Showing 3001 words to 6000 words out of 31162 words

Chapter 2 - Matar Police Book Complete document .txt

koma fada ya hana haki sai zufa fifita kawai ake yi mishi ya na hamdalal Allah ya taimake shi.




Jiddatu da Iya na shiga gida.......




Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°




*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 3/4_*




****************
************
******************


Kan su shiga ciki Jidda ta ce, "Ke tsaya in sauka anan, bari kiga yadda za mu na tafiya, kun San ni dai ban son raini, Dan haka dole muna tafiyar yan matan birni, bari kuga Yadda Mamana a birni ta ke tafiya."


Tafiya Jidda ta farayi tana harde kafa kamar agwagwa sai wani rangwada ta ke tana fari da ido abin ka da mutum kamar tsinke ta na tafiyar kaman za ta fadi,


Ta cigaba da fadin, "muna daga daki ni da Iya muna lekyota in fada mu Ku har wani rangode kai ta ke fa."




Indo ta ce, "Ke kan kinji Dadi Mamanki yar birni, Jidda mu ma yaushe za ki kai mu gidanku na birni."
Jidda ta yi tsaki, "Tab ni ai bazan kara zuwa ba, bayan dukana Mama ta ke ga masifa tab Ni ko bikin Anty Mariya ma ban zuwa duk yan gidan fa masifaffu ne."


Lantana ta ce, "ni kam dama nice ai tuntuni zan koma can da zama."




Jidda ta ce, "Ai sai kuyi ta yi ni nan ya fi min dadi, kunga kuzo mu fara tafiyar nan tin kan na manta."


Su Ku fara shiga kasuwa, wajen wani mai goriba Jidda ta tsaya tana kifta mi shi ido.


Abin ka da Dan karkara anga yan mata mai kwalliyar yan birni tuni ya birkice sai kallonta kawai ya ke.


Ita kuwa Jidda kara wani rankwashewa ta ke tana, "Gaskiya Gorubar nan za ta yi zaki fa, bara in fara dandana Wannan muji."




Daya ta dauka ta fara ci ta ce, "Kai Gaskiya da zaki sosai Indo, lantana kuma ku zo Ku zabi na Ku."


Da sauri su ka karaso su ka dauko daddaya ita ko Jidda ban da Wanda ke hannunta sai da ta kara diban manya guda uku.


Nan fa Mai Goriba hankali shi ya fara dawowa seti ya ce, "To Yan mata kudin fa."




Jidda ta kyakyale da dariya kan ta ce, "Kudi kuma? Ai ka kalli rabonka, tinda ka kwalla min Ido ai ba a banza za ka kalli kwalliyar Dompol kon ba."




Mai goroba ya ce, "Dan Allah Ku ba ni kudin ba nawa ba ne na ajiya ne fa."




Da ido Jidda ta yi ma su Indo magana sannan afili ta ce, "Ku je gun IYA Ku karbomin kudin in bawa Wannan mayyen."


Su ka tafi abin su.
Ita ko ta kara dumbuzan guda biyu ya zama shida kan ta zura aguje, ba abin ya bita ba azo a kwamushe sauran kawai hawaye ya fara ya na, "Allah ya isa Wallahi ni dai ban yafe ba , Wannan yarinya akwai mugunta Allah zai sakamin."




Jidda da su Indo ko na labe ban da dariya ba abinda su ke yi mi shi.


Jidda ta ce, "yauwa Ku zo muyi gaba abin mu saura Addu'Ah Dan na jima ban sha ba wallahi."


Sai ga Umaru na washe baki ya ga masoyiyarsa da kawayenta, da sauri ya karaso garesu shi da abokinsa Adam.




Lantana sai wani fari ake da ido anga masoyi.


Ta na saurin domin karasawa garesu, Jiddatu tai ma ta wata tsaya, "Dalla chan ki tsaya ya karaso wawiya kawai Ki ja ma sa aji mana haka yan matan birni su ke, na alama yau in mu ka koma gida sai na koya mi ki soyayya yadda naji yayata na yi intana waya."




Lantana dai ba da son ranta ba ta tsaya har su Ummaru su ka karaso.




Ummaru ya ce, "Ah Su Jiddatu manya kenan Yau anshigo gari, ." kawar da kai Jidda ta yi ta na, "Eh fa munzo gaisuwa ne."




Lantana ta ce, "Wato shine jiya ka ki zuwa ko?"


Ummaru ya ce, "Haba Lantana kema kin San dai anfara shirye-shiryen bikin mu dole sai na kara dagewa da noma."




Adam ya ja Ummaru gefe, "Kai nikam dai fa ina son Wannan Jiddar nan ta min wallahi gashi yanayin ta na yan birni."




Ummaru ya kama baki, "tab wai Jiddatu ka ke nufi ko Indo? Ai in fada ma kaf kauyen nan ba Wanda ta ke kulawa, Amman gwada sa'ar ka dai."


Su dawo
Adam ya ce, "Jidda Dan Allah ko za mu iya magana?"


Da Murmushinta ta Amsa da Eh suka ja gefe.




Adam na Sosa Kai ya ke fadin, "a Gaskiya kin min matukar kyau tinda nake akarkarar nan ban taba ganin mai kyau kamar ki ba."




Wani irin dadi Jidda ke ji har cikin ranta kara kallon kanta ta ke tana wani fari da Ido harda juyawa irin ya ma kara ganinta da kyau sosai.




Ya cigaba da fadin, "da ya ke kinsan ni natafi birni Neman kudi Yanzu ma maganar auren Ummaru ne yadawo Dani, Dan Allah ko zaki so ni Wallahi ni dai na mutu aso da kaunarka."




Tini ran Jidda ya baci ba abinda ta tsana fiye da mutum ya ce ma ta wai yana sonta, can kuma sai ta kyalkyale da dariya ta ce, "Amman kaban kunya na aza kawai zakata yabon kyau na ne sai ka bige da wai ka na sona? To ahir din ka ni ko mai maigarin garin nan ma bai isa ya ce ya na sona ba bare kai, kagan ni nan ni Jiddatu kyau iya ka kyau to ka kiyayeni da Wannan rashin kunyar ta ka, yara ba ko kunya wai ka na so na?"


Tsalle tai ta Zungure ma sa kai tai ta ce, "Dama wasa kaje kayi ya fi ma danni in yaro ya karamin Zane shi zan wallahi."






Adam kawai tsayawa yayi yana kallonta domin agirme dai yasan ya ba Jidda shekara goma ko fi ma Amman har ta na zungure mi shi kai.




Tsaki tai ganin ya tsaya kallonta ta ce, "Ke Lantana Soyayyar nan ta isa haka anfa zuwa siyan Addu'ahn ma sai wani makon Yanzu yunwa na Ke ji muje gida."




Sallama Lantana ta yiwa Ummaru shi ko Adam ya yi suman tsaye.



A komawa Indo ce ta Goya Jidda har gida suna shiga ta baje," IYA ina tuwona ni wallahi yunwa nakeji in banci ba ina ganin mutuwa zan yi."




Iya ta fito, "Ina kan ki fita ki ka karya Jiddatu malmala uku fa kika cinye, wai Dan Allah ina zaki kai ci ne? Ni naga ta kai na Ke gashi ba kiga ba Amman sai bala'inci."




Harararta Jidda ta fara yi, "Ai dadinta ma Dai Babana Ke kawo abincin nan bare amin gori."




Iya ta ajiye mata tuwon masara miyar kuka malmala daya.




Jidda na gani ta kurma ihu kambu, "Dan Wannan tuwon Wallahi ni ya min kadan ki karamin."


Iya ta ce, "Saura fa malmala biyu ne kadai kuma kinsan yau har rana daman nayi mana."




Jidda kawai ta fashe da kuka ta na rikye ciki, "Wayyo Iya za ta kasheni da yunwa, wayyo cikina shikenan shikenan zan mutu da yunwa."


Kuka ta Ke tana bori tare da suruntai.


Kan kace miye iya ta diri mata tukunyar tuwon gabanta.


Tana gani ta tashi tana share hawaye ta ce, "Indo Ku tafi gida sai na gama cin abinci kwa dawo."




Fita kawai su ka yi domin sun San koda sun zauna Jidda ba sammusu tuwon nan za ta yi ba.




Fara cin tuwon nan tai ba kwakkwotawa kai kace bata taba cin abinci ba cikin dakiku kadan Jidda ta cinye manyan malmalayen tuwo guda uku.




Tana cinyewa ta ce, "IYAtuna Dan Allah ki daura ma na wani abincin kan anjima kin San cikina da jin yunwa."




Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°




*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 7/8_*




****************
************
******************


Su ka tintsire da dariya , "Iya Taji kunji min Fitinanniya wato kina sane da labarin jummala mai Jinnun karya."




Jidda ta ce, "Eh mana ai nikam ma Yau dole ki kara bani labari domin kare kai na ko wataran ma za akara hakan."




Iya ta tabe baki , "Ja'ira kawai ai ina ganinki nasan cewa wannan iya shegenki ne kawai."




Jiddatu ta ce, "umm nikam dai Wallahi yunwa na ke ji Iya."




Iya ta ce, "Aiko ban ko daura sanwa ba na fito kenan aka sanar dani halin da kike ciki."




Nan take Jiddatu ta baje awajen tana bori, "Ni Wallahi yunwa nake ji kuma mutuwa zanyi in banci abincin nan ba, wayyo hanjin cikina suna magana wallahi Iya kinji ko magana suke Wallahi Yunwa nakeji kaman cikin zai fashe hanjin su fito."




Iya ta dafa hannu aka ta na fadin, "ki rufamin asiri Jidda karki mutu wallahi in kika mutu bin ki zan yi ko mahaifinki ban mai son da na ke yi mi ki ba kiyi hakuri kinji ki bawa hanjin cikinki hakuri yanzu zan dafa miki taliyar birni (indomie) ko Leda biyu ai ya isheki ko?" Iyatu na maganar ta na goge guntun hawayenta.




Jiddatu ta gyara zama ta na, "Yauwa sun tsaya ma yanzu ki dafamin ko da Leda uku dai zanyi maneji dashi kin San tsutsar cikin nan nawa da hanjin kwashewa su ke, kuma ki daina kuka bazan mutu ba kinji mutuwa ma tare zamuyi."




Jiki na rawa Iya ta tashi ta na shekan majina ta ji yar lelenta na maganar mutuwa tuni ta dafa ma ta indomie.


Tana gamawa kuwa Jiddatu ta langwabe sai da Iya ta bata abaki.






Da daddare Iyatu zaune da Jiddatu tare da su indo da lantana anzo hirar dare.




Jiddatu ta tintsire da dariya, "Wayyo Allah na Wallahi yau Baku ga maigari ba harda fitsari fa, lokacin da ya cire rawanin shi saura kiri in sa dare sai na wayance da ihu."




Indo ta ce, "Haka Baffa ya zo yana fadawa Inna ai wallahi na so ma ina wajen daman gashi mugu aj gwanda da ki ka mishi hakan ma."




Lantana ta ce, "Hhhh wayaga mai gari na fitsari f
Indon nan ya yi zuru-zuru kamar magarya."




Jiddatu ce ta katse su, "Ai Wallahi da ace ya sa andakeni ko? Daga shi har mai hukuncin sai na rama in nemo wannan abin kaikayin in sa ma su ajiki."




Iyatu ta ce, "Ai ko ba Ku da wayo irin namu na yan da kinga ai ni naso ma ki bari ya Dan tabaki kan daga baya ki tsere kinga daga nan zamu hada ma su damurmurar Dana sani."




Jiddatu ta shekye da dariya, "Kai Amman dai Allah shiryaki Iyatuna Wallahi kin San salon mugunta da ace azamanin fir'auna ki ka zo dole Ku sasanta.".




Iya ta gyatsine fuska kinci gidanku sai dai Wannan masifaffiyar uwartaki Amman ba ni ba."




Jiddatu ta fara hararar Iya, "Ni dai wannan ba Uwata ba ce bayan ma ba ta so na, yauwa Iyatuna kawo kudin tsiren ma nasan yanzu Mallam Audi ya fito."




Iya ta lalubo gefen zaninta ta Ciro wata fatakakkiyar naira Dari ta ce, "Gashinan ki ce mishi acikamin kulli kuma gashasshe mai zafi za abani."




Jiddatu ta tashi tana yauwa Indo da lantana Ku tashi mu je dagan sai Ku huce gida kun ga dare ya yi kar amaku masifa kun San fa ina sonku.




Washe baki su ka yi dukan su adole yau Jiddatu ta ce ta na son su.


Suna zuwa wajen Mallam Audi Jiddatu ta ce, "Mallam Audi abani tsire Amman wai yaji kuli fa inji Iyatuna."




Mallam Audi ya ce, "Ah Yan mata Jiddatu kenan yau kece da wuri haka?"




Murmushin dole Jiddatu ta kakalo ta na, "Amman fa Iya ta ce sai na dandana naji ko na yau ne domin jiya kwananne ka ban."


Mallam Audi ya ce, "Yoo ai ba matsala ga yanka daya nan ki gwada."




Mika ma ta yayi, tafara ci, girgiza kai take kamar wata mai cin abinda ya fi komai dadi aduniya chan sai ta ce , "Gaskiya ne Mallam Audi Yasin sai da kunnena ya amsa fa, naman nan ya ba da kala sosai fara zuba min dai, Amman fa naman na ya yi wallahi."


Magana ta cigaba da yi tana kara daukan wani shi ko hankalinsa ya yi gaba yana ta zuba ma ta harda sa gyara, mika matan da zai yi kawai ya ga ai ta cinye tsinke guda Babba ke wajen, tana ganin ya lura da hakan cafkan Wanda ya kulle ma ta atakarddan ta yi gudu mai na ci ban ba ka ba, bin ta ya ke shima ya na haki, sai da ta bari sun shiga wani lungu mai shegen duhu ta labe aciki, shims ya na zuwa ya shige, Jan kafarshi ta fara tana katuwar murya, "Yeeeeeeeeee Ina kuke Ku fito ga nama nan mun samu har gida Yau akwai walimar dare daga ji zai yi tsoka."
Ihu ya fara ya na, "Dan Allah kuyi hakuri Wallahi ban San cewa Wannan gidanku ba ne na tuba Ku yafemin Ku sakeni Dan Allah."


Kara kankameshi Jiddatu da su Indo ke yi shi kuma ya na kokarin kubucewa ai ko da kyar ya yi nasarar subucewa aguje ya fita alungun ya na, "Yau ni naga jaraba wallahi nikam na yafe maganar tsiren ma akan na rasa raina."






Ya na fita suka fara dariya kan suka fice daga lungun


Suna fita Jiddatu ta lalubo wani karami, ki ince figagge daga cikin tsiren ta mikawa Indo, "Gashinan tin da kece Babba ki raba mu Ku nikam natafi gida."




Lantana ta ce, "Ayya Jidda ki Dan kara mana karami ne fa."




Jidda ta ce, "Iyee kwadayi ko? Lallaima yaran nan kun iya samun waje maimakon kuce min kun Gode sai kuce wani in kara ma Ku, to kwaddayayyu Wallahi bazan Kara ba kuma kucemin kun gode."




Ba yadda Suka iya haka suka ce ma ta sun gode.


Ta washe baki, "Yauwa yaran kirki maza atafi gida dare ya yi saura kuma gobe Ku ki zuwa yimana wanke-wanke sharar gida, kuma karku manta zamuje makarantar allon yamma fa."






Sai da ta gama tsattsayar ma su tare da kafa dokoki kan ta bari su ka tafi.






NA SAN MA SU KARATU ZA SU SO SANIN WACECE JIDDATU TO KU GYARA ZAMA DARAM DOMIN YANZU ZA KU SAN ASALIN JIDDATU.






JIDDATU 'Ya ce ga Alhaji Ibrahim hamshakin Dan kasuwa da ke zaune agarin kano tare da Mahaifiyarta Hajiya Zainab, Jiddatu ita ce 'ya ta uku wajen iyayenta kuma ita ce ta karshe, Babar Yayarta Mariya mai shekara 20, sai Hamza mai shekara 18 sannan Jiddatu da ta ke da shekara 9 aduniya, Iya mahaifiya ce ga Alhaji Ibrahim mahaifin Jidda,Wanda Iya tinda aka Haifi Jidda ta daura son duniyar nan ga Jidda, mussaman ma da taji ansa sunanta, Iya na son rayuwa da Jidda Amman ba ta son zaman birni ko kadan hakan ya sa ta nemi da abata Jidda su dawo kauye tin bayan suna, da kyar Alhaji Ibrahim ya rarrashi mahaifiyarshi kan cewa ta bari sai Jidda ta kai yaye, aiko Jidda na cika Wata bakwai Iya ta kasa hakuri ta zo ta tayar da masifa kan dole sai anbata Jidda, daga Alhaji Ibrahim har Hajiya zainab ba su so ba Amman ba yadda suka iya haka su ka tattara komai na Jidda aka danka ma Iya ta tafi da ita chan kauye.






Kwata-kwata ba shiri tsakanin Jidda da mahaifiyarta domin bata jin dadin irin rikon da Iya ke yiwa Jidda hakan ya sa da zaran ta yi Abu Hajiya zainab ba ta iya hakuri sai ta tanka.




Ita kuwa Iya da taga ana yiwa Jidda masifa ta gwammance su daina zuwa.




Akwai lokacin da akayi Hutu Alhaji Ibrahim ya tattaro iyalansa domin yin Hutu wajen mahaifiyarshi, Amman kwana daya sukayi iya ta koresu sabida kawai Mama ta daki Jidda akan ta ki yin wanka, kuka iya ta fara ana ma ta bakin ciki za a kashe ma ta Jika, ta dinga masifa hadda hada ma su kayansu su koma garin su ai ba ita ta gayyace su ba Dan haka baza atakura ma ta yar jikarta ba, haka su ka komo kano ba da son ran su ba.






Jiddatu Yarinyace karama kimanin shekara shida, rigimamiya, ga tsokana ga tsoro sannan ga bala'in ci.




Jiddatu kyakkyawace dai-dai gwargwado, chocolate in color sannan kullum fuskarta cikin murmushi ta ke hakan ke kara bayyanar da Dimple din da ke fuskarta wadda yayarta ke ma ta ikirari da Dimple Queen,ita kuma ta ke fadin (dompol kon), Jiddatu ta tsani wanka arayuwarta duk da cewa bata son kazanta Amman ta fannin wanka fa sai anyi daru kan Jiddatu ta yi.


Wani abin mamaki duk abun nan na Jiddatu ta na da kwakwalwa fiye da yadda ake tsammani ta na zuwa makarantar boko da islamiya na kauyen duk fitinarta ba ya hanata iya karatu ko fahimta domin har mamaki ake, hakan yasa wani lokacin ma ko ta yi Abu malaman kan kokarin kawar da kai,yanzu ta na aji hudu na matakin primary kuma tun da ta fara zuwa makarantar nan daga islamiya har boko na daya ta ke zuwa bata taba zuwa na biyu ba ma bare na uku, su Indo da lantana kuwa kullum su ne na karshen aji.


Abu daya kullum maganar Jiddatu daya ne ita fa *MATAR POLICE* da wannan Kalmar ma kadai ta kan iya kwatan kanta in ta yi laifi abin ka da yan kauye akwai tsoron jami'an tsaro.


Ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login