Showing 18001 words to 21000 words out of 31162 words

Chapter 7 - Matar Police Book Complete document .txt

ya fara tafiye- tafiyen nan wace makaranta ka ke ganin yadace akayi ta duk da tafara a kauye dai Amman yakamata amaidata baya kasan karatun chan da nan ba daya ba ne bare bana jin cewa ma ta na wani kokartawa."




KHALEEL ya ce, "Zan sa aduba ko ta su Ameera ne asata."




Mama ta ce, "yauwa hakan ma ya fi."






KHALEEL ya ce, "Bara na koma office ni kam Dan nasan yanzu za kiji anfara kirana."




Mama Ta yi dariya, "ai kuwa dai kai kam ba ka da hutu in ka bar office kamar komai ya tsaya sai ka dawo sun ta damunka da kira kenan."




Khalil ya ce, "Bari kawai Mama."




Jidda na labe tana jin KHALEEL zai fito ta shiga kicin da sauri ta dibo mangyada.




Dai dai kofar fita ta je ta kwarara mangyadan da ya ke golden ne mutum ba zai lura ba.




Ya fito kenan aka fara kiranshi awaya tsaki ya yi, ya kalli wayar ya ce, "An fara kenan."


Kara sauri ya yi domin fita ya na yiwa Mariya magana, "Ki min magana A WhatsApp ina so mu yi wata magana."




Kan Mariya ta amsa sai ga Khalil tim akasa.




Jidda ta kyalkyale da dariya tare da shige wa ciki.




Ba karamin buguwa KHALEEL ya yi ba domin ya ma kasa motsawa da sauri, Mariya ta kira Mama su ka fito.




Urs Xayyeesherth
[11/19, 3:56 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

19November


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 26/27_*




****************
************
******************






Iya ma da saurinta tana, "Munafukan banza Munafukan wofi to nima sai na ga abin da karewa buzu nadi, e ankira mahaifiya tazo ni kuma ko oho to gani nima."




Ganin KHALEEL dumus akasane ya sa Iya yin shiru.


Mama mika mi shi hannu, ta ce, "Sannu to wai ma mai ya kawo danko wajen nan ne ikon Allah, Mariya ko yau Laure ba tai mopping ba ne?"




Mariya ta ce, "Aa na ga ni tun safe ta yi ma kan ta daura breakfast."




Da kyar KHALEEL ya tashi jiki duk ya yi tsami.




Mama ta ce, "Anya zaka Iya driving din ma ko?"




Ya tsina fuska ya yi ya ce, "Ah zan kokarta insha Allah na ji kaman targade ne ma na yi akafar , zan biya agyara kan na shige gida."




Iya ta ce, "Sannu Dannan kaji, mutan gidan ne sun San salon mugunta kusufa-kusufa sai hakuri."




Mama da Mariya kawai kawar da kai su ka yi.




KHALEEL ya ce, "Ayya Hajiya ai ba komai sauri na ke ma ban sami damar shigowa na gaisheki ba."




Iya ta ce, "Ayya ince kai ne Dan Yayan Zainabu ko?"




KHALEEL ya ce, "Eh ni ne."




Iya ta ce, "Naga kama kam in kaje kace ma Hajiya mun zo gari fa, yakamata ta zo ta gan mu."




KHALEEL na kokarin dingisa domin shiga mota ya ce, "To."




Jidda ce ta fito ta na kyakkya dariya har da rikye ciki ta ce, "shikenan wani ya zama gurgu, hhhh Dan gurgu zo inma jagora."




Cije baki Khalil ya yi tare da kawar da kai cike da jin radadi ya bude kofar motar ya shige.




Mama ta ce, "Jidda ke dai Allah ya shiryaki ni ina shakku ma in ba ke kika zuba mangyada agun nan ba."




Karaf Iya fara surfa bala'i , "Ku jiye min
Iskanci abin har ya kai ga sharri? Yaushe mu kazo gidan da har za ace ta San ta dibo wani mangyada ta zuba ma sa, to ahir din Ku walle ban son takura na fada ma Ku daga ke har yar korar yar ta ki."




Janyo Jidda ta yi tana, "Maza zo mu shige, kinji yar albarka."




Jidda ta bi Iya ta na waigowa tare da yiwa Mama gwalo.




Suna shiga Daki Jidda ta kyakyalle da dariya, Iya ta ce, "Kaniyarki kinji ko ai tunda na ga idonki nasan ke ki ka zuba mi shi mangyada kina ganinsa da Kayan Yan Sanda fa to walle in ya zo tafiya da ke ni ba ruwana ban koya mi ki haka ba tam."




Jidda ta shagwabe baki, "Umm ni fa shine dazu yatabamin kallona kuma ya matsemin baki, gashi ya ce min kazamiya ni kuma bazan Yarda ba ai ni ba kazamiya ba ce."




Iya ta ce, "kyaji dashi dai ni dai in yazo tafiya da ke ba ruwana tunda dai ke baki jin magana."






Jidda ta fita tana, "Ni dai Wallahi duk wanda ya ta ba ni sai na ta ba shi ni ina ruwana da mutane."






*****Sai da KHALEEL ya je aka gyara mi shi targade kan ya nufi gida.




Da sallamarshi ya shiga Hajara na zaune ta na aiki da system din ta, ta amsa da cike da Murmushi.




Da kyar ya karaso sannan ya zauna.


Hajara ta ce, "Soulmate ya na ga kaman da kyar ka ke tafiya Office din fa?"




Numfasa KHALEEL ya yi kan ya ce, "Hmm Wallahi targade na yi agidan Mama."




Hajara ta ce, "Ayya Sorry Sannu ka ji."




"Yauwa Dan Allah ki taimaka min da ruwan zafi mana." Cewar KHALEEL.




Hajara ta bata rai tare ta ce, "Ayya Soulmate aiki fa na ke, bara dai na kira Jummai ta kawo ma."




KHALEEL ya ce, "Haba Hajara Yanzu Dan Allah ki na nufin aikin ki ya fini mahimmanci ne? Ace komai sai dai mai aiki ta min Amman ke kwatata bakya kishina kullum ki fita aiki nima na fita shikenan burinki, kin ma fita aikin bai wadatar ba agidan ma bazaki ajiye kiji Dani ba? Haba Dan Allah."




Tashi ta yi ta na, "Soulmate! Kai kam ai daman kiris ka ke jira ka farawa mutum masifa nikam dai aiki na ke Yanzu, wannan masifar sai tasa na ma manta inda na ke bara na haura sama in turoma Jumman sannu kaji Allah kara sauki, Love you."


Tafiya ta ke tana waka abinta hankali kwance, shi ko KHALEEL ta kai ci ne ya kudumemasa akirji tun abin baya dumunsa har ya fara damunsa domin lamarin Hajara kullum cigaba ya ke daga tace ba za tai wannan ba sai wancen ita dai son duniya da karya kawai ta sa agaba.






Kan mu yi nisa nasan masu karatu za su so sannan wanene KHALEEL.


KHALEEL dai da ne ga Alhaji Muhammad tare da mahaifiyarshi Hajiya Maryam wadda ta kasance Yayace ga Hajiya zainab mahaifiyar Jidda,shine Dan sa na fari Wanda tunda su ka haifeshi Allah bai kara ba su haihuwa ba sai bayan shekara a shirin da su ka sami Yan Biyu Amira da Amir wa inda su ke sa'anni ne ga Jidda.
Asalin Sunan KHALEEL Ibrahim ana masa lakabi da KHALEEL ne domin Sunan mahaifinshi yaci, Tun ya na karami ya ke da sha'awar zama Dan sanda Wanda mahaifinsa ya dauki aniyar cika ma sa burinshi har Allah ya yi kuwa, sai da ya fara aiki kan Allah ya hada shi da Hajara, ya na matukar son ta ita ma ta na son shi har Allah ya sa su ka yi auren soyayya, Amman matsala daya da Hajara kwata-kwata ba ta da lokacin KHALEEL kullum cikin aiki da yawon biki na yan karya yan uwanta, ko daga cokali ba ta yi agidannanta hatta daki sai dai mai aiki ta gyara, girki ma ko ita batama Iya ba bare ta yi, sannan tasa aranta cewa ita sai ta cika shekara biyar da yin aure kan ta haihuwa dan ita ba za ta haihu Yanzu tai saurin tsufa ba, duk irin son yara na Khalil dole Hajara ta sa shi ya ajiye agefe, sannan ta raina danginsa ko biki ko suna Indai ba na danginta ba ko bata zuwa




KHALEEL mata shi ne kyakkyawa son kowa kin Wanda ya rasa ya na kokari wajen ibadarsa, ya tsani rashin kunya da raini arayuwarsa,hakan ya sa ko kannnensa ba ya wasa da su bare wasu, ya na da mutukar zurfin ciki in kika ga furta Abu to ya kai shi makura ne ya rasa hanya, kuma wannan dinma sai dai ya sanar da Mama kadai wadda ta kasance uwar dakinsa, ya shaku da mama fiye da mahaifyarsa domin ita ta raine sa tin yana karami,tare da Uncle Wanda ya kasance yaro ne Dan tsuntuwa da Alhaji Ibrahim ya tsinta ya mai dashi tamkar Dan shi, amman uncle ya sa wata mummunar niya azuciyarshi ba ya ga nin alkairin da aka mai,,, makusar Khalil Daya ya na shaye-shaye tare da bin matan banza , Wanda zan Iya cewa ya na da halaka da Matar shi Hajara domin kulawar da ba ya samu daga gareta.




KHALEEL ya na matukar Son hajara hakan ya sa bai da niyar Karin Aure ko kadan aransa ya gwammace da bin mata tare shaye-shaye, tun ya na gudun matan da kawo mishi hari har ya kasance shi da kan shi ya ke Neman su domin biyawa kan shi bukata.


Kadan kenan daga cikin tarihin KHALEEL.


CIGABAN LABARIN


**************abun ka da namiji har KHALEEL ya ware kwana biyu, Mama ta kirashi domin ya zo ya kai Jidda makaranta.




Tunda Jidda ta ji cewa za a ka ita makaranta ta ke murna Amman da aka mata maganar wanka sai ta fara kuka.




Har Khalil ya zo anata fama da Jidda ta ki yin wanka, fincikarta ya yi kawai ya shige da ita Toilet ya fara ma ta wankan, Ihu ta ke tana, "Wai ana dole ne ni to ka bar ni zanyi da kai na mugu kawai ruwan fa na zafi wayyo Allah Iya na kizo ki kwaceni ZAI kasheni Wallahi."




Ko saurarenta KHALEEL bai ba sai da ya ma ta wanka tsaf sannan ya fito daga toilet din ya na, "In kuma ki ka tsaya wasa Wallahi man ma sai na shafa miki in sa miki kaya, office fa zan tafi kina batamin lokaci ana jirana.....




*_MY GROUP MEMBERS LAST WARNING KO A GYARA KO IN DAINA DAGA YAU AM SERIOUS🤷‍♀️_*
[11/24, 10:58 AM] Xayyeesherth: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

21November 2020


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 28/29_*




****************
************
******************




Hajiya Iyatu ana jin tsoro da kyar aka Iya cewa, "Ayya D'ana adan barta ta shirya da kan ta."




KHALEEL ya ce, "To."




Wata irin shegiyar dafaffiyar doguwar Riga Jidda ta sa, ko hijabi babu sai wani fingilin Dan kwali ta fito ta na, "Na gama."




Wata irin tsawa KHALEEL ya ma ta wadda sai da ta ra zana ya ce, "wannan wani irin kaya ne? Dalla jeki cire kuma ki dauko hijabi ba na son iskanci fa."


Murguda mi shi baki ta tsaya yi, "To ai ni sauran kayan sallah na ne."




KHALEEL ya ce, "Kin san Allah ko ki chanja kayan nan ko na baki mamaki ta ke awajen nan."


Komawa daki ta yi ta na un'uni daga karshe sai ga ta fito cikin wata atamfa mai Dan kyau dai-dai gwarwado, Amman ba hijab.


Cikin fushi KHALEEL ya ce, "Ina hijabin?"




Tebe baki Jidda ta yi, "Ni ban da shi."


Kallon Mariya ya yi ya ce, "Ki ba ta Aron hijabi ta sa Dan bazan tafi da mai sufar slinda tsirara ba."




Da sauri Mariya ta dauko ta na, "Amman fa ya mata yawa nasan har kasa zai kai mata ma."




KHALEEL ya karba ya mi ki mata, "Eh tasa hakan."






Fita sukayi KHALEEL na sauri ya shige wajan driving ita ko ta tsaya chak kallonta ya yi sannan ya ce, "Bazaki shiga ba ne ko sai na mammakeki awajen kazamiyar banza da wofi."




Murguda baki ta yi ta ce, "Ni dai ba kazamiya bace kuma ni ban Iya budewa ba."




Tsaki ya yi yana, "Bagidajiya sai rashin kunya Amman ba abin da aka Iya." Fincikarta ya yi ya bude kofar ya na hankadata kamar mai tura kura.




Zama ta yi tana, "Allah ya isan min wallahi, kuma sai na fadawa Babana, mugu kawai."




Kallonta ya yi sannan ya ce, "In baki min shiru ba wallahi yanzu zan Ciro bindiga in harbeki haba yarinya sai ka ce yar Aljanu."




Tunda Jidda ta yi maganar bindiga ta ta gama razana hadda rikye baki ta kasa motsawa, ji tai cikinta ya fara murdawa, sai tusa bumbubum da karfinta ga bala'in wari.






Tsaki KHALEEL ya yi ya na, "Miye haka wannan wani irin iskanci ne da salon kazanta."




Da ya yi kokarin to she hancinsa da hannunsa ya ga dai abin ba da sauri ya nemi waje domin yin parking ya fice ya na rikye ciki,ba iyaka hanci ba, har cikin cikinsa ya Ke jin warin tusar Jidda da ke kokarin galabaitar da shi.






Ita ko Jidda ban da dariya ba abin da take hadda ya rikye ciki.


Ga KHALEEL da kyankyami duk ya bi ya tsargu ban da yawu ba abin da ya ke zubarwa.




Tunawa Yayi da turaren da ke cikin motar da sauri ya koma ya feshe motar da turaren kan ya shiga ya zauna, "Wallahi in kika Kara min tsinanniyar tusarnan sai na jefarki waje, kazamiya kawai ke bazaki Iya cemin zakiyi tusa ba in tsaya ki fita kawai Dan iskanci sai ki min amot....


Ba karasa ba kawai shima sai ga tusa wadda ta fi ta Jidda ma kara illa banbanci da ita ba tai wari ba.




Kyakyallewa da dariya Jidda ta yi ta na, " Wayyo garde ya yi tusa, hhhhhh kai meyasa baka fita ka yi awajen ba? Ai da ka gwada fita mun gani."




Har cikin ranshi ba karamin kunya ya ji ba, Amman ya daure tare da fadin, "Ki min shiru ko na harbeki Wallahi."


Azuciyarsa ya na mai takaici tare da fadin, "Ni dai na hadu da jangwamgwam ko na yi shiru sai tasan yadda ta yi sani yin magana dole Anya wannan yarinya ba Aljana ba ce in ma ko ba aljana bace to tana da aljanu ajikin Amman zan yi maganinta insha Allah."






Suna isa kofar makarantar da sauri ya bude ma ta kofa ya na, "Maza ni ki yi sauri duk adalilinki na makara wajen aiki."




Jidda ta chuno baki ta na, "Eh dai eh dai na ji dadinta ma ni dai ni karamace Amman kai kato da kai kana tusa."




Tsaki ya yi kawai, ya cigaba da tafiya.


Suna shiga office din da ya ke headmastern ya abokin Khalil ne ya ce, "Ah abokina ai na zata ma ka fasa kawotan ne sai gobe."




Khalil ya girgiza kai"Aa dai gata nan ko play class amaka ta Dan zubin kauyece."




Dariya Umar ya yi, "Lallai abokina ba ka da dama kana ganin katuwar budurwa ka ce asata a ajin wasa, ba ma nan ba, ya naga kaman Ku daya ta ma fi kama da kai fiye da Amir da Amira ko daman yan uku ne?"




Tsaki ya yi, "Aa fa ni ka bar hadani da kwailar nan, yar Mamanace."




Karaf Jidda ta ce, "Ni Wallahi na fishi kyau kaf garin mu ma ansan ni kyakkyawace shi da ya ke tu.........




Mari ta ji ya sauka afuskarta , gudun kar ta mai baram barama ya sa shi saurin marinta domin karshen maganar ba ta huce na tusa ba.




Kuka ta fara ta na, " Mugu azzalumi kawai, ni Allah ya isana."




KHALEEL ya ce, "Iyee rashin kunyarki har anan ma ko lallai zanyi maganin...


Bai karasa ba wayarsa ta fara ringing ya na dagawa ya yi saurin dagawa Umar hannu zan tafi kawai ka yi abin da ya dace.






Ko da Umar ya sa aka ma ta interview ya ji matukar mamaki domin ba yadda ake tsammani ba ne, hakan ya sa shi kai ta ajinsu Amir da Amira kawai primary three.




Ko da ya kai ta bancin su Amira ya ajeta ya na, " To Amira ka kawarki nan kuma yar uwarki."




Da sauri Amira ta ce, "Ke ce Jidda ko? Daman Yaya da Mama sun fadamin za akawoki makarantar mu."




Jidda ta ce, "Eh mana Amman yayankin nan mugu ne fa, ni wallahi na tsaneshi ko yanzu ma sai da ya mareni."




Amira ta ce, "Laa Yaya Khalil din? Ni dai ba ruwana."




Malami na shigowa kowa ya mikye ya gaidasa ban da Jidda da ke zaune hankali kwance.




Lekowa ya yi ya na wace gwanarce zauna ba ta shi ba, cikin harshen turanci.




Wata baiwa Jidda na jin duk abinda za afada ma ta da turanci amsa ce dai ba ta Iya ba dawa ba.




Ta yike tasan da ita ya ke cewa ta yi, "Na me Na Jidda I no go tsayawa walle, sabida in Our gari an ce ba kyau."






Tsabar salo na turancin Jidda daga yan ajin har malamin ban da dariya ba abin da suke, daga karshe ma kawai cewa ya yi kowa ya zauna.


Lokacin yin drowing ne ya yi, shi su ke da a time table hakan ya sa Malam Ahmad yin drawing din kuliya, tare da rubutu a kasa THIS IS A CAT.


Bayan ya gama rubutawa Ya ce, "Wacece ko waye zai karanta min? Jidda ta Riga kowa daga hannu, hakan ya sa Uncle Ahmad zabanta ya ce, " Oya Jidda muna saurarenki."




Da karfin ta cike da karfin gwiwa ta ce, "This is a kuliya, mis mis kuliya."




Ilahirin Ajin ba su San sanda suka tsinci kan su da yin dariya ba, Jidda kuwa tsalle ta yi ta na, "Yeee to atafamin mana, mu fa a garin mu ana tafawa."




Uncle Ahmad cikin dariya ya ce, "Oya clap for her."




Tun daga ranar Uncle Ahmad ya ji Jidda ta shiga ranshi komai ta yi kawai birgeshi ta ke.




Ko da aka tashi driver ne ya zo ya dauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login