Showing 15001 words to 18000 words out of 52544 words
Chapter 6 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Jidda s Mapi.txt
shikenan na d'ibo ruwan dafa kaina, yana cikin tunanin yaji tace "kamar muryan Bilal nakeji? Saura kad'an yace "mata eh saime?....amma bayason asirinshi yatonu, Madina ce tace eh Minal shi kika Aura shima naganshi da Sanda,
Minal tace Allah shikara ai daba makaho yazama ba da gurgu ne mugu kawai,
Bilal ranshi yab'aci yace " ke karkimin rashin kunya zanci Ubanki Idan kika rainani danasan ke za'a Auramin da saidai inmutu ba Aure k'azamar banza....haba yaya? Aina Kasansu dahar zaku fara fad'a kaida bagani kakeba? Cewar Sabir Wanda yashigo da Plates na Abinci guda biyu ahannunshi,
Kame-kame Bilal yafara Am..Amm Dama naji suna hirane kuma ina bacci shiyasa nake musu fad'a, yaya ai dakasansu dako tsawa bazakayi musu ba kawar Amaryace da Amarya, yafad'a yana murmushi,
Bilal ne yafara magana azuciyarshi shikenan nashiga uku na cuci kaina.
Wannan me kamada Aljanarce mamata, wayyo Allah ya zanyi? Anya bazan janye Aurennan ba?
(Nikuma nace waya fad'a maka ana janye Aure Bilal?)
โote & Comment
Jiddah S Mapiโ๐ป
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*MAKAUNIYA CE*
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
By
Jidda S Mapi
Page 12...
Yaya tunanin me kakeyi? Ai kamata ace kayi farin ciki tinda burinka yacika koba hakaba? Cewar Sabir, eh hakane Sabir ai yanzuma ina cikin farin cikin Kaine baka luraba, Sabir ne ya ajiyewa su Minal abincin Untyna kuci Abinci bismillah, zama sukayi suka fara cin abincin, kallonsu Bilal yayi tacikin glass d'inshi, azuciyarshi yace "wayaga Amarya da kawarta Allah yakyauta"
Minal kuwa cikin ziciyarta tana tunanin yanda zatayi zaman Aure da wannan mugun mutumin, Idan nayi mishi rashin kunya nasan zasu fasa fitar dani kasar waje aduba idona, Idan nabishi ahankali kuma zai rainani dayawa ya zanyi?
Madina taga cowslow dayaji bama da cocumber sai tura abincin take kamar ba gobe, Madina zafi nakeji kayan jikina sunyi nauyi wallahi bazan iya bacci ahakaba, to yaya kikeso muyi minal? Ina zan shiga in nemo miki kayan bacci? Idanun Minal ne yafara cika da hawaye tasan da tana gidansu da Umma ta canja mata kaya zuwa na bacci Amma yanzu haka zata kwana da kayan jikinta...kiyi hakuri Minal Idan yaso gobe saiki tambaya subaki ko?
Gyad'a kai kawai Minal tayi,
Suna gama cin Abinci Madina tafitar da plate d'in, suna hira kad'an kad'an har bacci ya d'aukesu awajen."
Bilal kuma yana shiga d'aki ya kwanta agado yana tunani ya akayi yarinyannan ta makance? Wata kila garin Neman tsokana ta tsokano wanda yayi mata illah, tab'e baki yayi yace "Anyway matsalarta ce bata shafeni ba, kuma koda tana makauniya Idan tayimin raini sainaci ubanta"
Shima ahaka bacci yad'aukeshi.
Hajiya Babba kuwa aje Afrah tayi tana koya mata kissa da kisisina da munafinci kala kala saida ta tabbatar Afrah tahau layi kafin takyaketa sukayi bacci.
_washe gari_
Minal ce zaune akasa tarike gyallen Madina kemkem tana kuka wallahi Madina babu inda zaki nasan Umma bazatayi fad'a ba,
Minal wai bakida hankaline? Agidan mijinkifa kike ya za'ayi muzauna tare?
Suna cikin haka Hajiya Babba tashigo d'akin wai ina Makauniyar take? Kinzo kin zauna ad"aki baki iya gaida mutane bane? Ko agidanku ba'a baki tarbiyya ba? Koda shike ina zaki samu tarbiyya awancan akurkin gidan, tashi Minal tayi tana cewa gani Hajiya kiyi hakuri,
Bazanyi hakurin ba kifito kidafamin shayi me citta sabida nan gidan d'ana ne zanyi yanda naso.
Madina haushi gidan yafara bata bata kara cewa komai ba ta d'auki jakarta sai tafiya, Minal batasan ta tafiba.
Rike sandarta tayi tana laluben inda zatabi, dakyar tasamu kofa tana tafiya tana lalube, dab kofar falo taji karar tafiyar mutum, tsayawa tayi tana tambaya Dan Allah inane kitchen? Kitchen kikeso kisani Makauniya? Bataji dad'in sunan da ake fad'a mata ba tace eh, okay kibi hannun damanki zakiga wata kofa saiki shige ciki kinji?.
Minal tace "to nagode"
No need cewar Afrah wacce take murmushin muginta.
Hanya Minal tad'auka har inda akayi mata kwatance, tana zuwa tabud'e kofar tashige, shiganta keda wuya taji kare yafarayi mata haushi, rud'ewa tayi jikinta yafara rawa har sandarta yafad'i, jin Karen yana shunshunarta yasa tafara ihu tana bubbuga k'ofar amma taji an rufe kofar daga waje,
Afrah ce tarufe kofar tanata dariya yau bazan barki ba harsai karennan ya cinyeki mayya kawai,
Suna cikin haka motar Daddy tayi horn jin Daddy zai shigo yasa Afrah sake kofar tashige falo dagudu,
Minal kuwa ganin kofar yaki bud'uwa yasa tafara tsalle acikin d'akin tana ihu tsakaninta da Allah, Daddy ne yaji ihun yayi yawa sai kawai yabud'e kofar Jin anbud'e kofa yasa Minal fita dagudu mamakine yakama Daddy meya kawota d'akin kare? Cheww wannan wawiya ce wallahi ke...ke ubanme kikeyi ad'akin kare? Minal ko jinshi batayi tsabar tsorata. Tsawa yakuma daka mata keba tambayarki nake ba? Ubanme kike ad'akin kare?
Ki..kitchen nake nema, kitchen d'in anfad'a miki nan gidanku ne? Mayya wayasan ko nama kikazo nema.
Wallahi ba nama nake nemaba Hajiya babbace tace min in dafa mata shayi....la'ila ha illallahu ke Aljana bakya tsoron Allah, nida nake d'aki tin d'azu ina bacci taya zance miki kibani shayi cewar Hajiya babba, wacce take tsaye abayan kofa tin shigar Daddy.
Minal ce tafara rantse rantse wallahi tallahi Daddy itace ta aikeni...ke wayake karya kenan? Uwatace take karyan? Aa gaskiyafa nake fad'a maka...Tass Daddy yawanketa da mari har saida tafad'i akasa, daga yau karki kara rainamin uwa kinaji?
Gyad'a kanta tayi cikin hawaye tace to.
Bilal ne yaji hayaniyar tayi yawa yana zuwa yaga fuskar Minal tayi jaa ta b'angare d'aya, Ke meya sameki kike kuka?
Daddy yayi caraf yace babu abinda yasameta wai karene yabita shine kaji tana kuka, tashi kutafi d'aki yarinya sannu kinji? Cikin mamaki Minal tace Aa dama... Daddy yayi saurin zuwa gefenta ahankali yace "idan kika sake koda wasa Bilal yasan abinda yake faruwa wallahi saina fasa fitar dake kasar India"
Jin ance kasar India yasa Minal saurin share idonta tace "eh Bilal karene yabini shine nafad'i,
Duk abinda akeyi akan idon Bilal saide yakasa jiyo abinda Daddy yake fad'awa Minal"
To Bilal ga hannun matarka riketa kutafi d'aki, hannun Minal yakamo yahad'a Dana Bilal.
Jan hannunta Bilal yayi zuwa d'akinshi, suna shiga yakulle kofar da sakata yaja hannunta zuwa kan gado, ajeta yayi tareda cewa "ke zanyi miki wata tambaya idan kika sake kikamin karya saina kwakwule idonki da wuka"
Firgita Minal tayi tace wallahi bazanyi maka karyaba Karka kwakwule idona Daddynku zai kaini kasar India agyaramin Dan Allah kayi hakuri.... Naji me Daddy yake fad'a miki d'azu? Babu komai, ke wato karyan zakiyi ko bayan naga duk abinda yafad'a miki,
Bama wannan ba tin jiya wannan kayanne ajikinki har wari yake tsabar dattin jikinki, kalli yanda janbaki yab'ata miki fuska, ke wace irin k'azama ce?
Ya akayi kasan kayan jiyane ajikina bayan idonka baya gani, kodai karya kake kaiba makaho bane? Eh niba makaho bane pretending nake, mezakiyi? Kuma idan kika sake kika fad'awa mutum cewar niba makaho bane wallahi saina hana akaiki kasar India, Dan Allah kayi hakuri wallahi bazan fad'awa kowa ba, dayafi miki alkhairi, tashi kije kiyi wanka karki cikamin d'aki da tsami, shiru Minal tayi, yasake cewa nace kije kiyi wanka.
To ai Ummace takemin wanka, what? Ke wannan katuwar ce ake yiwa wanka? Kinga idan baki tashi kikayi wankarnanba saina saki aruwan daya tafasa.
Hawaye Minal tafara zanyi Amma kanunamin toilet d'in, Jan hannunta yayi zuwa toilet d'in ya d'auko towel yawurga mata yace "saura kib'atamin toilet" bai Jira me zatace ba yafita tareda tura mata kofar.
Minal tsayawa tayi kamar gunki tana tunanin ta ina zata fara wankan, Zama tayi akan tyles na toilet d'in tafara rusa kuka, nashiga uku Umma bazan iya rayuwa babu keba, Umma kece gatana aduniyarnan, Umma nayi Alkawarin idan aka kaini India idona yabud'u bazan zauna da kowaba sai ke....tana cikin kukan taji muryanshi ke soson da sabulu yana cikin bathtub idan kin gama ki aje awajenki Dan banason datti,
Oh ni Minal tinda Allah yahalicceni ban tab'ajin Abu wai bathtub ba ta ina zan fara nema?
Tashi tayi tacire kayanta tareda d'aura towel d'in lalube lalule tafara a toilet d'in cikin ikon Allah ta tab'o soso acikin wani k'aton Abu, azuciyarta tace yawwa nasamu badroom d'in (to kuji wai badroom ni turanci irin nasu Walidation s Mapi da Hafsat Ibrahim Khalil d'innan ba ganewa nakeba, lols) kan pompom ta tab'o batayi wani jira ba ta kunna taredasa hannunta taji ko ruwane, ihu ta sake tana tsalle jin ruwa tafasasshe ahannunta bata daina ihunba kuma bata kashe pompom d'inba cikin zuciyarta tace (hande min boni) yau nashiga Uku.
Saurin shiga toilet d'in yayi yana tambayarta ke meye haka kikewa mutane ihu? Nalura bayan Makanta harda hauka ke daminki, yanzu me akayi miki?
Cikin kuka tace (wala kod'ume) babu komai.
Ke gashi kina kuka kuma kicemin (wala kod'ume). Zaki fad'a kosai na tattakaki?
Na..na kone ahannuna tafad'a tana murza hannunta.
Meya konaki? Ruwan zafine na kunna a badroom shine yakonani, dariya yaso yayi Amma saiya fuske, yace chewww idan baki iya abuba kitambaya mana akoya miki, girman kai da jiji dakai basa tab'a Barin mutum yakoyi abu, Akwai Wanda yakaika girman Kaine mugu kawai duk cikin zuciyarta take maganar, saida yahad'a mata ruwan wanka yad'auketa yajefata a bathtub d'in kafin yafita.
Wanka tafara cikin jin dad'in ruwan harta gama tayi ta Neman hanya kafin tafita.
Tana zuwa tayita neman man dazata shafa Bata samuba, dahaka tahakura ta kwanta akan gado, tana kwanciya tajita akan wani abu, data tab'a sai taga mai da kaya d'auka tayi tasa kayan tashafa mai tayi kwanciyarta.
Duk abinda takeyi akan idon Bilal lumshe idonshi yayi azuciyarshi yace Ashe dagaske MAKAUNIYA CE ai nazata pretending takeyi yanzu inyi mata dukan tsiya, to Amma meya sameta? Ya akayi ta makance? Tab'e baki yayi yace (d'okam damuwa mako) wannan damuwanta ne.yafad'a da yarensu na asali wato fulatanci.
"Waya yad'auko tareda kira hello DPO? d'ayan b'angaren akace yes dawa nake magana? Sunana Yusuf d'an kanin baban Latif Wanda kuka rikeshi sabida sharri da akayi mishi, okay meyafaru? DOP zan baka miliyan Biyar karike Latif ko ciwon kai banason yasameshi, idan kuma nasa akayi bincike Nagano kana hukuntashi zan kai karanka koto dasunan ka karb'i cin hanci, sannan banason kowa yasan wannan zancen, idan ka yadda katuromin account numbarka yanzu, miliyan Biyar? Cewar DPO, kana tantama ne? Bilal yafad'a,
Aa nayadda zan turo maka insha Allahu yanzu za'a cireshi a cell a office nawama zai rink'a zama...okay
Bilal ne ya katse wayarshi tareda cewa zanyi maganinkane kwad'ayayye"
โote comeent & share
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*MAKAUNIYA CE*
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
By
Jiddah S Mapi
Page 13...
"Tashi yayi yashiga toilet domin yayi wanka, saida yawanke cikin bathtub d'in sosai kafin ya iya wanka aciki, towel ya d'aura babba tareda sa karami akanshi yana gogewa,
fitowa yayi yaje gaban mirror yashafa manshi me kamshi tareda taje gashin kanshi Wanda yake bak'i wuluk, agogonshi yad'auka yasa a hannunshi na dama, kafin yajuya zuwa wajen wardrobe, wani dark blue na polo yad'auko da farin wando dogo, jikin aljihun wandon dark blue ne, sawa yayi a hankali, nan asalin kyaunshi na cikakken Fulani ya bayyana,
jikin rigan an rubuta Mad Over You da manyan harufa.
zuwa wajen mirror yayi yana kallon kanshi a madubi, a zuciyanshi yace " Alhamdulillah ko ba'a fad'amin ba nasan inada kyau, to meyasa zan cuci kaina in Auri Makauniya?
Dolene in nemo wacce takeda lafiyan idanu, wacce zataga cikin k'wayan idanuna tafurtamin kalaman soyayya, wacce zansan tana cikin farin ciki ko bak'in ciki, Amma wannan Makauniyar ai bazata iya wad'annan abun ba, Anyway zansan abunyi" yana fad'in haka yad'auko eye glass nashi bak'i babba yamak'a afuskarshi, sandarshi yad'auko tareda Fita a d'akin"
Har ya iso bakin kofa yatuna cewa yafad'awa Minal shiba makaho bane "to idan tafad'awa Daddy fa? Kai anya banyi kuskure ba? Wannan yarinyan da karamin bakintan nasan magana baya mata wuya, kai dolene naja mata kunne yafad'a tareda komawa cikin d'akin"
Minal kuma bacci yayi mata dad'i cikin baccin take mafarkin an kaita India an gyara mata idonta yayi sauk'i, murmushi tafara najin dad'i.
"Wato ta kwanta akan gadona tana bacci harda murmushi ko? Zakici Ubanki yarinya, sandar hannunshi yad'auko yakwala mata a bayanta, afirgice Minal tafarka tana salati, ke? Harkin samu damar yin murmushi akan gadona? Wato baccin dad'i yake miki ko? To bari kiji daga yau idan kika kara kwanciya akan gadona saina kwakule idonki d'aya"
Da sauri Minal ta dirko akan gadon, Ash tafad'a cikin Azaba Dan ta bugu da jikin gadon ba wasa.
"Kad'an kika gani, nan gaba wuta zan aje akasa kifad'o akai mayya, kuma idan kika sake Daddy yasan cewa niba makaho bane saina kwakule idonki da daddare kina jina?"
Cikin rawan jiki Minal tace "eh"
"Kitashi ki gyara d'akinnan sannan kicanja bedsheet d'in akwai wani a cikin wardrobe ki shinfid'a,
Minal tace "to"
Saura nadawo bakiyi ba saikin gane kuranki Miskiniya kawai.
"Yana fita Minal takwanta akasa tana kuka, nashiga Uku ni Minal wannan wani irin bak'ar kaddara ne? Dana sani baya maganin komai, ya Ubangiji ina rokanka daka fitar dani a wannan rayuwar, ya Allah ka d'auki raina, awannan lokacin..kukane yakubce mata tasa hannunta ta toshe bakinta dashi, hawayene yakebin hannunta har zuwa wuyanta. kitashi kiyi aikin daya saki Minal karki jawa kanki matsifa cikin zuciyarta take magana, tashi tayi tafara laluben gadon, cikin ikon Allah tasamu tacire bedsheet d'in, d'aukan bedsheet tayi tafara share cikin d'akin dashi, dakyar tagama sharan, tafara Neman inda wardrobe yake, ahankali takeyin komai cikin nutsuwa Har Allah yasa taga bedsheet d'in d'aukowa tayi ta shimfid'a dakyar,
Haka tagama gyaran d'akin cikin zuciyarta tace Alhamdulillah nahuta dawannan matsifaffen, koba komai zai barni da idanuna koda bana ganin komai"
Kwanciya tayi akasa tana d'an hutawa, muryan Hajiya babba taji afalo tana cewa "ina Makauniyar takene? Yarinya bazaki fito ki zauna a cikin 'yan uwanki ba? Wannan wani irin bakin haline? Zaki fito ko saina zo?"
Dasauri Minal tamike tana Cewa "gani Hajiya babba kiyi hakuri gyara nake"
Gyaran Ubankine? Akwai gyaran dayafi sada zumunci ne?
Fita Minal tayi tana lalub'en kofan falo, ahaka harta iso cikin falon tazauna akasa tana baiwa Hajiya babba hakuri,
Ke dallah kimin shiru, tashi zakiyi kishare cikin falon nan sannan ki goge ko ina, kina jina?
Minal ce tace "to" Hajiya zanyi....kada kiyima kiga ikon Allah mayya kawai Mara gata kwad'ayayya, tashi kifara maza"
"Mikewa Minal tayi tana Neman tsintsiya bata ganiba, Hajiya a taimakamin da tsintsiya, Wani irin tsintsiya? Kiyi da d'an kwalinki, sa'arki ce ni dazakice in nema miki tsintsiya? Mara tarbiyyar banza,
Minal cire d'an kwalinta tayi tafara goge cikin d'akin, gashin kanta ne ya bazu yazo mata har fuska, idan ta d'aure gashin saiya kara kuncewa,ga falon yayi mata girma harta gaji tabarshi haka, laluben inda take jin karan TV tafara don ta goge, dakyar tasamu ta goge TV da receiver, Bilal ne yayi sallama a falon tsayawa yayi yana kallon yanda take kokarin gyara gashinta daya zubo mata afuska, azuciyarshi yace " me kuma takeyi afalo? Wannan yarin yan mahaukaciya ce, nida nace tagyara d'akina kuma tazo tana gyaran Babban falo?"
Karasawa inda take yayi, yana zuwa yarike gashinta yana ja, "wato ke bakyajin magana ko? Ince ki gyara d'akina kizo kina gyaran falo? Kuma ba d'an kwali akanki? Ko bakisan maza suna shiga falon bane?.....kayi hakuri yaya Bilal Hajiya babba ce tasani gyaran Falon,
Shine me? Bata kai tasaki gyaran bane?
To barima kiji kina gama gyaran nan kije kibawa flower ruwa kina jina?
Tace eh, cikin azaba Dan ita kad'ai tasan irin rik'on da yayiwa gashinta, saketa yayi tayi tangal-tangal tafad'i akasa,
Tashi tayi dakyar tafara Neman hanyar Fita, tana fita taci karo da Hafeez Wanda yake tsaye abakin kofa yanajin duk abinda sukayi da Bilal, hannunta yarike tareda janta, tsorata Minal tayi tafara tambaya wayene? Ina zaka kaini?
Shiiiii kidaina magana wajen flower zan kaiki, da Minal taji haka sai tayi shiru"
"Bayan lambu yakaita yace " zauna" zama tayi shima yazauna agefenta har jikinsu yana gugan juna, d'an matsawa gefe tayi atsorace tace "lafiya kuwa"
Haba baby meyasa kika cika tsoro ne?.
dafarko dai sunana Hafeez, matsayin kanin Bilal nake agidannan, naji duk yanda kukayi dashi, nasan Bilal baya sonki kuma bazai tab'a sonki ba musamman yanda kike miskiniya, Bilal da mata manya yake harka, masu kud'i da aji ba irinki kamar tsinken tsire ba, bugu da kari gaki Makauniya"
Nasani baya sona nima kuma na tsaneshi cewar Minal.
idan harkin yadda da abinda zan fad'a miki kuma kika Amince, na rantse da Allah a cikin kwana Uku zan kaiki India agyara idonki tsaf kifara ganin duniya, idan kuma baki yadda ba to wallahi yanzu kika fara ganin wulak'anci a gidannan kai ba gidannan bama ako ina,
Da sauri Minal tace menene kakeso kafad'amin Wallahi zanyi Inde zakasa akaini India infara gani"
Numfashi Hafeez yaja tareda cewa "kiyimin Alkawarin bazaki fad'awa kowaba" dasauri tace "nayi maka Alkawari"
"Okay to idan kin yadda zan rika biya miki bukatanki wanda nasan Bilal bai tab'a yimiki ba, nima kibiyamin nawa bukatan, Minal tace " menene bukatan naka?"
Bawani Abu bane domin nasan mafi yawan 'yan mata yanzu Bazawaraye ne, kema inasa ran haka kike ko?
Dasauri Minal tamike tareda cewa "kasan me kake fad'a kuwa Hafeez? Baka da hankali ne? Zinafa kake niyan muyi, hawayene yafara bin kumatunta, ina matsayin untynka kake min irin wannan maganar? Minal kin shiga uku, ina rayuwarnan zata kaimu, mutane ba tsoran Allah kowa yazo wajenka daniyan taimako saiya nemi yayi lalata fakai, Hafeez idan haka ka d'aukeni Allah ya isa tsakanina dakai, bazan yafe maka ba mugu azzalimi, don 'yan mata bazawaraye ne shine nima kakeson ka lalatamin rayuwa? Gara na zauna babu idanu da inyi zina".......ke ya isa dalla karki rainamin wayo, an fad'a miki bansan sirrinki bane?
Inace ke kike ciyar da gidanku da sunan talle kije kina rabawa gayu jikinki a titi, shine yanzu Dan kina gidanmu kike nema kiyi pretending, to bari naja kunnenki, idan kika fad'awa mutane abunda yafaru tsakaninmu saina saceki insa acire idon naki gaba d'aya, yana fad'in haka yabar wajen,
Minal zama tayi akasa tana kuka. Wannan wani irin k'azamin gida kika shigo ne Minal? Ya Allah katsareni ka kareni daga sharrin mutanen gidannan"
Bilal saurin juyawa yayi don bayason Hafeez yaganshi azuciyarshi yace "wato soyayya sukeyi shine yajuya mata baya, shiyasa take kuka, nasan Hafeez nasan halinshi akan mata babu macen da zaiyi soyayya da ita wani Abu be shiga tsakaninsu ba, wannan ma Ashe mazinaciya ce, Karuwar gida wacce tafi na waje hatsari, dolene insan abunyi"
โote & comment
Jidah S Mapi
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
*
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*MAKAUNIYA CE*
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
By
Jiddah S Mapi
Page 14...
*___________________________________*
*๐KAINUWA WRITERSโ๐ผ ASSOCIATION*๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
"Barin wajen yayi da sauri yana sake sake azuciyarshi, lalle yarinyannan tacika Karuwar gida,