Showing 15001 words to 18000 words out of 29796 words

Chapter 6 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt

29 Oct 2025

425

mgnr cikin dake jikin karime harda kukata nace karya takeyi batada komai, idan har da gske takeyi to meya kawo jini zananta.

"Gani yadda na hakikice harda rantse-rantse na yasa jikin karime sanyi, duk da batabar faďan ba amma ba kamar da farko ba.

" Malam yace, tunda haka nace to me nene shedata?.

"Gani ga jini a bayan zaninta, snn kuma kwanaki har ďaki ta bini take sanar dani, ita bata aureka domin ta haihu dakai ba, domin gidan tsohon mijinta takeson komawa,dan haka bazata sake tayi ciki da kai ka.

"Nan take jikin karime ya hau rawa, tana faďin nice zakiyi wa sharrin zulka? yanzu makircinki har yakai ga haka?.

" Abinda da me baki, harshena yafi na uban kowa a gu, kan malam ya ďaure yakasa gane waye mai gsky a cikinmu.

"Gani haka yasa nace idan kokonto yakeyi to aje asibiti a gwada a gani,amma kada aje asibitin da akaje da farko domin baya faďin gsky.

"Jikin karime yai sanyi da mgn ta, malam Harisu yace to yaji amma yanzu yamma yai a bari gobe aje, kuma wlhy baya kaffara, a wnn karon babu sausauci idan har aka kuma irin ta kwanaki saiya ďauko mummunar hukunci a kan kowaye, da sairu nace na amince sbd tasan nice da gaskiya.

"Hankalin karime ya tashi ainu, jikinta har rawa yakeyi, kallo ďaya nayi mata na gano haka, shi kuwa malam Harisu yana gama mgnrsa ya fice daga gidan.

" Malam Harisu na fita nayi ďakina, murna a guna kamar na zuba ruwa a kasa nasha, "A ban garen karime kuwa komawa tai ta zauna, sai faman sake-sake takeyi, wata zuciya na cewa jeki ki samu zulka ku daidaita a fasa mgnr zuwa asitibi, wata zuciya kuma tace kaďa kije, washe gari da safe har malam Harisu ya fita da zance ya shirya zuwa unguwa gani har goma yayi malam beyi mgn ba, mikewa nai naje har ďakinsa na samesa nai masa tuni,bayan na kare mgn har na juya zan fita da sauri malam Harisu ya kira sunata da zulka.

"Na'am malam.

" Wai meyasa kika nace da wnn mgnr ne?ni dai inda zakiji tawa abar mgnr kawai shi ciki dumane baya boyuwa, idan har da gske karime nada ciki zai fito zuwa wani lkc....

"Da sauri na taresa da a'a malam wlhy Allah karya takeyi batada komai, shi isa ma nace aje asibiti a gwada a gani idan karyan nakeyi.

" To naji gaskiya kika faďa amma mgnr zuwa asibiti a barsa kawai".

"A'a nidai nafiso aje kawai sai dai idan ba bayawa karya baya zakai ba...

" Kamar yaya?.

"Nan nasa masa kuka ina faďi duk abinda zangani na fito na faďi kullum baka yarda, sai ka karyatani, kace ba gaskiya bane, bayan har ďaki ta biyoni take faďi min cewa batada komai domin bata aureka ďan ta haihu ba, shi isa bazata yarda tai ciki d'akai ba, kuma tace idan har nasake na faďi maka sai tai sanadiyar da zaka sakeni shi isa nabar mgnr a cikina ban faďi wa kowa ba.

"Duk mgnr da nakeyi ido malam Harisu ya zuba min, irin kallon ďa yakemin ya isa na gane cewa be yarda da mgnta ba, amma duk da haka besa nayi shiru ba.

"Sai da na gama mgnta snn malam Harisu ya kara matsowa kusa dani, snn yace zulka!!.

"Cikin kuka nace na'am.

"Abinda kike tunani ba haka bane zulka, ke yarinyace ba lalla bane ki hango abinda nake hanga maki, karime ba yarinya bace, shi isa nakeso ki bar mgnr kawai zaifi, amma idan kikaga tafiya asibitin yafi, ni tawa mai saukine.

" Amma inaso ki sani,idan har aka kuma irin ta kwanaki wlhy bazan sausauta baku ba,daga ke har ita, tunda kince ke bamaijin mgnta bace, ina kokarin fitar dake daga shirrin karime amma ke baki gani, tunda kin natse shikenan, zamuje amma wlhy idan aka kuma, a bakin aurenki,....

"Da sauri na am'asa da eh, na amince.

"Cikin jin daďi na mike na fice daga ďakin malam Harisu, ina fita mukai karo da karime ashe duk mgnr da mukeyi tana make tana jinmu.

" A zuciyata nace oho dai, tunda ya amince zasuje.

"Malam na fita ďaga ďakinsa ya kwaďawa karime kira haďi da cewa fito muje.

"Duk da ta amsa amma ta jima snn ta fito suka fita, kallo ďaya zakai mata ka gano a sanyaye take tafiya, niko da nake ďaki ina kallonsu nace adai je, shegiya kawai.

" Yau dai karken tika-tika tif.

"Suna fita karime ta nufi hanyar asibitin dake garinmu, da sauri malam Harisu yace a'a banan zamu ba, asibitin dake makwamtan garinmu suka je.

"Masan ba sbd mgnta bane malam Harisu ya ďauki karime zuwa asibiti,Sbd shima akwai abinda yake tunanine.

"Suna isa tare suka shiga ďakin likitan,gwajin farko aka gano tana ďauke da ciki na wata ďaya, a kididigan likita ma bai gama cika wata ďayan ba.

" malam Harisu yai matukar mmki,amma be nunawa likita komai ba, godiya yai masa sukai sallama.

"Suna shiga kowa ďakinsa ya nufa' dama tun akan hanya karime ke sake saken irin karyan da zatai wa malam, snn wani abu da yake ďaure mata kai shine cikin dake jikinta'wanda ita kanta batasan dashi ba'to wai ma yaushe tasamu cikin ne da'ita kanta wanda take ďauke dashi bata sani ba.

"Idan har kuwa mgni likita ya kasance gaskiya duk dik ďinta ta rushe kenan.

" Kashhhhhh amma banso haka ba, yanzu yaya zanyi da alkawarin da naiwa iro?kodai na sha magani na zubar ne?to idan nai haka ban kashe rai ba,snn kuma Allah bazai kamani da laifi ba?tunda cikin halasne ba shege ba, kai gaskiya bazan zubar ba, sbd ban san baiwar da Allah yai mata ko yai masa ba.


"Dole hakuri zanyi na rungumi cikin haka,amma yanzu abinda zanyi shine naje na shirya wa malam karya sbd nasan yanzu yana nan yana juyayin al'amarin'sbd karyan da nai masa a baya.

" Da sauri ta mike zuwa ďakin malam'da sallama ta shiga haďi da faďin sannu da gajiyar hanya.

"Babu yabo babu fallasa ya amsa mata,nida nake zaune a ďakin dama tun lkcn da suka shigo gabata tai mummunar faďuwa take hankalina ya tashi, cikina ya'hau kuki a guje na ďauki buta zuwa ban ďaki.

"Na jima ina ďuke akan salga amma babu abinda ya fito'duk da haka besa na mike ba, amma jin muryan karime a ďakin malam yasani mikewa na fita daga ban ďakin'ba tare dana ije buta ba naje na lebe domin naji mgnr da zasuyi.

"Nan najiyo karime na sake faďawa malam wani karya, wai dan Allah yai hkr domin akwai abinda ta boye masa'ita dama idan tasamu ciki haka yake mata wanj sa'in ma nunawa yake babu komai a cikin tata al'halin ita tasan tana'dashi, ko wnn ma ba wata ďaya bane a yadda take lissafi zaikai wata uku zuwa huďu amma kaga yadda ďan sharri sai ya nuna wata ďaya'karime ta karisa mgnr ne haďu da kuka tana faďi nidai wlhy na rasa yadda zanyi da raina domin ba'tun yanzu ba haka yake kasancewa dani, aduk lokacin dana sani ciki sai haka ya kasance, ni bansan yadda zanyi da rayuwata ba.

"Gani irin kuka da takeyi yasa malam Harisu fara rarrashinta haďi da bata mgn mai sanyaya zuciya" Saida ta numfasa snn yake tambayarta tun yaushe ya fara yi mata haka?.

"Tun inada cikin fari.

"A lokacin da ciwon ya sameki magani asibiti kika sha kota gida?.

"A'a ta gida ne?.

" To kada ki dame'tunda abin ya zama haka'daga yau ta asibiti zaki koma amfani dashi har Allah ya saukeki lafiya"Zuwa gobe ko jibi akwai wani kuďin da nakesa rai za'a kawomin in sha Allah sukazo hannu zanbaki ki koma asibitin.

"Inajin bakar manafukan tace to babu damuwa" nida nake make ina jinsu, idan banda kwalla babu abinda nakeyi.

"Sann karime taci gaba da cewa babu damuwa malam nasan kai mai al'kawari kacika ne, domin yasa haka ba face sani girma da darajan al'kawarin ba komai yasa haka ba illa tsoron Allah dan haka nake tunasar dakai duk abinda kai al'kawari akai yanada'kyau kayi kokarin cikawa duk da dai nasan kai me kokari ne.

" Inajin haka nace auzu'billahi minal'shaďeni rajin, laqal'jaa'akum akan karime, Allah ka shiga tsakanina da shegiya mai neman gani bayata.

"Duk inayi ne ina kwalla haďi da rokon Allah kada yasa malam Harisu ya fahimci abinda karime ke nufi.

" Inajin malam ya mike da sauri nabar gun na koma ďaki na'malam yana fitowa kai tsaye ďakina ya nufa'inajin shigowarsa ban san lokacin dana fashe da kuka ba ina faďin na shiga uku na lalace dan Allah malam kayi hkri ka rufemin asiri wlhy Allah daga yau bazan karaba, take na zube a gabanta ina bashi hkr.

"Ba tare da malam ya kalleni ba yace zulka tun kafin hakan ya kasance saida na faďi maki idan har aka sake memeta irin abinda ya faru a baya saina ďauki hukunci akan ko waye kikace kin amince dan haka kije na sakeki saki ďaya"....take na kwarrrrrrma ihu ina faďin na shiga uku na lalace wayyooooo Allah na, idan Allah dan annabi malam kayi hkri kajanye wnn sakin.

" Duk kukan da nakeyi ko'a jikin malam juyawa yai ya fice daga ďakina, bayi dake ďakinta tanajin duk abinda muke ciki nida malam'malam na fita ta shigo ido da kwalla taba bani mgn tana kwalla'batafi minti goma da shigowa ba saiga karime itama ta shigo kona saurareta balle nasan da shigowarta sbd nasan halinta sarai' buďe bakin bakin karime tace"to makira manafuka yau reshi ta juye da mujiya bakar alguguma ta Allah ba taki ba dan haka a yau ďinnan zakibar gidan nan domin yanzu ya haramta da kizauna a cikinta.

"Dan haka tashi zakiyi ki bar mana gidan.

"Karime na mgnr ne tana haďomin kaya nata watsemin a jiki, duk da masifata da rashin kunya amma a yau saida jikina yai sanyi'domin bata kanta nakeyi ba ta "ya"yana da zan tafi na barsu nakeyi.

"Gani banida wata mafita dole yasa na mike na haďa kayana a ďankwali, tun kafin na kare haďawa sai mashin yai sallama" wai malam ne ya turosa akwai wacce zai kaita garinsu'naso ďayan Yahuza da Husaina amma nasan koda nace zan ďaukesu malam ba yarda zaiyi ba, dole yasani tafiya na barsu a gidan, dan ma Allah ya raimakeni basu gida a lkcn.

"Bayan tafiyata karime da kanta ta kwashi su Yahuza suka koma hannunta'shi kuma malam ba karami kuďi yake kashewa karime ba,wai ta ringa zuwa asibiti ko Allah zaisa adace.

_WACECE KARIME?_

_"Karime yar'asalin garin *rub*_ _ne wato garin su malam Harisu kenan tayi aurenta na farko a cikin garin ne, yaranta biyar maza biyu mata uku suyi zama da mijinta mai suna alhj audu'alhj audu mutum ne mai rufan asiri a kauyan.Suna zamane ta amana da yarda babu mejin tsakaninsu_ _kwatsem sheďan ya ratse tsakaninsu babu faďa suka tabu.tun daga lkcn taci alwashin saita goma gidan mijinta, duk da yanzu yanada wata matan._

" Bayan wata ďaya da barina gidan malam Harisu naji labarin ya siye mashin'hakan yasa na shirya batare da sani iyayena ba nayi hayan wasu samari duk yadda za'ayi suje gidan malam Harisu su nuna kamar mashin ďin sukazo ďaukewa snn kuma idan har suka bari aka kamasu babu ruwata".

Amma idan hakan ta faru suce karime ce ta aikesu' nan mukai tsaďance na biyasu.

"Nan muka rabu akan yau da dare zasu.....









*dan Allah kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu, wlhy wasu uzuruzuka ne suka shamin kai, sannan kuma ga maganar exam daya zo mana baga datan, ba tare da musan da zuwansa ba, dan haka nake kara baku hakuri na sake jina shiru da zakuji na wani lokaci amma insha Allah muna kammalawa zaku jini da yardan mai mana ruwa da iska. Ngd sosae da soyayyarku a gareni*










*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥


_*FITSARIN FAK'O*_

💥💥💥

_(mugunta)_

*FASAHA ONLINE WRITERS*

_F.O.W_

_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_


🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹



بسم اللة الرحمن الرحيم


*∅∅∅*📝
*page14*


............."Misalin sha biyun dare lokacin kowa ya kwanta' mutane da iya Ummai ta turosu suka shigo ashe lokacin malam Harisu bai daďe da fitowa daga ban ďaki ba, jin tafiyar mutane ne yasa shi samu lungu ya boye, duk abinda suke akan idansa ba tare da susani ba.

"Kai tsaye gun mashi suka nufa, gani a kulle yake da key yasasu cici6awa sukai sama dashi zuwa zaure, babu yadda basuyi da sufitar da mashin ďin ta kofa ba amma su kasa hakan yasa sukaje ta katanga suna k'ok'arin turawa ta sama"

"Malam Harisu dake ra6e yana kallensu murmushi kawai yai,sbd yasan babu inda mashin ďinsa zai tafi,domin yariga dayai kafi a gidansa.

"Suyi iya yinsu amma abu ya gagara' hakan yasa ďaya daga cikinsu ya haura saman katangan shi kuma ďayan dayake kasa shine zai turo sai wnda yake sama ya kama.

" Tun dare suke abu ďaya amma abu ya gagara' duk su biyun zufa ya jikesu kamar wanda suka wanka.

"Saida malam Harisu yai ra'ayi dan kansa snn yaje kusa dasu'tsawa kawai ya daka masu snn suka samu natsuwa, nasama ya sauko kasa,snn suka mata mashin ďin suka tsaidashi, " Malam Harisu yace dana ina kuke?.

"Muzo satan mashi ne.
"Sata fa kukace?.
"Eh, sata.
"Saku akayi ko kune kukasa kanku?.

" Duk su biyun suka bashi amsa dasa my aka.

"waye ya saku?.
"Har ďayan zai furta sunana da sauri ďayan yace karime ce tasamu.

"Karime fa kukace?.
" eh itace wlhy.

"Sani halin kauye da ďaukar mgn ayita yawo dashi yasa malam Harisu sallamarsu, ba tare daya ja mgnr ba, amma tun daga lokacin karime taga canji.

"Ita kanta tai mamakin yadda malam Harisu ya canza mata haka, hakan yasa batai kasa a guiwa ba, ta bisa har ďaki ta tambayesa dalili canza mata haka.

" Babu komai kawai yace mata.

"Niko da nake garinmu, ba karami daďi naji ba dajin wnn labarin, hakan yasa na sake amfani da damar dana samu, na sake ďauko hayar wasu, kar'fafan samari maza uku, na basu kuďi mai yawa snn nace idan aiki yai kyau zan kara masu."da suje garin su malam Harisu su bisa har gona su nuna masa zahiri kashesa aka turosu suyi,amma ganisa da sukai yasa tausayinsa ya kamasu, ďan haka yanzu su fasa".

" Nasan zaiso jin waye ne ya turesu?.

"Suce karime ce, kunga daga nan zai karajin ya tsaneta koma ya saketa, idan har yaja mgn zuwa kotu, bana shakka sbd al'kalin mutumina ne.

" duk yadda na shirya masu haka suka aikata, inda na gode wa Allah malam Harisu beja mgnr ba, saima godiya da yai masu.


"Jikinsa har rawa yakeyi, be tsaya ya kammala aikin da yakeyi ba, ya koma gida, yana shiga, da sauri karime ta mike haďi da faďin sannu da zuwa malam.

"Cikin tsawa ya dakatar da'ita, haďi da faďin Allah ya'isa tsakanina dake muguwa azaluma to ta Allah bataki ba, wanda kika aika su kasheni Allah be basu iko ba.

"Duk mgnr da malam Harisu keyi karime bata fahimta ba," Shiko yaci gaba da cewa Allah ya'isa kuma wlhy a yau zaki barmin gidana dan haka kije na sakeki saki uku....

"Duk da dama abinda take nema kenan amma batai tsammani samusa a wannan lokacin ba, hakan yasa ta ďora hannu akah tana kuka da ihu na shiga uku na lalace.

" Malam Harisu yana faďi yafice abinsa.

"Bayi dake ďaki, duk jikinta yai sanyi.

"A ranar karime tabar gidan malam Harisu,tun daga lokacin nake shiga da fita gun malamai da bokaye wajan gani na koma gidan malam Harisu.

" Kwatsam ranar wata kasuwar garinmu saiga malam Harisu yazo shiga abokinsa mai suna malam Habu, a k'ofar suro suka tsaya, babana ne ya fita suka gaisa snn malam Habu yake bawa babana hkr bisa abubuwan da sukai ta faruwa,snn kuma yai masa alkawarin idan har ya barni na koma hakan bazai sake faruwa ba.

"Koda babana ya tambayeni inada sha'awar komawa?.

" nace eh, cikin satin ya kawo kuďin sadaki aka meda mana aure, amma nace sai wani sati zanbtare.

"Duk da malam Harisu beso haka ba amma yaya zaiyi dole ya hakura.

"Koda babana ya siyemin kayan gara,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login