ya gama kamata tayi hanyar waje da gudu da niyyar nuna wa mahaifiyarta, har tana dariya ta ma manta da cewar zaman makoki suke yi. Ai kuwa suna zaune a gurin gaba ɗaya Binta ta shiga palon tana dariya tana cewa "Umma Mommy Mama kuzo kuga Anty Siyamar mu ta zama tauraruwa. Ta faɗa tana dawo musu da kallon baya. Umma da ta ƙaraso gurin tana cewa wacce Siyama kuma. Nan dai suka fara kallo. Tabbas Siyama ce ga rabin nonuwa a waje, ga kai a bude ga wani irin ɗan banzan ɗinkin da ya gama fitar da mazaunan ta. Sosai Umma tayi sumam tsaye daidai lokacin da Farida ta ƙara kiran Binta... 📝
Muje zuwa masoya, kubi komai a hankali har mukai gurin da kowa zai fuskancin hanya. Yanzu dai kowa yasan abun da ya faru, dama Umma ka dai ta rage...
Love all
One love
Comments
And shering
Love my fan's
By S-Reza....✍️
[7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
_By S-Reza_
*FCWS*
_Duk mai son samun cigaban wannan labarin to ya shiga wannan WhatsApp channel ɗin_👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*Page 5️⃣*
Nan take Binta ta ɗaga kiran tana sanar musu cewar Siyama ce acikin vedio ɗin, ai kuwa tana jin Farida ta ƙundumawa Lailai wani ƙatoton zagi jin tayi nasara. Jin haka yasa Binta kashe wayar tana ƙara yiwa su Umm ƙarin bayani ganin sun kasa magana. Ta ce "Wai baku gane ta bane? Ina wannan taron da akayi jiya na sarauniyar kyau, to shine fa Anty Siyama ta shiga kuma tazo ta biyu kun gani?" Ta faɗa tana nuna musu takardar shedar zuwa ta biyun da Siyama ta riƙe ana ɗaukarta hoto. Taci gaba da faɗin "kuma Mommy wallahi shi kenan Siyama ta zama.." Wani tsawa Mommy ta daga mata yasa tayi shiru tana bin fuskokinsu da kallon mamakin irin wannan abun farin cikin sukuma duk sun ɓata rai.
******
*SIYAMA*
Lokacin da suka shiga cikin shagon nasu duk wata ƴar team members ɗin su maza da mata duk sun hallara, dama daga ita sai Aida suka rage. Ai kuwa suna shiga gurin ya ruɗe da ihu barin ma ganin irin shigar da tayi. Sosai members ɗin su ke ƙoƙarin nuna mata farin cikin su, amma duk karr take kallon kowa. Haka ta dinga binsu mazan da matan tana runguma suna wa junansu kiss a gefen kumatunsu. Bayan sun zauna Oga Fita ya fara magana cikin harshen Ingilishi. "Muna sake godiya ga Allah da ya ƙara bamu nasara tun bayan shekara shida da muka taɓa zuwa na uku sai yau gashi mun samu ta biyu a cikin mu, kuma nuna san rai shekara mai zuwa mu samu ta ɗaya. Duk suka yi tafi suna amsawa da amen in sha Allah. Ya cigaba da faɗin "Wannan nasarar ba iya ta Siyam Olosha ba ce, nasara ce ta duk wani members da ke cikin wannan group ɗin mai suna wait house (Farin gida). Kuma ina so na sanar daku cewar yanzu haka sabo da wannan nasar da muka samu mun ƙara samu karrama wa ta musamman, sannan mun samu dama guda uku daga kamfanin Baby and me na yin aki damu a matsayin sabbin Models ɗin su na wannan shekara, kuma sun tabbatar da cewar Siyam itace zata gudanar musu da duk wasu tallukansu na kamfanin su muddin ta yarda, yanzu haka sune ke jiran ta a ofec ɗin tan ɗazu". Ai yana ƙarasa wa suka fara ihu da farin ciki jin abun da suke buri zai tabbata. Aida kuwa kamar ta tashi ta taka rawa tsabar farin ciki, tana son zama Model amma ba irin wannan na ƙaramin kamfani ba, tana so ace irin manyan kasashen duniya su gaiyaceta domin yi musu talla, amma babu laifi idan ta samu wannan ɗin ma Alhamdu Lillah, a hankali watarana zata kai har gurin da take so. Ita kuwa Siyam Olosha farin ciki baki har kunne, dama Oga Fita ya sanar da ita cewar muddin tana son zama Model to wannan hanyar ita ce mafi sauƙi gashi ta yarda tun ba'a je ko ina ba har ta fara zama Model. Adawiya da Badawiya sune suka fara faɗin "Oga Fita amma masu kamfanin babby and me ba wai Siyam Olosha suke so ba, sunce a basu mutum uku ne kawai a cikin members domin ba irin ta suke so a talansu ba. Adawiya da Badawiya sune manya a cikin wannan group ɗin hakan ya Oga Fita baya son rabuwa dasu, domin suɗin sune fitilar wannan taem ɗin, yasan yadda suke nuna ƙiyayyar su akan Siyam, saboda Badawiya ce zata jagoranci team ɗin amma zuwan Siyam da kuma yadda shi Fita ɗin yake ganin zata fi bada abun da ake so ba wai sabo da tafi Badawiya kyau ba, a'a saboda da irin zubin halittar tane yasa ya yarda da ita. Fita ya ce "No ba haka bane, sunce bayan ita a samu mutane uku kuma ke Adawiya ai kina da Contract akan ki, ita kuma Badawiya tace bazata yi aikin Model a ƙananan kamfani ba hakan yasa ban saka sunan ku ba. Na saka Siyama da Nusee sai Sarah da Hafness. Da sauri Siyam ta miƙe jin babu sunan Aida ta ce "Oga Fita banji sunan Aida ba? Oga Fita ya ce "Kamfanin Baby and me kin san basa aiki da baƙin mutum, sunce farare suke so kin ga kuma ita Aida ai bleak biyuti ce, shi ne yasa ban saka da ita ba. Lokaci ɗaya Siyam taji kamar cin fuska ne a kaiwa Aida domin kuwa Aida ai ba baka bace, kuma ma ko bakar ce ai bai dace yace haka ba. Nan take su Adawiya suka fara dariya jin cewar Babu Aida domin sun san abu sai yafi ɓatawa Siyam rai, domin kowa yasan burin Aida kenan zama Model. Haka aka gama taro duk ran Siyam da Aida a ɓace. Sai da tafi komai da ta samu ta saka hannu kafin ta warewa team nasu ita kuma ta tafi gidan Aida da sauran. Kyautar motoci uku, sai kuɗaɗe masu yawa. Sun yi magana da masu kamfanin Baby and me Kuma ta yarda zatai musu aiki amma sai ta shirya tukunna kafin ta saka hannu, domin tana so taje tayi bincike akan irin aikin nasu. Haka suka bar maganar akan zata ne mesu. Koda suka isa gidan Aida sun tara Jamila da jamilu har sun gama abinci sun ci nasu suna kallo. Sannu da dawowa su kai musu suka ci gaba da kallonsu. Ganin Aida bata tada maganar ɗazu bane yasa Siyama faɗin "Ɗazu munyi magana da Fita akan ina so na sanar da iyayena gaskiya dukda cewar lokaci ya ƙure amma ya kamata na nemi yardar su, domin yanzu Kinga zan fara taka wani matsayi da dole ina buƙatar addu'ar iyayena da ƴan uwana, nasan abu ne mai wahala Umma ta yarda nayi sana'ar Model amma idan aka fahimtar da ita zata yarda domin kisan mu Hausawa duk wani abu da bai shafi addini ba gani ake duk mai yin sa ɗan iska ne, so yanzu ina so naji shawarki yanzu na samu damar zama Model, idan sun ce sai na gama karatu ne shima mai sauki ne shekara biyu ya rage min, amma dai na gaji da yin amfani da sunan wani wai Olosha.
Aida taja dogon numfashi, tana haɗeye wani ƙatoton abu a ranta na irin cin mutuncin da a kai mata, wai itace baƙa, sosai ta danne komai kafin ta ce "Kin yi shawara mai kyau, amma gaskiya ina tabbatar miki da cewar babu yadda za'ayi Umma ta yarda kiyi Model, domin yadda suka ɗauki abun ba haka yake ba. Yanzu shawarar da zan baki itace kije gida ki fuskanci komai in sha Allah zasu yarda ni na faɗa miki. Siyama ta ce "Ta sanadiya ta Yaya Bala wanda ya zama kaman Uba a garemu ya rasa matarsa, ya karye a hannu, ga Nasiru ya karya a hannu da ƙafaɗa kuma yana karshen shekara kenan a karatun sa, anny kuwa na kyautawa dangi na. Sosai take kuka tana cigaba da faɗin "Wallahi badan kaina nake wannan abun ba, ina yi ne domin na taimaki su, wannan dama na samu kuma in sha Allah sai nayi amfani da ita. Aida ta ce "Yanzu ni dubeni, badan ina yin wannan sana'ar ba ina zan sa kaina da ƙanne na, da yanzu muna bin gidan ƴan uwa ana cimmana mutunci, a matsayin ki na mace yana da kyau ki kare mutuncin ki, kuma ki tsaya da ƙafafunki babu Maraya sai raggo". Sosai Aida ta danne nata abun ta bawa Siyama goyon baya da kwarin gwiwa. Haka Siyama ta bar komai a gidan Aida sannan ta shirya da niyyar tafiya sai ga kira ya shigo wayar ta. Ganin sunan Ibrahim ne yasa gaban ta faduwa domin har ga Allah ta manta da shi a gaba ɗaya. Nunawa Aida fuskar wayar tayi suka yi dariya kafin ta ɗaga Aida na cigaba da dariya. "Siyama da gaske wai kece ake cewa kin shiga gasar kyau jiya? Ibrahim ya tambaya a dan rikice. Dariya ta ɗanyi ta ce "Baka taya ni murna bane?" Ibrahim da ransa ya gama ɓaci da kishin ganin video ɗin ta da irin wannan kyawun da tayi yasa yake jin kamar zuciyarsa zata soye, yana kishin abun da yake so hakan yasa yaƙi yadda lokacin da aka nuna masa sai yanzu kuma tazo tana masa dariya. Cikin wata iriyar muryar da baisan yana da itaba ita kanta Siyama ɗin a karo na farko kenan da taji shakkar sa ya ce "Siyama bana son hauka ba wasa nake ba, da gaske kece? Siyama da sai da ta ɗauke wayar daga kunnenta tsabar tsoro tana haɗeye yawu, ta kalli Aida da itama ta tsayar da dariyar. Cikin rikicewa ta ce "Kazo gida muyi magana" tana faɗa ta kashe wayar, ai kuwa sai ga wani kira, take ta kashe wayar tana faɗin "Na shiga uku ni Siyama! Aida karfa wannan mutumin ya zama min masifa fa, naga har na fara tsoronsa. Aida ta ce "Ai ni dama na faɗa miki wannan shirin naki daga baya ke zai dama, kika ce wai babu komai shima ai ba zai gane ba, harda cewa wai wawa ne, bashi da wayo, yanzu dai ga shi kina gani tun bai gano komai ba zai fara kawo mana matsala. Siyama ta ce "Karki damu a kwai kudi idan ya gansu ko da yaji dalilin na a kan sa ba zai yi komai ba idan yaji kuɗaɗe. Aida ta ce "Hamm ayi dai mugani idan tusa zata hura huta" Siyama ta amsa da cewar irin tusar ki kam sai dai ta kashe wutar ma". Haka Siyama ta fita ta tare mai ɗan sahu ta shiga izuwa anguwarsu, tayi niyyar zuwa asibiti amma tana so ta sauya kayan jikinta, sai ta biya ta gidan su Anty Zainab da ake makoki. Tana sauƙa taga mutanen unguwa kowa na kallonta, hakan sai yanzu ta kalli jikinta taga babu hijjab, da sauri ta shige cikin gida, tana shiga ta tarar da Ibrahim zaune ya dafe haɓa alamar tagumi yana kallon waje. Ai kuwa yana ganinta ya taso yayo kanta kamar wani zaki, sosai Siyama ta tsorata har ga Allah Ibrahim ya sauya sosai. Yana zuwa kusa da ita kallo ɗaya taiwa idanunsa taga sun yi jaa, ai kuwa ta kawar da kai gefe tana jin kamar ya cika gidan nasu. Ya ce "Da gaske kece wannan Siyama? Ya faɗa yana kallon kayan jikinta.
Takurewa tayi a guri ɗaya tsabar wani irin tsoro da ya shigeta, sosai ta matse a guri guda tana jiran sauƙar mari ko kuma taji anyi kutuball da ita, jin shiru ne yasa ta ɗaga kai ta kallesa ya tsaya a gaban ta sai sakin huci yake yi. Lokaci ɗaya ta tuna da cewar Ibrahim ne fa, wanda ta mayar kwandon shara, wannan talakan da ta fake da shi take cika muradanta, sannan yanzu fa ita Siyam ce ba Siyama, zata iya sa a kulle duk danginsa ma ba shi ba, kuma ai yanzu ya gama mata duk wani amfani, lokaci ɗaya taji wani