Showing 15001 words to 18000 words out of 31162 words

Chapter 6 - Matar Police Book Complete document .txt

kuma kin San za ayi Fada."




Lantana ta ce, "umm Shikenan to Yanzu ina za mu je?"




Jidda ta ce, "Yauwa muje gonar Malam bala mai kan tabarya hhhhhh wayyo Wallahi goshin mutumin nan dariya ya ke ba ni."




Indo ta kyalyale da dariya, "Ai Wallahi ni goshin sa ma kadai na ke son ja fa."




Lantana ta ce, "Ai ko mu rufawa kan mu asiri Dan naji Ummaru na cewa ciwon hauka ya kama Malam balan fa in akaje gonarshi bugu ya ke."




Jidda ta ce, "Ku ji ma fa sallah ake kira in ban koma gida Yanzu ba Baba zai min Fada kin San yazo, gobe da safe kan mu tafi sai kuzo gidan kunji."




Lantana ta ce, "To Shikenan."




Indo ta ce, "to muje in raka kan na wuce gidan."


Su ka tashi sai da Indo ta raka Jidda gida kuwa kan ta tafi, Jidda na shiga gida.




"Mama tun da kika ci abinci fa kike fice agidan nan sai Yanzu." Cewar Alhaji Ibrahim.




Jidda ta shagwabe fuska, "Umm Baba fa na je sallama da Kawaye na ne."




Gudun kar ya takura Iya ta tunzura ya sa shi fadin, "Allah dai kyauta to."




Iya ta ce, "Ameen Uban kanzagi."




Jidda ta ce, "Iya ina shinkafar kince ita zaki dafa da daddare."


Iya ta ce, "Yoo gatanan ki diba na bar mi ki atukunya."




Sai da Jidda ta makare cikin roba kan ta zauna ta cinye tas, Baba kawai tsayawa ya yi kallon ikon Allah ba halin magana, mamaki ya ke da irin ci na Jidda.






****Washe gari da sanyi Safiya Iya ta fara tattara kayan su harda su tukwane.


Baba ya ce, "Iya akwai komai na girki agidan ba sai kin dauka ba."




Harararshi ta yi Tare da fadin, "Ni to zan tafi da nawa ina fadama ba abin da zan bari agidannan gwandama ka ji ehee kalan mu je ana raina mu akan abincin Da Jidda za ta ci? Bar ni na tafi da komai nawa."




Haka Baba ya yi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.




Jidda ma ko ta na nan tana hada tarikicenta.




Sai da suka kwashe komai kaf su ka yi wanka, ganin baba ya sa Jidda yin wanka ba musu.




Sun fito za su tafi Iya ta ce, "Ayya mai gari nasan zai yi kewarmu ka bi da mu ta gunshi mu ma sa sallama."






Mai gari na ganin Jidda da Iya sai da gabanshi ya fadi ya ce, "Hajiya Iya ba dai wani laifin aka ma Ku ba."




Dariya Iya ta yi ta ce, "Aa fa maigari sallama na zo yi ma za mu koma birni da zama."




Wata irin ajiyar zuciya maigari ya yi wadda sai da ta bayyana azahiri.




Ya ce, "Ayya Yanzu dai za Ku tafi ku bar mu kenan Amman da Jidda zaki tafi?"




Iya ta ce, "Eh Wallahi tausayinka kawai na ke na tafiyar nan ta mu shiyasa na zo ma sallama."




Wani irin dadi maigari yaji aranshi fal farinciki azahiri kuwa kukan munafurci ya fara kakalowa, "Ai Wallahi ko ni ne abin tausayi nasan kaf garin nan sai ya yi rashin ki, Allah sarki Hajiya Iyatu kamar in bi Ku Wallahi."


Nan ta ke ma Iya ta fara kuka ta na goge majina da bakin zani ta ce, "Allah sarki Anya ma zan Iya tafiyar nan ko ni kam na fasa tun da dai ka ke kuka."




Da sauri mai gari ya share hawayen tare da Jan majina ya durkusa gabanta tare da fadin, "aa ba za ayi haka ba nikam na hakura Wallahi na yafe mu je ma in rakaku."




Maigari ya kalli ya Fada ya ce, "Maza Ku hanzarto mu raka Hajiya Iyatu."




Haduwa sukayi duka suka nufi hanyar rakiyar Su Jidda, Lantana da Indo sai kuka ake za arabu da Aminiya.




Jidda ko sai washe baki ta ke tana, "Lantana karki damu in kin haihu ai zan zo suna da bikin Indo."




A haka dai har su ka isa Motar sai da maigari ya tabbatar andaina hango motar su Jidda kan ya ce, "Alhamdulillah Nagode wa Allah, Allah raka ta ki gona yanzu ba ni ba jin batun mutuwa."




Jidda da Iya kuwa tunda suka shiga mota ban da barci ba abin da su ke sai da aka kusa isa garin kano su ka farka.


Kamar jira Jidda ta ke asauka ta na fita ta fara tsalle-tsalle ki cibis ta bangaje wani Matashin saurayi.


Ko juyawa ta kalle shi ba tai ba bare ta bashi hakuri.




Hakan ya sa shi saurin shan gabanta tare da kwalla ma ta wani hamshakin mari, ya cigaba da tafiyar shi.


Kuka ta fara ta na, "Allah ya i San min wallahi mugu kawai azzaalumi mai kan tabar...






Urs Xayyeesherth
[11/19, 2:08 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°


16November


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 23/24_*


_*Free pages na daf na karewa wa inda ba su biya ba su hanzarto domin biya tare da samun cigaba akan lokaci*_
****************
************
******************


Tabarya, kuma sai Allah ya sa ka min."


Ta na ta tsine-tsine dawowa ya yi, ya tsaya ya kare ma ta kwallo da kyau jikin shi ya ba shi cewa wannan yar uwar shi ce, duk da kasancewar bai San ta ba kuma bai taba ganinta ba sai yau, tsanarta ya ji kawai ya shiga ranshi nan ta ke domin in akwai Abin da KHALEEL ya tsana bai wuce rashin kunya ba,bayan ya gama kare ma ta kallo, wani hamshakin tsaki ya yi sannan ya ya juya da niyar tafiya.




Ita ko Jidda kan ta akatsa ko kallon fuskarshi ma ba tai ba bare tasan waye har sai da taji takun tafiyarshi na barin wajen kan ta murguda baki tare da dogon tsaki kan ta ce, "Aikin banza duk da ban ga fuskarka Amman zan ganeka da wannan zoben hannun na ka, kuma wallahi sai na rama Marin da ka min, mugu kawai duk gida anbi antara mugaye kawai, kuma duk sai na gyara ma Ku zama."




Iya ce karaso tana fadin, "Jidda wai ina ki ke ne? Daga zuwa naji kin fara un-uni kar dai wani ne ya ta ba min ke?"




Jidda ta ce, "Wani ne fa wai Dan natakashi ba da Sanina ba shine ya mareni, kuma fa ni ban sani ba."




Iya ta ce, "Lallai ma suna so daga yau in fara tsine ma su kenan ko? Gida duk anbi antara azababbu mugaye agida to wallahi ba zata sabu ba."




Mama da Mariya sun fara jin kwaroroton Iya hakan ya sa su saurin fitowa.




Mama ta durkusa , "Ina kwana Hajiya."


Kau da kan ta gefe tai tare da amsawa kamar me shan magani.


Mariya ta ce, "Ah Hajiyar mu an iso kowa sai ya San da zuwanki."




Iya ta ce, "Ba dole ba daga zuwa har an taba min abar so na."




Mama ta ce, "Iya Kiyi hakuri yanzu dai mu shiga ciki."




Iya ta ja Jidda su ka yi gaba fuuu.


Mama ta tsaya ta na fadin, "To Allah ga mu gareka, Allah ne kadai ya San yadda zaman gidannan zai kasance."




Mariya ta ce, "Mama Kiyi hakuri ai anyi mai wuyar tunda suka Yarda su ka dawo komai zai yi dai-dai."




Mama ta ce, "to mu shiga kar wani abun ya biyo baya ni ban San ma waye yadaketa ba tunda dai duk antafi makaranta, Uncle ma ya na kasuwa KHALEEL ne kadai ya fita yanzu." Ta na maganar har su ka shige ciki.






Iya zaune akasan kafet Jidda kuwa ta Dane kan kujera ta na kwance ga kafa duk datti kamar an kwato ta daga filin dambe.




Kawar da kai Mama ta yi kawai daga baya kuma wani tunani ya zo ma ta tace, "Jidda ko gaisuwa ba bu? Ko ba ki ganni ba ne?"




Jidda ta murguda baki tare da fadin, "Ni ai bakyasona ni bazan gaisheki din ba ni ke ba mamana ba ne, Kaka ta fi sona tinda ita bata dukana."




Dan takaici Mama ba ta Iya kara fadin uffan ba, sai zuwa ta dauko abinci da tayi.




Ajiye ma su foodflask din tayi gaban su sannan ta dauko flat da cokali.




Da sauri Jidda ta sauko ta bude flask din ta na ganin abinci jallop din shinkafa ce taji nama da kifi akalla mutane biyu zuwa uku za su ci su koshi.




Jidda ta fara ci tana, "Iya kice fa ta kawo mi ki naki abincin ke ma kin San yunwa na ke ji, wannan ma da kyar ya isheni."




Iya ta ce, "ai kinga irin matsalar da na ke jiye ma na kenan anzo abincin ma ba za a ba mu ishasshe ba sai an mana rowa, maza zainabu in za a Iya atashi adafamin nawa abincin yanzu in kuma da sauran na Ibrahim ki ba ni shi ya nemi wani abincin."




Mama ta ce, "Iya ki kalli abincin da ke cikin flask dinnan fa? Wallahi ko namiji ma da kyar za asamu mai Iya cinye abincin nan bare wannan yarinyar."




Iya ta rikye baki , "Abu yanzu ni ki ke fadawa maganar nan iye? E sabida ke kin saba da yiwa 'ya'ya mugunta ai ba za ki ba su abinci ishasshe ba to ni ba na haka kinga abincin nan? To tas Jidda za ta kare shi kuma atanadan ma ta na anjima ma."




Iya na jin sallamar Alhaji Ibrahim ta fara kukan munafurci, "Zainabu yanzu ni zaki ce ba zaki bawa abinci agidannan ba? Ni za ki hana abincin da 'Dana ya fita ya nemo, ni za ki ciwa zarafi, daman nasan ni ba so na kike ba daman ai da kina da dama da tuni kin illatani."




Mama tsayawa ta yi kawai ta ma rasa abin cewa, Iya sai da ta tabbatar baba ya ji komai kan ya na shigowa ta kara fashewa da kuka.




Tsawa Baba ya yiwa Mama tare da fadin, "Wannan wani irin iskancine? Mahaifiyar tawa za ki bari da yunwa da ace ta ki ce ni zan mata haka ko ko? Ke za ki mata haka? Kin nunamin cewa mahaifiyata ba komai ba CE awajenki ko."




Durkusa wa Mama ta yi ta ce, "Ayi hakuri akasi aka samu, bara na dauko abincin."




Dauko abincin Baba ta yi ta ajiye wa Iya agabanta dagowan da zatayi sai hawaye, Jidda na ganin hawayen nan ta kyakyalle da dariya, "Hhhh Katuwa na kuka."




Da sauri Mama ta bar falon, Mariya ma ta bi sahun bayanta ta na kuka.




Iya ta ce, "Munafukan banza munafukan wofi mu har agaya mana munafurci mu da mu ke namu akasan rafin maliya ma da gangun kifaye, an koyawa 'ya ma munafurci kai wannan lamari dole in gyara ma Ku zama agidannan."




Baba ya ce, "Adai kara hakuri Hajiya ki ci abincin sai ki yi wanka Kiyi sallah."




Iya ta ce, "Sallar dai ko? Ai naga na yi wanka da safe kan mu tawo ko ance ma ni ma agwagwace kamar waccer MATAR ta ka? To bazan ba kuma ba mai sani dole, ba gwanda ni ba ma ina wankan sau daya arana mahaifinka kan ya bar duniya sai ya yi wata bai sa ruwa ajikin shi ba, wani lokacin da dambe zan je in fadawa kakanka ya zo ya taimaka a mishi da girmanshi."




Jidda ta kyalkyale da dariya, "Ashe su kaka dai antaba Kazan ta."




Iya ta ce, 'Sosai ma Yo ai Wannan kadan ma kikaji."




Baba ya San In Iya ta fara zuba ba kakkautawa hakan ya sa shi gaggawan fadin, "To adai yi hakuri, ni bara na shiga masallaci in kun gama in gyara dakin tin jiya kuma nasa ankai kayan da kukazo da su."




Iya ta na sharban loma ta ce, "To to Masha Allah."




Da sauri Baba ya fice afalon ba inda ya fara nufa sai Dakin Mama wadda suna zaune da Mariya ban da kuka ba abin da suke.




Da sallamarshi ya shiga ya ce, "Farincikina, dole ki yi hakuri, ban da wata mafutar da ta wuce wannan, ke kan ki kinsan halin Hajiya tunda ma bare yanzu da tsufa ya kamata, magaifiyata ce dole mu yi hakuri da ita mussaman akan Jidda da ba wanda ta bari ni kai na ma da na ke danta ba ta barni ba, bare ke da kike matata, yi mata biyayya ya zama dole agareni ko da ba na so Indai ba zarce ka'idar musulunci ba ya wajaba akaina, dawo da su gidannan ba karamin jahadi bare Wanda ke da kanki ki ka kara karfafamin gwiwa domin inganta rayuwar 'yar mu, kin ga kuwa hakuri tare da kau da kai akan lamarinsu ya zame ma na dole, mussaman Jidda sai munyi kokarin janta ajiki, Mariya ina so daga yau ko fita za kiyi kunayi tare, kan asan makarantar da za a sata."




Mama ta share hawaye ta na fadin, "Ni lamarin Hajiya ba ya da muna ko kadan wallahi, damuwata Jidda ne da bata daukeni abakin komai ba illa wadda ta tsana abin nan na min zafi wallahi, inda wadda na Ke so aduniya bayan Jidda ne wallahi, ita ce 'ya ta karshe wadda na daura buri na duk a kan ta Amman kaddara ta shiga tsakanin mu ."




Baba ya ce, "Ki daina fadin hakan insha Allah komai zai huce, Yauwa dazu na ga KHALEEL da mu ka iso Allah ya sa dai lafiya ko?"






Mama ta ce, "Hmm to za ace Lafiyar kenan, matsalar dai ta Hajara ce, har yanzu ita fa bata shirya haihuwa ba gashi shi kuma ya kasa hakuri da son 'ya'ya, kuma shi ya na sonta ba zai iya ma ta kishiya ba, na rasa ta inda zan fuskantowa lamarin."




Baba ya ce, "Yanzu irin case din da ake ta fama da su kenan wallahi Allah dai ya kyauta bara na je sallah, kuma kuyi sannan Ku koma falon kar abarsu su kadai."






Urs Xayyeesherth
[11/19, 2:08 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°


18 November


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 25_*




****************
************
******************


Washe gari.




Jidda da Mariya zaune afalo Mariya na chatting, sai ga sallama.


KHALEEL ne ya shiga cikin Uniform din sa na Police Rai abace ya zauna yana, "Mariya ina Mamane?"




Mariya ta dago ta kalle shi tare da fadin, "Ah Yaya Khalil kai ne? Ai ko Yanzu Uncle ya fita, Mama kuma tana dakinta."






Kallon agogon hannunsa ya yi cike da takaici ya ce, "Owk wato ba zai Iya jirana gaba ai ya kyauta bara na je na sami Mama daman ni gun ta na zo."




Jidda ko tana gaban TV kallon Tom and Jerry ban da kyakyala dariya ba abin da ta ke.




Wuce wa Khalil ya zo yi kwatsam ya taka igiyar TV ya dauke.




Tsaki Jidda ta yi tana, "Wannan ai Iskanci ne kawai mutum ya na kallo anzo an kashe, Allah ya isana wajen da aka tsallake ban ga ni ba."


Mariya ta ce, "Ke Jidda miye haka ba ki da kunya ko?"




Murguda mata baki Jidda tai ta ce, "To ni waya ce ya ta ba min kallo na."






Kamar zai yi gaba ya dawo baya ya kare ma ta kallo ya tuna da abin da ya hadu su ajiya tsaki ya yi tare da karasowa gaban ta, bakinta ya riko da hannunsa ya na, "Ke ba ki da kunya ko? Ko dai makauniyace ke? Wawiya kazamiya kawai, ki fita a idona Tin ka saki agaba."


Jidda na kokarin yin kuka ya kara bige bakin ya na, "Ni ban ma San me ya kawo wannan sharar gidannan ba, Mariya anya ko wannan ba yar tsutuwa Mama ta jajibo ma na ba ko?"




Mariya ta kyakyalle da dariya Yaya Khalil adai yi hakuri abar ta haka in ka shiga ka tambayi Mama.




Tsaki ya yi ya sake ta tare da tashi domin tafiya.




Da gudu Jidda ta mikye tana, "An Fada din wallahi Allah ya isan min mugu mai kan mangoro bakin gwanda kawai gatun banza da wofi kuma kai ne kazami ba dai ni ba."




Abin ya matukar bawa KHALEEL haushi tafiya ya yi kawai ba tare da ya waigo ba.




Ya na shiga ya sami Mama ta sa Qur'ani agaba tana karatu.


Sallamarsa ce ta katseta ta amsa tare da kokarin rufewa, "Ah KHALEEL har ka iso anji asibitin an cire ko?"


Cike da takaici Khalil ya ce, "Ina fa Mama ni kam na hakura kawai duk sanda taso ganin 'ya'yan ta je acire."




Mama ta ce, "To shikenan Amman ya naga ranka abace ko wani abun ne kuma?"




KHALEEL ya numfasa kan ya ce, "Wata yarinyace wallahi, wai ma wacece ne yarinyar nan tin jiya fa zan fita ta takeni ni ko na maketa."




Mama ta yi tsaki kan ta ce, "Jidda ce wallahi, ni nasan ba mai aikata wannan lamari sai ita."


Khalil ya ce, " Jidda dai Auta Mama? Kar kice Min itace ta zama Mara kunya haka?"




Mama ta ce, "Hmm ka manta ne kai kafi kowa sanin damuwata bai huce halin da Jidda ke ciki ba, gashi andawo da itan ma ni naga kamar abun karuwa ya ke, Yanzu za ta yi abu ka yi magana Hajiya Iya ta fara tsine ma ka."




KHALEEL ya ce, "Ai ko ni Wallahi Indai zan zo gidannan to sai na gyarama Jidda zama daga ita ma har ita Hajiya Iyan."




Mama ta yi murmushi ta ce, "Khalil ai da ka taba Jidda gwanda ka rufama kan ka asiri ka taba koma waye, yau ka ga Hamza na School, Uncle kuma ba ya zama tunda Alhaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login