Showing 9001 words to 12000 words out of 31162 words
Chapter 4 - Matar Police Book Complete document .txt
ban da kararta ba abinda ake ji, Iya da ke gida ma sai da ta jiyota."
Tuni Iya ta zagaro kafa ko takalmi ba bu bare mayafi.
Jidda kuwa ta kidime"Wayyo mallam zai kasheni shikenan mallam zai kasheni, mallam Wallahi kashi na Ke ji ka barni na je na yi nadawo sai ka cigaba, mallam zan yi agun wallahi gashinan zai fito mallam, mallam zai fito."
Shi ko mallam kaman ana Dada tinzirashi ya cigaba da dukanta.
Yan makaranta kuwa ban da dariya ba abin da su Ke.
Iya ta shigo cikin masifa, "Wai wannan wani irin bala'i da masifa ne yarinya kowa ya na hassada da ita duk kun bi kun tsaneta son ko kowa kin Wanda ya rasa."
Ta fisge Jidda awajen mallam ta cigaba da fadin, "Gani nan sai ka hadamu ka daka ai ko in tsinemaka, in tsinewa kakan kakanka, ban da mugunta irin taka wannan yarinyar nawa ta ke yaushe ta kai duka wannan ko goyo abayama ba ta zarce ba bare amata duka da wannan tsimagiyar, kana nan da hanci kamar fantekar da ta yi wata ba waiwayeta ba, ba ki kamar tuwun dawan da ya shekara, to wallahi ahir din ka da jikata karkasa in maka baki domin gadon mu kambun ba ka."
Shi dai Mallam tunda Iya ta fara magana ya ja bakin shi ya yi tsint tare da saukar da kai kasa domin yasan ba abin mamaki ba ne Iya ta mai tijara cikin dalibansa ya gode ma da abin ya tsaya iyaka masifa ban da mari Dan in taso sai ta rama ma ta.
Cikin shagwaba da gulma Jidda ta ce, "Iya kuma fa na fada mishi kashi nkeji ya bar ni nayi Amman ya ki."
Iya ta dubeshi tare da zungure mi shi kai, "Kai baka kashin ne ko ko ba kasan yadda ya ke matsin mutum ba, nan nan naga kana yaro kullum in ka zo gidana wasa sai kasani aikin kashi ga kashinka da uban wari, yo ai ko ubanka ma lokacin ahe haka ya ke gadone abin."
Ta kyalyale d dariya.
Yara na son yin dariya Amman ba yadda suka iya suka gimtse.
Jiddatu ta ce, "To Iya ki tafi ni nama daina jin kashin ya mana karatun kawai."
Iya ta ce, "Shikenan yar lelena,kai kuma Audu ka ke ko mudi, ahir dinka ko kallon banza ban so akarayiwa Jidda, maza ka ma su karatu jikin lumana kasan ba mu son tashin hankali, Ah to."
Ta fice ta na kanun maganganunta, "Yo in ban da tsiyama har an iya ayi mana kallon banza sai inyiwa mutum baki ya ba ce aradu
, Ni fa tausayin yan kauyen nan ma na ke, kar in tafi komai ta barbare,da tuni na koma birni,Amman su ba sa ganin hakan, Oh ni Baba Kulu."
Iya na tafiya mallam ba yadda ya iya haka ya cigaba da ma su karatu ko hada Ido ya yi da Jidda saurin kawar da kai ya ke yana fadin, "A uzubillahi."
Ita kuwa Jiddatu sai kallon shi ta ke tana kyakyalewa da dariya.
Ana cikin karatu ta katse, "Mallam zan yi kashi."
Kawar da kan shi ya yi daga I donta ya ce, "To jekiyi."
Ta kara da cewa, "Kai baka jin kashin ne?"
Ya ce, "Eh."
Ta ce, "To ai shikenan ni dai zanje na yi kuma in ka na ji kaje ka yi karka ma na tusa a aji."
Yara suka tintsire da dariya sai da ya ma su tuzuren dole kan su ka kumshe dariyar.
Kuwa Jidda fita tayi ta yi wasanta son ranta kan ta dawo ajin.
Mallam Addu'a ya ke kawai lokacin ta shi ya yi ya kadasu gida.
Jidda sai kakale-kakale ta ke daga tace zata sha ruwa, sai ta zatayi fitsari.
Daga karshe dai lokaci bai ma yi ba mallam ya kadasu gida ya ce antashi, Jidda kuwa sai murna daman abin da ta ke so kenan ahanya su lekya gona su diba karas.
Tafiya su ke Jidda ban da tsokanar mutane ba abinda ta ke yi.
Indo ta ce, "Laa Jidda kin ga fa Mallam Ya'un ya na barci dadin ma diban kenan."
Lantana ta ce, "ai kuwa kin ga shikenan ma diba son ran mu."
Jidda ta ce, "Ku Je Ku diba ni zan tsaya anan inna tsokanarshi."
Tsinke ta dauka ta karasa wajen shimfidar mallam ya'u dai-dai kunnenshi ta tura ahankali..........
Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝
__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________
_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_
_*LABARI DA RUBUTAWA*_
_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_
AND NOW *MATAR POLICE*
_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*_FREE PAGE 14/15_*
****************
************
******************
Rankwashi Jiddatu ta kaiwa lantana
Ta ce, "Mara kunya kawai, ni daman so na ke in Dan ba tsofin nan wahala Amman kin wani kofsa wawiya kawai ai sai mu shiga."
Su kuwa tsofin da ya ke sun San halin Jidda sarai kawai shigewa gidan su kai ba tare da sunce kala ba.
Ko zama ba su yi ba ana ajiye Lantana tsoffafin su ka bar indo da Jidda.
Jidda ta ce, "Yauwa ki saurareni in mi ki fada ehee ban da rawar kai, kuma karki Yarda ya rainaki Wallahi, kina sa shi aiki, kamar irin wanki da sharar tsakar gida, kar ki kuskura ki na washe ma sa baki kalan ya rainaki kin San haka mazan su ke fa hmm na fada mi ki nidai, sannan yadda na ga Mamana na yi dare na yi kiyi kwaskwari ma ki chanja kaya, ita dai kam wanka ta ke Amman ni kwaskwarima zannayi Dan wanka zai na kodar min da jiki, ke ma in kinga zaki iya wankan to Shikenan ki na yi,kuma zan zo ma in koya mi ki girkin yan birni, sannan fa in kin gashi karkina zama ba hijabi kin tuna abin da mallam ya ke fada mana amakaranta? Yauwa sai ma me zan ce miki? In him ki dinga irin kwalliyar nan da na koya mi ki kinji."
Ita kuwa Lantana sai bin Jidda da Ido kawai ta ke.
Indo ta ce, "Kin manta baki tuna mata maganar tafiyar nan ba."
Jidda ta ce, "Yauwa wannan tafiyar da na koya mi ki haka fa zaki na mishi kina Dan fari da ido, hhhh haka ake yasin."
Ta ce la na Dada mantawa ma kawo kunnenki kiji Lantana ta kawo kunnenta suna gama magana kawai naga sun birke da dariya.
Angwaye su ka yi sallama da sauri Jidda ta rufewa Lantana fuska da mayafi.
Suna shigo Jidda da indo su ka amsa.
Ummaru ya ce, "Ah Hajiya Jidda Ikon Allah."
Hararshi ta yi ta ce, "Kai dai kaji da shi, sai wani washe baki ka ke ko kunya."
Adamu ya ce, "To mallama Jidda amana Addu'a."
Gyara zama tayi tare da murtuke fuska kamar wa ta babbar ma ta ta ce, "To bismillah da fatiha, ta kammala da fadin Ammen kan ta cigaba, " To Allah ya sanya alkairy, Allah ya sa kar ka mata kishiya, Allah sa kana tayata aiki, Allah rabaku da dambe kamar yadda Innar lantana da babanta ke yi, Allah ba Ku 'ya'ya dozin-dozin."
Amsawa su ke da amin kawai, Jidda ta ce, "To maza asallame mu muyi gaba."
Adam ya ce, "Gashinan awajena in mun fita zan Baku."
Har sun tashi za su fita Jidda ta je dai-dai kunnen lantana ta ce, "Ni dai karki manta aragemin sauran tsire da kifi har ma da lemun kwalbar da asuba za mu zo karfa, sannan kar ki manta da abin da na fada mi ki dazu."
Har sunje bakin kofa ta kara juyowa ,"karki manta fa."
Lantana ta daga ma ta kai.
Su na fita Jidda ta fara Harar Adamu ta na murguda baki , "Ni ka sallame mu kawai mu yi gaba mu na da abin yi fa."
Har da juya mi shi baya.
Ciro dubu daya ya yi ya ce, "to gashinan."
Karba ta yi tana washe baki, "Ah lallai ka ce kai ma Alhaji ne kamar babana to mungode."
Adam ya ce, "Ah tsaya ma na kiji."
Gwalo ta mi shi ta na tafiya tare da fadin, "Sai da Safe Dan samrayi."
Ba ason ran Adam ba haka Jidda ta tafi ta bar shi tsaye awajen.
Jidda ta ce, "Indo ga kudin nan ki tafi dashi kawai da safe in zamu tafi boko kya mana chanji, yauwa karki manta da asuba za mu je cin tsiren Lantana."
Dariya Indo ta yi kan ta ce, "Shikenan ina idar da sallah zan zo yasin."
,,,,,, haka kuwa akayi Jidda na idar da sallah ta sha ruwan shayin ta na fama sai ko ga Indo.
Iya ta ce, "Ina za Ku je haka?"
Jidda ta ce, "Gidan lantana ma na cin tsiren amare kalan mu bari aje a cinye."
Iya ta daura hannu a ka , "Oh ni Ibrahim ya haifo min wadda ta fi ni iya shegeni, ni ko zamanin mu mu kan bari hantsi ya fito kan muje Amman fa Ku da duku-duku haka? Ku bari garin ya Dan washe mana."
Jidda ta murguda baki , "Mu ina ruwan mu walle sai munje in ma ba su tashi sallah ba ma tashesu kin san lantana da shegen barcin tsiya."
Iya ta ce, "Yo ai Shikenan ni dai aragomin tsiren."
Jidda ta ce, "Tab walle cinye kayanmu za mu yi naga ke ma lokacin da Kakana ya ke Raye ai kinci kuma Baki rage min ba."
Iya ta yi shewa, "Lallai ma Jiddatu yo shi kakan na ki ma da bai kawo tsire ba sai kosai."
Jidda ta galla ma ta harara , "andai ji kuma ysin ba zana ragoma ki ba."
Fita suka yi suna zuwa kuwa ko Sallah su lantana da ummaru ba su yi su na ta barci, kwankwaso kofar galan-galan din ne ya farkar da ummaru, azubure ya je ya bude kofar ganin Su Jidda kafe ne ya sa shi suman tsaye.
"Wato ma ko tashi sallar ba kuyi ba yanzu ai kwayi ni matsamin in shige." Cewar Jidda.
Abin ya matukar batawa ummaru rai Amman ba yadda ya iya haka ya nufi massallaci.
Suna shiga Jidda ta fara dukan Lantana, "Dallah ki tashi wawiya ko sallah daga ke har mijin na ki ba Ku yi ba, ni tashi ki ba mu tsiren mu da sauran lemon kwalba."
Ta shi Lanta ta yi ta na mitsika Ido ta daga filon ta ta mikawa Jidda.
Jidda ta sake baki, " kambu Dan wannan za Ku rage ma na."
Lantana ta ce, "Jidda Wallahi wannan din ma da dambe da kwatan ma Ku fa sai ci ya ke ya ma fi ni ci."
Jidda na ci ta na, "Amman lallai wannan Ummaru ya Iya shege sai mun gyara ma sa zama wa to ko kunya ma."
Indo ma naci ta na, "Amman yau za ki shirya mu je boko ko?"
Jidda ta ce, "Ai dolen ta ma Yanzu ki tashi ki yi sallah, in kin gama komai za mu biyo mi ki mutafi bokon."
Lantana ta tashi ta na, "To ni kayan boko na ma na gida."
Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝
__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________
_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_
_*LABARI DA RUBUTAWA*_
_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_
AND NOW *MATAR POLICE*
_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*_FREE PAGE 16/17_*
****************
************
******************
Jidda ta ce,"Ai sai ki tafi dana jikinki kawai."
Sannan ta tashi.
Indo ta ce, "Mu kam mun tafi muje mu shirya, Yau fa in aka tashi za mu zo nan mu yi girki."
Lantana ta ce, "To daman ni ban ma Iya girkin ba kwa koyamin."
Jidda na fita tana fadin, "Ai ko za mu koya mi ki irin na yan birni ma."
Lantana harda tsalle ta na murna za ta koyi girki,irin na yan birni ma.
Kamar yadda Jidda ta ce ko haka akayi Ummaru na shigowa ya ga Lantana na kokawar fita.
"Ah'ah Amarsu ina za kije yanzu ko kin manta cewa amare ba sa fitane bare ma in za su fita sai da izinin mai gida ko?"
Lantana ta tabe baki za ta yi kuka, "Ni Wallahi zan je, ni Wallahi in ba ka barni na je ba, ba ma ruwana da kai, kuma kai ba Angona ba ne, kuma fa in ban je ba su Jiddatu ba za su zo su koyamin girkin yan birni ba."
Ummaru ya ce, "Dan Allah ki yi hakuri kar ki sa a zata wani abin na ke mi ki, yi shiru za ki je, ai ko Dan girkin birni ma na barki ki je, kin ga yau na fadawa su Adamu da Mustapha har ma da Lawandi su zo, su kwashi girkin yan birni."
Lantana ta yi tsalle ta na, "Yauwa Angon lantana, shiyasa na ke son Ka fa."
Ummaru ya ce, "Allah ko?"
Lantana ta ce, "Eh ma na irin Son yan birni ma na ke ma, me ma suke cewa? Kamar Jidda ta koyamin Yauwa, Lilivi lovi yoh."
Ta karasa fada ta na rufe fuska.
Ummaru ya sa hannu a kirji, "Aradu har kin sa na ji kifiyar so da kaunarki ta cekeni a kirji, yanzu to fa ko wanka bakiyi ba ko sai kin dawo ne."
Ta na wani fari da Ido ta ce, "Eh mana."
Ummaru ya ce, "To ai karki tafi da yunwa bara in karbo ma na shayi da burodi mu ci ko."
Lantana ta ce, "Yauwa daman rabona da burodi tin ran Sallah da Jidda ta sammana."
Cikin Murmushi Ummaru ya ce,"yau kam zakici har ma sai ya ginsheki."
Zuwa ya yi, ya siyo ma su, kan kici me lantana har ta kusa cinye biredin.
Ummaru dai ya siyo Abu Amman ya fi karfin shi haka ya yi hakuri har su Ka kammala.
Lantana ta tashi , "To ni natafi Ka gyara gidan Ka yi wanke-wanken ko?"
Ummaru ya ce, "Angama Amarya Amman mu je in fara rakaki ko?"
Lantana ta ce,"To mu je."
Suna fita sun fara tafiya kenan sai ga su Jidda da Indo.
Indo ta ce,"Yauwa sai mu hice makarantar ai daman gidan ki mu Ka nufa."
Ummaru ya ce,"To ai hikenan mu je in Dan taka ma ku. "
Jidda ta galla mi shi harara, "To bayan ma ko rikye ma ta hannu ba kayi ba wannan ai kauyancine."
Ta yo gabansu ta daga hannun Lantana da na Ummaru ta hada ta na, "Yauwa kunga yanzu kowa ya ganku ya San amarene."
Sai da suka isa kofar skul din kan Ummaru ya jiyo da niyar komawa gida.
Da karfi lantana ke magana, "Kar Ka manta da wanke-wanke fa kaji ko."
Ummaru ya ce,"Yanzu ma kuwa Amarya."
Suna shiga ana dukan wa inda suka makara Jidda ta ce, "Lallai Yau in malamin nan ya ta ba ni zai ga masifa."
Indo ta ce, "Allah sarki ita kam lantana Yanzu ba mai dukanta kamar yadda ba a dukan su Sha'awa."
Jidda ta ce,"Mu ma din Wallahi ba Wanda ya isa ya dakemu ai inko ya dakemu aradu yau sai ya cire wannan bujen wandon na shi batare da ya sani ba. "
Suna cikin hakan kuwa Maman buje ya ce, "Ah Amarya Lantana har andawo makaranta ne? To ma za shige aji ki barni da wa'innan shirmammun."
Lantana ta tashi ta shige aji, sai ga Zainab ta zo.
Zainab wata yarinyace sa'ar Jidda Amman kwata-kwata ba sa jituwa da Jidda, mussaman Zainab yadda ta ke nuna ma su gadara ai ita budurwa Malam buje ce, hakan ya sa ta zuwa makaranta a duk lokacin da ta so domin tasan ba dukan letti ake ma ta ba, ita kuwa Jidda kullum abin na tsaya ma ta arai ta dauki alwashin wataran sai ta yi maganin Zainab, Abu daya ke ba ta tsoro tasan ba ta da karfi kar azo ita ba ta daka adaketa.
Kallon Zainab ya tsaya yi yana wayancewa kan ya ce,"Ah'ah Zainabu yau an makara kenan? Ya akayi hakan ya faru Dan nasan ba halinki ba ne."
Marairaicewa Zainab ta yi ta ce, "Wallahi Malam cikina ke ciwo shiyasa Yanzu ma da kyar na tawo."
Daga ma ta gira ya yi kan ya ce, "Ayya sannu to maza huce ki shige aji."
Jidda ta yi kwafa.
Ta na fadi aranta yau insha Allah ko ma miye zai faru sai na yi maganin yarinyar nan.
Murmushi ta yi da ya baiyana afili.
Sannan Malam buje ya fara doka.
A na zuwa kan Jidda ta tsere aguje sai da suka zagaya makarantar nan kaf kan Jidda ta tsaya kan lokacin ma ya gaji, Dan mugunta kuwa sai da ya ma ta bulala daya.
Shige wa aji ta yi ta na ma sa gwalo, "Ai ko ba komai dai wani ya ji ajikin shi, hhh mallam mai buje kawai."
Tunda Jidda ta shiga ban da tunanin abin da za tayiwa Zainab ba abin da ta ke, ai ko sai lokacin Break ya yi, da sauri cikin yatsine Zainab ta ta so za ta huce Gaban Jidda da gangan ta ta ke wa Jidda kafa.
Karaf Jidda ta tashi nan ta ke ta wanke ta da mari, Zainab ta ce, "Kambu ni ki Ka Mara? Ni sa'arkice."
Ganin Jidda ta ga Zainab ba ta da niyar ramawa ya sa ta cigaba da dokanta ta na, "Eh din andake ki din ni sa'arkice da zaki takana ki huce kamar kin taka dutse ko hakuri ba za ki ban ba."
Kamar ta sami jaka dukanta kawai ta ke ta inda ta so.
Zainab kuwa raguwa tuni anfara kuka hawaye da majina ne kadai ke gangarowa daga fuskarta.
Ita ko da taga tana kuka nan ta ke karfi da kwarin gwiwa ya kara zuwa ma ta, tana dukan tana, "Yara sai shegen raini ai daga yau na ga wadda zaki karawa rashin kunya, gwanda ma ki kiyayeni ke kin San karfi na kowa? Ko shi mallam bujen ma kawai ina raga