Showing 1 words to 3000 words out of 29796 words
Chapter 1 - FITSARIN FAKO Hausa Novels Complete By Maman Usman.txt
FITSARIN FAK'O BY MMN USWAN
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAKO*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page1*
......."Anya iya Ummai ba wani mummunar aiki kika aikata yasa Allah yake nuna maki ta wnn sigar ba?,sbd Allah duk inda ake tunanin idan anje za'a samu waraka amma abu ya gagara, wanda cutarsu yaki naki ankai kuma su warke amma sai nakine mai magani zaice adawo gida?.
"A gskya wnn al'amari ya fara bani tsoro, kullum ke kenan kashi zaune fikiri zaune kamar wata yar goye? Ki dubafa sbd Allah tafiya ma ta gagareki, idan kin san da wata a kasa gwama ki faďi ki daina wahalar da jama'a.
"Duk mgnr da juwaura keji shiru kawai iya Ummai tai mana jinta, har saida tai shiru, snb iya Ummai tace uhmmm haďi da ijiyar zuciya.
*∅∅*
"Shekaru talatin da suka shuďe, na kasance macece mai kushe da hassada, ga sonkai.
" Koda na auri malam Harisu yanada mata biyu nice ta uku a cikin kuma nice mai karancin shekaru a cikinsu, hakan yasa ba karamin gata malam Hasiru ya nuna min ba.
"Duk da irin gatan daya nunamin da fifitani da yakeyi akan sauran abokan zamana amma besa na kyalesu ba.
"Domin tun ina dandali, (wato budurwa kenan) Allah yani yarinyace mai tsiwa da rashin kunya, duk girman mutum bana shakkan na faďi masa mgn, har takai ta kawo, idan har za'aje nimo mgn a makwabtan garinmu nice nake jagoran.
" haka yasa akemin lakani sa *tsilaga gashin gira.*
"Ni kuma a lkcn daďi nakeji domin gani nake dyk abinda nakeyi birgewa ne, babana yai faďa har da duka amma baisa na daina ba, asalima duk ranar daya dukeni akan na daina abinda nakeyi, in har nafita saina ďauko masa mgnr da yafi wanda nayi a baya.
" gani duk da zagi bazasu yi, saiya koma addu'a, hakan yasa koda malam Harisu yazo niman aurena ba'ai shakkan bashi ba, sbd ansa nima ďin ba kanwan lasa bace.
"Lkcn da zanyi aure yan' garimu har murna sokeyi suna faďin Allah ya barasu da ala'kakai.( wai gawa da maka)
"Uwar gidanmu itace Maryam amma ana kiranta da *MARY* sai wacce nakebi ita kuma sunanta Salamatu, ita suna kiranta da *BAYI* duk da irin son da malam Harisu kemin be yarda na raina masa mata ba, hatta sunayensu be yarda na rinka kira ba sai dai yaya, a lkcn mary na goyan yarta mace wacce ake kira da Suwaiba, ita kuma bayi Allah be bata haihuwa ba a lkcn.
"Gani su haďa kai su biyu duk abinda zasuyi basu sani a lissafi, yasa nasha alwashin farrakasu, duk da na kasance mai karancin shekaru a cikinsu.
"Da shike malam Harisu ďan kasuwa ne, kasuwannin kauye yake ci, hakan yasa nayi amfani da wnn damar duk ranar da baya gida, nake takaransu domin su tanka na zagesu.
" Tun basu biyeni har yasa ga su fara, biyeni, da zaran mu fara faďa zagesu nakeyi wani lkc kwabta ke shigowa su rabamu, gani haka yasa malam Harisu yai mana iyaka dasu, da cewa duk wacce ta sake nimata da faďa a cikinsu tofa a bakin aurenta.
"Koda makwabta sukayi lbri irin hukuncin daya yanke, babu yadda basu domin nusar dashi gsky ba, amma ya kasa fahimta, niko daďi naji ba kaďan ba.
"Da haka naci gaba da ruwa wa malam Harisu gida, bayan mary ta yaye Suwaiba ta sake samu wani cikin, ni kuma har lkcn ban samu ciki ba, hakan yasa naji bakin cikin samu wnn cikin nata.
Tunda mary ta yaye Suwaiba bayi ta ďauketa, gaba ďaya komai na Suwaiba ya koma ďakin bayi.
"Ni kuwa tunda naga basu shiga harkata yasa duk nabi na tsigu, musamman idan naga su kebe kansu suna hira, gani bazan jurewa haka ba, isa duk lkcn da naga suna hira duk da nasa badani sukeyi ba amma bai haka na tsoma masu baki.
" da suka ga haka, da zaran na saka masu baki sai su daina mgnr.
"Hakan ba karami batami rai yakeyi ba matuka, saida cikin mary ya tsofa snn nima na samu nawa cikin.
"Tunda na gane inada cikin yasa na ďauko sabon salo kala-kala, su kansu su mary da bayi har mmkina sukeyi, dimin basu taba zaton da karanci shekaru na zan iya aikata abinda nake aikatawa ba, shi kuwa malam Harisu duk sai abinda nace masa, musamman ma da yaga inada ciki.
"Da shike malam Harisu mutum ne maiso yara.
"Gani komai ya ciyo idan yana dawowa kasuwa yace Suwaiba ba, hakan yasa nima na kirkiri karyan bazan iya cin abincin da ake girkawa a gida ba, kullum bakin tasha yake zuwa ya siyomin tsire ko balangu da shayi.
" Idan naci sai na rage raguwa da safe har bakin kofarsu nake zuwa na zidda, sbd sugani suji haushi.
"Gudun kada suyi mgn cibi ya zama kari tsakaninsu da malam Harisu yasa suka zubamin ido....
*wnn kenan*
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page2*
..........."Haka yasa nake yadda nakeso ba tare da shakka ko shayi ďaya daga cikin su ba.
"Ciki wani daren juma'a Allah ya azurta mary da sambalelen ďinta na miji, malam Harisu yai murna sosae,tun wayewar gari yan barka suka cika gidan mu, gani haka ďaki na koma na zauna, shiko malam Harisu sai faman rawar jiki yakeyi, duk abinda akace ana bukata jikinsa na rawa yake kawowa.
"Ban tsinke da al'amarin ba sai ranar suna, hatta kayan fitan suna kala uku malam Harisu yai wa mary, mu kuma nida bayi yai mana kala ďa'iďaya, duk da banso haka ba, amma dole nayi godiya, sbd kaďa ya gano ni.
"Yaro yaci suna *MUHAMMED KABEER* da rana sbd yan suna keyi illa mgnta babu abinda sukeyi, gani haka yasa har taro ya tashi ina kwance a ďakina.
"Tun daga lkcn nasha alwashin bari mary da gida,amma hakan ba zai samu ba, saina fara takan bayi,duk da ta kasance bamai mgn bace kuma sufi kusa da mary ďin, amma idan banbi ta kanta ba, bazan samu cinma burina ba.
"Bayan kwana biyu da haihuwar mary, tambyi malam Harisu zanje garunmu ziyara, cikin sa'a ya amince, tsaraba sosae ya siyami har kofar giday yazo da mai mashin ya ďaukeni zuwa garinmu.
"Sbd babu hanyar da mota zai shiga garinmu, idan ma ansamu mota sai ranar kasuwa,ranar kasuwan ma, motar dake ďaukar tumakai ne kawai yake shiga garinmu, hakan yasa malam Harisu ya biya mai mashin na tafiya dana dawowa.
"Muna isa, bayan na gaida mmnta da bbna saida muka ďan raba hira snn na mike da sunar zan zaga na gaida ďangi.
"Ina fita ban tsaya ko'ina ba, sai gidan malam na giďin dutse, cikin sa'a ranar babu jama'a ba kamar sauran ranakun ba, bayan mu gaisa na sanar masa abinda ke tafe dani.
"Jin haka yasa malam na giďin durse tambata yanzu mai nakeso ayi min.
"Sai nace inaso a raba mary da gidan, snn kuma idan ta tafi kada malam Harisu ya sake tunata ko abinda ke tsakaninsu balle har yai tunanin dawowa da'ita.
"Ba tare da yai min mgn ba,wani fefe mai ďauke da kasa akai sai wuri dake kan kasar ya ijiye a gabana, hannu yasa ya ďibi wurin yai wani irin abu haďi da tofe wurin da iyayyaiyaku da yasaba yi snn ya watse wurin akan yashin.
"Duk abinda yakeyi idona na kai, koda ya watse wurin komawa sukai suka sake haďewa gu ďaya, sau uku malam keyi amma wurin suki rabuwa, shine yakw shedamin, raba mary sa malam Harisu abune mawuyaci, sai dai na canza shawara.
" Duk da banso haka ba amma babu yadda zanyi dole na canza shawara, nace idan zai wuce ya tura mata da ciwo wanda zaiyi wiyar magani.
Take malam ya turawa mary da kaďangaruwa, kuďi masu yawa na bashi, snn mukai sallama.
"Koda na koma gida ban zauna ba, tun da bukatata ya biya.
"Sallamar mmnta sa bbna nayi naje na hau mashin zuwa gida, ďan murna harda tsaraba na siye masu, ina sallama Suwaiba dakw zauna a kafar bayi tana bata abinci a guje ta mike tazo natamin oyoyo, hakan yasa nayi amfani da wann damar na bata tsarabar dana siyo, dama tunani nakeyi yadda zan tukaresu sa tsaraba tunda lkcn da zan fita ko sallamarsu banyi ba.
"Koda Suwaiba ta kaiwa bayi ledar sai bayi tace ta medomin, nan take na shashe ina basu hkr, haďi da zabga masu karya nace suyi hkr lkcn da zanfita ban sallamesu ba wlhy mai mashin ďin da zai kaini ne ya matsa a cewarsa wai sauri yakeyi.
"Nan ta shashar da mgnr harda godiya, a tawa zcyr kuwa cewa nake nafiku godiya.
"Ina shiga ďaki na busa da dariya ta murna.
"Da dare misalin goma na dare mary taje ban ďaki kama ruwa, har ta duka tana boli kawai taga wani abu kamar kaďangare ya gilta ta gabanta, a tsorace ta mike haďi da kuwa, jin kuwanta yasamu fitowa daga ďakunarmu su malam Harisu da bayi suna tambayar ta lafita?.
"Jikinta na karma take masu bayani, buďe bakin malam Harisu yace rashin addu'a, nan tazo ta shige ďakinta muma mukai namu ďakin.
"A daren ranar bcc da mary batai ba kenan, sbd kadangariyar tariga ta shige mata jiki......
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page3*
..........."Tunda naga haka, ba karami murna nayi ba, domin hakona ya kusan cinma ruwa,malam Harisu da bayi kuwa kusan nace akan mary suka kwana, addi'a kam babu irin wnda malam Harisu beyi wa mary ba amma abu ya gagara,ita kuwa mary idan ba kukan ciki ba babu abinda takeyi, domin a cewarsa abu nayi mata motsi a ciki.
"Duk da kowa yasan waye malam Harisu a cikin garin, domin mutum ne mai tatako ga sani darajar ďin Adam, snn kuma gashi malami, domin duk garin babu mai iliminsa, hakan yasa shike masu limanci.
"Hakan yasa baiso asan abinda ke faruwa a gidansa ba, amma wani abin mamaki ba'a yini ba mgnr rashin lafiyar mary ya karaďe gari, duk wacce dubiya da abinda take faďi, sai wani abu ďaya shine har a lkcn babu wacce ta gano matsalar dake damu mary.
"Tun malam Harisu naki yarda da mgnr masu bada magani gargajiya da gaya abu yaki ci yaki cinyewa da kansa yake zuwa amso mata.
"Wasu suce sai sun ganta kafin subada magani wasu kuma babu ruwansu domin kuďin kawai suke bukata.
" Tun mary na iya tashi har abu yakai ga kwanciya, komai yi mata ake, cikin kuwa kace yan'uku ne a cikinta, gani haka yasa bayi ta ďauki Muhammed ta haďa shi da Suwaiba ta rike, malam Harisu yaji daďi hakan da tai,amma ni kuwa banji daďi ba, domin har cikin zuciyata banki ace harda goyon ne ya kamu da laluran ba.
"Kwatsam muna zaune da rana a tsakar gida kawai muka jiyo sallama,ido na zuwa ina kwallonsu sbd bakin fuska ne, ban taba gani su ba"Amma jin bayi tace maraba da yan *kwatankwaro* na gano yan'uwan su mary ne.
" bayan mu gaisa na tashi daga gun na koma ďakina, su kuma ďakin mary suka shiga har da ita bayin,snn suka gaisa, gani halin da yar'uwansu ke ciki hankalinsu ya tashi, ko ruwa basu iya sha ba, kuka kawai sukeyi, jin muryan kukansu, nayi dariya haďi da cewa kaďanma tagani.
"Ana cikin haka saiga malam Harisu yai shigo, dama tunda mary ta kamu da wnn laluran bai cika nisa ba, ďan kasuwan da yake zuwa ma duk ya daina, tunda dama yanadai zuwa ne kawai sbd kayason zaman gu ďaya, da fara'arsa suka gaisa sukai masa snn da mai jiki, gani kwallar da sukeyi yasa shi basu magana haďi da nasifa.
"Kwanansu biyu a garin snn suka koma,amma duk duba, mutum ďaya ta rage,wacce suke ciki ďaya da mary, a cewarta bai kamata a bar bayi da aiki ita kaďai ba, ga raino snn kuma ga jinya.
"Nida dake ďaki zaune nace ohoo dai, cokali bazan kauda ba.
"Tunda yan mary sukazo suka ga yadda jikinta yake yasa duk inda sukaji mai magani sai suje su amsa mata,amma har a lkcn basu dace ba.
"Shima malam Harisu haka, sai dai idan beji lbrin mai magani ba, addu'a kuwa safe da rana, yai yayi mata abata tasha snn kuma a shafe mata jiki dashi.
" Da haka saida mary ta shafe wata takwas a kwance, snn ina gam da haihuwa, gani cikina ya shofa yasa kanwar mmnta da yayar bbn sukazo ďaukata,zuwa gida haihuwa, duk da banso haka ba,amma babu yadda na'iya dole nabi umarni iyayena da mijina na bisu zuwa garinmu *wasagu*, gani kwana biyu bayi bataje gida garinsu duba mahaifiyarta ba kamar yadda ta saba, hakan yasa mmnrta ta shirya zuwa ďubata daga garinsu *ďaki takwas* bayi taji daďin gani mmnrta da tai, bayan tayi sallah taci abinci snn ta shifa ďikin mary dubata, gani yadda mary ta koma ne yasa mmn bayi tace akwai wani mai magani a makwabtan garinsu, kuma ana dacewa,idan har zasu iya mai zai hana bazasu kaita nan ba.
"Har malam Harisu yaki yarda da mgnr,amma da shike akwai yar'uwan maryn yasa ta tirje tace sai anje, idan Allah yasa ba'a dace bane sai su hkra.
" Washe gari da mmn bayi zata koma tare suka tafi, ita da marin da kuma yaruwanta.
"Cikin sa'a suka sami mai maganin a gida,bai tafi daji ba, sbd dama yawacin zamansa a jeji yafi zamansa a cikin gari sbd yanayin aikinsa.
" koda yaga jikin mary, kallo ďaya yai mata, ba tare dayace uffan ba kai kawai ya kaďa, wani ďan karamin littafi ya snn yajima yana dube-dubensa snn ya matse kusa da inda mary ke kwance ya fara wani irin iyayyaku.
"Mary dake kwance wani irin kara tasa, haďi ta lekewa kamar zata mike, hannu mai magani yasa ya ďauko ďan karami tulu ya karkata ya tsiyayi ruwan dake cikin tulu ya watsa wa mary har sau uki, a karo na ukune tafara mgn, da cewa turowa akai ya shiga jikinta, ba kowane ta turota ba illa abokiar zamanta.
"Take mmn bayi dake zaune hankalinta ya tashi, hanji cikinta ya kaďa matuka.
"Sabida tasan babu wacce za'a zarga illa y'arta.
"Ita kuwa kanwar mary duk da batace komai ba, amma saida ta canza fuska.
"Itama mmn bayi dake zauna tun a lkcn tafara danasanin........
*mmn uswan ce📚✍*
[6/30, 6:16 PM] Momcy: 💥💥💥💥
_*FITSARIN FAK'O*_
💥💥💥
_(mugunta)_
*FASAHA ONLINE WRITERS*
_F.O.W_
_*💥{In facing valuable knowledge and entertainment is our concen }💥*_
🌹
*NA:MMN USWAN* 🌹
بسم اللة الرحمن الرحيم
*∅∅∅*📝
*page4*
.............."Saida mai magani yasha fama da aljani snn ya yarda zai fita,haďi da alkawarin bazai dawo ba snn ya fita.
"Da shike kauye ne, be amshi kuďi masu yawa ba.
" Hayaki da wasu itatawa ya basu snn sukai sallama, masu mashin ďin daya kaisu garin sune suka dawo dasu, amma wnn karon ba irin wacan bane, domin wnn karon mary da kakafarta take tafiya, wace karo kuwa ririke ake da'ita.
"Tun daga bakin kofar garin *bena* jama'a ke mmkin gani mary yadda take zaune akan mashin daram,ai kuwa tun kafin su iso gida abinka da kauye nan da nan mgn ya