Showing 12001 words to 15000 words out of 29796 words
Chapter 5 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt
gaba da barinmu muna zuwa unguwa.
"Malam Harisu ya kwashi yara ya sanyasu a makarantar boko, Muhammed Ďabsiya da Yahuza, bayan shekara biyu kwatsam ranar wata juma'a, misalin goma na safe, muna zaune muna waďar gyaďa saiga malam Harisu yai sallama, da shike nice da girki nai masa sannu da shigowa, ya amsa da yawwa sannunku.
"Mikewa nai na ďibo masa ruwa, bayan ya shane yake cewa" kada anjima kuga baķi daga sama, batare da kunsan da zuwansu ba, insha Allahu anjima bayan saukowa daga masallacin juma'a za'a ďauramin aure.
"A gigice na watsar da gyaďan dake dukule a hannuna na mike haďi da faďin mai kace malam???hannu nasa na dafe kirjina..
"Malam dake zaune yai banza dani, kamar bejini ba.
"Itako bayi babu abinda ya fito bakinta, illa Allah yasa mukai ya bada zaman lafiya, yasa abokiyar arzikinka ce.
"Cike da jin daďin addu'ar da bayi tai masa, sa fara'arsa ya amsa da ameen.
"Gani haka yasa na dawo na zauna, jiki a sanyaye.
" baifi minti goma da fita ba, masu fanti sukazo yiwa ďayan amarya, ďakin dake kusa da wata,sukace malam Harisu yace na kwashe karikitaina, domin a cikine zai ije amaryansa.
"Kiji a sanyaye na mike naje ina kwashe kaya ina kwalla, itako bayi ko'a jikinta sbd dama na hanata ije komai a ďakin, ni kaice nake amfani da ďakin.
"Kafin lkcn zuwa masallaci har su kammala komai, ana saukowa daga masallaci aka ďaura auren malam Harisu da amaryansa *karime,* nayi kuka ba ďan kaďan ba.
"Bayan la'asar malam Harisu yai sallama hannunsa rike da zabbi guda biyar wani yaro dake biye dashi a baya kuma ďauke yake da karami buhu, kai tsare ďakin bayi ya nufa, ya mika mata yace, tayi masa aikinshi.
"Shinkafane mudu biyar sai kayan miya da kuma zabbin daya kawo, kafin ya fita har ta hura huta, shi kuma duk ya yanke zabbin.
"Yana zaune suna aikin tare, yara kuma na kewaye dasu, niko da nake ďaki ina kallonsu, wata zuciya tace naje nasa hannu muyi aikin tare,wata zuciya kuma tace kaďa kije.
"Haka na ďaka ta zuciyata naki zuwa,kuka kuwa babu sassauci, har bayi ta kare aikin abincin ban fito daga ďaki ba, bayan ta kare kwalla mai hoton murtala ta zuba abincin a ciki, namar zabbin kuma tasamu karamin langa ta zuwa.
" ina zaune a ďaki,abin duniya duk yabi ya isheni, kawai najiyo sallamar Muhammed hannunsa rike da kwanu yace gashi inji bayi tace na kawo maki.
"Bansan lkcn da zuciya ta ďibeni ba na haďa dashi da kwanu abinci na likasu da bango.
"Ihun da muhammed yai ne yasa bayi zuwa a guje tana tambayar lafiya?.
"Banza nayi da'ita sbd tsabar banida lkcnta, hannu tasa ta ďaga muhammed suka fita, niko nace aikin banza kawai, ni za'a kawowa rainin hankali?.
"Duk irin tambayar da malam Harisu yai wa bayi akan kukar da Muhammed keyi, bata faďi masa, illi cewa tai faďuwa ne yai.
"Da dare bayan sallar isha, tun daga kofar koro nake jiyo sallamar yan kawo amarya.
"Take hanji cikina yai wani irin kugi, naji cikina ya murde, a guje na fito daga ďaki na ďauki buta zuwa ban ďaki.
///don't 4get cmmnt
and
vote///
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page12*
............."Tun daga lkcn na fara shakkanta amma ban yarda ta gane ba, snn kuma koda zan takareta banayi sai malam Harisu na gida, sbd nasan zai taremu.
"Duk irin abinda mukeyi bayi bata sanya mana baki, asalima idan muka fara sai tabar gun, ďaki take komawa ta kwanta shiyasa shima kansa malam Harisu koda mgn yakeyi baya sanya bayi a cikin.
"Gani haka yasa na nimi bayi damu haka kai mu kori karime,bayi tace babu ruwanta, tunda ba'a kanta take zaune ba.
"Baki daďin irin amsar da bayi ta bani ba, amma tunda haka tace yasa ban sake tunkaranta da wani zance ba,ni kadai nake hankata.
"Wanda ya rigaka bcc dole ya rigaka tashi, duk abinda kakeyi a ratuwa wani na gabanka, babu boka babu malam amma kissa da kisisinar karime kawai ya isa na saurara mata,ďan tsabar makirci irin na kishiya saida karime ta hana malam bamu kuďin cefane, tace ya rinka siyowa da kansa, wani lkc kuma koda zai siyo hanashi takeyi, a cewarta wai mu koyi maleji sbd yau da gobe sai Allah, idan ya saba mana da haka duk ranar da babu ba yarda zamuyi ba.
" Amma da shike ita tafini sani kan yadda ake dunuyanci cikin kissa da kisisina take lallabashi ya bata kuďi ta siye duk abinda takeso.
"Gani cikina ya tsofa nace malam ya bani kuďin da zan siye kayan yara, kamar daga sallama karime ta shigo mana buďe bakinta tace da malam kada ya bayar, tunda ba haihuwar farko bane, haihuwar farkone ake siyayya, amma sauran ba'ayi sbd bazan rasa wasu kaya ba.
"Ni banida wasu kaya da suka rage wanda ban buďe ba, duk kayan da muke samu bata ijewa buďewa nakeyi nasawa yara.
" Nai faďi hakane kawai,domin kare kai, asalima duk kayan da zan samu tarasu nakeyi na saida kuďin nakaiwa malam yai min aiki, idan har nabuďe kayan da mmnta kemin da kuma wanda yan'biki ke kawomin basu wuce kala uku ko hudu.
"Buďe bakin karime tace idan babu sabo ai bazaki rasa kwance ba.
"Harna buďe baki zanyi mgn kenan, malam ya daka mana tsawa, karime ce tayi shiru amma ban dani, zaginta kawai nakeyi kamar Allah ya aikoni gareta, sbd takaici da bakin ciki har kuka karime saida tayi, nima nayi haka ne nasan idan ba ta zagin ne zan rama ba banida wani hanya da zan iya ramawa, shiko malam ya hana karime ta tabani, saida nayi mata ratassss snn na fice daga ďaya.
"Bayan fitata daga ďakin hakuri sosai malam Harisu ya bawa karime haďi da cewa tayi hakuri ni yarinya ce, be kamata tana biye min ba.
" A gun ta nuna komai ya wuce ashe ba bane na zuci na zuci, bayan kwana biyu na saki jiki ina zaune kusa da bayi ina ina tayata tangaďe, kamar daga sama naji saukar bulala, sbd azaba saida na ďimauce, domin shammatata tai, koda nai yunkurin tashi na guje na kasa sbd ga ciki ga shi kuma tarikeni,bata sakeni ba saida rai min lilis snn ta halboni da bulalar haďi da cewa gobe ki kara.
"Nayi kuka har na gode Allah, gashi malam baya gida, ko kafin malam ya dawo ďaki karime taje ta kwanta tana nishi wai batada lafiya, hakan yasa koda malam ya dawo na faďi masa bai ďauki mataki akai ba, duk da gazanan bulala kwance a jikina amma be yarda ba, sbd yariga ya sanni da baki.
"Tun a ranar naso zuwa gun malam domin a wnn karon so nake ya kashemin karime kawai gaba ďaya na huta da gani shegiya, sai dai rashin kuďi ya hanani zuwa, sbd dama a cikin na cefane nake samu to wnn bakar shegiyar ta hana malam bamu kuďi, ďan waďar gyaďan da nake amsa na kwadago yanzu basu kawowa sbd ba lkcnsa bane, wanda kuma nake tarawa duk su kare sbd bin malamai da bokaye, dole yasa nayi hakuri da zuwa gun malamai.
"Cikin daren wata asabar nakuda ya kamana, haka nai tayi har na haihu ba tare da na kira wani ba, sbd nasan koda nai mgn karime ce zatazo ni kuma yadda na tsani kwanar mutuwata haka na tsani gani karime.
" Ha nai tayi har na haifi yata mace, sai dai kafi safe ta koma, duk ban luraba sbd gajiyar da nai,sai sai kusan asuba, gani yarinya bata motsi yasani kwarma ihu, da sauri malam da karime sukazo suna buga min kofa dana buďe.
"Ina buďewa gani irin kukan da nakeyi yasa karime jarisawa cikin da sauri, duk da mutuwar dake cikina amma be hanani zuwa a guje na ďauki gawar ya" ta na rungume ba, malam kawai na mika mawa, da sauri yasa hannu ya amsheta haďi da tambyr yaushe kika haihu?.
"Ban bashi amsa ba, sbd kuka, kallo ďaya malam yaiwa yarinya yai kabbara haďi da cewa ai bata da rai, wani sabo kuka nasa, juyawa yai ya mikawa karime yarinya suka fita da'ita da same aika binneta, duk daga lkcn na kara tsabar karime sbd gani naka kamar sanadiyar dukan da tai min ne lkcn inada ciki yasa yarinyar mutuwa.
" Bayan uku na sami malam a ďaki da mgnr, be bari na karisa ba ya ha'uni da faďi, dole yasa nai shi, ranar dana cika kwana bakwai da haihu bayi ta haihu ďanta namiji, ranar nayi kuka sosae, sbd bakin ciki yanzu yaran bayi hudu kenan amma nawa uku.
"Ranar suna malam ya haďawa bayi sha tara na arziki, yaro yaci suna *SALMANU RASHIDU* nai baki ciki ba kaďan ba, gani yadda banida wata magora dama karar da iyayena zasu haďi min ne idan na haihu na dogara dashi, akan na siyar na canza gu wani mai magani to yadda al'amari ya kasance.
" ina zauna sai fama tunani kala-kala nakeyi, a gun tunanine mgnr cikin karime ya faďo min ace har yanzu ciki bai nuna wani alama ba?anya kuwa wnn cikin gskya?.
"Ina cikin hakan ta fito daga ďaki, ido na kafa mata na kare mata kallo, a ranar ne magano batada komai, ashe dama duk karyane.
" Tun daga lkcn naketa takalar ta faďa dan dai ta tanka na tuna mata asiri, duk irin abinda zanyi mata sbd tayi mgn karime bata kulani gani haka yasa na bari ranar da take da girki har ta hura wuta da gangan naje na ďibi ruwa na kwarawa iccen wutar ta mace, da shike tariga tasan da gangane nai yasa bata tsaya wani mgn ba tana zuwa ta hauni da duka.
"Niko na kamata da ďanbe, duk irin hkrin da bayi tabamu amma muki hakura, muna cikin haka saiga malam yai sallama, jin sallamar malam yasa ta ha'u karime da zagi ina tuno mata asiri akan karyan cikin da tai.
"Babu yadda malam beyi dani dana daina faďi haka amma naki sbd a lkcn gani nake akan gskyta nake mgn.
" gani na nace da mgnr yasa karime cewa aje asibiti a kwada, duk da besa na karaya ba, nace eh aje.
"Jin haka yasa malam gindaya mana sharaďi idan har karya nakeyi daga nan bazan dawo gidansa ba.
" nace eh na amince.
"Idan kuma karime ce ke karya itama bazata dawo gidan sa.
" Tace ta amince, snn malam yace muje, a gaba yasamu yana biye damu a baya har muka isa, cikin zuciyata ina faďi Allah na gode maka yau zaka rabani da ala'kakai.
"Muna isa malam ne yaje yaga likita yai masa bayanin abinda tafe damu, likita yace wacce za'a gwada tashiga.
" beci dake gefe na samu na zauna ina jiran fitowar shegiya tazo tasan inda dare yai mata, ina cikin haka kenan saiga karime ta fito haďi da cewa to bakar alguguma manafuka ta Allah ba taki ba, km daga yau keda gidan malam har abada.
"Da sauri na mike haďi da sake tambayar karime abinda tace.
" nan karime ta sake maimaita min, tun kafin malam ya fito daga ďakin likita nasa ihu ina faďi na shiga uku na lalace.......
///don't 4get cmmnt
and
vote///
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page13*
................"Ihu nake sosae, nan da nan jama'ar dake asibitin dukajo kaina haďi da tambayar lafiya?.
" gani haka yasa Karime komawa gefe ta zauna tamkar batasan abinda ke faruwa ba.
"Kuka kawai nake babu sausauci haďi da ihu, jin ihu nane yasa malam da likitan da suke ďaki fitowa da sauri likitan ke tambaya lafiya?.
"Wani irin kallo banza malam yai min haďi da cewa karime tazo su tafi, jin haka yasa nima na wawuri takalmina da mayafi na bisu, suna gaba ina biye dasu a baya.
"Tafiya suke tamkar basu sanni ba.
"Da haka har muka isa gida, kai tsaye ďaki karime ta shige taje ta keanta, lkcn bayi na nata ďakin kwance, shima malam nasa ďakin ya shige, gani duk ni kaďai aka bari tsaye a kofar gidan kamar wata sakarai, yasa na juya na nufi nawa ďakin naje zan shiga kenan har nasa kafa ďaya naji kira kamar daga sama.
"Da sauri na juya haďi da daďin na'am.
" tun kafin ya kariso inda nake tsaye nariga na zube a gabansa na fara da cewa, ďan Allah ďan annabi kayi hkr ka yafemin insha Allahu bazaka sake kamani da wani laifi maka manci haka ba.
"Duk ina mgnr ne ina kuka, gani haka yasa jikin malam sanyi," yace na yafe maki,amma kada ki kara, idan har kika kara zan ďauki mumunar mataki a kanki.
"Da sauri nace na amince.
"Jiki a sanyaye naje ďaki,zuciyata cike da mmki karime, nidai nasan ba cikine da ita ba, to amma yaya haka ta faru? kodai haďa baki sukai da likitan,amma babu komai zanci gaba da biniyan lamarinta har nagano gaskiyar lamari.
"Kwanciya nai al'amarin karime yai matukar ďaure min kai, ina cikin haka saiga sallamar karime, jin muryanta yasani kwanviya kamar mai bccn gske, amma ba bccn nakeyi ba.
"A baki kofa taja ta tsaya haďi da kiran sunata zulka!!!.
" Banza da'ita nan ban amsa ta ba.
"Nasan kina jina, dama nazo nayi maki gargaďine, akan idan kinason kanki da lafiya to ki fita harkata,idan ba haka ba wlhy subma tallahi kinaji kina gani saikin bar gidan nan, idan kuma kice karyane to muzuba,nidake shege ka fasa.
"Mgnr ciki kuma ba karya kikai ba tabbas banida komai, sbd ba shine a gabana ba, domin nan da ďan kwanaki tafiyata zanyi na barku gidan, amma wlhy in har wnn mgnr ya fito waje wani yaji to nidake ne,domin saina kulla maki makircin da sai kinyi nadamar zuwanki duniya.
"Duk da a kwance nake amma kallo ďaya zakai min ka gano a tsorace nake,wnda ba komai yasa ni haka ba illa kalaman karime.
"Himm lallai kam,komai kake a duniya wani ya fika.
" Tun daga lkcn kamfa-kamfa nakeyi da karime, daga malam har bayi suyi matukar mmki gani yadda na canza.
"Ita kuwa karime dama yasamu, mulki kawai take zubawa a gidan yadda takeso, abin duniya duk yabi ya isheni hakan yasa kullum ina kunshe a ďaki, bana fita filin tsakar gida sbd babu hali nayi kwa'kwa'ran motsi idon karime na kaina.
" bayan wata uku abin duniya ya usheni hakan yasa na yanke shawarar faďi wa malam gsky,koda ko hakan shine sanadiyar barina gidan, domin cutar yana yawa, domin yanzu kusan neman malam akan karime ke karewa, abinda ďah yake mana duk ya rage, tun daga lkcn nasaka mata ido, kwatam da ranar litani da yamma bayan la'asar saiga jini a bayan zani karime, itama kanta bata sani ba.
"Mikew nai daga inda nake zaune naje kamar zan shige ta gabanta da gagata nasa kafa na hanbareta, muna haďa ido sai tace, baki ganine?.
" Au dama mutum na bige?.
"Lallai zulka, to wlhy saina nuna maki kuskurenki.
" ko kuma mu nunawa juna bah.
"Bayi dake zaune tace, wai meye haka ne, kamar kuna jirace da juna? Nifa banga abin faďa ba, dan Allah kuyi hkri.
" duk mgnr da bayi keyi babu wanda ya kulata, inda muke shiga banan muke fita ba, sai dai duk abinda nakeyi bana yarda nayi kusa da karime domin nasan idan har nasake na shiga hannunta sai ta Allah bata mutum ba,sbd kiran samudawa ne da'ita.
"Gani abu yaki kare yasa bayi tura muhammed ya kira malam a kofar gida, koda malam yazo banbar faďan ba,da naga nayaso ya goyawa karime baya, nanfa na taso da