Showing 27001 words to 29796 words out of 29796 words
Chapter 10 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt
ta fara da cewa"kinsan ni nima na sanki, kin san abinda zan iya aikitawa haka kema nasan abinda zaki iya aikatawa"." To wlhy koda da wasane kika sake ďanki ya medamin yarinya bazawara, wlhy Allah bazai sake aure ba, shida aure saidai yaga anayi dan haka ku kiyaye, snn ta juya gun Safiya dake tsaye tace" yar'albarka jeki ki kwanta, ni natafi.
"Inaji ina gani mgn ta gagareni, sbd nasan halin jummai sarai ba mutunci ne da'ita ba, yanzu inda na biyeta sai tai min zanzare a gaban kiyoshi tabar min abin faďe.
"Har bakin k'ofar garka Safiya ta raka uwarta snn tadawo ta zauna a cikinmu, gani haka yasa nabar gun.
"Tun daga lokacin nake kiyaye abinda zai haďani da Safiya bare taje ta gaiyato min shegiyar uwarta bara mutunci da kunya.
"A ban garen muhammed kuwa tunda ya koma birni bai sake waiwaiyar gida ba kwatsam yaji ana neman ma'aikata ta hukumar yaki da fasa k'wauri ta kasa yaje yai aplying cikin sa'a sunarsa ya fito, bayan kwana biyu suka sake tura masa da sak'on zuwa exam snn zasuje da takarďunsa ta makaranta.
"Jin haka yasa Muhammed baiyi k'asa a guiwa ba ya garzayo zuwa gida, a ranar daya iso da yamma bayan sallar isha har cikin ďaki ya sami malam Harisu bayan su sake gaisawa snn ya sanar masa abinda ke tafe dashi.
" malam Harisu yai murna dajin haka sosai haďi da fatan alkhairi.
"Tunda naga Muhammed ya shiga ďakin malam hankalina yaki kwanciya.
"Mikewa nai daga inda nake zaune naje na ra6e domin jin mgnr da zasuyi, bayan su sake gausawa muhammed yake sanar wa malam yasamu aiki a abuja yanzu haka ma takardunsa yazo ďauka.
"Saida na k'are ji tsam snn na koma ďaki sbd kada ya fito ya gani, bayan Yahuza ya dawo gida, nasa aka kirasa, bayan yazo ne nake tambayarsa abinda muhammed ke nufi da fasa k'yauri.
"Banso ace Muhammed ne yasami irin wnn aikin ba to tunda haka ya faru ni nasan ta inda zan 6ulo masa.
" duk da abin na cima dole na ďanne zuciyata, sbd idan ba nike da girki ba bana sakewa nai mgn da malam.
"Kafin girki ya zagayo kaina har muhammed ya amshi takardun ya koma birni, yana fita ya fara addu'ar Allah yasa yai hatsari a hanya ya mutu, ko kuma yasamu wani nakasu a jikinsa yadda koda yaje tireniďin bazasu ďaukesa ba.
"Duk irin addu'oin da nai tayi Allah bai amsa ba, gani haka yasa ban tinkari malam ba saida nai masa k'yank'yawar shiri snn na tukaresa da mgnr Yahuza, duk da nasan ba malam ne ya samowa muhammed aiki ba, amma nai fur nace shine ya samo masa aikin ďan haka sai dai yakai Yahuza makaranta.
" Duk yadda malam yaso gocewa ya kasa dole yasa ya amince.
"Zulka tai hakane ba tare da tasan cewa yanzu ba dah bane, domin tunda Safiya taje gidansu ta kwanshe duk irin abinda takeyi mata, mmn ta zaunar da'ita ta shirya mata kissa ta yadda zata kamo Yahuza a hannu snn kuma ta juyasa da son ranta idan uwar tashi tai mata kuma ta zage.
"Tun daga lokacin Safiya ta fara yarda da Yahuza, duk da dai ba yadda yakeso take masa ba amma motsi yafi labewa.
"Shi isa koda tajasa da faďa baya biyeta, sbd yasan zasu haďu da dare.
"Rashin sani yasa Zulka tunkarar Yahuza da mgnr komawarsa makaranta, shiko Yahuza yai fur ya tsibbace yace babu inda zashi, domin bazai iya tafiya yabar matarsa ba.
"Nan Zulka ta hausa da faďa, ina matar take?yarinyar banza yarinya wofi, mara kunya da mutunci shine har kake cewa bazakaje makaranta ba sbd ita ko? " to wlhy baka isa ba, karatu babu fashi, kuma matar da kake ikiriri matarka sai tabar gidan nan naga ta faďi, wowo wanda bai son mai sonsa ba.
"Karam Zulka taji ance idan ban bar gidan ba ke zakibar gidan, tsohuwar banza tsohuwar wofi kawai kuma aurena da Yahuza mutu ka raba....
"Cikin fushi na mike ina faďa yanzu sbd Allah Safiya nice kike faďi wa haka?inda uwar...." cikin tsawa naji Safiya na cewa ke dakata nasha faďi maki tun ba yau ba duk abinda zakiyi kada kisako uwata a ciki"."Domin uwata ba irinki bace mai mugun hali wacce batasan Allah ba".
"Gani Yahuza na tsaye bai iya cewa komai ba yasa nai kukan kura na shakota nahau duka kamar Allah ya aikoni gareta.
" Wani abin mmki danaga Yahuza ya mike na ďauka tayani dukarta zaiyi kawai sai naga yana k'ok'arin k'wance matarsa daga hannuna.
"Cikin kuka da takaici na mike daga kanta ya fice daga ďakin' ita kuma langa6ewa tai wai ita a dole bazata iya tashi ba.
"Akan idona Yahuza ya ďauki matarsa ya wuce da'ita ďakinsu," (kai duniya kenan, komai kake akwai wanda ya fika)".
"Yahuza na fita safiya ta zari kyale zuwa gidan su, ko sallama babu tun daga k'ofar soro ake jiyo kukanta, da sauri mmnta da kiyoshinta suka biyota waje, domin gani mai kukan.
"Karo sukai a zaure da Safiya, Safiya na ganinsu ta zube a k'asa wai ita "yar sharri, da shike halin nasu iri ďaya da uwarta," nan suka ďauketa zuwa asibiti, ina zaune gani lokacin sallah yayi yasa na mike na ďauki buta domin shiga makewayi, har na ďaga k'afa kenan na jiyo sallama daga waje.
"Da shike lokacin babu malam a gida, snn kuma babu yara, dole yasa naje da kaina, kyale na ďauko na yafa snn naje, ina zuwa zaure ďaya daga cikin yaran dake zama a faďar sarkine na gani.
"Cikin girmamawa muka gaisa, bayan mu gaisa ne yake shedamin ana nemata a fada, banyi mmki ba sbd nariga da nasan halin jummai ba tun yau ba.
"Gani malam baya gida yasa nace masa yaje inanan zuwa, idan maigidan ya dawo zanzo." babu yadda banyi dashi ba amma yak'i tafiya dole na bisa muka tafi tare.
"Ina isa duk abinda nake zato ba haka bane,shi isa akace duk wani abinda kake tunani wani ya fika, wai nice Safiya zatai wa shirrin na zubar mata da ciki, lallai idan kanada rai zakai kallo.
"Banja mgnr ba sbd nasan idan ma nace zanja k'arsheta nice zankwan ciki, sbd duk abinda nake gadara dashi jummai ta damani ta shanye,"dole yasa na amshi kaifin da batawa ba.
"Nan sarki yace na bawa Safiya hkri haďi da yimata al'kawarin bazan k'araba, abu ya haďu yai min yawa,gashi na amshi laifin daba tawa ba, snn kuma ance na duk'a gabar yar'cikina yarinyar dana haifa na juya na bawa hkri," ban san lokacin dana fashe da kuka ba.
"Duk abinda akeyi Yahuza bai zo gunba har akaci aka suďe, bayan na gama bata hkri mike da niyyar tafiya sai naji ansake tsaidani, buďe bakin jummai wai tanaso aimin iyaka da Safiya, muddun taga baki a jikinta nice.
"Tunda muka koma gida, ban sake shiga harkanta ba,amma nariga nasha alwashin sai Yahuza ya saketa.
"Ina fama da wann bakin cikin kwatsam saiga Suwaiba tai sallama, wani abin mmki wai tazo sallama sbd inda mijinta ke aiki su turasa Egypt yanzu haka yazo ďaukarta su tafi tare, shine tazo sallama.
" da shike yaron sarkin garinsu take aure, shi kuma ba anan ya tashi ba a birnine ya tashi gun ďan'uwar mamansa, shine ya sashi a makaranta bayan ya k'are ya samo masa aiki.
"Sbd bakin ciki ďaki na shige haďi da fashewa da kuka, amma dasu bayi suka tambayi dalilin kukata kawai cewa nai ta sabone.
"Suna fita na yanke wa kaina alkawarin a yau ďinnan Yahuza zai saki Safiya koya samu yaje yai karatu ko yasamu yai kuďi kamar yadda muhammed yaje zaiyi kuďi ya barsa a baya.
"To wlhy bazai yuwu ba dole yau ya saki Safiya domin na lura in har suna tare babu wani abin arzikin da zaiyi a duniya, ni kuma bazan yarda Muhammed yai kuďi ya barsa ba.....
_///don't 4get cmmant_
_and_
_vote///😻_
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{Imfacing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
_not editing⛏_
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*LAST PAGE*
.............."Tun bayan tafiyar Yahuza makaranta, bashida aiki sai na a turo masa da kuďi, tun abin baya damuna har yakai ga yafara damuna." sbd a halin yanzu kusan duk gonakin da malam ya mallaka su kare sbd karatun Yahuza.
"Bayan shekara biyar lokacin su Suwaiba su dawo daga k'asar da suka tafi, amma basu dawo kauyen da zama ba a birni ya siya masu gida sukaci gaba da zama acan.
"Gashi bikin Ruma ya taso malam kuma baida kuďi dole ya sake saida gonarsa yai mata kayan ďaki, ragowar kuma akai shidimar biki.
" Da haka rayuwa yaci gaba da tafiya, al'amuran Yahuza sai dai addu'a domi a yadda nake jiyo labarin ba karatun yakeyi ba, sharholiyarsa kawai yake da kuďi da malam ke tura masa, nayi takaici ba ďan kaďan ba hakan yasa dana samu masu zuwa can sokoton na aika masa daya dawo gida haka tunda karatu bai yuwu ba, amma da shike ďan yau ne bai dawon ba."Haka yaci gaba da zamansa acan har tsawon shekara goma".
"A lokacin yaran Muhammed hudu mata biyu maza biyu, lokaci yana zuwa da matarsa gani gida, idan har bazai samu zuwaba yakan turota tazo da yara.
"Ba k'aramin bak'in ciki nakeso ba, idan har suzo garin, sbd yadda malam yakewa yaran muhammed kamar a kansa aka fara gani jikoki, shiko Yahuza yanacan yana gantalewarsa a bariki, a cewarsa karatu yakeyi.
" Banida yadda zanyi sbd magani danai tun farko, dama saida malam ya faďimin bashida makari, nace na amennce a hakan, "ban ta6a kawowa reshi zata huye da mujiya ba,domin har cikin zuciyata Muhammed naso ya zama haka saiga hakan bai samu ba.
"Dare wata litani bayan sallar isha muna zaune a tsakar gida muna shira kwatsam saiga Yahuza yai sallama, kasancewar acikin duhu muke amma hakan bai hanani gano babu wani abin arzikin daya dawo dashi, amma da shike akwai kiyoshi snn kuma nariga da nasan hassada irin tasu yasa bai nuna 6acin raina a gabansu ba, a guje naje na rungumesa inayi masa oyoyo.
" batare dasu luraba ina kallonsu suna yi mana gyatsine, muka shiga ďakin,wai shi ďan duniya ashe takardun hugice ya samu ya kawo gida a matsayin takardan kammala jama'arsa,"a rashin sani fitowa nai dashi tsakar gida ina nunawa su bayi da Saro hausa da habaici kuwa ba'a mgn,"Ashe duk abinda nakeyi kallona kawai malam keyi, sbd yariga yai bincike akan Yahuza.
"Gani yana zaune babu sana'a yasa nace yaje gonar malam ya ďibi fili yai gomar kansa idan kuma bazai iyaba saiya aimasa, ba tare da musuba yace to" yana fita gonar ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya iske malam yana aiki a cikin ganar, ba tare da tambaya ko nemar izina ba Yahuza yasa mazana ya zana iya inda yakeso.
"Gani haka yasa malam tambyrsa lafiya da ďibami gona batare da tambyata ba?.
"Cikin isa da rashin kunya irin ta Yahuza ya basa amsa cikin galatsi.
" Nan zuciya ya ďibi malam yace bazai bada gonar ba, shima Yahuza baibi a hankaliba, nanfa musu ya kancame tsakani malam da Yahuza, ina zaune a gida najiyo labari ga malam da Yahuza a gidan sarki, wai Yahuza ya shake malam yace saiya kashesa, wasu mutane ne suna wucewa suka hango Yahuza ya shake malam a cikin sukusu yanada niyyar kashesa.
"Ihu da malam yaine yasa mutane sukayo kansu.
"Nai kuka baďan ba ďan ba, sarki yai masa iyaka da duk wani k'adarar malam, tun daga lokacin malam ya fara da zazzbi, abu kamar wasa har ya kaisa ga kwanciya ya koma komai yi masa akeyi, muyi yawo dashi asibitoci kala-kala amma ba'a samu magani ba, kowani asibiti idan muje da irin abinsa suke faďi akan jikin malam, daga k'arke dai gida muka dawo dashi muka zuba ido muga yadda Allah zaiyi dashi," Duk wann gwagwarmayar da akeyi Muhammed baizo ya duba malam ba, duk juyi da malam zaiyi babu wanda yake kira illa Muhammed, gani haka yasa kullum idan ni kaďaice a ďakin malam banida aiki sai zugasa daya tsine wa Muhammed sbd baizo ya dubasa ba.
"Ranar da jikin malam ya tsananta mu kanmu da muke jiyarsa gani muke lokacin sa ne yai, muna cikin haka muka jiyo sallama, koda zan leka Muhammed ne nagano da matarsa harda yara suzo, banso haka ba, nasone da kafin malam ya mutu ya tsinewa Muhammed idan yaso su taru su zama iri ďaya da Yahuza." kwanan su Muhammed uku da zuwa malam rai yai halinsa, ranar juma'a kenan.
"Dukkanmu mu shiga damuwa sosai, musamman ma ni, da basuyi rabuwar arziki da Yahuza ba.
" Bayan bakwai Muhammed ya kwashi iyalansa suka koma inda yake aiki, hankalina bai tashi ba saida za'a raba gado, babu yadda ba'ai da Muhammad ba amma yaki zuwa yace duk yadda akai dai-daine. Nida Yahuza kuwa kane-kane mukai a gaban liman har saida aka k'are komai, da shike kuđin gado ba kowane ne mai albarka ba, kafin shekara komai ya kare, amma banda na bayi da Saro domin yanzu haka Saro tanada shanayenta sufi a k'irga, itama bayi haka, nice kawai a cikinsu na zama koma baya, ga kuma cutar da Allah ya jarabceni dashi.
_To kinji dalili da yasa duk inda zaku kaina ba lallai ne kusamu magani ba, sbd irin abubuwan dana aikata_
_wanda nakeyi ďansu, sai gashi sune yanzu suke taimakani min, shi kuwa Yahuza idan ya bar gida tun safe sai dare yake dawowa, wani sa'inma kwana yake a waje, duk da yafi kowa sani halin da nake ciki_
_Hakan yasa zanyi amfani da wnn damar wajan yiwa jama'a nasiha da su guji son zuciya da kuma son kansu da yawa, sbd ranar irin ta yau, yadda ya zomin_
_Zuwaira dake zaune ajiyar zuciya tai tana nesawa, snn tace yanzu dama duk irin abinda kika aikata kenan iya Ummai?_
_Amma ya kamata kije ki nemi gafarar mery da karime, sai kuma sauran yaran gidan da iyayensu._
_Eh duk na rikesu,yanzu haka ma Muhammed yazo ya ďauki mary ta koma birni inda yake zaune da matarsa."ita kuma karime har gidan mijinta na bita na roketa gafara,kuma tace ta yafemin, suma su Saro da bayi duk su yafemin, Ubangiji Allah ya yafe mana bako ďaya_
_Alhamdulillahi_
_nima a nan nakawo k'arke wann littafi mai suna FITSARIN FAK'O ba iya Ummai ba duk wani mai hali irin tata Allah ya shiryesa ya ganar dashi ameen_
*a k'arshe inayiwa ďaukakin masoyana na nisa dana kusa fatan alkhairi, ngd sosai da sosai da irin soyayyar da kukewa books ďina, sai mu haďu a sabon littafina wanda zaizo maku nan bada daďewa ba insha Allahu.*
_Snn kumaina baku hakuri mistake nayi wajan posting a:m soso srry_
_///don't4get cmmnt and share pls😻///_
*mmn uswan ce📚✍*