Showing 30001 words to 31162 words out of 31162 words
Chapter 11 - Matar Police Book Complete document .txt
ta kalleta tai Murmushi ta ma rasa abin fadi.
Mota suka shige da niyar komawa gida.
Mumy ta ce, "Alhaji shin me ka ke ganin ya dace mu yi a yanzu?"
Girgiza kai kawai Dady ya yi, "Ni nasan me zanyi abin da na ke gudu ya zama dole ne inyi domin in taimaki marainiyar Allah, kar ki CE min za ki ja da hukunci na domin sai bayan na aikata zakiji bayani, Yanzu dai ki saurareni zuwa safiyar gobe kawai in sha Allah komai ma ya zo karshe."
Mumy ta yi shiru kamar yadda mai gidanta ya umarci da tai hakan.
Suna isa gida Jidda na ganin Amira sai dariya da murna hadda tsalle kamar wadda akayiwa allura.
Wanka Mumy ta ma ta sannan ta hada ma ta tea da indomie Jidda na zama ta fara cin abincin nan kamar mayya ko na bakinta bata bari ta ke kara sa wani.
Mumy na kallon Jidda sai kwalla.
Ita ko Jidda intaci taci sai ta dago ta kalli Mumy ta ma ta gwala tana, "Ni Wallahi ba zan sammaki ba."
Dan dole dai sai Jidda ta sa Mumy dariya.
Ko da dare ya yi, Mumy daukan Jidda ta yi, suka nufi dakinta domin ta ce ba za ta rabu da da 'yarta ba.
Dady ko sai dariya ya ke, Amir ya ce, "Mumy katuwa da ita bazaki bari ta kwana dakin Amira ba?"
Mumy ta ce, "Aa din Ku bar min abata."
******Washe Gari da asussuba Dady ya na fita massalaci, dawowan da zai yi gida sai da ya kira KHALEEL ya zo.
Zama sukayi afalo ya sa aka kira mi shi Mumy da Jidda.
Dady ya ce, "To Yanzu za Ku ji, hukuncin da na yanke, kuma ba na son amin jayayya daga ke har 'Dan ki domin kamar yadda Jidda ta ke 'ya agareki nima haka Jidda ta ke ya agareni, kamar yadda ki ke da iko da ita, nima ina da iko da ita, so na gama yanke hukunci ko ince nama yanke , asafiyar yau ban shigo gidannan ba har sai dai na Daura AUREN JIDDA DA KHALEEL A masallaci.
Nan ta ke KHALEEL ya mikye tsaye sai kwalla, " Dady Dan Allah me zanyi da wannan yarinyar? Dady aduba agani dai ni kam dai anga...
Tsawa Dady ya ma sa ya na fadin, "Na aura ma ka Jidda, kuma ba rabuwa sannan kasani yau Jidda ba inda zata kwana sai agidanka na fadama."
Mumy ta ce, "Alhamdulillah nasan cewa daman bazaka taba yanke hukuncin da bai dace ba, Na gode sosai Alhaji Allah kara girma."
Dan takaici Ma KHALEEL hanyar fita ya nufa.
Mumy ta ce, "Ka dawo, nace ma ka dawo,ga Jidda nan ka rikyemin ita amana, Wallahi Wallahi in ka rabu da jidda bazan taba yafe ma ka ba, nafadama."
Jidda na zaune kawai bin duk mai magana ta ke da baki, damuwarta kai tai abin da za akomar da ita wancen gidan, domin tasan duk muguntar KHALEEL ba dai zai hanata abinci ba.
Kuma daman ita babbar damuwarta ba ta huce na ciki, in taci ta koshi shikenan.
Tunda KHALEEL ya fita ma ya kasa komawa gida Office ya nufa hankali Tashe, shi ba ma ta Hajara ya ke a yanzu ba, tsanar da ya yi Jidda ke dawainiya da shi.
Misalin karfe hudu na yamma Mumy ta shirya Jidda cikin bakar doguwar Riga tare da golden din bols da golden din gyale, simple makeup ta ma ta, Wanda ba karamin kyau ta yi ba, kiran KHALEEL mumy ta yi awaya tana fadin, "Ga mu nan fa mun gama in zaka tafi gida ka biyo mu tafi tare."
Ba yadda KHALEEL ya iya haka ya biyo gidan kuwa.
Mumy ta bude baya za ta shiga Jidda ta bita.
Mumy ta ce, "Iye KHALEEL fito ka budewa matarka gaba ta zauna maza."
Jidda ko ajikinta ta lura ranshi abace ya ke yana bude ma ta ta shige da sauri tare da yi mi shi gwalo.
Suna isa Hajara ta dawo daga wajen aiki kenan.
Mumy ta ce, "Yawwa daman ke na fi bida a yanzu, zauna ko."
Zama Hajara tai tana mai kallon Jidda cike da Mamaki.
Mumy ta nuna Jidda tare da fadin, "abokiyar zamace akayi miki gatanan, kuma 'ya ta, dage ke har shi yadda kuka bi da ita haka itama zata bi da Ku, kunsan da hakan domin yarinyace, ko da yake mijin na ki ba son ta ya ke ba, to Amman ni fa ina sonta kuma ba na son abin da zai sameta dai dai Dana lokaci gudu, Dan haka KHALEEL ka ji nan adakinki Jidda za ta zauna, sannan ba ta da lafiya ga magungunanta nan in dare ya yi abata, maganar abincin na San ba Ku da matsala ni zanyi mai aikin ma magana kan na tafi."
Kallon Mumy Hajara tai cike da gyatsina fuska ta yi tsaki tare da tashi ta na fadin, "Me zan kisa agun wannan yar shilar? Shi kan shi ma baya gabana bare ita mtsw."
Ta haura stairs abinta.
Mumy ta yi Murmushi ,"to ka dai ji, ni dai akulamin da 'ya ko asami matsala Jidda ta shi muje dakin."
Sai da Mumy ta kai Jidda dakinta, Jidda na ta tsalle tana murna kan Mumy ta fito ta sami KHALEEL, "Kasan Allah yau adakin nan zaka kwana domin kuwa nasan halinka sarai, karka kuskura ka ce zaka bar Jidda ta kwana ita kadai."
Daga wannan maganar Mumy ta fice daga gidan.
Dare na yi mai aiki ta kawo ma Jidda abinci, ta ci ta koshi son ranta kan ta haye kan gado tuni barci ya yi awon gaba da ita.
KHALEEL na shigowa ya yi tsaki tare da mata tsawa wadda sai da ta sa ta farka wa.
"Dalla sauka min agado chan kasa zaki kwana, ko da ni kike so in kwana akasan?"
Jiki asanyaye Jidda ta kwanta akasa.
Kamar KHALEEL zai ce ta dawo sai wata zuciyar ta ayana ma sa da ya kyalleta.
Cikin dare kamar amafarki Jidda na fitar da wani irin numfashi, ga shi ta kyankyame jikinta waje daya da alamar cewa sanyi ke damunta.
KHALEEL na gani ba wadda na tuno sai Mumy hakan ya sa shi saurin dagata daga kasan ya mai da ta kan gado, da sauri ya dauko maganin ta ya ba ta, ya lullubeta zai sauka kan gadon ya ji Jidda ta kyankyame ma sa jiki.
Ba yadda ya iya haka ya kwanta akan gadon nan.
Kallon fuskarta ya ke zuciyarsa na ayyana ma sa, "Ashe yarinyar nan kyakkyawace haka."
Can kuma sai ya yi saurin kawar da kai tare da daina kallonta.
KHALEEL ya tashi sallar asuba ya nemi Jidda ciki da waje ya rasa ga Mumy ta kira waya abata za ta gaisa da yarta.
KHALEEL ya gama duba ko ina agidan nan ya rasa Jidda zama ya yi kasan bishiyar da tsakar gidan har gari ya yi haske ya ma rasa inda zai sa ransa.
Ya tashi da niyar kirin Mumy ya Fada ma ta halin da ake ciki daga kan da zai yi sai ga Jidda Asama bishiya.
_*HHHHHH AMARYA MAI HAWA BISHIYA*_
_*TO ALHAMDULILLAH YAU DAI ANZO KARSHEN FEJIN KYAUTA DUK MAI SON CIGABAN ZA TA IYA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 08103080717*_
Love you oll lodilodi
URS Xayyeesherth