Showing 27001 words to 30000 words out of 31162 words

Chapter 10 - Matar Police Book Complete document .txt

batasan sanda hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta ba.






Dady ya kalleta sannan ya kau da kai izuwa duban Alhaji Adamu ya ce, "Alhaji Dan Allah ka tsaya mu yi magana ta fahimta, ina ganin bai kamata ace wannan maganar har ta zama Babba ba, ka dubi yar uwar mahaifiyar ta mana, kaga irin halin da ta shiga, da zaka taimaka da ka bar mana Jidda har lokacin da zakai ma ta auren."






Tashi Alhaji Adamu ya yi, yana kwallawa Jidda kira,"Ke Jidda ina kike fito za mu tafi, inna biye ta mutanen nan zasu batamin lokaci. "




Mumy ce ta durkusa gareshi ta na, "Dan Allah Alhaji kar ka min haka, wallahi ina yiwa Jidda So fiye da 'ya'yan da na Haifa domin ita din tamkar yar uwata daya tilo da na rasa ne Dan Allah karka rabani da ita."




Fitowa Jidda ta yi da gudu Alhaji ya rikye mata hannu tare da tsaki ya ja ta suka bar gidan.




Ahanyar fitansu su kai kicibis da KHALEEL ya na shigowa.


Abin ya bawa KHALEEL mamaki Amman ya basar, Jidda ce ta kalli Khaleel tare da yi mi shi gwalo.


Kallonta ya yi, ya yi tsaki tare da kau da kai, kan ya nufi cikin gidan.




KHALEEL na shiga ya tarar da Mumy na kuka Dady sai faman ba ta hakuri ya ke.




Karasawa ya yi yana, "Lafiya dai kuwa?"




Mumy ta ce, "KHALEEL sun rabani da Jidda Dan Allah ka kar bomin ita, wallahi jinta na ke tamkar yar uwata."




KHALEEL ya ce, "Haba Mumy akan wannan yarinyar zaki tada hankalinki? To miye ma yata tafiyan da ita ai sai me, mu daman ba nema mu ke ba, ni wallahi daman ma na tasan....




Cikin tsawa Mumy ta dakatar da shi, "ba ita ka tsana ba ni ka tsana, domin duk abin da kayiwa Jidda kamar kaiwa Amir da Amira, Yanzu yarinyar nan abar tausayice ba abin da take bukata fiye da taimako, wannan mutum ban da son duniya ba abin da ya sa agaba, ni nasan ba Dan Allah ya ke son komawar Jidda da hamza garesa ba, dukiyarsu kawai ya ke so, ni dama ace dukiyar zai ci kadai da sauki in zai bar ma na su, Amman ni nasani cewa Jidda wahala zata sha itace abar tausayi, domin ni nasan ya tsaneta, sanadiyarta su ka fara samun matsala da Hajiya Iyah."






KHALEEL ya yi shiru ya ma rasa abin fadi.




Dady ya ce, "ni ban damu da maganar Hamza ba daman maganar Jidda ne ya dameni kuma ma na aure Yanzu, ki jibeta yar karamar yarinya kawai abata ma yarinya karama rayuwa."




Mumy ta ce, "Hmm kai ma ka Fada dai, Yanzu yazama dole mu nemo mafitar da zamu bi domin taimakon yarinyar nan karta Fada Ga mummunan yanayin da ke bibiyarta."


Dady ya ce, "Wannan ya zama dole in sha Allah zan yi iyaka bakin kokarina."






************Alhaji Adamu Ba inda ya nufi Da Jidda sai cikin garin Katsina inda iyalansa su ke da zama.




Tunda daga shiga cikin gidan Jidda ta fara fuskantar sabuwar rayuwa, mai cike da al'ajabi tare kaddara.




MATAR gidan ce zaune wadda ake yiwa lakabi da Ammie ta taso ta yiwa Jidda wani mummanan kallo tare da fadin, "Alhamdulillah ,Allah dai ya yi wai kishiyar Tsohuwa ta haihu."




Alhaji Adamu ya kyalkyale da dariya, "Ai fa kam lamari ya tabbata ko ince ya kusa, domin wannan shine farko."




Karewa jidda kallo tai sama da katsa tai tsaki tare da fadin, "Ke Fatima, zo ki dau yar shilar nan Ku bata abinci ta ci, sannan ta na gamawa daman washing machine din mu ya sami matsala ki Ciro ma ta wankin nan ta yi."




Fatima ta ce to tare da kallon Jidda da harara ta ce, "Mu je."




Sai da Ammie ta lekya tare da tabbatar wa su Jidda sun shige cikin kan ta fara magana kasa-kasa, "Fatan dai ka kwamuso mana dukiyar?"






Dariya ya yi yana, "Ke kin cika azarzababi walle, yaushe Yanzu zan fara maganar kudi, ke baki San komai kan tsari ake ba ne? So na ke sai na Aurawa waccer matsiyaciyar yarinyar sulaiman, shi kuma hamza yadawo kan afara maganar dukiya, in ba haka ba ina farawa yanzu ai za su gano mu, su fahimci inda mu ka dosa, Yanzu ma ba ki San yadda na sha fama da mutanen nan ba ne Wallahi."




Ammie tayi shewa ta ce, "hihi na dai kusa zama Hajiyar gaske, Wallahi ni har ma na zaku ayi ayi aure."




"Ke dai kiyi shiru kawai akan maganar auren nan ma sai da na ya fito karyar cewa munyi alkawarin aura wa ya'yanmu juna, ni dama na tsani yarinyar da ta sa Iyah ta fita sabgata ni mai zai kani gareta in ba kaddara ba, hmm Wallahi ana samun kudin nan sakesu zamuyi subi duniya, Chan ta matse ma su, daga ita har Dan uwan na ta ba damuwata ba ne."
Cewar Alhaji Adamu.




Ammie ta ce, "Ai fa kam shiyasa tun yau ma zata fara aikatuwa, kaga ma bara na shiga daga ciki in taci abinci Yanzu zata fara duty."




Dariyar mugunta Alhaji ya yi ya na, "Hajiya ba ki da dama."




Ta na shiga ciki ta tarar da Jidda ta yi tsili-tsilli da ido ta ci abinci bai isheta ba tana Neman kari Amman tsoro ya ha na ta magana.




Tsawa ta ma ta ta na, "Ke nan gidan fa ba na lalaci ba ne, na Fada miki, kima daina wani zare min ido, Inda cen kin saba iskanci agidan Ku to nan ba zan dauka ba, Dan haka maza tashi kije ki wanke min kayan nan tas, kuma ba na son ganin datti ko kadan ajiki."




Ko da Jidda ta ga wankin sai da gabanta ya fadi, ba abin da ya zo ranta sai Iyah, lokacin da ke ma su wanki.
Nan take kwalla ya fara kwarara daga idanunta.




Tsawa tare da Mari alokaci daya Ammie ta kai ma ta, "ba ki isa ba fa dole sai kinyi wankin nan wallahi agidannan ko da zaki kai tsakiyar dare ne, to yazama dole ki yi na Fada miki, maza ki fara."




Haka Jidda ta fara sabar wankin nan ba yadda ta iya ban da hawaye ba abin da ke zubowa daga idanunta.




Urs Xayyeesherth
[11/30, 7:39 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

30November


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_FREE PAGE 38/39_*


_*Karku Manta daga wannan saura free page dayane za a shiga na kudi, in aka yi posting 40 shikenan nadaina posting a ko ina sai payment group Wanda tuna nafara sambada wa inda suka biya*_


****************
************
******************




Ta na gama wankin nan yunwa kamar za ta kashe ta.


Kallon Fatima tai da ke ta danne-danne waya ta ce, "Anty Fatima na gama yunwa na ke ji Dan Allah."




Dalla ma ta harara Fatima ta yi ta ce, "Dalla matsamin anan wawiya kawai, sai shegen ci kamar kaza naga dazu ki ka gama cin abincin nan dai ko?"






Shiru Jidda tai ta zauna daram awajen da ta gama wankin ta fara kuka.


Ihu ta ke tana, "Wayyo Allah Iyah na, Iyah na Dan Allah ki zo ki taimakeni, Wallahi yunwa na ke ji Zan mutu."




Ammie ce ta tawo bijigin-bijigin ta na, "Fatima wannan wani irin iskanci ne nake jin ihu ana kuka."




Fatima ta ce, "Ammie Wai ta gama wankin Yunwa ta ke ji, kuma fa kina gani kan ta fara na bata sauran abincin da Yaya Sulaiman ya rage."




Kallon Jidda, Ammie tai cike da takaici, ta karasa gareta tare da fadin, "Daman an kawo ki ne Dan kici abinci an Fada miki? To daga yau ma ki sani nabari a rana sau daya zakina cin abinci agidannan, kuma duk zan kori yan aikin mu ke zakina komai girki ne dai kawai mai aikin za ta na yi, ina Ita Hajiya iyar ta gama sangartaki? To za mu gani, mu zuba mugani ni da ke agidan nan."




Kuka kawai Jidda ta ke ta ma rasa abin fadi.
Dare na yi Jidda ta rasa wajen kwanciya, cikin tsawa Ammie ta mi ka mata taburma, ga sanyin tais ga gari sanyi, ba abin luluba, abin tausayi, da ka ganta za kasan cewa ta na cikin maraici.


Haka Jidda ta kwana da yunwa
Washe gari da asussuba Ammie ta tasheta tai sallah za ta koma Ammie ta ce , "A'a ai yarinya yanzu za ki fara aikin ki, ki fara share kaf gidannan sannan kuma kiyi mopping, ki wanke toilet, ina son ganin gidannan ta-tas kan na farka daga barci karfe 9 na ba ki awa uku kenan .


Da sanyin asubar nan kowa na barci haka Jidda ta fara zabgar aikin nan ba ji ba gani, tun tana kwalla har hawayen ma ya gaji yadaina fitowa.




Ta kammala kenan, ta zauna domin hutawa nan taji an zuba ma ta ruwan sanyi, bude idon da zatayi Sulaiman ne tsaye ya na, "Yar shillar Amaryata MAZA tashi ki fara aikin lada, ga wanki chan ki wanke mun su tsab domin fita wajen ball zan yi."




Tashi Jidda tai ta dauki kayan ga yunwar jiya ga ta yau, ta fara wankin nan.


Ta kammala wajen karfe sha biyu na rana, Sulaiman na shigowa ya yi ma ta wata irin tsawa, "Wannan wani kalan iskanci? A haka kikeso na sa kayan duk jurwaye? To MAZA ki tashi ki kara wankemin har sai ya fita tas."




Ya na gama maganar ya tafi ya na wakarshi hankali kwance hadda fito.




Jidda na kuka haka ta kara sabar kayan nan ba ita ta gama ba sai wajen karfe hudu.




Zama tai atakure ta na tagumi, yunwa ta Riga da ta gama cin ta, Jidda ta ci abinci ma ya aka kaya bare ba ta ci ba, da ka ganta zakasan cewa tana cikin wani hali, abinka da Mara jiki nan da nan sirantarta ta kara fitowa fili.








Chan anjima sai Ga Fatima nan ta turo ma ta plate din wata ya mishasshiyar shinkafa, wadda ba ta fi loma biyar ba, ko da Jidda ta kalli shinkafar nan sai da tai guntun hawaye.


Fara ci kawai ta yi tamkar wadda ba ta ta ba cin abinci ba, maimakon ta koshi sai yunwar ta karu, ruwa kawai ta dunga durawa har cikin ta ya fara kullewa kan ta bari




***Tun da Jidda ta koma gidan Alhaji Adamu ban da bauta ba abin da ta ke, ta gama fita a haiyacinta, ba zama bare Hutu, sai aiki.




Mumy kuwa ta na nan cikin damuwa hankalinta ya gama fita a kan ta domin jikinta ya ba ta cewa Jidda ba ta cikin yanayin walwala.


Dady ya na ta faman nemo mafitar da zai kwato Jidda.




*****A kwana a tashi Jidda na cikin sati uku da zuwanta gidan Alhaji Adamu.




Da sassafe ta fito ta na shara Fatima ta fito Jidda ba ta lura ba ta watsa ma ta shara, nan Fatima ta fara jabga ihu ta na kuka," wayyo Allah Ammie na kinga za ta kasheni, ta watsamin shara. "




Da sauri Ammie ta dauko Bulala ta fito , "Ke Wai wace irin yar iskar yarinya ce? Bakin ciki kikemin da ita ko? To yau sai naci uban ki agidannan Wallahi."




Dukan Jidda ta farayi da bulala ba ji ba gani, tun tana ihu har tai shiru.


Nan ta ke Ammie na dukanta har tayi barci awajen.






Urs Xayyeesherth
[12/1, 9:04 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°


1December2020


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝


__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________


_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_


_*LABARI DA RUBUTAWA*_


_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_




_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_


AND NOW *MATAR POLICE*


_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_




_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_




*_LAST FREE PAGE 40_*


_*KAMAR YADDA NA FADA DAGA WANNAN ANDAINA POSTING AKO INA SAI PAYMENTS GROUP WANDA YA IYAKA WAN INDA SUKA BIYA ZAN SAMBADA ACIKI, SANNAN INSHA ALLAH LITTAFINA BA ZAI TABA FITA BA IYAKA ADADIN MUTANEN DA SUKA BIYA IYAKA SU ZA SU KARANTA🥰 KO BA KOMAI YAU ZAN GA MASOYANA DA MA NA JIDDA DIMPLE QUEEN*_


****************
************
******************




Jidda na cikin barci tai mafarkin Hajiya Iyah , "Jidda me ki ke yi na haka? Jidda me yasa ki ka yi sanyi aka rainaki? Jiddatuna ki tashi ki tuna labaran da na ke baki, ki kwaci kan ki daga gidan nan,Jidda ba na son zamanki agidannan ki tashi ki koma Chan wajen Mumynki in ba haka ba Jidda daga ni har Iyayenki ba za mu yafe mi ki ba, Jidda ki tashi na Fada mi ki ,ki tashi Yanzu." Cewar Iyah




Afirgice Jidda ta farka dai-dai lokacin da Ammie ke zuwa tashinta, ta mikye kenan sai ga Ammie da ruwan sanyin nan kamar yadda ta saba.


Kallon Jidda tai tare da watsa mata, "Munafuka duk da kin tashi sai na watsa mi kin, shegiyar yarinya kawai ba ni waje, kuma maza ki yi sallah afara gyaran gida, Dan yau za a daura mi ki aure da Sulaiman ki tabbatar kin gyara ko ina."






Maganar Aure da Jidda taji ne ya rikita ma ta kwakwalwa nan ta ke, ta kara tuno mafarkin Hajiya Iyah.






Fara gyaran gidan tai kamar kullum Amman adai dai lokacin da ta zo mopping wa ni hamshakin Murmushi ne ya bayyana daga fuskarta, azuciyarta ta na fadin, "Wallahi sai dai akasheni Amman Yau sai na yi abin da naga dama agidannan kuma na gudu."




Shiga kicin tai ta dibo mangyada tare da zubawa acikin ruwan Mopping din, har ta kammala ba Wanda ya farka agidan abin ka da yan Hutu.




Jidda na gamawa ta sulale tare da barin gidan.




Ko da ta fita asanyin asuban nan mai gadi bai farka ba, bare ma ya San da fitarta ko ya hanata.






Tafiya kawai Jidda ta ke cikin daji ba ta San inda ta ke shiga ba bare tasan inda ta ke fita.




Yunwa ta gama cinta gabadaya ta gigice da kyar ta ke tafiyar ma.




****Karfe Tara dai-dai Ammie an dau wanka ana tafiyar kwalisa, sa kafar da za tai kan tais nan take tajita akasa, kwallawa Fatima kira tai ta na ihu, Fatima ma na sa kafa ta ji ta dim, sai kuka, Alhaji Adamu na jin hakan fitowan da zai sai gashi shima a kasa tim.




Ammie na kuka, Fatima na kuka Alhaji kuwa ya yi tsiru-tsiru da ido ya na kallon kowa daya bayan daya, radadi ya ke ji inda hali zai yi kukan Amman ba dama.






Dakyar su ka sami damar janye cikinsu su ka koma daki.


Ammie ta fara masifa ta na kwallawa Jidda kira ta kira ya fi sau Dari, Amman ko alamar Jidda ba ta ji ba bare motsinta.


"Shedaniyar Yarinya na San ba Wanda zai yi wannan aika-aikan sai Ita Wallahi, kuma yau inna kamata sai ta manta garin su, Wallahi sai na ci uwar yarinyar nan, ji kina kamar wadda aka ma duka nasan dole in yi zazzabi."






Sai ta kira ma su aikin su kannan aka gyara gidan.




Ko da Ammie za ta fito, nemo zukyekiyar Bulalarta ta yi ta cigaba da masifa ta na ke waye gida adole ta na Neman Jidda.


Daga karshe ta ga ba alamar Jidda agidan, nan ta ke hankalinta ya tashi tana yiwa Alhaji magana ya fito, aka tambayi mai gadi ya ce shi bai San inda Jidda ta ke ba, domin ko fitartama bai ji ba.




Daura hannu ya yi akai ya na, "Wayyo Allah na, na shiga uku wannan jarababbiyar yar za ta ja min masifa, in dai ta tafi ta chuceni Wallahi, shikenan an gama dani, kai Wallahi ma sai na nemota ko ina ta shiga ba gudu babu ja da baya sai na Aura ma ta Sulaiman.




Firgar motarshi ya yi nan ta ke ya fice.




Ita ko Ammie sai hamami ta ke, " Ni Wallahi akawomin ita ma in ci uban shegiya yadda tasani ciwon jikin nan nima sai na sa ta.


A bangaren Mumy da Dady kuwa sunji labarin cewa za ayi auren Jidda da Sulaiman hakan ya sa su yin asuban ci domin su riski auren, su dakatar.




Suna cikin tafiya kamar wasa Mumy ta hangi wata yarinya ya she akwance ga dukkan alamu ma ta fita a haiyyacinta.




Mumy ta ce, "Alhaji tsaya mu duba yarinyar chan."




Dady ya ce, "Kin San dai mun makara kar fa a daura auren nan."




Mumy ta ce, "Ayya wannan yarinyar ma ga dukkan alamu ta na bukatar taimako tamkar Jidda, mu tsaya mu taimaketa, watakil in mun taimaketa mu ma Allah ta ji kan mu ya kufuto mana da Jidda."




Suna fita Mumy na zuwa ta tatarar ai Jidda ce kwance, numfashi ma da kyar ya ke fita, kana taba jikinta sanyi karara, da alamun sanyi ya gama shigar ta.




Kuka Mumy ta fara ta na, "Wallahi Jiddatu ce, Ita ce, Alhaji Dan Allah ka taimakeni kar Jidda ta mutu numfashin ma da kyar ta ke iya yi.




Nan ta ke Dady ya sa Jidda amota su ka shiga gari domin Neman wani asibitin da ke kusa.




Cikin sa'a kuwa suka hangi wani karamin asibiti, suna shiga aka farayiwa Jidda taimako har Allah ya sa ta farfado cikin ikon sa.




Amman likita ya sanar Mumy da Dady cewa, " Nemoniya wa to ciwon sanyi ya Riga ya ma ta shigar sauri, ta indai in ba a tsaya ma ta ba zai iya halaka ta, sannan yunwa ta fara cin jikinta tana bukatar kulawa ta mussaman a yanzu dai kam.




Mumy ta yi kuka sosai domin jin hakan ta ke har cikin ranta.




Jidda ko sai kallon Mumy ta ke tana kyalkyallewa da dariya, in Mumy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login