Showing 6001 words to 9000 words out of 29796 words
Chapter 3 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt
banji daďi ba, domin a tawa tunanin ta tafi kenan, ashe ba haka bane.
"A lkcn yaso na dawo ďakina amma iyayena suka haka, wai nayi hkri na karisa wanka, tunda kwanaki kaďan ne suka rage, dole yasa na hkra amma baďan nasi hakan ba.
"Tunda mary ta dawo gidan zama ya canza ba irin wanda sukai a baya ba, domin kuwa yanzu mary tasaki jiki da bayi sosae musamman ma idan tai la'akari da irin zamansu na ďah, snn kuma gashi tunda tabar gidan Suwaiba ke hannunta idan abinda aljani ya faďi gskya ne da suwaiba batakai wnn lkcn ba........
///don't 4get cmmnt.
and
vote///
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page5*
............"Ranar Allah kaďai yasa irin murnan da nai, bayan addu'ar uku malam Harisu da kansa yaje kwatankwaro ya smso Suwaiba ya bawa bayi, banso haka ba, domin nice naso abawa Suwaiba, ba bayi ba, amma duk da haka be baci ba.
"Bayan wata biyu na sake samu wani cikin, daga lkcn dana fahimci hakan wani sabon kisisina ya tashi,da shike wnn cikin bamai laulayi bane, amma a duk lkcn da malam ke gida, haka zan dunga kirkiran abu iri-iri, koda banajin amai amma da karfin tsiya zan kakaro, bayan na gama na kwanta na kama nishi ina kukan cikina na ciwo ni bszan iya aikin komai ba.
"Gani haka yasa malam Harisu ya saukemin girki sai dai adafa naci na kwance, duk a lkcn mary na gidansu, ko mgnrta malam Harisu bayayi musamman ma yanzu dana samu wani cikin, aikin gida yai wa bayi yawa, ďan ma akwai masu kawo mana ruwa, shara wanke-wanke abinci duk itace keyi.
"Hakan yasa duk tabi tai jugu-jugu,niko sai dai naci biyar na wanke goma.
"Cikina na wata shidda, ina kwance a ďaki bayan la'asar, bayi na bakin murhu tana shara domin ďora abincin yamma, duk abinda takeyi idona na kanta, tana cikin sharan kenan kawai amai ya kamata, hurgi tai da tsintsiyar dake rike a hannunta ta sura a guje ban ďaki.
"Nima da nake kwance a guje na fito domin shedawa idona gsky, a zuciyata kuwa tambyr kaina nakeyi, badai cikine bayi ta samuba? " To idan ba ciki bane menene zai sata amai haka".
"Tunda nake da'ita ban taba gani tayi ciwo ba, balle nace ko masassara ne ya kamata," amma komai menene zan gani".
"In har kuma cikine, to wlhy bata isa ta haifeshi ba, domin babu wanda ya'isa ya haihu da malam Harisu in har ina gidan nan.
_" To fa masu karatu, kuji fa dan Allah, idan har Iya Ummai ta faďi haka ita kuma mary tace mai?ita da take uwar gida, sann kuma ina Iya Ummai zatakai Suwaiba da Muhammed? Muje zuwa dan jin yadda zata kaya._
"Jin motsin bayi na fitowa daga ban ďakin da sauri na koma cikin tawa ďakin na kwance, ďan ma kada ta gano naji abinda takeyi.
"Har ta koma bakim murhu domin ci gaba da aikinta ta gagara,domin a yadda nake hangota da alama jira take gani, kawai dai sai naga ta duka ta ďauki Suwaiba dake wasa a bikin murhun suka koma ďaki, mikewa na sakeyi naje na lekota domin gano abinda takeyi a ďakin, sai kawai na hangota ta kwance haďi da rufe jikinta da fallen zani Suwaiba kuma na zaune a gefenta tana wasa, a lkcn ne na tabbata da abinda nake hasashe ya tabbata.
"Tun daga lkcn nasha alwashin duk halin da zan shaga saina shiga domin raba bayi da wnn cikin.
"Da yamma bayan sallar isha lkcn malam Harisu ya shigo gida, duk da ina cikin kunci da bakin ciki haka na tarsa da fara'ata sbd kada ya gane halin da nake ciki.
"Bayan na amshi ledar dake hannunsa nake na ďibo masa ruwa yasha, bayan ya sha, ni kuma ina zaune a gefensa, bayan ya shane nake sanar dashi yaya bayi batajin daďi..
"Da sauri yace subhallh meya sameta?.
" Nima ban sani ba,amma tunda kafita take ta amai.
"Jin haka yasa malam Harisu mikewa, nima da nake zaune na mike yana gaba ina biye dashi a baya muka nufi ďakin, da sallama muka shiga,duk a lkcn bcc takeyi itama Suwaiba dana barta zaune tayi bcc, hannu nasa na ďan bibigeta haďi da kiran sunanta, snn ta buďe ido ba tare data amsa ba.
"Nice yaya jikin yaya?.
"Malam Harisu dake tsaye ya zauna a gefe kusa da kafarta haďi da tambyrta abinda ke damuta.
"Bata kawo tunanin ciki bane yasa tace masassara ne ya kamata.
" Allah ya sauwake yace gaďi da mikewa, nima na mike,bayan mubar ďakin, gani yanada niyyar fita yasa na taresa da sauri ina zaka kuma malam?.
"Magani zan siyo mata.
"A'a malam in da zakaji tawa shawarar, kada tasha kowani magani, tayi hkri har zuwa gobe sai a tafi asitibi da'ita, kasan ko wancan sati da yan kiwon lafiya sukazo sun kara jadada mana idan masassara ya kamamu mu daina ďaukar kowani irin magani munasha muje asitibi likita ya dubamu maganin daya rubuta mana dashi zamuyi amfani.
" Eh kuma haka ne, mgnrki gaskiya ne,"to bari mugani zuwa goben".
"Nayi haka ne domin akaita asitibi na kara tabbatar wa kaina, snn nasan matakin da zan dauka a kan.
*mmn uswan ce📚*✍
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page8*
.............."Tunda na fara tafiya ban tsaya ba saida nakai bakin fita gari snn na tsaya, juyawa nai na dubi gabas da yamma kudu da arewa naga babu mai zuwa, snn na karisa inda karnunka suke taruwa da aladu da mai dai sauran ďabbobi snn naje gun juya ladar nayi na zazaje ya faďi a kasa, ban bar gun ba saida naga suzo su rufe mahaifar snn nai hurgi da ladar haďi da alhamdullh, snn na juya zuwa gida.
"Banbi hanyar nadabi naje ba,canza hanya nai sbd banda kama.
"Cikin sa'a har na isa gida na shige ďaki babu wacce ta ganni, sbd a lkcn duk suna ďakin bayi suna hira, shima kansa malam Harisu bai dawo ba, hakan ya bani damar shigewa ďaki ba tare da wani ya ganni ba.
"Tun daga lkcn nake sa ido domin gani abinda zai biyo baya,amma naji shiru, ni kenan har safe banyi bcc ba, asalatun fari na buďe kofa,sanyokai da zanyi kawai mukai karo da bayi tafito daga ban ďaki.
"Da sauri na meda kaina ďaki haďi ta faďi auzubillahi minalsheďanin rajin, ni kaina bansan lkcn da wnn kalman ya fito daga bakina ba.
"Sbd bakin ciki ban fito ba, gu na samu na zauna, sallar da banyisa ba kenan har saida rana ya fito, snn nayi.
"Tun daga lkcn nake na baza kunni domin ji abinda zai biyo baya amma shiru, har ranar suna.
" Yarinya taci suna *ĎABSIYA* nayi mmki sosae, domin ban taba zaton bayi nada gata ba sai yau, musamman ma garan da iyayenta suka kawo mata, tun daga kan zannuwa har zuwa hatse.
"Jama'a kuwa kusan na iya cewa gaba ďaya yan'garinsu ne sukazo, sbd yawan jama'a gidan mu bai ďaukesu ba,saida aka haďa da makwabta.
"Niko sbd bakin ciki ko wanka banyi ba, snn kuma ban sanar wa kowa daga cikin ďangina ba, ita kuwa mary harda gayyata saida tai, niko nace ba uban da zan gayyata, kowa yai wanka yai kwalliyarsa amma banda ni, tun jama'ar da muke tare dasu a ďakina basui mgn har saida sukai min mgnr wankan.
"Kawai karya nayi masu nace banida lafiya,sauran dake ďakin sukai min Allah shi kyauta, ko sun ganoni ne oho, ďaya daga cikinsu ce tace naje nayi snn zanji daďin jikina snn sai nasha magani.
"Haka dai naje nayi baďan naso ba, bayan wata buyu mary ta samu ciki, ranar dana sani ba karamin bakin ciki nayi ba, gani bazan iya jurewa ba, yasa na tambayi malam Harisu zuwa gida garinmu amma yaki, ban musa masa ba, na koma ďaki kwanciya nayi akan gadon Yahuza ina nazarin yaya zanji.
"Nafi minti ashirin ina tunanin, can na tuno da wani malam da naji wasu suke labarinsa ranar da naje suna, da sauri na tashi zaune ina faďin yawwa, kawai nan ďin zani, amma wani irin karya ne zanyi wa malam Harisu da zai barni naje.
" Take wani basiran yazo min, bayan sallar isha har ďaki na bisa bayan na gaishesa cikin girmamawa kamar yadda na saba, snn nake sanar dashi gobe inaso zanje gaida kanwar mmnta, sbd tunda nayi haihuwar fari tazo suna nayi mata alkawarin zuwa na gaida ta, shine banje ba, gashi har na sake wani haihu kuma batai fushi ba tazo suna.
"Gani malam Harisu bashida niyyar yarda kuka nasa masa, gani haka yace ya amince amma shi baida kuďi.
" Da sauri nace babu damuwa, ni inada shi.
"Washe gari na ďauki buhun gyaďe ta da nace ijewa idan damina yazo na bayar rance idan aka noma bayan an kwashe a medamin da buhu biyu, na kai wa alhj iro, na saida masa, dama duk garin idan har wata matsala ta taso maka, in har kanada ijiyar hatse ka ďauka kakai masa take yake biyanka, amma idan a kasuwa ana siyarwa dubu biyu ne to dakar zai siye dubu ďaya.
"Haka na siyar masa,sbd biyan bukata yafi dogon buri, washe gari nayi sallama na kami hanya, duk ban taba zuwa garin ba,amma banji na karaya da rafiyar ba.
"Da kar na samu mashin ďin da zai kaina garin,muyi tafiya mai tsayi wanda ban taba tsammanin haka ba,
gani tafiya yaki karewa yasa na fara tsota, kodai shima besan gurin bane,ah'ah tun banyi mgn ba har yakai ga saida nayi masa mgn, wai kai har yanzu bamu kai garin bane?.
"Yana jina yai banza dani, saida na sake mgn snn yace, ai ko rabi bamuyi ba, snn kuma na mance ban sanar dake ba, akwai rafi da za'a tsallaka kafin a garisa garin,ni kuma bana tsallaka rafi.
"Take naji anji cikina ya kaďa, sbd nima bana tsallakar ruwa.
"Cikin rawar murya nace to yaya za'ayi kenan, wlhy nima bana tsallaka rafi.
" To kodai juyawa zamuyi?.
"Da sauri nace a'a, muje dai, a cikin zuciyata kuma nace, duk wnn uban tafiyar da mukai shine zan koma da baya batare da na cinma burina ba?ai abinda bazai wuyu ba kenan, gwamma naje duk abinda za'ayi ma sai dai ayi.......
///don't 4get cmmnt
and
vote///
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page7*
............"Shi isa ta saki komai, suka ci gaba da zaman lafiya babu mai jin tsakaninsu,.
"Inayin arba'in da kwana biyu na dawo gida,gani yadda suka haďa kai har ma zan iya cewa shakuwarsu tafi ta ďah.
"Hankalina ya tashi gaba ďaya na kasa sukuni, duk abinda sukeyi idona na kai, sbd kuruciya da kuma kishi irin tamu ta mata, idona ya rufe, idan ba haka ba, hausawa suce duk wanda yaso maka naka ya gama maka komai, idan nayi duba da kuma la'akari da irin ďawainiyar da bayi tai da Suwaiba, a rayuwa komai mary taiwa bayi bata biyata ba,amma na kasa gane haka.
"Shiko malam Harisu ba karami daďi yaji ba, gani yadda iyalansa suka haďa kai, a bawa ban garen kuwa ba haka naso ba.
"Kaf-kafa nakeyi da Yahuza bana yarda na bawa kowa shi, sbd kada suzo su kashe min shi, koda ban ďaki zani dashi nake zuwa.
"Suko ko a jikinsu domin basuma san inayi ba, bayan watanni da dawowa ta gida,ranar wata laraba bayan sallar nakuda ya kama bayi, da shike batasan kai ba, nan take ta kira mary, domin ta taimaka mata.
"Niko dama tunda naga cikinta ya tsofa, dazaran najisu shiru zuwa nake na makale na lekesu, idan naga ba nakuda bane saina koma.
"Haka yau ina ciki sallar magrib har nakai sujuda jin kiran da bayi taiwa mary yasani yanke sallar danakeyi, mary na shiga ďakin bayi nima na fito daga nawa ďakin.
"Ta window nake lekansu duk abinda sukeyi, batare dasu gani ba.
"Da haka har saida akayi sallar isha bayi bata haihu ba, jin tafiyar malam Harisu alamar yana shigowa, da sauri na kauce daga gun, ďaki na koma na meda kyale na nayi kamar mai sallar gaske, saida ya shiga ďaki snn mary tazo ta sanar dashi hakin da ake ciki.
"Nan kare faďi ta fice daga ďakin,saida naga shigewarta ďakin bayi snn na ďauki Yahuza naje ďakin malam da sallama na shiga,dai-dai lkcn ya ďauki allo zaiyi mata rubutu, yasa ban jasa da wani hira ba zama kawai nayi, yanayi inawa Yahuza wasa.
"Bayan ya kammala ya mika min yace nakai masu, saida na mika masa Yahuza snn na fita daga ďakin.
"Da sauri yaje gu da muke wanke-wanke na zidda ruwan rubutun snn na ďauko tukuya na wanke bayan snn takai masu, haďi da cewa Allah ya sauketa lafiya.
"Mary dake zaune tana rike da'ita ta amsa da ameen.
"Ban tsaya ba, juyawa nayi na fita na koma ďakin malam Harisu, duk yadda naso ďauke masa gankali sbd ya mance dasu amma haka bai samu ba, domin bini-bini sai dai naji yace Allah ya sauketa lafiya.
"A fili nace amen, a zuciyata kuwa nace ba amin ba, dama ta mutu.
"Har asuba bayi nata haihu ba, hankalin malam Harisu ya tashi,domin dazaran yabawa mai nakuda irin wnn rubutun bazata gaza mintin biyar zuwa goma ba zata haihu,amma gashi akan bayi baiyi aiki ba.
"Amma bazaija da ikon Allah ba, mikewa yai yaje yai alwala yazo ya fara jere nafilfili yana roka mata sauri agun ubangiji.
" Ana sallar asuba ta haufi yarta mace, daga malam Harisu har mary sai faman murna suke amma bandani.
"Gani daga uwa har yarta dukkansu lafiyarsu qlau, yasa ni nimar hanyar da zai nakasasu.
" Da safe bayan malam Harisu yaje ya binne uwa( mahaifa) gani haka yasa wani tunani yazo min, mai zai hana naje na buďe ramin daya binne uwar na ďauke, na kaiwa kaje ko wani ďabba da zai iya ci.
"Wato kila kafin safe yar ta mace.
"Domin nashaji ana cewa ba'aso abar uwa idan aka haihu yakai wani lkc domin komai zai iya faruwa, shi isa nayi amfani da wnn mgnr dana faki idon jama'a naje na ciro uwar nasamu leďa nasata a ciki na kulle saida na faki ido jama'a snn na fice daga gidan, da sauri nake tafiya sbd naje na dawo kafin malam Harisu ya shigo..........
///don't 4get cmmnt
and
vote///
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝