Showing 18001 words to 21000 words out of 29796 words

Chapter 7 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt

29 Oct 2025

420

ranar kasuwa na kwashe na saida nace zanyi amfani da kuďin na rika sana'a domin zama babu sana'a babu daďi.

"Da kuďin sukazo hannuna, sisi ban taba ba kai tsaye gun wani bakon malami naje bayan mu gaisa nake sanar dashi abinda yake tafe dashi, so nake na rinka juya yan gidan duk abinda nace ya zauna, snn kuma kada malam Harisu ya sake wani aure.

" Jin haka yasa malami yankami kuďi masu waya, ban damu ba sbd biyan bukata yafi dogon buri.

"Sisi ban sire ba, haka na ďauki kuďin na basha.

" Saida yai wani tsafbace-tsafbacensa sannan ya ďauko wani ďan karami kwarya ya bani, yaje idan na tare na ijesa ba ďakina can k'ark'ashin gado inda baza'agani ba.

"Koda na dawo gida ban yarda wani ya gani ba boyewa nai, har zuwa ranar dana tare.

"Tunda na tare a gidan malam Harisu nake juyasa son raina, bana lissafin bayi,domin ita da jaka ďaya na daukesu,amfaninta kenan aimata ciki ta haihu.

" koda ta haihu ba lailaine abinda malam yai min yai mata ba,amma duk da haka besa ta daina haihuwa ba.

"Da haka saida mukai haihuwar shidda, nikeda shidda ita kuma biyar,amma da shike muyi yan'bibiyu sau uku-uku yasa yaran sukai yawa, sai dai cikin yan'biyu wasu basuda mahaďi,duk su koma.

"Su muhammed da Suwaiba kuwa duk suyi girma.

" Sbd kada malam ya kulla wa Suwaiba abin arziki idan aurenta ya tashi, yasa naje na haďa kamar da gaskiya a gun Rakiya kanwarsa, har da cewa malam yace kwanana zaizo ya ďauki Suwaiba domin tunda kika ďauketa bega abinda kika tsinana mata na arziki ba, kullum sai faman yawo takeyi a cikin tsumma, kinai mata rikon ko ikula ne sbd bakisan zafin haihu ba.

"Ranar rakiya tai kuka kamar ranta zai fita, gani haka yasa nace mata mafita ďayane kawai shine,idan har tasan Suwaiba tanada manemi ta aurar da'ita ba tare da malam Harisu yasani ba,idan yaso daga baya a sanar dashi.

"Sbd idan har akai mata aure bai isa yazo ya rabata da gidan mijinta ba.

" Nan rakiya ta ďauki shawarata, bayan na koma da kwana biyu mgnr auren Suwaiba ya taso, inajin hakan har ďaki na sami malam Harisu na shirya masa karya da gaskiya, duk nace Rakiya ce daga bakin Rakiya suka fito.

"Duk garin nan kallesa kawai sukeyi domin tunda iyayensu suka koma ga Allah yaiwa zumuncinsu rikon sakainar kashi, bayaso taimawa yan'uwa da ďangi, nace haka Rakiya ke yawa gidan suna da biki tana faďi, bayan Allah ma ishedane irin k'ok'arin da kakeyi akansu.

"Gani ran malam Harisu ya baci sosai, ni kuma nai ta ďurawa auduga fetur, har yakai ga cewa tunda bata gani abinda yakeyi akanta to shikenan insha Allahu daga bazai yarda wani abu ya sake shiga tsakaninsu ba, yarinya kuma zaije ya amso kayansa.

" Jin haka nace a'a kada yaje, ido kawai ya kamata ya zuwa masu, sbd idan yaje yanzu za'ace dama ba sbd Allah ne kadata Suwaiba ba,amma yanzu idan har bafita harkanta da kanta zatasan bata kyauta ba.

"Haka dai naci gaba da zuzuta malam Harisu har naci karfinsa.

"Koda biki yazo babu abinda malam Harisu ya sinanawa Suwaiba, itako Rakiya koda itace ta haifeta iyaka kenan.

"Ranar wata talata aka ďaurawa Suwaiba aure da shehu ďan mai garin garinsu.

"Ni kaďai naje, nabar bayi a gida da raya, ban dawo ba saida naga kwal uwar daka snn na dawo.

"Yan uwan mary kuwa su haďawa Suwaiba sha tara ta arziki, suma saida aka kare kibi kaf snn suka koma garinsu.

" A lokacin su Muhammed da Yahuza sai Husaini duk suna aji uku na karamar sakandiri, gani hazakarsu yasa malam Harisu ya yanzu shawarar kaisu makarantar kwana (boading) dake wata gari da ake kira kagara, makarantar kimiya da fasaha(science and technology) jin haka yasa hankali tashi matuka badan kowa ba sai ďan Husaini da Muhammed kada suje can suyi karatu suzo su zama wani abu a duniya.

"Cikin dare muna cikin hira da malam Harisu, da shike ranar nice da girki, nace" malam.

"Na'am Zulka.
"Wlhy wani abi ke damuna.
"Name fa?.

" Akan mgnr yaran nan mana.

"Wani abune ya faru dasu?.

"A'a, sai dai akan mgnr makarantar da zaka kaisu.

" Nan nai shiru ban karisa ba,"sai naji yace ina sauraranki Zulka".

"Sai naci gaba da cewa, dama gani nayi idan ka turasu wata duniya kamatu, su waye zasu tayaka aikin daji, bayan kana gani yadda yarinan suke maka, duk da kuďin da kake basu amma hakan besa su tsaya tsakani da Allah suyi maka aiki me'kyau ba, dan ma Allah ya taimaka ga yaran nan su fara kawo karfi, shine nake gani ya dace kabarsu suyi karatun ana kawai zaifi, kaga daga nan sai su rinka taimaka maka da aikin gona, ko yaya kagani?.

"Eh kam, kin kawo mgn mai kyau anan, amma zan sake dubawa na gani.

" Tun daga lokacin suka cika da karatunsu a nan gida, zuwa gona kuwa daga Muhammed sa Husaini, sai dai yanzu da kaninsu suka fara tasowa wani lokaci dasu suke tafiya, da shike yara maza sufi yawa a gidan.

"Da haka su Muhammed da Husaini har suka kare maratun a gantale, gani su kawo karfi yasa malam Harisu ya sakarwa Muhammed ragame komai na har kan yau da kullum a hannunsa sbd shine babba.

" Tun daga lokacin nasa masa karan tsana.

"A ban garen Suwaiba kuwa haihuwarta biyu, mace itace babba sai namiji *MUHUSANA da AL'AMEEN.*

" Alhamdllh, zamane Suwaiba da mijinta sukeyi na daďi, bata rasa komai sai dai halin yau da gobe.

"Tunda banji daďin yadda na ganta ba, amma saida batan sha'awa, sbd yadda tai kyau.

"Ranar wata kasuwa malam ya kwashe kayan hatsinsa yakai kasuwa ya saida, bayan ya dawo, bai faďi wa kowa ba daga cikinmu, gani ya shiga ďaki nima na bi bayansa har saida naga inda ya ije kuďin snn ta dawo naci gaba da aikina.

"Da mangaruba,bayan su fita masallaci a gurguje naje na kwashe kaďin kam, naje ďakin su Yahuza na buďe jakan Muhammed na zuba masa kuďin a ciki snn na zuge zip na fita.

"Tun daga lokacin kunnena na kofa domin jiyo abinda zaibi baya, shiru naji sai bayan kwana uku, ranar malam yanaso yai aike kurni yaje ďauko kuďin kenan kuďi yace ďaukeni.

"Babu inda malam Harisu bai duba ba a ďakinsa amma bai gani ba, daga har bayi muna zaune a gefe muna waďar gyaďe ji kawai mukai ya kwaďa mana kira.

"Da shike akwai tazara tsakanin ďakinmu ta nasa, jikina har tsama yakeyi, da sauri na karisa ďakin, gani malam Harisu ya haďa zufa yai sharrrkam yasa nace anzo waje.

"Bakina har rawa yakeyi haďi da tambatar malam lafiya kuwa duk ka wargaza ďakin haka?.

"Wani abu nake nema.

" Abu, wani irin abune haka da zaisa ka wargaza ďakinka haka.

"Wata ijiya ne na ije anan shine yanzu nazo ďauka kuma ban gani ba.

"To shi abu bashida sunane ko kuma....

" Cikin fushi yace min ke ďallah kuďine aka ďaukemi.

"Kuďi kuma? To Allah dai yasan ban san kanada wani ijiya ta kuďi ba, sai dai ko yaya bayi, wata kila ita aiya faďi mata...

" Uhmm Zulka kenan, wacce bayi ido ba yar ciki, ke kenan ma ba'a faďi maki ba balle ni.

"Banza nai da'ita sbd ba itace a gabata ba.

" tsawa duk yaka mana, snn yce duk mutayasa nema.

"mu kwashi mintoci muna nema snn yace, tunda an nema kuma ba'a gani ba mai zai hana yatara yaran gidan duk ya tambayesu.

"Da kar naci k'arfinsa ya amince da'a kirasu,domin a cewarsa yaransa bazasu aikata masa haka ba.

" Duk tarasu akai, takan kananun aka fara bi, babu irin tambayar da ba'ai masu ba amma sukace basu suka ďauka ba.

"Marasa wayun cikinsu ma har kuka saida sukai.

" Snn aka koma takan yayyun, kowa da aka tambaya babu wanda yace yagaji ko kuma shine ya ďauka.

"Gani haka yasa malam Harisu cewa su tashi suje.

"Da sauri na dakatar dasu nace aje a duba kayansu ďaya bayan ďaya.

"Nice jagorar tafiya binciken, su kuma suna biye dani a baya har da malam ďin.

"Jakar Muhammed na fara dubawa,amma ban kai hannu ta inda kuďin suke ba, snn nabi kan na yan uwan, duk saida aka duba babu, har zamu fita, sai naga malam ya koma da kansa yasa hannu yake zazzage kayansu a k'asa, duk zazzage bai gani ba sai ana Muhammed kuďi suka zubo.

" Ina gani haka nasa salati da sallalami, shiko malam jikinsa yai sanyi matuka, hankalinsa ya tashi, Muhammed kuwa babu abinda yakeyi sai kuka haďi da rantse-rantse.

"A sanyaye malam ya kwashi kuďin ya fice, nayi tunanin malam zaiyi faďa, sai naga bece wa Muhammed komai ba, shiko Muhammed kwana yai kuka, gani hankalinsa ya tashi yasa malam kiran Muhammed batare da sanina ba, ya sake tambayarsa gaskiyar malari, nan Muhammed ya faďi iya abinda ya sani har da kukansa.

"Gani haka yasa malam be sake gana mgnr ba, sukaci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.

"Gani haka yasa, nasha alwashin saina raba tsakaninsu, tun daga lokacin nake ďauko kuďi ko kayan jama'a na sawa Muhammed a cikin kayansa, kau harda na makwabta ma,sbd dai malam yaji baya sonsa, tun malam Harisu na kin yarda har yakai ya fara yau da gobe sai Allah, a hankali malam yaji ya tsanar Muhammed na kamasa, tun baya nunawa har yakai ga a ko'ina ma yana nunawa, ko a tsakanin yaran yan'uwansa ne saiya nuna masa babanci,sai ya siyewa sauran yaran gidan kaya amma banda Muhammed idan yai mgn sai malam yace, tunda ya iya sata yaje ya siye da kuďin satar da yake satowa.

"Yau da gobe ya woci wasan yaro, dare ďaya Muhammed ya tsallaka yabar garin.


" Koda muka tashi bamu gansa ba babu wanda ya damu da yaje nemansa.

"mary ce kawai naji labarin ta shiga damuwa ainu.

" Niko wani sabon duniya na buďe, domin yanzu kusan komai na malam su dawo hannu Yahuza, tare suke lisafin duk wani kuďin da zasu shigo ko su fita daga wajan malam, mgnr kara wani aure kuma babu ita.

"Hakan yasa nake tsuuula tsiyata yadda nakeso.

" bayan shekara ďaya da barin gida da Muhammed yai, bayan sallar isha, ita zaune da tsohuwar cikina a waje sbd lokacin zafine, kawai naji kararr mota a kofar gidanmu, kamar daga sama najiyo guďa.

"Da k'ar na mike haďi da tambayar su waye kuma akai wa amarya babu ko gaiyata, koma wanene oho sudai suka sani, tunda ba gidan nan bane, idan jifa ya wuce kanka ya faďa gidan kowa ma.....


" Ban rufe bakiba najiyo wata uwar ĝuďa, aeriririrrrrrrrir matan da ke biyo dasu a baya kuma suna biye dasu suna faďin _*Munafukan duniya mata ana bikinku kuna kuka*_ gani gidanmu sukayo take naji cikina ta murďe, adaddafe na ďuka na kama kujeran da dah nake zaune akai, mikewar da banyita ba kenan saida abinda ke cikina ya fito duniya.......



Kai duniya ashe masifa nasa mace ta fito da abinda ke cikinta batare da lokaci yai ba?.







*///don't 4get cmmnt*
*and*
*vote///*








*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥


_*FITSARIN FAK'O*_

💥💥💥

_(mugunta)_

*FASAHA ONLINE WRITERS*

_F.O.W_

_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_


🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹

_not editing⛏_

بسم اللة الرحمن الرحيم


*∅∅∅*📝
*page15*


................"Bayi dake ďaki, jin guďa na tashi ne yasa ta fito da sauri domin gane wa idota abinda kunnita ke jiyo mata, gaskiya ne?.

"Gani cicirindon jama'a yasata tsayuwa sokoko tana binsu da ido, tafi minti biyar a tsaye snn hankalinta ya dawo gareni, da sauri ta kariso inda nake duke, ina ce ta taimaka min muka koma ďaki.

"Su kuwa yan kawo amarya a tsakar gida muka barsu, duk da takaina nakeyi amma bai hana na kasa kunni domin jin yadda za'ai ba, sbd tunda muke da malam koda da wasa bai taba kawo mgnr karin aure ba balle har yace yasamu matar da zai aura.

"Bayi na cikin wanka yaro kenan, ni kuma ina zauna akan kujera najiyo munryan malam Habu yana mgn da mutane dake waje.

"Ďakin malam Harisu aka buďe masu suka shige, haďe da rangaďa guda, take na sake jin wani bakin ciki ya sake kamani.

"Da shike budurwace kwana sukai a gidan, da shike bcc 6arawo shine kawai ya saceni, sai washe gari suka tafi, tun bayan tafiyarsu nakesa idon shigowar malam Harisu ya dubani da abinda na haifa amma shiru har dare bai shigo ba, sai kawai muga yayowa amaryansa sako, mu kuma ko oho.

"Tun bazanyi mgn ba har saida yakai na 6ara, sai wani abin takaici, koda naiwa bayi mgn" cewa tai hakuri kawai zamuyi, hakan yasa ban sake bi takaima ba, sbd nalura da ita har yanzu batasan ciwon kanta ba.

'Bakin kofa na dawo na zauna ina jiran shigowarsa, har goma na dare malam Harisu bai shigo ba, daga k'arke dole naje na kwanta, abubar fari na tashi naje ina kwan'kwasa masu k'ofa, na jima ina biga kofar snn malam Harisu ya fito ďaure da zani a k'ugunsa, gani nece yasa shi cewa"lafita Zulka?.

"Ko kallonsa banyi ba, na h'au zaginsa, inda nake shiga banan nake fita ba, zagi da gori babu irin wacce ban masa ba.

."Ido kawai ya bini dashi, har na kari abinda zanyi bai tanka min dama yaga zan damesa juyawarsa yai ya koma ďakin haďe da rufe kofa,duk duk da haka baisa na saurara masu ba, daga shi har amaryan saida na zage.

"Bayi dake kwance jin hayaniyata ne yasata fitowa, ta fara bani hakuri, itama haďawa nai na zageta tasss snn na koma ďaki.

"Tun daga lokacin nasa malam sa amaryansa a gaba, zagi da rashin mutunci babu irin wacce banayi masu.

"Gani haka yasa tsoro ya kama Saro, da zaran malam Harisu yafita, tsakar gida nake dawowa na zauna, musamman idan Saro ce dake girki, haka nake sata a gaba da zagi, duk abinda tai bata iya ba.

"Saro ta shiga tsorona sosai, duk lokacin da malam baya gida bata fitowa tsakar gida kowani lokaci tana ďaki zaune, da haka take rayuea a gidan malam Harisu ba tare daya san halin da take cikin ba.",har tasamu ciki, muddu malam Harisu ya siyo mata abu, tasata nakeyi a gaba ko kuma na kwace snn nace idan har tasake ta bari malam Harisu yasani ni da itane a gidan.

" Duk da tsohon cikin da take ďauke dashi, amma bai hana tai min hidima, duk ranar girkina ita kemin girki wanke-wanke shara,duk abinda nake ciki a gidan ita dai bayi tata idone, da shike nasan bani ke waďar gyaďar ba shi isa nake zuwa na amso waďa buhu biyu wataran kuma ďaya, natasa Saro a gaba nace ta waďe min, babu musu haka zata zauna tai min da haka har lokacin haihuwarta yai.

"Ranar wata juma'a bayan malam su tafi masallaci shida yara, bayi kuma taje gidan biki, tunda na lura da yanayin da Saro ke ciki yasa nayi shigewata ďaki na kwance, tun tana ďaurewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login