Showing 21001 words to 24000 words out of 29796 words
Chapter 8 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt
har yakai ga abin yafi karfinta, ina kwance ina jiyo ihunta amma ban tashi naje na dubata ba, shi kuma malam tunda suka fita masallaci basu dawo ba saida akai sallar ba'asar duk a lokacin Saro nakan guiwa, jin sallamar malam ne yasa na mike da sauri na fita haďi da cewa sannu da dawowa.
"Yawwa kawai yace, har zai shige na tsaidashi da mgnr Saro, da sauri yace tana ina?.
" Ďakinta.
"Ba tare daya shiga ďakin ba, ďakinsa ya nufa yaje ya ďauki allo, saida ya kirani ya tambayeni tun wani lokacin ta fata?.
"Bata daďe da farawa ba.
" Na faďi haka ne sbd idan nace ta daďe nasan zai rubuta mata wanda tanasha zata haihu,amma da nai haka nasan bazai rubuta wanda zaisa tai haihuwar gaggawa ba.
"Cikin ikon Allah ina zungura mata ruwan rubutun batafi minti nishin da zatai saiga jijiri ya faďo.
" Wani irin bakin ciki ya kamani ji nai kamar na murk'ushe kan jijirin ya mace amma babu hali, domin iďon Saro nakai.
"Tunda na fita a ďakin ban sake dawowa ba, bayi ce tai ta mata aikin jego har ranar suna, yaro yaci suna muhammed Yaseer.
" Babu yadda yan'uwanta basui da malam ba akan ya barsu su tafi da'ita gida wanka amma yaki, nima na kara zugasa km ya hau ya zauna daram.
"Tunda suka tafi cokali ido na kawo na zuba masu, ko wanka ta shiga idan yaseer na kuka bana ďaukarsa har sai ta fito ta ďau kayanta, mafi yawanci lokuta bayi ke tayata aiki ko kuma raino, da haka har yaseer yai girma, (Allah maji kan bawansa shike raya matance a cikin yayyayye snn kuma ya raya rayyaye a cikin matance) ko sheka ba'ai ba yasser babu inda baya zuwa, shekaransa ďaya aka yayesa sbd wani cikin data samu.
"Bayice uwar raino yar niman gindin zama, gani yadda take kulawa da yasser yasa malam Harisu na yawan yi mata al'khairi sosai, saiya fake da yaro ya.
" Duk da haka bai ďameni ba, sbd daga ita har shi kansa malam ďin duk suna k'ark'ashin ikonane.
"A lokacin da cikin Saro ya tsofa kwatsem muna zaune saiga muhammed kamar daga sama, yai sallama ya shigo gida, ba niba hatta malam mahaifinsa be ganesa ba, yai kyau fatan jikinsa ya canza idan banda k'amshi dake tashi daga jikinsa babu abinda yakeyi.
" Take naji wani irin bakin ciki da kishi ya kamani, har dana sani nakeyi meyasa na kulla masa shirrin da har yasa ya tsallake zuwa birni yanzu gashi kenan yaje ya waye ya goge ya koma saikace bature, amma zanyi maganinsa.
"Da sauri na mike ina yimasa sannu da zuwa, manyan jakukuna biyu daya shigo dashi na kwashe zuwa ďakina, take masa aka kamo min kajina danake kiwo manya dakwale guda biyu aka yanzu, ni kuma na hau aiki kamar da gaske.
" bayi dake zaune idan ban da uhmm babu abinda take cewa,sbd tariga tasan bana aikin banza......
*///don't 4get cmmnt*
*and*
*vote///*
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
_not editing⛏_
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page16*
............."Ina kare aikinsu nakai masa ďakina, lokacin shi kuma yana ďakin malam suna gaisawa.
"Gani su jima bai fito ba yasa duk nabi na tsargi hankalina ya tashi, da sauri na mike zuwa ďakin.
"Bayi na ďakinta, duk da nasan zata iya hangoni amma bai dameni ba, dab da ďakin naje na la6e domin jin mgnr da sukeyi.
"Nafi minti goma ina tsaye ba tare da su sani ba, snn nai sallama cikin ďakin, sabida abinda nake tunani ba haka bane.
"Cikin fara'a ta nace sannunku da hutawa, kai kuma malam ka tsare mutum da surutu, bayan akwai gajiya a tattare dashi, tafiya mai nisa irin haka.
"Daga shi har malam murmushi kawai sukai, snn malam yace idan banda abinki Zulka shekara nawa rabon da muhaďu, idan banda abin Allah ma ni har nafiddaran sake haďuwa da muhammed.
"Ashe dai ba haka abin yake ba.
"Duk da naji zafin mgnr amma sai na faske da, dama mana ai kana nakane Allah yana nasa kuma nasa shine gaskiya, da shike da rabon ku gana ba gashi Allah ya kawosa gareka ba.
"Kwarai kuwa Zulka, nidai babu abinda zance sai dai nawa ubangiji godiya, musamman ma a yadda na gansa, ga dukkani alama ina masa kyankyawar zato.
"Gani yadda malam ke zaro zance da alama idan ba katsesa nai ba, sai zuciyata ta buga, da sauri nace" malam kenan, yanzu dai barshi yaje yaci abinci idan ya kamnala sai yazo ku karisa.
"To Zulka ngd sosai, shi kuwa muhammed ďin mikewa yai ya fita zuwa ďakin na.
"Washe gari da safe, bayan mu karya sai mukaji malam ya kiramu dukkan mu, duk tare mukaje, koda muka shiga ďakin zannuwa ne guda uku rike a hannunsa duk iri ďaya.
" Bayan mu shiga ne malam ya ďauka ya mika wa bayi da shike itace babba yace"ďanku muhammed ne yace na baku, nima da tawa.
"Shaddace fara rasss yadi goma, sai hula da takalmi da kuma turare.
"Mu kuma aka haďa mana da vasilin ďai-ďai, godiya mukai masa amma har cikin zuciyata banji daďi ba, hakan yasa tun daga lokacin muddu nagansa zaune da malam sai na aika yara suje suce bbnsu ya basu kuďin sabulu ko omo ko maggin.
" Duk inayin haka ne sbd nasan in har muhammed yana gun bazai yarda malam ya fidda kuďi daga jikinsa ba, musamman ma da yanzu malam baida kuďi, kwana biyu saiga Suwaiba tazo gun ďan uwarta ko'ina taji labari oho.
"Ganita da nai rike da kaji yasa na amsheta hannu bibiyu sbd koba komai zan meda gurbin kajin dana yanka wa ďa'uwarta, tunda abinda nai tsammani samu daga garesa ban samu ba.
" Haba-haba nai mata, duk da shakuwar dake tsakaninsu da bayi, na rikon da tai mata amma saida na lala6eta ta sauka a ďakina.
"Kwanan ta biyu ta koma, shi kuma muhammed yaje garin su mary yai kwana biyu snn ya dawo.
"Yana dawowa ranar daya ďawo da yamma yake sanar wa malam cewa gobe yakeso ya koma, sbd ubangidansa yace kada ya daďe.
" Jin haka yasa da dare lokacin kowa yai bacci, dama ranar nice da girki, har malam ya kwanta na tadashi, bayan ya zauna, nan na ha'u zugasa ta inda nake shiga ba nan nake fita ba, akan kada ya bari muhammed ya komai birni, daya koma gwamma ya tsaya ya rinka tayaka aikin gona.
"Da safe har muhammed ya shirya malam ya aika aka kira masa muhammed, bayan yazo malam yake sanar dashi mgnr komawarsa birni babu, sbd yanaso ya tsaya ya tayasa aikin gano, har muhammed ya buďe baki yanaso yai mgn da sauri malam ya tsaidasa da cewa banason jin komai daga gareka, idan har kanaso ka gama da duniya lafiya kawai kabi abinda nace.
"Babu yadda muhammed ya iya dole yasa ya hakura, ba karamin murna nai ba, da naji bazai koma birni ba, haka kawai daga haka yazo yai kuďi malam yazo ya daina son Yahuza tunda yanzu dameshi akeyi.
" Tunda daga lokacin dashi ake zuwa gona, kusan aikin gonarma shi keyi.
"Shi kuwa Yahuza hanasa zuwa gonar nai, tunda ga muhammed ya dawo, dama rashinsa ne yasa yake zuwa amma yanzu tunda yana gida Yahuza bazai k'ara zuwa gona ba.
" Mudda malam ya fara mgn hayesa nakeyi da masifa da bala'i a dole yake shiru ya kame bakinsa.
"Bayan wata biyu da dawowar muhammed gida, tunda wata yarinya yar makwabtanmu mai suna Safiya ta k'yalla ido taga muhammed tace babu wanda takeso sai shi,tun tana kunyar faďi masa har yakai ga tacire kunyar ta faďi masa, " shima ya amince".
"Nan suka fara soyayya, ina zaune Yahuza yazo ya bani labari, tunda yace Safiya ce muhammed ke nema nan naji babu daďi har cikin zuciyata,sbd yarinyar mai natsowace ga hankali, snn kuma gashi ubanta mai rufin asirine.
"Daga lokacin na fara tunanin irin abinda zan aikata masa wanda zaisa su rabu, amma kuma rabuwa ai bashine mafita a gareni ba, tunda nasan waye uwarta macece maison abin duniya, to da wnn damar zanyi amfani wajan nemawa Yahuza auran Safiya.
" Tun daga lokacin na kuma muminar k'arya a unguwa, alkhairi kuwa iri-iri nake turawa Hiďe, cikin k'ank'ani lokacin na shawo kanta, da shine itama a gidan sai yadda tai dasu yasa batasha wahala wajan shan kan mijinta ba.
"Ba tare da sani Safiya ba muka shirya komai, da shike shima malam ďin mgnta yakebi hakan yasa ban samu matsala ba, kwatsam muhammed na zaune yaji mgnr airen Safiya da Yahuza, tun daga ranar ya shiga kunci da 6acin rai, niko nace oho ko a jikina.
"Ba'a yanke lokaci mai yawa ba, hakan yasa nan da nan lokaci yazo, ranar sa aka ďaura auran Safiya da Yahuza muhammed yabar garin ba tare da ya sallami kowa ba.
"Tunda aka kawo amarya gidan bata fita koda k'ofar ďaki, kullum tana cikin ďaki zaune hatta gaisuwar safe bata fitowa tai, wani abin takaici ma sai idan dare yai, kome ke haďasu oho idan ta fara zagin da cin mutuncin Yahuza sai abinda ta mance.
"Ta kaici da bak'in ciki su isheni, wani babba abin 6acin raima kiyoshina duk sunaji, gudun kada ta bar min abin faďe a gida da safe bayan Yahuza ya fita har ďaki naje na sameta kwance, da alama ko sallar safe batai ba, tana gani shigata tana kwance amma bata tashi ba saima wani irin kallon da tai min na rainin hankali.
"Ban daka itataba nace mutashi lafiya." tana kwance tana jina amma bata amsa ba har sai da nai baki uku snn tace qlau".
"Ina mai gidan naki?.
" Oho!!.
"Kamar yaya oho?.
"Ke kika sani..
" Ninasa fa kikace Safiya, ko kin mance nine na haifi mijinki!!..
"Au dama kece uwarsa?ai ban sani ba sai yanzu.
" eyya sannu ko, Allah sarki, gaskiya ke abin a jajatamaki ne...
"Kamar yaya?.
"Sabida baki dacen haihuwa ba, domin rankatakam garin nan babu jahili dak'ik'i irin Yahuza, koda shike gado yai ďan shi isa duk abinda zai aikata bana gani laifinsa..
" Cikin takaici da bakin ciki nai saurin fita a ďakin, sbd kaďa raina ya 6aci nai mugun aiki gashi kuma ba abokiyar yina bane.
"Ina fita nayota tana faďin" in dai nice wlhy kaďan kuka gani, domin banyi komai ba daga cikin irin rashin mutuncin dana shirya maku.
"Kai tsaye ďaki nashiga na fara nadama gami da danasanin haďa wannan auran.....
*///don't 4get cmmnt*
*and*
*vote///*
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
_not editing⛏_
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page19*
.............."Tun bayan rabuwar Safiya da Yahuza ya shiga damuwa, gani haka yasa nasa malam a gaba a dole saiya nemowa Yahuza makaranta.
" Babu yadda beyi dan ya fajimtar dani ba akan bashida kuďi, rashin kuďin nema ya hanasa kai sauran yaran makaranta, niko nace ban yarda ba,gani yaki jin mgnta yasa na murďa kambun, kamar yadda na saba.
"Ina zaune saiga malam ya biyoni har ďaki yana tambayata wani makaranta nakeso Yahuza yaje, da shike ba kansa na sani ba, saida na kira Yahuza yazo snn na tambye makarantan da yakeso, nan yace sokoto yake da sha'awar tafiya.
"Jin haka yasa malam cewa bashi da kuďi, tunda akwai a makwabtan garinmu mai zai hana bazaije nan ba, ko zamu samu sauki.
" Gani Yahuza ya 6ata fuska yasa nima na canza tawa fuskan, nan na ďakarkare nace duk inda zaije saidai yaje ya nemo kuďi.
"Da malam yaga inada niyyar yi masa tijara da sauri ya dakatar dani, da cewa babu komai Allah zai rufa asiri.
"Hakan yasa malam yaje ya siyar da mafi girman gona daga cikin gonakinsa domin nemawa Yahuza makaranta, cikin sa'a yasamu gurbi a jami'ar sokoto.
" Tun daga lokacin daga Saro har Safiya kowa ya kami sana'a domin kai yaransu makaranta, sbd suga malam baida niyyar kaisu, daga mai waďar gyaďa sai mai dakau, ko k'ulili, duk da dai makarantar gwamnati ne amma wani lokaci sai abu ya gagaresu,hausawa suce idan dambu yai yawa bayajin mai.
"Musamman ma Saro da take yarinya, kafin ta yaye ta ďauki wani shi isa abubuwa suka haďu suka cakuďe mata, duk da k'arancin shekarunta amma sbd wahala saida ta koma kamar tsohuwa" itako bayi tunda tai haihuwa biyar bata sake samu wani cikin ba.
"Ni kuwa yar'kalloce domin kansa yasan koda wasa bai isa yacemin baida kuďin kai yarana makaranta ba.
"Bayan tafiyar muhammed da wasu watanni saigashi yai sallama jikinsa ďauke yake da wasu irin kaya kamar na sojoji, tun daga bakin tasha samarin gari ke kora masa baya har zuwa cikin gidanmu, tsakar gida yacika yai fak'il da jama'a waje babu masaka tsinke," shiko malam sbd murna har kwalla saida yai, takaici da bakin ciki yasa gaisuwar girki ban amsa masa ba, daga k'arshema tashi nai na nayi shegewata ďaki, a zuciyata kuma ina cewa inama da Yahuza ne ya sami irin wnn aikin.
"Gani na shiga ďaki yasa Muhammed bina har ďakin ya duka har k'asa ya gaidani, a fili kam ban nuna masa komai ba amma a zuciya cewa nake Allah yasa kafin ka koma su koreka," cikin girmamawa muka gaisa snn yabi sauran yan uwana duk ya gaidasu, kwanan Muhammed bakwai ya ya koma bakin aikinsa, tun daga lokacin yake aikowa malam kuďi, muddun naji malam na shiwa Muhammed albarka sai naji wani irin bakin ciki ya kamani, kai tun ina ďaurewa har yakai idan yafara mgn take nake dakatar dashi da cewa su kuma sauran yaran da basu baka kuďi saika tsine masu.
"Jin haka yasa koda zaiyi bayayi a gaban idona sai dai a bayan idona.
"Tun bayan zuwan Yahuza makaranta yanzu haka shekaransa biyu kenan bai sake lekomu ba sai dai aike, aikema na kuďi ne, tun su bayi da Saro suna gulmarsa idan naji mu kwashi yan'kallo har nima kaina abin ya fara damuna.
"Ban tsinke da al'amarin ba saida Muhammed yazo dagnr aure, yasamu mata a garin da yake aiki har ma su dai-daita mgnr aure yanzu haka zuwan iyayensa kawai akeyi.
"Ba k'aramin tashin hankali da ruďani na shiga ba musamman ma dayace baya buk'atar komai daga hannu malam domin yariga daya haďa duk wani abinda yasan ana zubawa cikin lefe.
" Ina cikin wani irin alhinin saiga sakon mutuwar alhj K'asim mijin da mary ta aura bayan fitarta daga gidan malam,"jin wnn irin labarin ya k'ara birkitani, kafin kwana biyu na nemawa kaina mafita".
"Gun malam zani nasa yai min aiki akan mary dashi kansa malam ďin, yasa malam yaji ya k'ara tsanar mary, kai ko sunarta ma bayason jin, ya jefa masu kiyayyar junar da tafi ta ďan.
"Saida naga ya aikata abinda nace masa snn hankalina ya kwanta naji na samu natsuwa.
"Sbd na tabbatar da magani yayi ko baiyi ya na tambayi malam zuwa yiwa mary gaisu, nan malam ya hauni da faďi inda yake shiga banan yake fita ba.
"A