Showing 51001 words to 52544 words out of 52544 words
Chapter 18 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Jidda s Mapi.txt
yayi yace "mommy waye wancan?"
Tambayar ta bawa mommy mamaki tace "mijin Minal ne shine d'ana danake Baku labari" a hankali ta labarta musu abinda yake faruwa, Jikin Hamma Yarda yayi sanyi sosai Sannan yaji zuciyarshi ta karye, lalle yayi hutun jaki da kaya yanda yasa rai zai
Auri Minal sai gashi Wani ya rigashi, Allah mai iko, Minal ce ta karaso wurinsu tana dariya da farin cikin ganinsu cikin murna tace "Hamma yarda yaushe kazo?"
Dakewa yayi yace "mun d'an jima anan, ya kike?"
"Lafiya lau ya Adamawa?"
Yace "Adamawa lafiya lau ya mijinki?"
Bataji dad'in tambayar dayayi mataba a hankali tace "gashi can lafiyarshi kalau"
'Dago kanshi yayi suka had'a ido da Bilal murmushi Bilal ya Sakar mishi, shima murmushin yayi ya Mika mishi hannu suka gaisa, Mommy tace "gobe ai tunda gakunan saimu tafi gaba d'aya ko?"
Inna tace "hakane zamuje duka"
_Washe gari_
Dukka Familyn suka Shiga Babban Mota sukaje Gombe wurin Mahaifiyar Minal, saidai Wani abin mamaki suna zuwa sukaga yanayin gidan ta canza daga gidan talakawa zuwa gidan masu kud'i, Minal ce ta zaro ido tace "kai gaskiya munyi b'atan hanya ba nan bane"
Bilal ma abin yabaahi mamaki, Sunyi parking domin tambayar gidan sai ganin wata mota sukayi yashigo layin, daidai kofar gidansu Minal motar ta tsaya, Latif ne yafito daga motar, jikinshi sanye da suited, yasa bakin glass, cikin Mamaki Bilal yace "kai nan nefa gidan mushiga dai mugani"
Dukka suka fito daga motar suka Shiga cikin gidan, Minal a bakin kofa ta tsaya tana tsoron had'a ido da Umma, saida Bilal yayi da gaske kafin ta yadda ta b'uya a bayanshi suka Shiga, suna shiga sukaga Umma zaune akan kujera tana shan Maltina gefe d'aya kuma Latif ne yake zaune yana danna waya, minal ce tafara sallama, Umma d'ago kanta tayi tace "aa minal 'yar Autan mata me miji sai yau kika tuna da uwarki? Koda shike ai kin samu gidan masu kud'i kina cin kaji da kayan sanyi, sannu da kokari, nima Allah bai barni hakaba Yabani d'a me hankali da kula dani kuma shine wanna tayi nuni da Latif.
"Minal ce ta zube akan gwiwowinta tace "Umma na tuba wallahi nayi hakane sabida wasu dalilai, nayi hakane sabida inason a kama Alhaji Umar ace ana sace matar d'anshi inason a kamashi da laifi a kullezhi ko za'a tsira daga zalunci da cin amana irin nashi, Cikin kuka ta fad'awa Umma duk abinda yake faruwa da Wanda yariga yafaru, Umma jin wannan bayani ba karamin rikita ta yayaiba , juyawa tayi gun Bilal tace " to amma meyasa bakayimin bayani da wuri ba?"
Bilal dukar da kanshi kasa yayi domin shi kunyar Umma yakeji sosai, Umma ce ta mike takawo ma su Hajiya da Daddy tabarma tanayi musu sannu da zuwa, Cikin fara'a suka Amsa, Baby waccetunda suka Shigo ta d'aura idonta akan Latif taji zuciyarta ta buga , Latif ma satar kallonta yake tayi tin d'azu lokaci d'aya yaji ta gudu da nutsuwarshi, Bilal ne ya bugeshi yace "da Allah ka daina ganemin kanwa wannanfa itace Nabeela"
A kid'imeLatif yatashi yana Kallon baby cikin mamaki yace "are you serious?"
Bilal ne yayi mishi bayanin komai, Latif yace "kai vary surprise to Amma meyasa tafi da kyau yanzu tazama fresh"
Bilal dariya yayi yace "saiba ka zuba mata ido shiyasa"
Dariya Latif yayi yace "to ai yazama dole nazuba mata idon ko"Bilal dariya yayi yace "kai sai yaushe zakayi Aure?"
Latif yace "sai kabani kanwar ka tukun"
Cikin jin dad'i Bilal yacenabaka bakada matsala ta wannan fannin"
Latif yace "nifa da gaske nake ba wasa ba"
Bilal ma yace "to ni dawasa nafad'a maka?"
Dariya sukayi suka suka tafa.
"Sunyi kwana biyu a gombe ranar da zasu koma, Daddy ne yace " to bai kamata abar Alahaji Umar wato yayana hakaba, sabida nasan duk abinda yake faruwa bani da Wani damuwa akaina INA cikin hankalina, nayi hakane domin na tsiratar da yarana daga tarkonshi, yanzu dolene ya girbi abinda ya shuka, waya yaciro yakira DPO yayi mishi bayanin komai, DPO yace sujirashi yana zuwa zasje gidan alhaji Umar tare, su Mommy da Baby da Bilal sunyi fari cikin jin Daddy yana cikin hayyacinshi, Mintina kad'an motar 'uyan sanda suka tsaya a kofar gidan Gaba d'ayansu suka shige ciki, Hangar gidan Alhaji Umar suka nufa, lokacin dasukaje Hajiya Babba ta rke Afrah tanata sheka Amai domin tin lokacin da Bilal yatafi takama zazzab'i, ta game sosai tayi fari wannan jikinnata duk ya zube dama dai Dan gatanai tazama shiru shiru bata yawan maganar Hajiya Babba da Daddy ne tsaye akanta daddy yarasa meyake ciki, Ciwon so yana nema ya kashe mishi 'ya, Gashi Hafeez yazama abinda yazama yanzu sat a komai bane a wurinshi, Yana tsaye yaji sallaman mutane juyawan da zaiyi yayi ido hud'u da Baban Bilal da Maman Bilal da Nabila sai DPO da kuma sauran da bai sansu ba, Baya baya yafara yana kallon kofar, hanyar gudu yake nema DPO yad'aga bindiga yace "kana gudu zan harbeka" cak ya tsaya yana kallon su, da Sauri ya karasa wurin Daddyn Bilal ya zube a kasa yana rokan gafara, Daddyn Bilal d'auke d'auke kashi ya d'auke yace "baking alkami yariga ya bushe yaya" yana fad'an haka ya juya yabar gidan gaba d'aya yanajin zafin ace d'an uwanshi shine ya cutar dashi, Sabir ne yafito daga site nashi ganin Bilal yasashi zuwa da gudu ya rungumeshi yana dariya , Bilal ma rungumeshi yayi yana dariya yace "I miss you" tureshi Sabir yayi cikin wasa yace "wani missing bayan ka tafi ka barni"
Dariya Bilal yayi yace "to Amma ai kana raina"
Afrah ganin Bilal da Minal datayi bakaramin tada mata hankali abun yayi ba, nan ta kara cire Bilal a ranta, "Sabir Bani Pow" Cewar Hajiya Babba, cikin Mamaki Sabir yace "pow kuma Hajiya me zakiyi dashi"
Ware ido Hajiya Babba tafara Ashe Ita tinda taga Polisawa cikinta ya rud'e shiyasa batayi magana ba, Dariya Sabir yafara yace "ni ai da sun tafi min dake Hajiya"
Bilal ne ya sunkuyar da kanshi yace "kayi hakuri Sabir"
Sabir hace "Aa babu komai ai duk Wanda yayi laifi Dole a hukuntashi"
Hajiya Babba ta bud'e Baki zatayi magana Sabir hace "basuyi nisa ba"
Cip Hajiya Babba ta rufe Bakinta bata. Kara koda motsi mai karfi ba, domin a rayuwarta tana bala'in tsoron 'yan sanda, Afrah kokarin Mikewa take Amma ta kasa, Minal ce ta iso wurin ta rikeata tana mata sannu.
✔ote & comments
*Wattpad*
_@Jiddah S Mapi_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Page 43...
By
Jiddah S Mapi
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio
~Afrah kallon Minal kawai takeyi cikin mamaki, Minal sai faman sannu kawai takeyi mata harta kaita d'aki, suna shiga Afrah ta rungumeta tana kuka tareda Neman gafaranta Minal tace ba komai Allah ya yafe mana baki d'aya, Bilal ne ya shigo d'akin fuskarshi a had'e yace "Babyna inajin yunwa fa ki nema min Abinci kar na mutu"
Dariya Minal tayi tace "rago kawai"
"Nine ragon?"
Minal murgud'a mishi baki tayi tace "eh"
Shiga d'akin yayi da gudu itama ganin haka yasata tashi ta d'ale gadon tana tana ihu, Afrah murmushi kawai tayi sun birgeta matuka, har takeji inama ace itace, Cikin share hawaye tafara Neman gafarar Bilal, Bilal ma yace ya yafe mata, haka sukayi kwana biyu a gidansu Afrah, Hajiya Babba sai nan nan take da Bilal idan yace zaisha ruwa saitayi wup ta d'ibo mishi domin tsoron kada ya kira mata 'yan sanda, Maman Afrah ma ta nemi gafaran su Minal da Bilal duk sun yafe mata, Hamma Yarda ganin Afrah tayi hankali yasashi tambayar Aurenta a wurin Bilal, ba b'ata lokaci Bilal yabashi itama Afrah taji Hamma Yarda yashiga zuciyarta, rana d'aya akasa Auren Hamma Yarda da Afrah, Baby da Latif akan sadaki Dubu d'ari, Daddy ne zai zama waliyyinsu 'yan Matan duka, gyare gyare akeyiwa Amaren gaba d'aya harda Minal Inda suka zama kawayen juna, sunja Afrah jiki tamkar 'yar uwarsu.
***************
"Cikin Minal sai kara girma yake, Bilal da mommy suna kula da ita sosai, Saidai muce Allah ya sauketa lafiya, sukuma Amaren Allah yasa ayi biki a sa'a"
Tammat bi Hamdilillah, Anan nakawo karshen wannan littafin me suna "MAKAUNIYA CE" Kuskuren danayi Allah ya gafarta mini, Tunatarwa danayi kuma Allah yabani ladanshi.
*GODIYA*
Banida bakin dazan gode muku masoyana masoyan littafin makauniya ce, musamman 'yan group na MAKAUNIYA CE FANS GROUP 1 da kuma MAKAUNIYA CE FANS GROUP 2 hakika kun bani gudumawa me yawa babu abinda zance muku saidai Allah yabar kauna, Aliyu Ibrahim kaima ina gode maka hakika kaima kabada gudummawa nagode sosai.
*BAZAN MANTA DA KUBA KANNENA*
Walida S Mapi
Abubakar S Mapi
Aisha S Mapi
Halima S Mapi
KHadija S Mapi
Zahraddeen S Mapi
Yasir S Mapi
*KE TA DABANCE*
Maryam S Mapi
*MUCH LOVE TO MY DAUGHTER*
Afrah
*GODIYA GAREKU MAPI FAMILY*
Maryam Mapi
Hauwa Mapi
Halima Mapi
Zainab Mapi
Hafsat Mapi
Na'ima Mapi
Sadiq Mapi
Haruna Mapi
Sudais Mapi
Aisha Mapi
Khadija Mapi
Shu'aibu Mapi
Faisal Mapi
Hajara Mapi (RIP)
Rukayya Mapi (RIP)
Sharifa Mapi (RIP)
Zuwaira Mapi
Khairat Mapi
Nana Mapi
Amir Mapi
Khalifa Mapi
Sadiya Mapi
Alkali Mapi
Jamila Mapi
Barista Mapi
Yusuf Mapi
Hafeez Mapi
Nagode sosai Saimun had'u a littafina na gaba Wanda insha Allah zanyi iya bakin kokarina Dan ganin na kawo muku shi bada jimawa ba.
"Kada Ku manta zaku iba bibiyana a shafina na.
Instagram @Pretty jiddah
Facebook Jiddah S Mapi
Wattpad Jiddah S Mapi
Har kullum ina tare d'aku.
Ban yafeba wa duk Wanda ya siyarmin da littafin Makauniya ce domin bana kud'i bane, ayi hattara.
Allah yahad'amu a haske
✔ote & comments
*Wattpad*
_@jiddah S Mapi_