Showing 39001 words to 42000 words out of 52544 words

Chapter 14 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Jidda s Mapi.txt

29 Oct 2025

552

yasata tashi da gudu taje ta rungumeshi, shima runtse idonshi yayi ya rungumeta sosai domin a wannan lokacin yanada buk'atar haka.

"Afrah jin bai hantareta ba yasa taji jikinta duk ya mutu da ganin yanayinshi, ya rame sosai saiya kara haske fuskarshi tayi fayau,
'Dago kanta tayi tace " Yaya meya sameka haka duk kabi ka rame?"

Idonshi ne yacika da hawaye a wannan lokacin idan baiyi magana ba zuciyarshi zata iya bugawa, cikin muryan Kuka yace "Afrah soyayyace, soyayyace tasa nazama haka, ta gujeni"
Kara rungumeta yayi yaci gaba da kuka kamar karamin yaro.

Jikin Afrah ne yayi sanyi, ganin yanda yake kuka, a hankali tafara bubbuga bayanshi tana lallashinshi,
Da kyar tasamu yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, Amma har yanzu yaki sakinta.

Hajiya babba ce taga Afrah ta jima, d'ankwali ta d'aura tafito tana kiran "Afrah ina kika shigane.....turus ta tsaya ganin Afrah rungume da namiji, Salati tafara tana tafa hannu, tace " shikenan Afrah kin zauce, yanzu tsabar rashin kunya zaki gayyato kato cikin gidannan da rana tsaka ki rungume? Hawaye tafara sharewa da bakin zaninta tanata salati.

Afrah ce ta saki Bilal, Hajiya babba tana ganin Bilal ta zaro ido, tace "La haula wala kuwwata illa billahi, Bilalu? Kaine ka rame ka fige kayi bak'i kamar d'an kasar Kenya?"

Bilal bai kulata ba ya d'au jakarshi zai wuce, Afrah ce tayi saurin karb'a tace "kawo nakai maka d'aki Yaya".

"Murmushi yayi ya mika mata suka Wuce Hajiya Babba data saki baki".

✔ote & Comment

Wattpad  @Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi


Page 36...
*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


Har d'aki Afrah takaishi, tana zuwa ta ajiye mishi jakarshi, tashige cikin toilet d'in, ruwan wanka ta had'a mishi, tareda fesawa towel nashi turare, fita tayi taje wurin dayake zaune gefen gado ta dafa kafad'arshi tace.

"Yaya kaje kayi wanka sai kayi sallah, sai kaci Abinci kafin ka huta"

Murmushi yayi yace "nagode Afrah"

Afrah ma cikin tausayinshi tace "ka daina godemin yaya"

Tashi yayi yashiga toilet itama Afrah fita tayi da niyar dafa mishi indomie.

Bayan Minti talatin Bilal yagama wankarshi, yana fitowa yaga Afrah zaune kan gado hannunta rikeda Plate, murmushi yayi mata Yawuce yaje ya shafa mai, wardrobe yaje ya d'auko kayan baccinshi, ya koma toilet yasa kafin ya fito,
Afrah ce tace.

"Yaya ga abincinka"

Karb'a yayi ya bud'e yafara ci, gishiri yayi yawa a abincin amma ya zaiyi yarinyar ta damu dashi sosai, dahaka ya daure ya cinye indomie Tass, yace.

"Yayi dad'i"

Dariya Afrah tayi tace "nagode, yanzu ka kwanta ka huta"

Bilal yace "sai nayi sallah"

Afrah tace "oh hakane fa, kayi sallah saika kwanta"

Tashi Bilal yayi, ya idar da sallah tareda yin nafila raka'a biyu, yana idarwa yahau gado ya kwanta zuciyarshi a cunkushe, bayajin dad'in komai, magana ma daurewa kawai yake yi, Afrah ce ta rufe shi da bargo, cikin sanyin murya tace.
"Good Night"

Juyawa tayi zata tafi taji ya riko hannunta, zuciyarta ne ta tsinke, da sauri ta juya Dan tabbatar da shine ya rike hannunta,
Ganin Bilal yana hawaye abin ya matukar tada mata hankali, da sauri ta karasa wurinshi tana tambayarshi ko lafiya?.

Hannunta ya damke yace "Afrah ki taimaka ki nema min ita, wallahi ina cikin matsala, bazan iya bacci ba sai naji muryanta, koda ba magana me dad'i zata fad'amin ba kitaimakeni...."

Afrah jin dalilin kukanshi ba karamin haushi abun yabata ba, ita ta tsani ayi zancen yarinyar a gabanta, ko sunan Minal bataso akira mata, cikin danne fushinta, tafara shafa gefen fuskarshi tana bashi hakuri, a Hankali yadaina kukan yana sauke ajiyar zuciya, Saida yayi bacci kafin tafice a d'akin tana kara jin tsanar Minal a ranta.

Minal da baby suna cikin jin dad'insu, yau suna zaune a falo Mommy tana yiwa Minal kitso tace "Albishirinku"

A tare sukace "goro"

Mommy tace "Daddynku yace zamuje Adamawa gobe idan Allah ya kaimu"

Baby ce tayi tsalle ta diro tace "da gaske kike mommy?"

Hararanta Mommy tayi tace "dama ina miki wasane?"

Cikin jin dad'i Baby tace "yawwa zanje inga baffa na"

Minal ma murna tayi Dan dama zaman gida ya isheta, tashi sukayi kowacce tafara had'a kayanta, Mommy ce tabaiwa Minal wasu dogayen rigunan Abaya masu kyau,
Minal godiya tayi tana kara jin matar a ranta sosai, ji take kamar Ummanta, hawayen da suka fito a idanunta ta share tunawa da Ummanta datayi,
A zuciyarta tace.

"Umma insha Allah zan dawo gareki Amma saina nemi ilimi yanda zan kwaci 'yancina koda na koma gidan Bilal ne, domin bazan iya jure wulak'ancin dana jura a baya ba,
Wasu hawaye masu d'umine suka gangaro kumatunta tunawa da Moment d'inta da Bilal, agogon dayake d'aure a tsintsiyar hannunta ta kalla a hankali tafara shafa jikin agogon tanajin wani Abu acikin zuciyarta.

"Minal kidaina sa Bilal a ranki, yariga yasamu abinda yakeso awajenki babu wani Amfani dazaki karayi mishi, Bilal ba sa'anki bane yafi karfinki nesa ba kusa ba" shine abinda take fad'a a zuciyarta.

Baby ce ta dafata tace "lafiya Minal wani irin tunani kikeyi haka tin d'azu nake magana baki ko jina?"

Minal tayi saurin share hawayenta, Murmushin karfin hali tayi tace "babu komai sister, kinsan rayuwarne wani lokacin Saida tunani".

Zama baby tayi a gefenta, ta riko hannunta tace " Minal? Na dad'e da sanin akwai damuwa a tattare dake, ki d'aukeni kamar 'yar Uwarki wacce kuka fito ciki d'aya, wani lokacin b'oye Abu a zuciya yana kawo babban matsala, gara kifad'a ko shawarane abaki wata kila ki dace, bance dole kifad'amin abinda yake daminki ba, Amma kisani ni 'yar uwa na d'aukeki".

Minal Murmushi tayi tace "bana b'oye miki komai fa sister, babu wata damuwa, kin fad'awa yaya Mujahid naki gobe zamuyi tafiya?"

Baby ce tace "la kinga kuwa wallahi na manta tsabar kaud'i, Allah Allah nake gobe yayi muje Adamawa wallahi kodan nasha Nono".

Minal dariya tayi tace " to Hajiya saiki kirashi ai yanzu".

Baby tace "yawwa Minal kinsan wani Abu? Wallahi namanta fad'a miki dama tin jiya yaya Mujahid yace natura mishi Nombarki, ina wancan abokin nashi Wanda sukazo dashi ranar jumma'a? To shine ya dami yaya Mujahid wai yana sonki, kuma yanada hankali zaku dace sosai"

Minal tashi tayi tace "kefa akwai ki da rigima sister, nida zan koma garinmu bada jimawa ba inani inayin saurayi anan?"

Baby ce tace "to ai idan Rabon Aure ya rantse a tsakaninku Ko awani gari kike sai anyi"

Minal tace "abar maganar nan, karki bashi nombar domin ni maza ma na tsanesu gaba d'ayansu bazan iya soyayya ba"
Tana fad'an haka ta fice a d'akin ta tafi d'akin mummy tayi kwanciyarta kan gado".

_Asuba tagari_

Baby ce tariga kowa tashi agidan tayi wanka ta shirya kayanta, tayi zaman jiransu Daddy,
Minal ce tashigo d'akin hannunta d'auke da plate, turus ta tsaya tana kallon Baby cikin mamaki tace

"Sister har kin shirya? Da karfe nawa kika tashi haka?"

Baby tace "kinsan yanda nakeson zuwa Yola kuwa? Ai nayi missing sosai".

Minal ta zauna akasa tafara cin Abinci ko magana bata karayi ba, Baby ma sauka tayi ta zauna suka faraci tare, Saida suka gama Minal tayi wanka, tashirya cikin wata doguwar rigar Abaya maroon colour, da gyallenshi maroon jikin kayan beats ne daga sama har zuwa kasa, bakar flat shoe tasa ta rataya wata karamar jaka baka, Baby datayi tsaye tana kallonta ne tace "gaskiya Minal kinada kyau, da ace inada yaya namiji wallahi dasai ya Aureki, kodan kyaun halinki" hawayene ya taru a idonta da sauri ta juya tana gogewa.

Minal ce ta karaso wurinta ta dafata cikin sanyin murya tace "meyasa kullum idan zakiyi maganar yaya sai kinyi hawaye? Kinsan banason kinasa kanki a damuwa, Bayan iyayena babu Wanda yatab'a nunamin so kamar iyayenki da kuma ke, kinga nima bazanso in ganki a damuwa ba".

Baby share hawayenta tayi tace "ba komai Minal".

Mommy ce tayi sallama tace "Ku fito maza kar gari yayi haske sosai"

Jakar kayansu Minal ta d'auko suka nufi parking space, driver ne yakarb'a yasa musu a Booth,bayan wasu mintina suka d'au hangar Yola, Baby sai jin dad'i takeyi zataje taga baffanta.

Da mangariba suka suka iso (Jippu Jam) Tsayawa sukayi a restaurant kowa yaci Abinci kafin suka shiga cikin Yola, A wani d'an madaidaicin gida suka sauka, Baby ce tafita da gudu tana kiran "tsohuwa!! Baffah? Hamma yarda ina kuke?"

Wata tsohuwace naga ta leko kofa tana cewa "muryar wa nakeji kamar na Babylon Binni?"

Baby ta rungumeta tace "nice mana tsohuwa ina mijina yake?"
Tsohuwar ce ta tureta tace "Dallah matsamin marar kunyar yarinya".

Dariya Baby tayi tace "na yadda kuma dole saina Aureshi"
Dukkansu suka kwashe da dariya.

Yaranane suka tayasu shigar da kayansu ciki,
Saida sukaci Abinci kowa yayi sallah raka'a biyu domin kasaru zasuyi kasancewa tsakaninsu akwai nisa sosai, Suna gaisawa ne wani tsoho shima yashigo gidan yana ganin Baby yace "ni bazan Auri kwaila ba"

Baby tace "nikuma saina Auri tsoho, in bawa tsohuwa wahala"

Dariya sukayi gaba d'ayansu, zama yayi suka shinfid'a tabarma babba acikin gida suna hira, Banda Minal datayi tagumi tana tunanin Ummanta, Innace tace "wannan wacece kuma maryama?"

Mommy CE tabaiwa Inna labarin Minal da fyad'en da akayi mata, Inna harda hawaye shab'e shab'e tsabar tausayin da Minal tabata, a lokacin ne wani dogon saurayi kyakkyawa yashigo gidan, jin labarin da Mmmy tabaiwa Inna yasa yaji tausayin Minal sosai aranshi, Baby ganinshi yasa ta mike da gudu ta rungume shi tace "Gamma yarda nayi missing d'inka".

Dariya yayi yace " to naji nima ai nayi missing naki sosai".

Karasawa wurinsu Daddy da Mommy yace (on wari jam?) Ma'ana kunzo lafiya?.

Mommy ce tace (eh min yatti Jam)

Daddy ma yayi dariya yace "Gamma yarda ka kara girma sosai"

Sunkuyar da kanshi yayi yana dariya, juyawa wurin Minal yayi yana murmushi yace "sannu kanwata ya hanya?"

Saida zuciyar Minal tabada wani sauti dummm ganin Murmushin dayayi mata, itama murmushin tayi mishi tace "yawwa sannu"
Ido ya zuba mata yana kallon yanda take motsa bakinta kamar batason yin magana.

Minal ganin yana kallonta yasa ta kawadda kanta gefe, dariya yayi Wanda ya bayyana dimple nashi ya mike, yace "barinayi sallah".

Nan su Mommy sukaci gaba da hiransu, cikin Hiram nasu ne Inna take tambayar Mommy " yanzu maryama babu wata labari akan lamarinnan?"

Shiru Mommy tayi idonta ya cika da hawaye cikin rawar murya tace "Inna banason ana tunamin maganar nan, banason in kara tuna baya, nabarwa Allah komai"
Daddy ma hawaye ya share yace "Inna mun barwa Allah komai"

Inna ma cikin kuka tace "Allah yana tare daku"

Baby kukan dayake kokarin b'oyewa ne ya kubce mata, Mommy ce ta janyota jikinta tana lallashinta itama bata bar kukanba.

Ahaka har Sukayi kwana Uku agarin Yola, yau suna zaune a cikin gida hamma yarda yashigo hannunshi rike da kwarya Wanda aka cikashi na Kindirmu fari Tass me kyau har wani kamshi yake, Minal ganin kindirmun taji yawunta ya tsinke, da sauri ta tashi ta d'auko kopi da cokali, ta iso wurin Hamma yarda tace "Dan Allah ka tsammin Nonon yashiga raina sosai"

Hamma Yarda ne ya murkud'a karamin bakinshi yace "bazan bada ba"

Minal ganin da gaske yake yasa tayi saurin isowa wurinshi zata kwaci kwaryan ya riko hannunta ya kuma sakewa da gudu yabar wurinta yana dariya, Minal ji take idan batasha Nonon nanba akwai babban matsala, binshi tafarayi suna zagaye gidan da gudu, Hamma Yarda sai dariya yake, Minal kuma ta had'a rai tana binshi.

Da sauri Daddy ya saki labulen window ganin sun iso wurinshi, gefen Mommy ya zauna yace "Hajiya me kika fahimta tsakanin Hamma yarda da Minal?"

Baby ce tafito daga cikin bedroom jin maganar da Daddy yake tace "Daddy nifa ina ganin soyayya suke, Dan wani lokacin sai naga Hamma yarda ya zuba mata idanu, ita kuma idan ta ganni a wurin saita d'auke kanta".



✔ote & comment

Wattpad

_@Jiddah S Mapi_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 37...
*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


Daddy ne yayi dariya yace "to masha Allah idan har abinda muke zargi a tsakaninsu ya tabbata to babu Wanda zai kaini farin ciki, domin ni na d'auki Hamma Yarda Kamar d'an Dana Haifa ne"

Baby tace "ai Daddy nima zanyi farin ciki matuka idan ta Aureshi sabida yanada hankali gashi kuma yana girmama na gaba dashi, kuma yanada fara'a"

Mommy tace "yanzu dai muyita Addu'a Allah yasa hakan ya kasance sannan mu kara zuba musu ido, mugano menene a tsakaninsu, idan yaso kafin mutafi sai ayi maganar Aurensu ko?"

Daddy cikin fara'a yace "kwarai kuwa Hajiyata"

Minal saida ta gaji da gudun kafin tasamu wuri ta zauna tana naki, Hamma Yarda dariya yayi yakarasa wurinta yace "sorry Hajiya nasan kin gaji sosai kawo kopin nasa miki"

Minal had'e rai tayi ta kauda fuskarta gefe,
Cikin tsokana Hamma Yarda yace "shikenan tunda bakyaso ni bari naje na shanye"

Minal taso tayi fishi taki shan Nonon Amma yanda takeson Nonon yawuce misali, Turo baki tayi tace "gashi kasamin kad'an"

Kwashewa yayi da dry kafin ya d'iba mata, karb'ar kofin tayi ta d'aura a bakinta saida tayi Tass kafin ta sauke.
Haka sukaci gaba dazama agidan har sukayi one weak,
Acikin 'yan kwanakin Minal Nono kawai takesha, idan har batasha Nono ba tofa ranar akwai matsala, komin dare sai Hamma Yarda yaje ya nemo mata tasha kafin take iya bacci, Abun har mamaki yake baiwa su mommy, 'yammata kuma sai zuwa gidan suke wai sunason Baby da Minal suzama kawayensu, wani lokacin Inna ta korasu wani lokacin Baby tabasu numbarsu.

Hamma Yarda kuma yakamu da soyayyar Minal bana wasa ba, Sam bayason yaganta tayi tagumi zaije ya zauna agefenta yayi ta bata labaran dariya, har saita warware tafara dariya.

Ta b'angaren su Mommy kuma gani suke kamar Minal da Hamma Yarda suna soyayya, hakan ba karamin dad'i yayi musu ba,
Ita kuma Minal a matsayin d'an Uwa ta d'auke Hamma Yarda kamar yanda Baby ta d'aukeshi.

Yau da yamma su Minal suna zaune acikin gida bayan Minal tagama shan Nonone, taji zuciyarta tana juyawa, da sauri ta tashi tabar wajen mutane, Amai take shekawa tsakaninta da Allah, mommy ce takarasa wurinta tanayi mata sannu, Minal ciwon ciki take sosai, Rike cikinta tayi tana kuka, Mommy ce taji gabanta yana fad'uwa Dan ita tunda dad'ewa taso ta fahimci wani abun, innace ta karaso wurin tana tambayar Ko lafiya?
Ganin Minal tana amai rike da ciki itama taji gabanta yana fad'uwa, hannun Minal tariko tana kallo, da sauri tace Muga idonki Minal?
Minal da ta fita a hayyacinta ta mike tazo wajen Inna, bud'e idonta tayi tana dubawa, Innace tayi Salati cikin kuka tace "Shikenan wannan yaron ya cuceki Minal cikine dake".

Minal tayi baya baya zata fad'i da sauri Hamma Yarda ya riketa, ya d'auketa cakk sai d'akin Inna, A hankali ya kwantar da ita akan gado yana me tausaya mata, Baby ce ta d'ibo ruwa aka yayyafawa Minal da karfi tasaki ajiyar zuciya, hawayene yafara bin fuskarta masu d'umi, Mommy ce ta riko hannunta tace " kidaina kuka idan Allah ya yadda bazaki zauna da cikin nan ba, dolene azubar dashi".... Da sauri Inna ta katse Mommy tace "bakida hankaline Maryam? Wani irin magana kike? Kinsan hukuncin Wanda yazubar da ciki kuwa? To kul karna sakejij kinyi irin wannan maganar koda wasa"

Mommy ce tace "kiyi hakuri Inna bazan karaba insha Allah to amma ina tunanin idan har mutane suka San ta haifi d'a ba Aure wazai Aureta?"

Hamma Yarda ne yace "ni zan Aureta Mommy"

Inna tace "yawwa yanzu abinda za'ayi asibiti zamu kaita a tabbatar da hakan, sai muci gaba da kulawa da ita idan ya gagara ma saiku tafi kubarta anan idan ta haihu saita koma, idan yaso sai ayi bikin a can"

Minal duk abinda suke fad'a tana jinsu, shiru kawai tayi musu Dan ita batasan ma me zata fad'a ba.

_bayan kwana biyar_

Minal ce ta tashi da tsakar dare ta tashi Baby, baby ce ta tashi a firgice tace "meya faru?"
Minal da idanunta suka cika da hawaye tace "Baby wallahi bazan iya bacci ba"

Baby tace "meyasa?"

Minal tace "Baby banason cikinnan ya dameni banasonshi wallahi"....shiiiii Baby ce tarufe bakin Minal da hannunta tace " bakida hankaline? Ana yabonki da sallah sai gashi alwalama yana nema ya gagareki, Dan Allah kada kikara wannan maganar kinji? Bagashi Hamma yarda yace zai Aureki ba, Kinga idan bakyason Ku zauna a garinnan sai in roka Daddy yasiya muku gida a Abuja"

Minal juya bayanta tayi ta kwanta, bargo taja tarufa daidai wuyanta tace "Baby kidaina kawomin maganar namiji yana sona, da kinsan abinda yake kaina to na tabbata bazakiyimin maganar Kowani namiji ba"

Baby cikin muryar lallashi tace "kiyi hakuri my sister insha Allah bazan karayi miki maganar namiji ba, Amma inaso kizauna kiyi tunani akan Hamma Yarda kidubi cikin kwayar idonshi kiga tsananin soyayyar dayake miki.....Dan Allah Baby ya isa nace miki banason kinamin maganar namiji"

Baby bata kara cewa komai ba, ita lamarin Minal yana d'aure mata kai matuka.

Bilal bashida magana kullum sai maganar Minal, Afrah tana kula dashi daidai gwargwado, wani abinda yake bata haushi shine idan tayi mishi Abu sai yace "Dan Allah ki nemamin Minal" wannan maganar ba karamin haushi yake sata ba, kamar kullum yauma Bilal yana kwance akan gado sabida zazzab'i dayake damunshi, Doctor ne yazo yayi mishi gwaje gwaje, Kiran Afrah yayi yace "ina Mahaifinku?"

Afrah tace "Daddy yayi tafiya sai jibi zai dawo"

Doctor yace "yayanki yana cikin matsala, kudaina barinshi yana tunani sabida lafiyarshi, idan yaci gaba da wannan tunanin tofa zuciyarshi zata iya bugawa"

Afrha share hawayenta tayi tace "to doctor nagode"

Komawa wurin Bilal tayi ta riko hannunshi tana kuka tace "yaya meyasa zakasa wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar a ranka? Yarinyar nan fa bata Sonka, da ace tana sonka wallahi data zo Inda kake, shawaran dazan baka shine kacire Yarinyar nan a ranka ka manta da ita kayi rayuwarka yanda kakeyi ada"

Da karfi Bilal ya kwace hannunshi, cikin tsawa yace "tashi kifita"

Afrah tabud'e baki zatayi magana yace "nace kitashi kifita"

Ganin yanda ranshi ya b'aci ne yasa ta tashi a fusace tafice a d'akin, sai d'akin Hajiya babba, tana zuwa tafad'a akan gado tana kuka me sauti, Hajiya babba ce tafito daga toilet tana ganin Afrah tace "Wace wannan nake gani a d'akina kamar matar Bilalu?"

Afrah tamike fuskarta duk hawaye tace "Hajiya babba kema tsokanata zakiyi? Inji da abinda Bilal yamin ko inji da maganarki?"

Hajiya babba ce tayi 'yar dariya tace "habawa Afrah, keda kika nuna Bilalu yafini matsayi awurinki, Har wani hararata fa kike idan kuna tare, ni dama nasani ba sonki yakeba, nasan wannan ranar tana zuwa, kad'anma kika gani ai, bani kika maida kamar wata bare ba?"

"Dan Allah Hajiya babba ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login