Showing 24001 words to 27000 words out of 29796 words

Chapter 9 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt

29 Oct 2025

424

fili kam nabasa hkr amma cikin zuciya idan banda murna babu abinda nakeyi.

"Da bikin Muhammed ya tashi, bayi itace babba ita yakamata taje amma sbd naga k'uk'yal uwar daka na ďikirkire nace nine zani, dukkansu babu wanda yaja mgnr tai tsayi, kai ranar naga almara, abubuwa ne iri-iri tunda uwata ta haifeni ban ta6a gani ba, yan'matan kirta(crestan)kuwa ba'a mgn sai faman shafe-shafe sukeyi da mazan dake gun nayi kallo harna gode Allah, amma cikin shagugulan bikin babu abinda yafi birgeni irin yake suke wani abu kamar masu fareti(crossing of swear) kae idan da badan hassada ba gsky danace su birgeni.

" Kwanana biyar a barikinsu snn na dawo gida, koda na dawo k'arya da gsky na shirya na faďiwa malam dasu Bayi, amma da shike duk sunsan halina babu wanda ya ďauki mgnta da muhimmaci......





_///don't4get cmmnt and share pls😻_





*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥


_*FITSARIN FAK'O*_

💥💥💥

_(mugunta)_

*FASAHA ONLINE WRITERS*

_F.O.W_

_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_


🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹

_not editing⛏_


_bestowed to my dote *❤FAREESA❤* yar'arziki irin albarka, yar da'aka haifa tsiya na bacci Allah yasa kifi haka my sweet dota. Bari na raďaki, kada mamanki tace banayi dake, su *FaTI* am mmnt.😏😻_


بسم اللة الرحمن الرحيم


*∅∅∅*📝
*page18*


................"Zama nai a tsakar gida ina jiran dawowar Yahuza yau duk wanda za'ai sai dai a yisa domin bazan zauna na zuba ido sbd wata shegiya ďana ya kare a tsiyace ba, gwama yai duk wanda za'ai a yau ďin nan ba gobe Safiya zatabar gidan tunda ba gidan ubanta bane.

"Gu na samu na zauna ina jiran shigowar Yahuza, tun ina zaman daďi har ya koma ta wiya, sallar kawai kesa na mike, nai haka ne sbd nariga da nasan halinsa sarai idan ba kasawa nai na tsare ba sai yazo yai shigewarsa ďakinsa ba tare dana gansa ba.

"Nan naci gaba da zama, tun ina zaman daďi har ya koma ta wiya daga k'arke dai tabarma na ďauko na shinfiďa na kwanta a gun, ina kwanciya bcc ya ďaukeni, ban tashi ba sai bayan ba'asar snn na tashi nai sallah naje na share murhu na gyara domin dora sanwa.

"Duk abinda nake ciki hankalina na kan hanya har na k'are girki Yahuza bai shigo gidan ba, hakan yasa nima naki shiga ďaki, bakin k'ofa nako nz zauma, da shike Safiya ba girki takeyi ba sai taga dama yasa ko lek'owa waje batai ba, Yahuza bai shigo gidan ba sai bayan goma, duk a lokacin ban tashi daga inda nake zaune ba musamman ma danaga dare yayi nasan yanzu haka ya kusan shigowa.

"Ko kibtawa banyi ba har Allah ya kawosa, da sallama ya shigo, yana shan kwana da sauri na mike haďi da dakatar dashi daya tsaya, ina isa gun nace ina zaka?.

" babu kunya bare tsoron Allah yace ďaki.

"wani ďakin?karaf saiga safiya ta leko, ganina da tai da mijinta wai ita fitsarirriya mara kunya hannu tasa ta jawosa jikinta tana faďin zomuje daga ciki.

"Tun kafin ya motsa hannu nasa na bigewa Safiya tata hannu snn nace babu inda zanje, juyowa nai na meda dubata ga Yahuza snn nace kaiiiiii!!!.

"Da sauri ya dago kai ya kalleni," snn nace kasan abinda nakeso dakai?.

"A'a iya sai kin faďi
"A yau ďinan nakeso ka saki shegiyar yarinyar nan, na k'arisa mgnr ne haďi da nuna mata ďan yatsa.

"Da shike rashin kunyarta ta gadone, tun kafin na sauke hannu tasa tata hannu ta bige min tawa, haďi da cewa ni ki daina nunani da ďan yatsa.

"Yahuza na kallo amma bai iya cewa komai ba, a fusace nasa hannu zai kai mata mari, da sauri ta tare, haďi da murďimin tawa hannu.

" Jin zafin murďewar yasa nasa ihu, a lokacin ne Yahuza yai mata mgn da cewa"ki bari ya isa haka.

"Tsabar takaici ban san lokacin nasa kuka ba haďi da ihu, azo a taimakeni Safiya ta kasheni tunda ta mallakeni yaro, ko kafin su bayi da malam su iso gun tuni na kamata da ďanbe.

"Yahuza dake gun babu abinda yakeyi sai k'ok'arin amsar Safiya daga hannuna, tun tana ramawa har jikinta yai sanyi ta kasa, sbd ďaneta da nai, ko kafin su malam da bayi su iso Safiya taji jiki dani.

"Da k'yar malam da bayi suka ďagani daga jikin Safiya, bayan na ďaga daga jikin Safiya ne malam yace nazo mu tafi, niko nace babu inda zani sai Yahuza ya saki Safiya, daga malam har bayi babu irin hkrin da basu bani ba amma hkra.

"Gani malam yana nemar tirsasani na hkra, da gangan na hausa da masifa da bala'i har saida yabar gun, itako bayi bana sata a lissafi, kallo ďaya nai mata ta kauce na bani gu." snn naci gaba daga inda na tsaya babu yadda banyi da Yahuza akan ya saki Safiya ba amma yaki, harda kukansa wai idan har ya saketa mutuwa zaiyi, gani bashida niyya yasa nace idan bai aikata abinda na umarcesa ba saina tsine masa, snn kuma saki uku nakeso yai mata ba ďaya ko biyu ba.

"Daga Yahuza har ita kanta Safiyar kuka sukeyi, ni kuwa k'ek'eshw idona nai nai kamar ban gansu ba, har saida ya saketa, da kaina na shiga ďakin na kwaso mata kayan sawarta na watso mata waje, tana kuka tabar gidan.

"Gani Yahuza yana da niyyae binta da sauri naje na kamota ita kuma ta kara gab, kaya kuma nace babu uban daya isa ya bata su zama mallakin Yahuza tunda bata haihu dashi, amma da shike jummai jidalillace asalatun farko saidata a gidanmu, na fito daga ban ďaki kenan na hango uwar masifa, take naji hanji cikina su yamutsa, dariya yak'e nai mata wanda yafi kuka k'una inai mata sannu da zuwa, duk da dai nasan ba Al'khairi ne ya kawota gidan ba.

"Itama da fara'arta ta amsa, hakan ya bani k'arfin guiwar k'arisawa inda take, tun kafin na duk'a tuni ta rigani, ko kafin na ankara jina nayi timm a k'asa, kafin nai wani yuk'uri tariga da tahaye kaina." nushi take kaimin kamar Allah ya aikota gashare bata ďaga daga kaina ba saida ta tambata naji jiki, babu yadda su bayi basu data ďaga daga kaina ba amma taki, shiko malam yana ďaki yana jin duk abinda ke faruwa amma yaki fitowa bare yabada hakuri.

"Tana mikewa daga kaina bata saurari kowa ba, ta fice daga gidan haďi da cewa na ramawa Safiya, shiru nai ban taka mata ba, da bakin ciki ya kamana har ďaki nabi malam na samesa inda nake shiga banai nake fita ba, da yaga zan damesa mikewa yai yasa kayansa ya fice daga gidan, haushi da takaici daya kamani nace zaka dawo kasameni.

"Tun daga lokacin nake jiran naji wanda zaiyi mgnta na sauke a kansu, da shike su riga da susan halina babu wanda ya tak'aleni da mgnr.

"Kafin dare jikina yai tsami, duk inda na jiya ciwo yakemin, gani haka yace Yahuza yaje ya haďomin mgnan rage gajiya, bayan kwana biyu saiga jummai da yara sukazo kwashe kaya, tana sallama na tashi na koma ďaki, duk irin habaice habaice da takeyi inaji amma ban tanka mata ba har suka kare.

" Ina zaune a ďaki ina jiyo muryanta tana sallama dasu bayi da Saro nace shegiya k'yadaiyi ki k'are bazan tanka ba bare ki tarami gajiya..........






_///don't4get commnt and share pls😻///_






*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥


_*FITSARIN FAK'O*_

💥💥💥

_(mugunta)_

*FASAHA ONLINE WRITERS*

_F.O.W_

_*💥{Infacing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_


🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹

_not editing⛏_


_*yaba kyauta tuqueci ka damu da wanda ya damu dakai, a gaskiya naji daďi sosai da sosai da kulawarki a gareni ngd Allah yabar dalili ta alkhairi, (RAHMA ABDULLAHI)marubuciyar WANDA BAIJI BARI BA.... one love keep us togeda❤😻*_

بسم اللة الرحمن الرحيم


*∅∅∅*📝
*page17*


.................."Tun daga lokacin tsigewa da rashin mutunci iri-iri nake gani a gun Safiya.

"Gashi babu halin yin mgn sbd su bayi da Saro, domin yanzu motsi kaďan nai idonsu na kaina, bakin cikina ďaya da nice kaďai take wa rashin kunya, tsakaninta dasu bayi kuwa farau-farau duk aikin datasan bayi nayi, kafin ta fito daga ďaki tuni ta tayata, idan ina ďaki sai dai kawai najiyo muryan bayi tasa sanya mata al'barka.

"Saro kuwa tamkar k'awaye suke sawa da dariya kace tare suka taso, tun safe idan ta ďauki yaron da Saro ke goyo baya meda mata shi sai dare.

"Sabida tsabar bakin cikin yasa yanzu ban cika fita tsakar gida ba, sbd zuciyata bazata ďauke ba.

"Da haka nake ta hkri, tun safe da Yahuza yabar gida bai dawo ba har yamma, da shike ba haka yakeyi ba yasa nabi na damu, sbd nariga dana san halinsa me zuciya ne, laifi kaďan kazai masa yai fushi.

"Gani har goma na dare yayi bai dawo gidan ba, gashi kuma ba naje na tambyi Safiya ba ta nunamin tafi kowa iya rashin kunya, amma to yaya zanyi dole naje na tambyeta, ko yasanar da ita inda yaje.

"Saida na bari k'afa ya ďauke snn naje har bakin k'ofar ďakinta gani k'ofar a rufe yasa na kwan-kwasa mata, duk da nasan tana jina ta kyale amma besa nai fushi ba, haka naci gaba da kwan-kwasawa, da k'yar ta tashi ta buďe k'ofar gani nice tsaye shegiyar yarinyar nan wani irin kallon banza ta bini dashi haďi da tambaya lafiya kuwa? mutum na cikin baccinsa daďi-daďi anwani zo kawai an katsemin.

"Sbd mmki hannu nasa na kama ha6ata ina mmki halin irin na Safiya, yarinya da kowa yai shedarta a garin nan.

"Jiki a sanyaye nace dama tun safe da maigidanki ya fita ban sake gani shigowarsa bane nace bari nazo na tambayeki ko lfy?.

"Da shike yar banza ce, babu abinda ya fito bakin Safiya sai" dama ta daďe da sanin ina sa masu ido, banji daďin kalmar ba amma yaya zanyi?,nasan ina ďaga murya su Saro da bayi zasuji, dole yasa na sausauta muryata na koma kamar me tsoronta.

"Yanzu Safiya nice kike faďi wa haka?nicefa uwarmijinki...

"A'a wlhy ke ba uwar mijina bane, kece dai Zulk'a...

"Cikin zafin raina na daka mata tsawa da ke Safiya, inda uwarki jummai ce zakiyi mata haka..

" Ke Zulk'a, idan muna abu kada ki sake sayo sunar uwata wlhy idan ba haka ba saina yaĝe wa tsohuwa hadda...

"Duk Safiya na mgnr ne tana nunani da ďan yatsa, jin haka yasa ban sake tanka mata ba, juyawa nai na koma ďaki, zuciyata cike da k'una haďi da danasani haďa wnn auren.

"Iya ummai batafi minti biyu zuwa uku da barin k'ofar ďakin Safiya ba saida Yahuza ya shigo hannu rike da leda, lokacin Safiya na bakin k'ofa tsaye, duk da tagansa amma sannu bai haďasu ba bare ta kyauce masa a hanya.

"Da shike yariga da yasan halinta yasa bai biyeta ba, k'aik'aitawa yai ya rabe ya shige ciki.

"Itama da take tsaye komawa tai ciki kai tsaye gado ta haye tai kwanciyarta, ko sannu da zuwa batai masa ba.

" Yahuza bai damu ba, kafin ya xauna hannu yasa ya ďauko plate a cikin kwandon dake gefe snn yaje bakin gado ya zauna, buďe ledar yai ya ďauko kunshin tsiran daya siyo ya juye a plate ďin snn yace sauko kici nama.

"Yahuza yai mgn har sau uku snn tace" bazanci ba.

"Meyasa bazakici ba?.

"Ban sani ba.

"Tun daga lokacin bai sake mgn ba, zama yai yaci kayansa, bai tashi ba saida ya cika cikinsa fal snn ya mike yaje ya rufe k'ofa yazo ya haye gado yai kwanciyarsa.

" Ko kafin yazo kwanciya har bcc ya ďauki Safiya, da shike batada wiyan bcc snn kuma idan ta fara tanada nawin bcc sai kai duk abinda kaga dama da'ita bata sani ba.

"Gani bcc yariga ya ďauketa yasa Yahuza zura hannunsa kirjinta yana shafewa, ya jima yana haka firgigi ta falka,shi kuma lokacin yariga da yai nisa, wank irin wawar mara ta watsa masa wanda shi kansa saida yaji wani iri.

" Amma da shike akan network yake bai fushi ba,"Ita kuwa hannu tasa ta igijesa ya faďi snn ta mike da sauri".

"Hannu yasa yana kokarin jawota da tadawo gadon haďi da bata hkri.

" Ko a jikin Safiya, gani yana nema yai mata ta k'arfi nan ta kamasa da kakawa haďi da zaginsa, daga shi har uwarsa Safiya bata ragawa ba, duk da Yahuza najin duk zagin da Safiya ke masa amma baisa yai fushi ba, sai faman bata hakuri yakeyi.

"Ashe duk abinda sukeyi a kunni iya ummai, tayi bakin ciki ba ďan kaďan ba, musamman irin zagin da Safiya ke masa.

" Shiko shugaba tunda ya mike tsaye kamar one yaki sauki, yi yake kamar zai dasa wando ya fito.

"Tun Yahuza na kokuwar wasa har ya koma ta gaske, duk yadda yake tunani Safiya tafi da haka, dole yasa ya k'yaleta,dukkansu gaba ďayansu kayan dake jikinsu ya yayyage, kan kujerar dake gefe yaje ya kwanta, rum da ciki hannu yasa ya kamo baban daďin yasa cikin matsematsin cinyarsa ya matse ko zausamu ya kwanta, ita kuwa Safiya kin kwanciyar tai, sbd kada yasake faďo mata.

"Da haka har safiya tai, bayan Yahuza ya dawo daga sallar asuba yaje ďakin iya ummai gaidata kamar yadda ya saba, sallamarsa kawai ta amsa, bata amsa masa gaisuwa ba, nan taha'u zaginsa harda ce masa mara zuciya, ita bata ta6a tsammani haka daga garesa ba.

"Duk iya ummai na mgnr ne ba tare da Yahuza ya fahimci abinda take nufi ba, shiru yai saida ta k'are tata snn yace" iya!! duk mgnr da kikeyi nafa ban fahimta ba....

"Cikin masifa da bala'i ta taresa da kace haka nama, ai dama nasan bazaka ta6a fahimtata ba, to ba akan kowa nake mgn illa shegiyar matarka bara kunya bara mutunci, wacce tai gaďon rashin kunya da mutunci a gun uwarta..

" Uhmm iya kenan, halin wani laifine tai maki?.

"Jin haka yasa ta fara zanzare masa abinda tajiyo jiya da dare," Yahuza bai ji daďi ba sam amma yaya zaiyi dole hkri zaiyi da'ita.

"Wato dama la6e kenan iya keyi masu ďan taji abinda suke ciki ko? lallai ma iya ďannan.

"Hakuri kawai ya bata haďi da cewa insha Allahu zai ďauki mataki, yana fita lekawa yai ya gaida bayi da Saro snn ya karisa ďakin malam, shima ba ciki ya shiga ba, a bakin k'ofa ta tsaya suka gaisa sbd ba wani ďasawa sukeyi da malam ďin sosai ba.

"Ita kuwa iya ummai tun daga lokacin ta kara ďabbaran k'ara tsanar Safiya, yanzu a gabon uban kowa mgn take, sai dai idan Safiya bata fito tsakar gida ba, zagi dacin mutunci jummai mmn Safiyar kenan babu irin wanda iya ummai batayi.

"Idan Safiya zata rama su Saro da bayi ke hanata, da shike tanajin mgnrsu saita fasa, yau kuwa da abu ya isheta iya ummai na farawa Safiya ta ďauki kyaletan taje ta sanarwa mmnta, itama jummai ta shike duk irinsu ďaya, taso Safiya tai a gaba suka zo gidan, dai-dai lokacin iya ummai nawa jummai zanzara' haba wa itama jummai ta kama tace idan bakayi kabani gu.

"Harda ďabbara saida jummai tai a dole zatai ďanbe da iya ummai.

"Bayi ce keta rabo, itama iya ummai ta shike taga masifar da tafi tata, bataja faďar sosai ba, dak'ar bayi ta shawo kan jummai ta hkra, har zata fita daga gidan sai kuma ta dawo, gaban iya ummai taja ta tsaya snn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login