Showing 9001 words to 12000 words out of 29796 words

Chapter 4 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt

29 Oct 2025

418

*page9*


.............."Da haka mukai ta tafiya bamu tsaya ba saida muka kai bakin kogin.

"Babu yadda banyi dashi akan ya taimaka min ya tsalakar dani ba, yace atafau shifa bazai shiga ruwa va,asalima idan karfe taji ruwa mutuwa takeyi, shi kuma sbd ďan kalilan kuďin da zanbashi bazaisa mashin ďinsa a ruwa ba.

"Nasan ya faďi haka ne kawai ďan bazai taimaka min ba.

"Sa kai yafi bauta, kwashe zanina saida nasa kafa ďaya ďan jin zurfin ruwan snn na kwashe zanina snn na fara tafiya, jikina har rawa yakeyi, da haka har na tsallaka snn na karisa cikin garin.

"Da tambya har na gane gida mutumi da shike gari ba wani yawa ne dasu ba, shi isa ban wani wahala ba wajan niman gidan.


"Ina isa gidan matan mutumi suka tarbeni hannu bibiyu harda abinci suka bani,bayan nayi sallar ne sukami iso gunsa, bayan mu gaisa ta tsara masa karya da gskya na faďi masa, nan yai dube-dubensa snn yace idan bayi ce sai dai ta Allah amma bata mutum ba.

" To ita kuma mary fa?.
"Nan ya sake dubawa snn yace, abu ďaya za'ai mata ya kamata shine asanya mata tsanar gida, taji batason zaman gidan.

"Itama bayi abu ďaya za'ai mata shine za'a medata kamar wacce batasan ciwon kanta ba.

"Da sauri nace eh duk haka za'ai masu, tun kafin ya faďi kuďi tuni na zuge pot na ciro kuďi na bashi.

"Godiya sosae mutumi yai haďi da cewa kafi ki isa kodai zai dai-daita.

"Nayi murna sosae dajin haka.

"Tun daga lkcn nake nake juya bayi son raina.

"Ita kuwa mary al'amuranta sai a hankali sbd idan tai wani abu har mmki nakeyi.

"Da haka har saida tabar gidan batare da malam Harisu ya saketa ba, ranar ba karami murna nayi ba da barin gidan da mary tai.

"Malam Harisu yai biko har ya gaji, amma taki amincewa ta dawo gidansa,gani haka yasa aka tara manya akan ta faďi laifi da yai mata da har tace bazata iya zaman aure dashi ba.

"Babu komai nidai auren ne banayi, da haka taro ya watse,dole yasa malam Harisu ya hakura da mary, bayan wata tara ta haifi ďanta na miji, malam Harisu yasawa yaro suna Aliyu Haidar.

"A lkcn na yaye Yahuza inada wani cikin, ita kuwa ďabsiya tana gudu ko'ina, duk a lkcn nike mulki a gidan, domin bana sanya bayi a lissafi, komai na malam Harisu sai yadda nai dashi, bayi naji na gani amma bazata iya mgn ba.

"Bayan na haihu yan'biyu duk maza amma ďaya ya koma, nasa malam Harisu yaje ya kwaso yaransa dasuke hannu mary, shima Aliyu ana yayesa nasa yaje ya amshesa, jin ya fara mgnr su Suwaiba da Muhammad makarantar boko, da dare bayan sallar isha har ďaki naje na sami malam Harisu lkcn yanacin abinda saida na bari ya kammala snn na fara da cewa dama wata shawara ce nake tafe dashi amma ban san yadda zaka ďauketa ba.

Maryam kenan, ina sauraranki.

"Gani nayi tunda nazo gidan nan da sunan aure yaya Rakiya sau ďaya tazo ko?.

"eh haka ne, lafiya?.

"Babu komai, amma kai baka tunanin wani abune yake hanata zuwa?.

" A'a ra'ayine dai irin tata..

"Malam kenan, ni kuma a tawa gani ba haka bane.

"To menene?.

"Rashin zuwanta baya rasa nasaba da rashin hauhuwar da bata samu ba..

"Kamar yaya Maryam?.

"Eh kasan duk wanda Allah be bashi haihuwa ba gani yake kamar tsanarsa ne Allah yai yasa bai bashi ba, snn kuma zakaga bai cika son shiga har kan nasu yara ba abinda kada azo a masu goro, kasan zuciya yadda take, batada kashi.

"Shiru malam Harisu yai, zuwa wasu mintoci snn yace kinyi gsky maryam.

" jin haka naci gaba da mgnta,da cewa shine nai wani tunani...

"Saida na ďan dakata domin jin abinda zaice,snn taci gaba idan har hakan bazai zama matsala ba, mai zai hana ka ďauki Suwaiba ka bawa yaya Rakiya riko, idan har kai haka bazata taba mancewa dakai ba, snn kuma zatayi alfahari dakai a cikin yan uwa, tunda mutune nawa suke yaran amma babu wanda yai tunanin haka.

"Shiruuuu malam Harisu yai haďi da zubamin ido na ďan nawa lkc snn yace gsky kinyi tunani, gaki yarinya amma Allah ya baki hankali da hangen nisa irin ta manya, nagode sosai maryam kuma in sha Allahu zanyi aiki da abinda kikace nasan Yaya Rakiya zataji daďi ba ďan kaďan ba.

" murmushi nai cikin kissa nace babu komai malam ai duk an zama ďaya.

"Malam kenan besan dawa yake zaune ba, nayi haka ne sbd banaso Suwaiba nayi karatun boko ta zama wani abu a duniya, shima muhammed ďin zai zaman yine zuwa wani lkc na kintima masa sharrin da malam Harisu zai koresa daga garin gaba ďaya.

" Itako yaya Rakiya da take fama da kanta ina taga kuďin da zatasa Suwaiba a makaranta, balle ma koda tanadasu garin babu makaranta sai dai makwabtan garin.

"Shiko mai gidanta malam ISA a yadda ake labarin mugun halinsa nasan bazai yarda ya wahalar da kansa akan yarinyar da besan zafinta ba........







///don't 4get cmmnt
and
vote////








*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥


_*FITSARIN FAK'O*_

💥💥💥

_(mugunta)_

*FASAHA ONLINE WRITERS*

_F.O.W_

_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_


🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹



بسم اللة الرحمن الرحيم


*∅∅∅*📝
*page11*


..............."Tun kafin na haye kan salgan kashi ya fara zubowa.

"Na jima sosai akan salgan snn nayi tsarki na mike jiki babu kwari na koma ďaki, ina shiga zubewa nayi kan gado nafara kuka.

" Yan kawo amarya kuwa guďa kan guďa cikin zuciyata ina faďin Allah yasa amaryan ta mace kafin safe.

"Kafin shaďaya kowa ya watse, malam Harisu ya shigo ďakin amaryansa, ban kara tsinkewa da al'amarin ba saida dare ya raba, duk abinda sukeyi a kunnina,hakan ba karamin tadami da hankali yai ba, yadda basuyi bcc ba hana nima banyi ba har safe.

"Tunda nayi sallar asuba nayi na shige ďaki ban sake fitowa ba,amma duk abinda sukayi akan kunnina.

"Ranar nice da girki amma naki fita daga ďaki sbd banida niyyar yi, gani har shaďya saura na safe yasa malam Harisu biyoni har ďaki duk mgnr ďa yai min ban tanka shiba har saida ya kare snn nace bazan yiba.

" ina mgnr ne cikin gatse da rashin kunya, ba tare dana kallesa ba,gani haka yasa malam Harisu juyawa ya fice daga ďakin, yasan ba komai ke damuna ba irin kishi, yana fita ďakin bayi ya shiga, koda yai mata mgn bata musa ba, mikewa tai ta fito domin ďora sanwa.

"Tun daga lkcn haka na hana kaina sukuni, kukan yau da ban na gobe daban, duk da naki amsar sanwa amma hakan be hana idan suyi su samin ba, sann kuma basu hana malam Harisu kwana ďani ba.

"Shima biyan bukatarsa kawai ke kawosa guna, kuma da zaran ya biya babu wani abu dake kara kawosa.

"Bayan wata ďaya nida bayi muka samu ciki, a wnn karo kam cikin bayi yazo mata da lalura sosae, hatta abinci bata iya ci, idan ma taci sai ta dawo dashi.

" Ni kuwa daram nake,idan ba fara danayi ba, bazaka gane ina da ciki ba.

"Amma sbd kada nai aiki yasa nima na samu gu na kwanta nace banida lafiya,irin abubuwan da nakeyi kace da gaske ďine banida lafiya.


"Tun daga lkcn aiki ya dawo kan karime, asalatun farko take tashi domin hura wuta ta sanya wa yara ruwan wanka, bayan tai masu wanka sai ta zuba ragowar tuwa wanka yara zasuyi kafin su tafi makaranta, idan kuma malam Harisu ya siyo kuni to, kullum aikin kenan, hakan yasa kafin wasu watanni duk tabi ta rame, ni kuwa na haďa baki da likita nace masa ya rubutamin cewa banida jini sosae a jiki, snn kuma kada nayi aiki mai karfi, koda na kawo wa malam Harisu amsar takarďan yai, kullum saiya siyomin magani jini na kwalba,(multina)ina sha safe da yamma.

"Tunda malam Harisu yake siyomi a ďaki nake zauna naci, ita kuwa bayi duk da tafini jin jiki, da kuma bukatar kayan karin jini dimin kallo ďaya zakai mata kasan tana bukata, sbd yadda tai fari'fal ta koďo, amma malam Harisu bayabi ta kanta.

"Yau koda malam Harisu ya kawo min kinci nayi na ije, da safe bayan ya fita kasuwa, ďauka nayi na fito dashi waje inda suke zaune, na samu gu na zauna snn na buďe bakin ledar saida na fara ci snn nace masu bismillh.

"Da shike bayi tariga tasan halina yasa ko kallon inda nake batai taga abinda ke ladar.

" itako karime hannu tasa ta cire taci, gani haka kullum saina fito dashi naci a gabansu, da shike karime bamai hakuri bane yasata tambayata aina nake siye, domin mai siyarwa ya'iya gashi.

"Jin haka yasa naji daďi,dama abinda yasa nake fitowa dashi kenan,buďe bakina nace bani ke siye ba, malam ne yake siyo min kullum dare.

" Take naga ta canza fuska, a zuciyata nace shegiya, na samu ďaya kenan.

"Ranar da girki ya juyo kanta,itama tace sai dai malam Harisu ya siyo mata tsire, babu irin rokon da batai masa ba amma yaki, hakan yasa ranar ta hanashi kanta.

" duk abinda sukeyi basusan ina make ina jinsu ba, ba karamin daďi naji ba, tun daga ranar idan naci sai na rage da safe nakai mata ragowa, ďan dai na tura mata takaici.

"Ashe duk taku karime kemin ban sani ba.

"kwarsem muka tashi tun safe karime ke aimai, duk da rashin imani ma amma saida na tausayawa karime.

"Ashe duk karya ne, da malam Harisu ya dawo daga kasuwa gani halin da karime ke ciki yasa hankali malam Harisu tashi, ba tare da bata lkc ba ya ďauketa zuwa asitibi,suna zuwa aka bata gano haďi da jona mata ruwa.

"Kamar da gaske, karime ta kwanta tana nishi sama-sama.

" Gani dare yayi kuma ga raya mu bari a gida, nacewa malam Harisu ni zantafi gida, nan mukai sallama malam Harisu yace ganinan zuwa.

"Jin haka yasa karime kara narkewa a gado.

"Duk yadda malam Harisu yaso dawowa gida amma karime ta hanasa, haka ta liliyesa da kisisina suka kwana tare.

"Sbd haushi da takaici yasa koda yazo gida duba kwananmu ban gaishesa ba, da haka saida karime ta kwana uku a asibiti kuma malam Harisu ke kwana da'ita, ranar da za'a sallamesu ta haďa baki da likitan ya rubutawa malam Harisu kuďin magani mai tsadar gaske.

"Bayan malam Harisu ya biya kuďin magani, snn likita ya sake rubutu a wani takarda wai tana bukatar karin jiki.

" koda malam Harisu ya biya kuďin raba dai-dai sukai da likitan, tunda karime ta dawo gida malam Harisu ke ďawainiya da karime, ni kuma tun daga lkcn ta daina siyomin tsire da multina ďin da yake siyemin.

"Kullum da safe karime ke fitowa da ragowa tace gashi na bawa yara, haushi da takaici ya isheni, tun ina amsa har yakai ga koda takawo a bawa yara, sai nace basuci,kafin na rufe baki sai dai kawai naji ta hurgomin a jiki.

"Ranar data sake min haka dauka nayi na hurga mata a jiki snn nace idan ta sake mai rabani da'ita a gidan nan sai Allah domin ko malam Harisu da kike zamansa bai isa ya hanani abinda nayi niyya ba..

"Ko? haka kikace?.

" kwarai da gske, ko zaki gwada ne?.

"Yarinya kenan, ta yaro kyau yake baya karko, ba'a sani maci tuwo sai miya ya kare, nida ke shego ka fasa, idan kika fasa abinda kikai niyyar yi min wlhy Zulka ban gode maki ba.

" duk da na girgiza da mgnr karime amma a fili nace muzuba mu gani.

"Sabo tirkin wawa, gani bazan iya hakuri ba yasa tayi takon karime da malam Harisu, ranar girkinta, bayan sallar isha malam Harisu ya shigo hannunsa rike da kunshin a hannu, kai tsaye ďakin karime ya shige niko da nake kwance na mike tsaye, sai dai nabari ya juma da shiga ďakin snn na afka masu batare da sallama ba.

"Takardan dake gaban karime na wawuso na kwashe namar dake ciki, ko kafin na mike tuni karime ta shako min kwalar rigata, malam dake zaune ya mike haďi da faďin subhallh, me zangani haka?.

"Ita kuwa karime kariga ta shakeni, haďin da danneni a kani, sai faman wultsin-wultsin nakeyi akan kuli-kuli na kasa tashi.

" Tsawa malam Harisu ya ďaka wa karime snn ta sakeni haďi da cewa kinci darajan malam.

"Duk da nasha wuya amma besa bakina ya mutu ba, kugu na rike ina karkaďe-karkaďe nace idan kin isa ki tabeni.

"Tsalle ďaya karime tai zata cafkoni, da sauri na hankaďe malam Harisu jikinta suka zuba a kasa, ni kuma a shittin na arca.......






///don't 4get cmmnt
and
vote///







*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥


_*FITSARIN FAK'O*_

💥💥💥

_(mugunta)_

*FASAHA ONLINE WRITERS*

_F.O.W_

_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_


🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹



بسم اللة الرحمن الرحيم


_Gaisuwa mai tarin yawa gareku masoya na kuma masoya littafaina. A gaskiya banida kalmar da zanyi amfani dashi wajan godiya a gareku,nagode sosai da sosai da cmmnt naku, babu lokaci ne da zanbiku one by one amma duk ina bibiye daku sannan kuma inajin daďi,domin cmmnt ďinku shike shara min karfin guiwa, ngd ngd ubangiji Allah ya rabamu da mai hali irin na *iya ummai* Allah ya tsaremu ya tsare zuri'armu yasa mufi karfin zuciyarmu ameen._


*∅∅∅*📝
*page10*


................"Washe ana idar da sallar asuba malam Harisu ya ďauki Suwaiba da kayanta zuwa *ďan'kolo* garin da yaya Rakiya.

"Bayi tai kuka kamar ranta zai fita, nasan ba komai ne yasa tai kuka ba, illa canjin rayuwa da Suwaiba zata samu, sbd garin kauye ne sosai.

"Niko ina kwance a ďaki ina kallonta, ko a jikina.

"Da haka naci gaba da juya su ita da malam Harisu, kusan kullum ina hanyar gurin malamai da bokaye, hakan yasa ban ije komai ba, sbd duk abinda nata tare a gunsu yake tafiya.

"Gani komai nawa su kare yasa na fara ansar waďan gyaďa,solon buhu ďaya jaka ďaya ake biyana, da haka nake samu kuďin zuwa gu malamai, ita kuwa bayi da shike bata biye biye irina buhun ďayar dake ďakinta yafi ashirin, mudda tamina yai badawa takai rance ayi noma dashi bayan ab kwaso amfani gona sai a ruba mata, hakan yasa tana zaune ta tara dukiyarta ba kamar niba.

"Yan'kauyenmu har gulmata sukeyi wai basusan mai nake da kuďi ba, amma basu gani a jikina ko jikin yara, niko be dameni ba, sbd bukatata tana biya, (hausawa suce biyan bukata yafi dogon buri) dan haka duk abinda za'ace an daďe ba'a ceba.

"Gani mgn tana nimar tai yawa a gari, na zuga malam Harisu ya hanamu fita gaba ďaya,daga biki har suna baya bari muje, naji daďin hakan sosai, koba komai kananar mgn zai ragu.

"Amma da shike yan'garinmu mana fukai ne, koda bayi ta sake haihu, taro sukai mata sosai, amma lkcn dani na haihu babu uban da yazo min barka balle kuma suna, ni kaina nasan ba komai ne yajami haka ba, bayi tafini iya mu'amula da jama'a, snn kuma tafini hakuri, kananar mgn be dameta ba.

"Gani haka yasa na dawo na lallaba malam Harisu ya hkra yaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login