Showing 6001 words to 9000 words out of 31162 words

Chapter 3 - Matar Police Book Complete document .txt

wanene wannan police din? Ku biyu ni domin sanin wanne Wannan jarumin na Dompol kon🤣




Kadan kenan daga cikin labarin Jiddatu wadda ta adabi karkarar.






_GASKIYA BA NA GANIN SHARHI KO DAI LITTAFIN BA YA MA KU NE?_




_GARABASA GA DUK MAI SON SIYAN *JAMEEL (Nafseen)* da *MATAR POLICE* DUK MAI SON DUKA BIYUN MAIMAKON BIYAN 400 ZAN BAR MA KU 300_




Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°




*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 9/10_*


_*🥳🥳🥳Har Yanzu ba afara wannan somin tabi ne, karku gaji Ku cigaba da bibbiyata domin wannan daban ya ke da wa'inda kuka karanta abaya, salon sa da ban haka ma tsarinsa da ban🥳🥳*_
****************
************
******************


Washe gari..


Jidda da Iya sunyi sallar asuba, nan fa Jidda ta janyo tea plask din da Babanta ya kawo ma su domin ajiyan ruwan zafi sabida Jiddatu, katon kofin da ke gefen plask din ta dauko ta zuba ruwan shayin tam da kofin sannan ta zuga uban sugar, da ta kafa kan ta ajikin kofin sai da ta shanye tas kan ta ce, "Alhamdulillah."
Sannan ta yi wata shegiyar gyatsa.


Wannan ka'idar Jiddatu ne da zaran tayi sallar asuba sai ta sha shayi wani lokacin ma harda dumame, duk ranar da bata sha ba kuwa akwai masifa agidan shiyasa Iya ta ke kokarin tanadar komai do min ta San in Jidda ta birkice ba za ta ga da kyau ba.






Ta shi tayi zata fita.




Iya ta ce, "Oh ni Hauwa kulu, yanzu Dan Allah ke ko komawan barcin nan ma da yan zamani ke yi bazakiyi ba sai kin fita kofar gida kin addabi jama'a."




Murguda baki ta yi, "Ni to ina ruwana barcin Daren ma dai Dan ya zama dole ne da Yasin bazan ba, ni natafi kawai ki min dumamena kan na dawo."
Ta fice abinta ta na tsalle-tsalle.




Iya ta tabe baki, "Allah dai ya shiryamin ke."






Jiddatu na fita ta zauna Adan wani karamin dutse da ke kofar gidan.




Rami ta yi awajen tana carafke.


Chan sai ga masu tafiya gona na fitowa.


Wani tsohone yazo hucewa Dan babur din sa irin na da ya ji, jiki ko a Ido ma ba kadan ba bare kuma kaji irin sautin da ya ke badawa.




Ta shi tayi ta na kyakyalle Dari, "Ah Baba ina kwana?"


Ko kallonta bai ba domin yasan halin Jidda sarai.




Dariya ta cigaba da yi ta ce, "Wuta sallau, wuta , wuta Yasin kaf karkarar nan ba abin hawa kamar na ka, wuta sallau."


Shi dai sauri kawai ya ke ya ga ya bar wajen.




Sai ga wani manomi ya zo wucewa da fatanya.


Jidda ta tashi ta karasa gabanshi tsalle ta yi ta taba, kan shi, ta kyakyalle da dariya, "Tab ji kan ka kamar na agwagwa?"




Tsorota manomin nan ya yi, ya ce, "mi ye akaina? Kar dai wani Abu ne ya zurmamin."




Dakewa Jiddatu ta yi, ta ce, "Eh mana, ai inaga sai na bubbuga ma ka, kan nan in ba haka ba zurmawa zai yi daman gashi ya fara zama irin na agwagwa."




Zama ya yi ya ce, "Dan Allah ki gyara min kai na Wallahi zan baki ko me kike so."




Jiddatu kamar za ta yi dariya ta damke, "To shikenan Amman fa da zafi kuma in kayi kuka nikam zan bar ma haka."


Da sauri ya ce, "Kimin Dan Allah bazan yi ba."




Hannu Jidda ta dunkule ta maka ma sa duka atsakarka, sai dai ya yi guntun kwalla, Amman ya daure, kara maka mishi wani dukan ta yi, sannan ta dibo kasa ta dinga watsa mishi akai harda laka, bai San lokacin da fitsari ya fara fito mi shi ba.




Dariya ta fara ta na to she bakin ta kardai ya gane, ta ce, "To Kawu na gyarama ba sai ka ba da komai ba ka tafi kawai Dan Allah na yi ma."




Ya ce, "to nagode Allah mi ki albarka 'ya ta."




Tafiya ya yi, nan fa Jidda ta fara lekyen kan shi tana kyalkyale dariya, hadda rikye ciki, ,"Wallahi yan kauyen nan ba su da wayo.






Zata shiga gida kenan sai ta hango wani mai rake na tawowa, tsayawa ta yi ta na son sha gashi ba ta da kudi, nan ta ke ta tuna da Ahlam din kuchakar kishiya yadda ta yi wa baba mai rake.




Dariya ta yi ta karasa gareshi ta na, "Mai rake in ba rake mutuwa ta zo ta tafi da kai."


Da bai kulata ba Amman da ya ji maganar mutuwa ya tsaya, "Ta Allah ba ta ki ba insha Allah ba dai yanzu ba."




Jiddatu ta ce, "To Wallahi ka bani raken nan ko in ma ka Addu'ar mutuwa, kasan fa ni da kakata in mu ka yiwa mutum Addu'ar mutuwa, mutuwa ya ke."


Nan fa cikin mai rake ya duri ruwa, da sauri ya ce, "Haba Jiddatu Dan Allah kar Ku min zabin Wanda ki ke so aciki."


Ta karkarewa Jiddatu ta yi ta kwashe manyan ciki guda uku ta ce, "Shikenan Baba nikam ma zan ma ka Addu'ar gadin duniya."




Ya ce, "Aa tab nidai kawai kimin Addu'ar kar in mutu yanzu Amman gadin duniya ai ya fi karfina."


Da dariyar ta ta ce, "shikenan jeka abinka baba kar ka damu."




Washe baki ya yi yaci gaba da tafiya ya na, "Tab Allah ya taimakeni yanzu ba da ban ba ta ba da mutuwa zan yi, tab aradu sai natara kudi na je birni ko da sau dayane, wannan yanzu shikenan za ta min Addu'a kar in mutu Yanzu ai gwanda da ma na biyo tanan daga yau kullum zan biyowa ta hanyar nan ina bata raken ta na min Addu'a."




Ita ko Jidda sai dariya ta ke, "wato dai duk tsofin kauyen nan ba sa son mutuwa, hhhhh ni ko na sami abin yi ai kenan."




Kallon raken hannunta ta yi ta na, "Yau zan sha dadi kuma Yasin ba zan samma iya ba."




Zama tayi ta fara sha sai da ta shanye guda daya kan ta lekya daga zaure ta na, "IYA kin gama ne inshigo? Iye, Iya kin gama nafara jin yunwa fa ni wallahi yunwa na ke ji."




Iya ta ce, "To uwata ai ba ni nace ki zauna awajen ba ko? Gashinan ki zo ki ci ai."




Jidda ta gyara daurin zaninta ta dammare sauran raken ajiki kan ta shiga.


Ta na shiga ta ci karo da malmalar tuwo biyu.


Ihu ta fara ta na tsalle, "Ni Wallahi tuwon nan ya min kadan Iya na fada miki ni yamin kadan me naci bare na bawa 'ya'yan cikina, ko hanjina ma ai bazai samu ko loma ba."


Ta daura hannu aka ta na kurma ihu.


Iya ta ce, "Ke matsalata da Ke wallahi kwata kwata ba ki da hakuri, yanzu ina ga sauran nan na ije mi ki in kin cinye wannan din kya kara."




Washe baki Jidda ta fara ta na, "Yauwa Sowaty Iya ta kin san ma miye sowaty? Sunan da Mama Ke cewa baba ne fa wai Sowaty (sweety) kin ga daga yau nima haka zanna ce mi ki, tin da dai ke kadai ki ke sona."




Zama ta yi ta fara cin abincin sai labari ta ke bawa Iya na abin da ta yi, Iya ko sai dariya ta ke tana jin dadi.






Ta gama ci kenan sai ga Indo da lantana.


Hararsu ta fara ta ce, "Ina yanzu Ku ke zuwa ko? Dan kunga Yau ba boko shine bazaku zo da wuri Ku tayani aikin ba ko? Kai nama daina Hausa daga yau turanci irin na Anty zan na yi, Oyoo You Indo, You Lanta landwon (nildwon),"






Tashi ta yi taje ta dauko bulala .




"As forom tode zan ga who you sa'a is, in gaya ma Ku ni Ina pale (play) da Ku ne?"




Jiki na rawa su Indo su ka yi nildwon.


Iya ta ce, "Haba ke kuwa Jidda ki ma su uzuri daga Nolnol dinnan."




Jidda ta kyakyalle da dariya , "Hhh Iya ke baki iya Abu ba kina cewa za ki yi Landwon ake cewa ba nolnol ba."




Iya ta ce, "Oho ko ma miye dai ki ma su uzuri."




Jidda ta hadda rai, "I rantsuwa You kunci sa'ar Iyatu bor if you kara it agan yasin I wol dagargaza if and if."




Tsayawa ta ma su ta kara da , "Oya sanda of kuma Ku ce min Sorry Madam."




Ta shi sukai jiki ba kwari , "Sorro Madam."




Dariya ta yi, taji dadi yau sai zazzaga turanci ta ke, "Iya Wallahi fa na gama iya turanci Yanzu kam Anty Mariya ba ta isa ta min dariya ba sai dai ma in koya ma ta."






Iya ta ce, "Ai kuwa dai nima nagani su kam ai basu iya komai ba daman sai iyayi."




Jidda ta koma ga Su Indo ysn kan I Bude Eyis dina Afara wanke wanke da sharar gidannan.




Da sauri suka tashi su ka fara, kamar uwarsu ko ince Jidda ma ai tafi iyayensu iko da su.




Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°




*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 13_*




****************
************
******************




Mallam ya'u na magagin barci ya bige wajen kunnen ya na, "Wai kudajen nan ba za su bar mutum ya yi barci ba ne, wannan wani irin bala'i ne?"


Ya gyara juyi sannan ya cigaba da barcin sa.




Su kuwa lantana sun diba karas iyaka son ran su da Jidda ta ga sun gama diba nuni ta ma su da su fara gaba ita kuwa ta kafa kan ta dai dai kunnen mallam ya'u.


Ta ce, "Yau sai muncinyeka, mun dagargaza namanka za mu cin yeeeeee kaaaa."


Murya abankare kamar tsohuwar aljana.


Jin maganar ya ke kamar amafarki chan ya ga dai ba sarki sai Allah sai cunkumarshi Jidda ke yi, gashi ya kasa bude ido ya make awajen.




Jidda ta kara fadin, "Sai muncinyeka Wallahi, Yau sai namanka ya shiga tukunyar kasa."




Azabure Ido rufe mallam ya'u ya zura aguje ya na, "Innalillahi wallahi su suke ganin mu ba mu, mu ke ganin su ba."




Jidda kuwa yadda ta ga yana gudu ban da dariya ba abin da ta ke yi har da rikye ciki.




Tashi ta yi ta nufi wajen su Indo da lantana ta karbe karas din ta na fadin, "Muje gidan Iya sai in ba Ku na Ku, kwa wuce gida."




Haka kuwa akayi Yau anci sa'a ta ba su guda bibbiyu sai washe baki su ke.






Bayan Sati daya an sa bikin Lantana su Indo amare an dage sai shirye-shirye ake.




Ta dage wai zatayiwa Lantana dilka yadda taga anyima wata abirni.


Ka sa ta samu ta kwaso irin lakarnan, da Jan kurkur, sannan lallai, ta kwaba.


Lantana, "ki zo in mi ki abin nan wallahi Dan inna tashi ba yi zan ba."




Da sauri lantana ta fito daga ban daki ta na, "Kiyi hakuri Jidda gani nan."




Kan kace miye yan mata manya da yara ancika agidan Iya ana ganin gyaran jikin yan birni.


Ita kuwa Indo sai gurzawa lantana jiki ta ke tana masifa, "duk anbi an cikawa mutane gida ni Wallahi na tsani irin haka yara kamar ya'yan Aljanu."




Iya ta ce, "Ai ke abun jin dadi ne ma azo kallo kinga nan gaba kya fara na kudi ma."




Jidda ta ce, "Tab ai aradu ko yanzu ma angon lantana sai ya biya ni, ai an hana aikin banza."




Cikin Ikon Allah kuwa a cabe-caben har fuskar lantana ta Dan yi kyau har cikin ma ya Dan yi luwai-luwai, kai kaji ihu agun yan kauye ai sun sami mai gyaran jikin yan birni.


Lantana kuwa sai wani botsewa ta ke tana matsewa, ana gama ma ta akayi wa Indo.


Jidda ta ce, "ni kam ba sai na yi ba, inna ma Ku ma shikenan."


Ana gama wa aka siyo bakin lallai ita da kanta ta Kara caccaba masu kafa da hannu, har ma da sarkan wuya.


Sai da Jidda ta yi kwana biyu ana dangwalawa cikin Lantana da Indo laka da lalle, kuma in za a fita sai ta sa su dauko zani arufa har kai wai Ido kadai za su na lekowa ba ason rana ta ta ba.




Daren Yau sa lallen Ummaru da lantana, Jidda an dage manyan kawayen Amarya sai ummaru ya ba da kudin sa lalle.


Haka kuwa dolen shi sai da ya ba da naira Dari kan Jidda ta bari iyayen ummaru su ka sata lalle.




Adaren ranar Lantana da indo agidan su Jidda su ka kwana.




Washe gari tun asuba Jidda ta sa Lantana da indo wanka aka dandasawa lantana kwalliyar yan birni mai kama da aljanu, ita kuwa kwaskwarimarta ta fama ta yi sannan ta dauko kayanta mai kyau ta sa ko kwalliyar ba tai ba ta ce, "yan kauyen nan da raini nasan ina kwalliya afuska za su fara jeruwa da warin hammatarsu wai suna sona, gwanda ma na zauna haka ko na tsira, Dompol dinnan ma kadai ya isa ya razana su."


Ta kyalyale da dariya kan ta tashi ta na" yauwa lantana ki ga ni fa yadda za ki na tafiya daga yau irin na manyan Mata, daura hannu za ki yi akwankwason ki kina tafiya kamar taliyar yan birni, kinga indai ki na mishi haka to fa ba zai kara aure ba, nima ranar da mukaje birnine naga ana fada a Talabijin."




Lantana ta ji maganar rashin karo kishiya tuni ta ta shi ta na kwaikwayon Jidda.




Kiransu akazo yi kan cewa angwaye sun dawo daga daurin Auren.


Wani mayafi Jidda ta dauko Wanda babanta ya aiko ma ta da shi ta lullube Lantana.




Suna fita antaro ana kallon Amarya mai irin adon yan birni.




Shi dai Adamu abokin ummaru hankalinshi na kan Jidda ita kawai ya ke kallo.


Ta na sane da shi suna hada ido za ta galla mishi harara tuni ya ke kawar da kan shi kasa.




Jiddatu ta ce,"Ummaru Amman zaka bar mu MU cigaba da zuwa makaranta da lantana ko? Kasan dai saura shekara daya mu gama."




Ummaru ya San halin Jidda sarai hakan ya sa shi saurin amsawa da Eh.




Yamma ta yi amfara zuwa daukan Amarya Jiddatu ta rankwashi kan Lantana "wawiya kin ki kiyi kuka ko? Ai ace mi ki Mara kunya ko kukan ya ki zuwa ki kakalo na karya."


Haka ba yadda lantana ta iya ta fara kukan karya ta na ihu.




Sunje har an wuce gidan ba a sani ba, tuni lantana ta cire ido amayafi ta na fadin, "An wuce gidan fa gashi cen wance da ke da dakalin ne."




🤣🤣🤣amaren zamani.




_*Karku manta fa har yanzu ba mu shiga birni ba🥳🥳🥳karku bari shiga birni ya kubuce ma ku, maza Ku hanzarta domin fara biyan 200 din Ku kacal*_




Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°




*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 11/12_*




****************
************
******************


Sai da suka kammala gyaran gidannan tsaf kan Jidda ta bari su ka je gida domin cin abincin rana tare da shirin islamiya.




Ko da suka dawo tana nan ta na gilu-gilu lokacin Islamiya har ya fara kurewa, ga shi suna jin tsoron mugun malaminsu, ba abin su yi magana ba Jidda ta hau su da bala'i, kwaskwarima ta fara yi sannan ta dauko kayan kwalliyarta, "Ku zo nan kuna YI da kan Ku duk abin da na YI kuma Ku yi."




Da sauri kuwa Su Indo da lantana ansami garabasar kayan kwalliyi akafara, tuni ma sun manta da maganar sun makara.




Jidda na gamawa ta kalli Indo tare da dafka wani hamshakin tsaki ta ce, "Dilla chan Ke ba a kan gira ake sa kallin ba saman gashin ne wawiya kawai."


Karfa ta yi ta kara chaba mata girar da eye-shadow .


"Woo kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa kamar yau aurenki, aradu in anzo bikin ki za aga tsiya a kauyen nan."


Karasa maganar ta yi cikin dare ta ce, "Ku tashi muje kan wannan masifaffen malamin ya fara."






Tafiyarsu su Ke su na ta dariya duk Wanda ya kalli Jidda su ka hada Ido sai ta galla ma sa harara tare da murguda baki.






Suna isa makaranta Malam ya yi suman tsaye ya ce, "lallai ma wato yau ba iyaka makaran Ku ka tsaya ba hadda kwalliyar Aljanu?"




Jidda ta fara murguda baki, "Ni dai Wallahi ban yi kwalliyar Aljanu ba Ehee, ni nasan ma haushi ka Ke ji matarka ba ta iya ba."




Mallam ya ce, "Ni kike maiwa da martani ko? Zan nuna mi ki ba ta iya ba kuwa, daga Ke yar yan korar na ki sai na yi maganinku yau."




Jidda ta ce, "Tab ni Wallahi an hana dukana kuma in ka dakeni za ka gani."




A fusace Malam ya dauko dorina domin ba Yau Jidda ta saba yi mi shi rashin kunya ba, ya na kyalletane sabida karatun ta.




Dukan su ya farayi suna kuka, mussaman Jidda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login