Showing 24001 words to 27000 words out of 31162 words
Chapter 9 - Matar Police Book Complete document .txt
ganta ai suma zan, na yarda za mu koma Amman fa kama Mamanku magana in ta kara tabamin 'ya Wallahi sai taga baje kolin iskanci agidannan, in mu ka fita ba ma zamu koma kauyen ba duniya zamu shiga."
KHALEEL ya ce, "Ba ma za ayi hakan ba insha Allah."
Mika hannu ya yi zai karbi daurin kayan, Hajiya Iyah ta ce, "O'o bar ni inshiga da kayana."
Jan Jidda tai su ka koma ciki, ta na shiga ta ga Hajara zaune ban da danna wayarta ba abin da ta ke Iyah ta kalleta tare gyatsine baki, "To fa wannan mai zubin tabaryar daga ina?"
Jidda ta kyakyalle da dariya su ka shige dakin su .
Mama da Baba suna ta yiwa KHALEEL godiya domin sun San in ba dan KHALEEL ba yau ba Wanda ya isa ya hana Jidda da Iyah barin gidannan.
Murmushi kawai KHALEEL ya yi ya na, "Bara na je na kira Hajara mu tafi nasan ta gaji da jirana yanzu."
Suna shiga Mota Hajara ta fara banbamin masifa," in ban da wulakanci ka tafi ka bar ni zaune kamar ka Shanya wake?"
KHALEEL ya ce, "Am So Sorry Madam baki ga case din da ya tashi ba ne, yakamata in tsaya in gyara tunda har da ni aka bata."
Hajara ta ce, "ai shisshiginka ya ja ma, to ma wai wannan yarinyar daga ina? Ga shi ma na ga kaman kuna kama duk da dai ban wani tsaya kallonta ba."
KHALEEL ya ce, "Hmm kanwata Autar Mama."
Tsaki Hajara ta yi, "Ka ji da shi dai in ma Matar ka ce."
Dagowa KHALEEL ya yi ya kalleta, "Haba Hajara mai zan yi da kanwata kuma? Kanwar ma Jidda, Allah ya sawake Wallahi kin chuceni ma, ko da wata ce awaje banjin zan Iya kara mi ki kishiya bare wannan yar shilar me nasama ya ci bare ya ba na kasa."
Dariya Hajara ta yi, "Yoo waya sani Abu aduhu Ai sa an laluba akan San na kwarai,hhhhhh ni ko ma zan so ace an baka wannan yar shilar ko na huta."
KHALEEL ya ba ta rai, "Stop it, Sweety ba na son irin wannan wasan kin fi kowa sani tam."
Duk kasancewar KHALEEL ya san wasa Hajara ta ke Amman ran shi ya matukar baci tun da ta dangan ta shi da Jidda kuma ma amatsayin ma ta, tsanar Jidda ne karara ya shiga ran shi, jima ya ke kwata-kwata ba ya son kara ganinta domin ya tsani yarinyar maganar ta ma inda hali bai son akara a inda ya ke.
1wk ltr
Jidda zaune afalo ban da tsalle-tsalle ba abin da ta ke yi, Hamza ne ya shigo da Sallamarsa da gudu ta je ta rungumesa , "Oyo yo Yayana."
Mamaki Hamza ya yi ganin Jidda agidan na su.
"Ah Jidda yaushe Ku ka zo?"cewar Hamza.
Jidda ta ce, " Tab ai mun jima tun kwanaki fa har ma Baba ya sani makaranta, Yawwa Yaya Hamza ka dawo Dan Allah za ka goyani?
Hamza ya rikye baki, "Kin gan ki Yanzu ai kin zama katuwa inna goyaki Mama za ta yi Fada, kin ga ma fa yunwa na ke ji, ya na ji gidan shiru, ina Anty Mariya da Mama?"
Jidda ta ce, "Anty Mariya ta je rabon ankon bikinta kuma ta ki tafiya da ni, Mama da Kaka kuma kowa ya na dakinsa."
Hamza ya ce, "Owk shikenan Yanzu dai bara na Je nai wanka na yi alwala, inna yi sallah ma gaisa."
Hamza na shiga daki Uncle ne ya shigo da sallamarshi, ko kallonsa Jidda ba ta yi ba, domin ta tsani mutum nan haka kawai batare da tasan dalili ba.
Ya ce, "Jidda ina Mariya."
Murguda ma shi baki ta yi, "Ta tafi anguwa nima ban sani ba ma."
Kallonta ya yi kawai ya cizan bakin sa ya wuce daki.
Kwanan KHALEEL wajen bakwai bai leka ko gidan Su Mama ba, sai da ta kirashi awaya ta ji lafiya kan ya yanke shawarar zuwa, Amman azuciyarsa ba abin da ya ke Addu'a illa Allah ya sa kar ya hadu da Jidda domin Dan ita ya kauracewa gidan ko kadan ba ya son ganinta ga yanayinta ya ki ficewa daga idanunsa ko ya yarufe ita kawai ya ke hange.
Ita kuwa Hajara ta sami abin yi, ta na ganin sa zata fara angon Jidda ikon Allah, ma su kitso duk bayan wata guda.
Kamar kullum dai yau ma shigarshi ya yi cikin Kanikinsa na yan sanda, ya yi matukar kyau ban da tashin kamshi ba abin da ya ke.
Hajara ta kalle shi tare da fadin, "Ango agaida Amarya Dan nasan wannan wankan sai Jidda ikon Allah."
Ko kallonta bai yi ba sai tsaki da ya jefar ma ta ya fice.
Driving ya ke ahankali kamar Wanda bai son Zuwa in da za shi bare ma amsar hakane ba son zuwa ya ke ba.
A haka har ya isa dai-dai get din gidan hamdala ya yi azuciyarsa da Allah bai sa ya fara karo da Jidda ba, bude ma sa mai gadi ya yi sannan ya je ya yi parking awajen da aka tadana domin yi.
Fitowar da zai yi ko ba wadda ya fara tozali da ita illa Jidda, tsaye ta yi daga daga da kwakwar manja daga bakinta har hannunta.
Kallonshi ta yi ta na washe baki, ya yi kokari domin kawar da kan shi, a zuciyar sa kuwa ya na fadin, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."
Wucewa ta zo yi gaban shi ta, taka mi shi kafa, zafin zuciya nan ta ke ya wasketa da mari, ita ko Jidda kyankyame shi ta yi, ta shafe shi da manjan da ke hannunta duk uniform din ya baci.
Bai Ankara ba kawai sai ga ni ya yi ta zura aguje ta na mai gwalo kallon jikinsa ya yi kan ya lura da abin da ta mai, shima bin ta ya yi aguje tamkar yaran da ke wasan kasa.
Urs Xayyeesherth
[11/27, 10:25 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°
27November 2020
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝
__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________
_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_
_*LABARI DA RUBUTAWA*_
_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_
AND NOW *MATAR POLICE*
_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*_FREE PAGE 34/35_*
😂 _*Salon fa ya chanja Amman Jidda bazata taba chanja wa, kurumin Ku yanzu aka fara*_🥰🥰
****************
************
******************
Ya na bin bayanta Jidda ta shige dakin Hajiya Iya, tsaki Khalil ya yi, ya kalli jikinsa cike da takaici ya nufi dakin Mama.
Ya na shiga Mama ta ce,"Subhannallah KHALEEL miye ne ajiki uniform din ka na ga kamar manja?"
KHALEEL ya ce, "Hmm yarinyarcen Ma na ina wata bayan ita."
Mama ta ce ,"Jidda ba, na sani za ta aikata fiye da hakan ma, sorry ka je bangaren su Uncle da Hamza ka sa wani kayan, ka kawo uniform din Mariya ta wankema A washing machine Yanzu zai bushe ka samu ka tafi."
"OK to Ashe fa Hamza ya dawo biki, lallai yaron nan ma ba ya son zaman makaranta." Cewar KHALEEL.
Mama tai Murmushi ta na, " kai ma dai kasan Hamza ba zai yarda ayi bikin nan ba shi ba."
KHALEEL ya ce, "Ai kuwa hakane bara na je in cire tun kafin mayun nan su fara addabata da kira."
Bangaren su Hamza ya nufa domin cire uniform din ya na cirewa kuwa ya bai wa Hamza ya kawo ma Mariya shi ko ya zauna ya danna wayarsa.
Jidda ce ta fito daga Dakin su domin zuwa wajen yayanta tafiya ta ke ta na mita , "Ni wallahi sai ka goyani Yau dinnan tin da ka dawo kullum sai dai katamin wayo nikam dai yau bazan yarda ba wallahi sai an goyani."
Da karfin ta ya bude kofar ta Fada dakin tana tsalle tsalle, alamar mutum dai ta hango hakan ya sa ta rufe Ido tare da yin tsalle ta Dane bayan KHALEEL. "
Abin ya matukar ba shi Mamaki ya zata hamza ne ya shigo, ita ko Jidda sai kara kankyameshi take ido rufe ba ta ma San waye ba.
Fisgota ya yi daga bayan shi ya sauketa kasa nan ta ke Jidda ta wangale ido.
Abin da tagani ne ya sa ta suman tsaye, KHALEEL daga shi sai singileta da gajeran wando, kara kallonsa ta yi sama da kasa, hadda murza hannu a ido domin kara tabbatar da cewa ba mafarki ta ke ba, ta ga dai KHALEEL din ne kuma ayadda ta gan shi, nan ta ke ta zura aguje.
Ta bar KHALEEL tsaye ya na mamaki azuciyarsa ya ke aiyanawa, "Anya kuwa yarinyar nan ba yar iska ba ce? To in ba haka ba miye na zuwa ta haye bayana hadda rungumeni?" Chan dai sai ya tuna wani Abu tsaki ya yi, ya na , "Allah ya kyauta." Sannan ya cigaba da danna wayarsa.
Jidda ko na fita ta shige dakin Iyah ta na haki, "Wallahi Dan iskane, ba kaya fa ya zauna adakin, tab Wallahi shima Dan iska ne,nikam dai ba ruwana dama ban gan shi ba."
Iyah ta ce, "ke dalla fadamin waye ne? Wai waye ne?"
Jidda ta ce, "Yaya KHALEEL fa, ina shiga dakin su Yayana na gan shi ba kaya."
Iyah ta yi wani hamshakin tsaki kan ta ce, "Yo daman ke sai yau ki ka sani? Ai daman Dan iska ne, Dan haka ma daga yau kar in kuskura in kara ga ni kina mai dariya ko washe bakin nan, kalan ya je ya iskantamin ke, ni fa ma nagama ganoshi son ki ya ke Wallahi."
Jidda ta ce, "Kambu ni dai Wallahi ba na son miji me tusa, tab me zan yi dashi ma, kullum ya na cika min daki da wari, kuma ya na zama min ba kaya tab ni dai ba ruwana."
Hajiya Iyah ta ce, "Ai ko ma kina son shi ni kam dai ba na so , wa inda ma suke kisa tab, ai sai ya hada dani da ke ya kashe, gaki ke me Sarar cewa ke MATAR POLICE ce to Yau kin ga ni daman na Fada mi ki duk yan sandan nan fa yan iska ne ah to ni dai ba ruwana."
Jidda ta gwalalo ido, "Ni fa Yanzu na daina son Dan sanda, daman akauyene na ke Fada Dan kar su rainani Amman yanzu kam nadaina ba ruwana da mai tusa Wallahi."
Hajiya Iyah ta tabe baki, "Ohon ma ki dai, ki na ganin shi ya na zare ido sonki ne ni naga alama, azamanin mu na da in saurayi na son budurwa za ki gan sa kullum idon nan azare kamar sabuwar gujjiya."
Jidda ta kyalkyale da dariya, "Tab wayaga mai idon gujjiya ni kam no me no you, aradu, hhhhhh, ba ni ba hi, turanci ma fa na mi ki."
Iya ta ce, "Ni dai kam ba ni waje ki ga, Gobe za mu tafi siyayyen Mariya."
Jidda ta tabe baki, "Nikam dai na tsani wannan Uncle din mijin Anty Mariya Wallahi, ba na so ya aureta mugu ne."
Iyah ta ce, "To ai ita dai ina ta na son sa? Dan haka baki isa ki hana komai ba."
Washe gari da sasaafe su Mama da Hajiya Iyah su ka kintsa domin tafiya siyayyen kayan auren Mariya, har ma da Baba, da ita kan ta Amaryar.
Anzo za atafi kenan Mumy ta zo amotarta, Jidda ta ce itakam ba zata bi su Mama ba, ita Motar mumy za ta bi, haka kuwa aka yi.
Baba ke driving, Hajiya Iyah na gaba, Mama da Mariya kuma abaya.
Motar mumy kuwa daga driver sai Jidda Da mumy abaya.
Tafiya su ke cikin kwanciyar hankali da nishadi, har su ka isa wajen.
Komai Mama ta samo sai ta mikawa Jidda, ita ko sai murna ta ke tana amshewa Mama ta ma manta da cewa siyayyen Mariya akaje Jidda kawai ta ke zakulowa kaya tamkar itace amaryar.
Sai da suka gama siyayya tsaf har sun kusan isa gida, karaf Babbar Mota ta hau kan Motar su Mama.
Ba karamin hatsari akayi awajen ba, nan ta ke, Baba da Hajiya Iyah, Mariya Allah ya dauki ran su, illa Mama da ke da sauran numfashi, duk da kasancewar itama ba asa ran cewa ba za ta rayu ba.
Inalillahi-wa'inna-ilaihir-raji'un kalmar da Mumy ke iya furtawa kenan.
Ganin Gawawwaki akasa kwance nan ta ke Jidda ta sume awajen lamari ya Dada rinchabewa.
Mumy ta rasa inda za ta sa ranta hakan ya sa tai saurin kiran Dady, da KHALEEL awaya.
Da ya ke kasuwar ba nisa gareta ba nan ta ke Daga Dady har ma KHALEEL da yan office din su suka hallarci wajen, Mama aka fara yiwa taimakon gaggawa sannan aka dauketa aka nufi da ita Asibiti, Jidda ma asibitin da aka kai Mama aka kaita, Hajiya Iyah ko da Mariya, da Baba gida aka nufa da su domin yi ma su sutura akai su makwancin su.
Har sai washe garin da aka kai binne su Hajiya Iyah kan Mama ta fara farfadowa, kamar amafarki Jidda ta ji motsin Mama, nan ta ke itama ta farka, Ta na farka wa ta tuna da abin da ya faru nan ta ke kwalla ya faru zubo mata tana fadin, "Iyata, Babana, Antyna,duk sun ta fi Mama, Mama ki ce su dawo Dan Allah, in ba su dawo ba nima mutuwa zan yi in bi su."
Mama ta kalli Jidda tare da rikye ma ta hannu ta ce, "Mamana kin San ina son ki ko?"
Jidda ta daga ma ta kai, "Amman ki dawo min da Iyata da Baba kin ji Mana Dan Allah."
Mama ta yi Murmushi kan ta ce, "Mamana sun tafi kenan ba za su dawo ba, nima zan bi su, ki yafemin kinji, nima na yafe mi ki, ki rage tsokana kinji, ki zama yar kirki jiddana."
Jidda na kuka ta ce, "Dan Allah Mama ke ma kirki tafi ki tsaya, mamana ki tsaya Dan Allah."
Mama ta ce, "Yayanki Hamza da Mummy na nan har ma da Yayanki KHALEEL, ina son ki Jidda."
Kuka kawai Jidda ta ke ta ma rasa abin fadi.
Mama ta fara salati nan da nan Allah ya dauki ranta, dai dai lokacin Da mumy ta shigo kenan.
Kuka kawai daga Mumy har jiddan su ke, sai da Khalil da Hamza su ka zo suka fara rarrashinsu.
Jidda ta fita ahaiyacinta gaba daya har akayi ukun su mama da Baba.
Mumy ce ta dauketa ta dawo da ita gidanta, shi kuwa hamza ma ya koma makaranta.
Uncle kuma ya na nan ya na surkullen da zai yi ganin cewa an ba shi Jidda ya aura domin ya yi alwashin ba zai tashi abanza ba, batare da yaci gadon Alhaji Ibrahim ba.
Jidda ta ma daina magana kwata-kwata arayuwarta sai ciwo da ta ke faman yi ko makaranta ba ta samun damar zuwa , abincin ma da ta ke kururuwar ci ba dama bata ma son ga ni bare ta ci.
Zaune ta ke ta kifa kan ta akan kafafuwanta karaf sai ga sallama sak irin muryan Babanta.
Nan ta ke Jidda ta, tashi taje ta rugumeshi ta na kuka.
Mumy da Dady na fitowa....
Urs Xayyeesherth
[11/28, 11:50 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°
29November 2020
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝
__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________
_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_
_*LABARI DA RUBUTAWA*_
_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_
AND NOW *MATAR POLICE*
_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*_FREE PAGE 36/37_*
****************
************
******************
Suka tarar da Alhaji Adamu ne, Dan Uwan Alhaji Ibrahim da mu kai bayaninsa abaya.
Dady ya ce, "Alhaji kai ne agidan na mu?"
Alhaji Adamu ya washe baki, "Eh Wallahi ni ne, zuwa ya kamani, banji rasuwar ta su ba ai sai jiya cikin dare, hakan ya sani gaggawan zuwa."
Dady ya ce, "Ayya kai ya yi zafi Wallahi, shiyasa ma ni kai na ban sami damar kirinka ba, ga wajen zama nan bismillahi."
Alhaji Adamu ya zauna tare da kakako hawayen gulma, "Allah sarki Jidda, Yanzu saura min ke kadai sai Hamza adangina, ba Hajiyarmu, ba Ibrahim da iyalinsa, wannan lamari ya matukar tadamin hankali."
Dady ya zauna kusa da shi ya na fadin, "haka Allah ya tsara lamarinsa Wanda ba Wanda ya isa ya kauce ma sa, Abu daya yanzu kawai suke bukata daga garemu Addu'a."
Alhaji Adamu na face hancin ya na, "Hakane kam shiyasa na zo in tafi da diyata ko da ta dinga dibemin kewa ta zauna Chan cikin yan uwanta, ina ganin hakan zai fi, shima hamzan zan biya ta makarantarsu in sanar da shi komai ake ciki, daman munyi alkawarin aurawa ya'yanmu Juna, kuma Alhamdulillah ga Jidda nan insha Allah sai mun cikawa Hajiya Iyah burinta, zan tafi da Jidda in aura ma ta yayanta Sulaiman."
Tun da Alhaji Adamu ya fara jawabi ya zo gabar Dauke Jidda nan da nan gaban Momy ya fadi, domin har ga Allah ta San cewa ba abin da Alhaji Adamu ya shirya illa mugunta da son rai.
Dady ya ce, "To Ina ganin ai anzama daya, bai kamata ka raba mu da Jidda ba a yanzu tunda ga Yayar mahaifiyarta, da kuma Yayanta ina ganin ai ba matsala, maganar aure kuma ai kana da iko a kanta ko da ma ba Dan ka bane ka isa ka badata bare danka to Amman aganina Jidda tai yarinta da aure a yanzu kam dai, yakamata ace ka bari ta Dan kara tasowa yanzu fa take cikin shekara ta Tara, to me za aurar, ita ba girman jiki ba, bare ace."
Sai da Alhaji Adamu ya numfasa kan ya ce, "Alhamdulillah naji dadi ka ce inada iko da ita, Dan haka ba fa zan barta ba, sannan ba fa zan bar maganar auren nan ba."
Tsabar takaici Mumy