Showing 9001 words to 12000 words out of 52544 words

Chapter 4 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Jidda s Mapi.txt

29 Oct 2025

558

Minal kawai sai jin hannun mutum tayi yarike hannunta, saurin janye hannunta tayi tace "Malam me haka?"

Haba 'yan mata yanda kike dakyau ai dolene in kosa, yanzu nasan bakya kallon komai Right?
Minal tace eh sai me?

"Relax Baby bawani sabon abu bane awajen 'yan matan zamani ace tana harka dame kuɗi kinsan zata huta, zan taimaka miki idan har zaki bani haɗin kai sannan babu wanda zesan abu haka yafaru tsakaninmu...."

"Tashi Minal tayi dasauri tace haba doctor, kaida mukazo kadubani amma zaka tsaya kanamin maganar banza? Hakika da ina ganinka babu abunda ze hanani tsinka maka mari mugu azzalimi..." kafin takarasa taji ya rike hijabinta yana kokarin cirewa".

Kokawa suka fara dashi aɗakin tana kokarin janye hijabinta shikuma yana cirewa, rokanshi Allah da Annabi tafara akan yabarta amma ina sam sam mutumin bashida Imani. Ganin yanason cire mata kayanta yasa tafara ihu tana kiran "Me mashin!!! "Me mashin!!!

Toshe bakinta yayi da hannunshi daidai lokacin me mashin ɗin yabuɗe kofar dasauri, saurin sakinta doctorn yayi yaja dabaya.

Me mashin ne yace Doctor menake gani haka? Me kake kokarin aikatawa?

"Shiru doctor yayi yafara kame kame amm.. Amm.. Dama idontan nakeson dubawa amma taki yadda..."

"Kaji tsoron Allah Doctor kaji tsoron ranar haɗuwarka dashi, kana tsoran mutum amma baka tsoron Allah? FYAƊE fa kakeson kayimin, bakaji kunyar Allah ba kanajin kunyar mutum? Allah ya isa, bazan yafe maka ba, abunda kayimin Allah yasa ayiwa 'yarka,
me mashin kataimaka kakaini gida dama nasani rayuwata tana cikin haɗari, babu masu taimako dan Allah saidan wani abu dazasu samu ajikinka, Allah ya isa"

Dama ai Allah isashe ne kufita kubar asibitinnan kafin nakira muku security.

"Hannun Minal me mashin ɗin yakama sukabar office ɗin,
Ya tambayi Minal inane unguwarku? Tace bayan kasuwa"

Me mashinne yataimakawa Minal yakaita har gida kafin yatafi,
Lokacin dataje gida Umma bata dawo ba haka tazauna a inda take tayi ta razgan kuka.

"Wannan wace irin rayuwace? Yanzu irin talauci da kuncin rayuwar damuke ciki ace wannan kaddarar tasake afkuwa"

Waze taimaka miki Minal?
Kin cuci kanki, kin ɓata rayuwarki akan wanda besan dazamanki ba, wanda yatsaneki, Duk maganar nan tanayi ne azuciyarta yayinda take kuka kamar hawayenta ze kare.

"Tana cikin kukane taji sallaman Umma, Saurin share hawayenta tayi domin batason Umma tasan abunda yake faruwa, Aa Minal meyafaru naga kin zauna shiru haka? Keda nagi zaton kina gidansu Madina, meyafaru?
Shiru Minal tayi tana kokarin maida hawayen dasuka taru a idonta.
Wai me yake faruwane Minal?
Umma bana ganin komai!!! "

Bakya ganin komai kamar yaya? Ban ganeba kiyimin bayani dalla-dalla in fahimta.

"Hawayen dasuka taru a idon Minal ne suka wanke mata fuska, Ahankali tabuɗe bakinta kamar batasonyin magana tace Umma Acid aka watsamin a ido,
Acid!!!? Garin yaya? Suwaye suka watsa miki? Ki amsamin suwaye??
Firgita Minal tayi da yanayin maganar Umma"

Bazaki faɗamin ba Minal ina kikaje?
Umma Dama ina zuwa gidansu Madina ne shine wasu samarai suka watsamin Acid takarashe maganar tana kuka sosai.

Ba kuka na tambayeki ba Minal amsa nakeson kibani ina kikaje yau?

Umma wallahi gaskiya nafaɗa miki ki yadda dani, cewar Minal
Ok bazaki faɗi gaskiya ba kenan?
Umma gaskiya nafaɗa miki.... Tassss kakeji Umma tawanke Minal da mari Bazaki fafamin gaskiya ba Minal yanzu kinzama makauniya wace irin rayuwa kikeson muyi? Nashiga Uku ni Maryama.
Kuka Umma tafara itama an rasa me lallashin wani.
Ta rungume Minal suna kukan bakin ciki.

"Ɗaki Latif yakai Bilal zaunar dashi yayi akan gado yace Bilal kaɗauki kaddara aduk yanda yazo maka alkhairi ko sharri, karkasa komai aranka insha Allah zaka fita daga wannan rayuwar, ba karamar jarabawa bace ace mutum yanada ido ada amma yanzu babu, saika daure kakai zuciyark da nisa kafin kaci wannan jarabawar.
Haka Latif yayita kwantarwa Bilal hankali"

Daddy kuwa yau babu wanda yakaishi farin ciki jiyake kamar yahaɗa party till down, waya yaciro yakira Alhaji Nura yace "Alhaji Nura aiki yayi kyau zaka samu babban kyauta daga gareni, saidai fa akwai matsala!"

Matsalar me kuma Alhaji Umar?
Latif zaibi diddigin abinda yafaru sabida yace koda zai rasa rayuwarshi saiya gano wanda ya aikatawa Bilal haka.

"Haba Alhaji Umar akan wannan shine zaka ɗaga hankalinka? Nawa Bilal yake balle Latif?
Idan bazaka damu ba muhaɗu a guesthouse nawa mana Cewar Alhaji Umar,
Ok ba matsala zanzo da karfe bakwai nasafe.
Nan suka gama shawararsu suka kashe wayar...

_✔ote Comment & share_


✍🏻 *JIDDAH S MAPI*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

(An heart touching story)


*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_


*Page* 7


"Kamar yanda Alhaji Nura da Alhaji Umar suka yanke shawarar haɗuwa a guest house hakan tafaru, da karfe 7:00 ciff motar Alhaji Nura yadanno kai cikin guest house ɗin, wani wajen shakatawa me kyau naga yanufa, yana zuwa yasamu wuri yazauna akujerar dake fuskantar Alhaji Umar"

Barka dazuwa cewar Daddy,
Yawwa barka Alhaji,
Alhaji idan har Latif ze zame mana matsala meze hana muyi gaggawar ɗaukan hukunci.

Wani irin hukunci zamu ɗauka kenan Alhaji Nura?
Kasan banason abunda ze kawomin cikass awannan lamarin, nasa an makantar da Bilal sabida dukiyarshi inason yanuna min komai kafin daga baya insa akasheshi gaba ɗaya yabar duniyar nan.
Amma Wannan Latif yana neman jazamin aiki
Narasa mafita.

"Inada mafita Alhaji"

Mecece mafitar?
Cewar Daddy

Meze hana ayi mishi sharrin shiya turo mutane su watsawa Bilal Acid, munemo mutane biyu su ɓoye fuskarsu sai suyi videon cewa Su suka watsa mishi kuma Latif ne yaturosu kaga saiya kare rayuwarshi agidan Yari"

Daddy ne yagyara babban rigarshi yace "wato Alhaji Nura ban taɓa zaton zaka kawo good idea kamar haka ba, to Amma baka ganin hakan zai kawo matsala?"
Babu wata matsala Alhaji kaidai muyi abinda nace kawai.
To shikenan amma idan zeyi gobe nakeson ayi videon domin da zafi-zafi ake dukan karfe,
Karka samu damuwa cewar Alhaji Nura, nan sukayi ɗan hira kafin daddy yaɗibo wasu maƙudan kuɗi acikin baƙar jaka yabawa Alhaji Nura, Alhaji Nura yayi godiya yatafi"

"Bilal tunanin daya dami zuciyarshi shine Wayake neman hallakashi? Meya tarewa meshi? A iya saninshi bashida abokin gaba, to wayene wannan, wayake kokarin illatamin rayuwa?
Haka yakarashe tambayoyinshi babu me bashi amsa, filo yaɗauko yarungume yana kallon silin ɗin ɗakin, tunowa yayi da kanwarshi Nabila wanda duk lokacin data ganshi cikin damuwa hankalinta baya taɓa kwanciya, Runtse idonshi yayi yana mejin bakon cikin rashin 'yar uwarshi da iyayenshi, hawayene suka fara fita a idonshi wanda yake ganin hakan shine maslaha agareshi, awannan yanayin idan beyi kuka ba zhciyarshi zata iya fasa kirjinshi tafito,
Yana cikin wannan yanayin Daddy yayi sallama yashigo, yadai Bilal?

Lafiya Daddy cewar Bilal,
Zama Daddy yayi agefen gadon yariko hannun Bilal yana shafawa yace "my Son Banaso kasa kanka cikin damuwa, da nayi niyan nakaika India aduba idonka konawa zan kashe idan lafiyar idonka zata samu ashirye nake nakashe, amma kash mumunan labari ɗazu munyi waya da Doctor Shankar babban likitan idanu dake kasar India, nayi mishi bayanin abunda yafaru yace ai idan an watsawa mutum Acid a ido kuma yamurza idon sosai Aciɗin yabi cikin kwayar idanunshi to bazai taɓa samun sauki ba sai wani ikon Allah,
Bilal am sorry nazama Helpless akanka nakasa taimakonka da'ace zan iya baka nawa idon wallahi dana baka Bilal sabida kai saurayi ne nikuma girma yazo, kayi hakuri Bilal Daddy yakarashe maganar yana kuka kamar dagaske"

"Bilal shiru yayi yana jin maganar Daddy yasan cewa duk duniya babu wanda yakesonshi bayan Family ɗinshi sai Daddy,
Daddy kadaina kuka Haka Allah yatsaramin rayuwata, amma dan Allah Daddy inason kayimin amsar tambaya ɗaya"

Zuciyar Daddy wani irin bugawa tayi dakarfi yace am am.. am wace tambaya ce wannan Bilal?

Daddy shin mahaifina yanada Abokin gabane?

Shiru Daddy yayi yana tunani,
Daddy please answer my question,
Ajiyar zuciya Daddy yasauke yace "my son mahaifinka yanada abokin gaba guda ɗaya wanda nasani amma yanzu sun shirya suna abota kamar ba waɗanda suka taɓa gaba ba,
Daddy wayene wannan?

Abban Latif!!!! Cewar Daddy,
Abban Latif kuma?
Aganina shine aminin babana kuma babana ya aminta dashi sosai.

Bilal wannan abotar tasu ta BOGE ce bata gaskiya ba,
Mahaifinka yanada tarin dukiya wanda har wani lokacin yakan manta da wasu kadarorinshi, sun kasance abokai sosai da Abban Latif amma me? Sai kawai wata rana Abban Latif yayiwa mahaifinka babban sata satar Company Uku.
Da Mahaifinka yagano hakan saiya koreshi a aiki tun daga wannan rana gaba me tsanani yashiga tsakaninsu, nine nakirasu nayi musu nasiha kafin mahaifinka yabashi hakuri sukaci gaba dazama tare.

"Nabaka wannan labarine sabida karka Aminta da mutum sosai, wanda ka amince mishi shine wanda ze cutar dakai"

Abban Latif kuma? Cewar Bilal.

Daddy ganin yasa shakku azuciyar Bilal ba karamin farin ciki yayi ba, yasake ɗaurawa da "Bilal banaso kafaɗawa kowa wannan labari kaji?
Bilal yagiɗa kai,
Yawwa sakko muje downstair kadaina zama kai kaɗai aɗaki sabida yawan tunani?
Bilal yace to Daddy"

Hannunshi Daddy yakamo suka nufi kasa, Afrah nakwance a falo daga ita sai wata 'yar karamar riga da wando skin tired Kanta babu ɗankwali tana cin cingom kasss kass kass rike da wata ƙatuwar waya tana chat da friends nata, ganinsu Daddy yasa ta tashi daga kwancen tazauna tareda cewa "Daddy kazama ɗan jagora ne?

What are you saying Afrah yayanki nefa kaddara tasameshi, keda kike sonshi ai kuka yakamata kiyi..... No no no Daddy ai ni nadaina sonshi yanzu, mezanyi da makaho? Ai kawayena sai suyimin dariya. Daddy ni raina ma ya ɓaci .... Bye

Tana gama faɗin haka ta mike santal santal santal kamar nakasasshen rakumi tayi gaba.
Bilal har cikin zuciyarshi yaji zafin kiranshi makaho datayi amma ba komai zanyi maganinki.
Daddy ya katse mishi tunani dace "Bilal sai kayi hakuri da Afrah kasan yarinya ce"
Eh Daddy ba matsala.
Yawwa yanzu ina makullin Companyn yake kabani saina nemi wanda ze zauna madadinka, koda shike ga Hafiz nanma ai kaninka ne saiya zauna kawai right?

Mamaki ne yakama Bilal ko kwana biyu beyi ba an farakarɓan makulli? Yace to Daddy ka kaini ɗaki in ɗauka mishi.


_✔ote comment & share_


✍🏻 *JIDDAH S MAPI*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

(An heart touching story)


*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_


*Page* 8


"Ɗakinshi Daddy yakaishi domin ɗaukar makullin, suna zuwa Bilal yaɗauko makullin har zai mikawa Daddy amma kome yayi tunani Oho, sai yace Daddy ina hanunka ga makullin, hannu Daddy yamika mishi yakarɓi makullin yana wani irin murmushi wanda shi kaɗai yasan ma'anarshi. Azuciyarshi kuwa yace gaba kaɗan rayuwarka zaka bani Yaro"
************

Da yamma suna Zaune afalo Daddyne yashigo falo a rikece yana kiran Bilal? Bilal? Bilal, Hajiya Salamatu ce ta amsa tace lafiya kuwa kake kiran Bilal da ihu haka?

Hajiya ina Bilal yau Allah yatona Asirin Wanda suka aikata mishi haka, yana faɗin haka ya karaso inda suke ya buɗe wata Video awayarshi yace kalli kugani wanda kayarda dashi shizai cuceka,
Sa Videon yayi a handsfree yanda kowa zeji me ake cewa,
Wasu mutanene guda biyu sun rufe fuskarsu da baƙin kyalle suna cewa Ai Latif ne ya aikasu su watsawa Bilal Acid a idonshi sabida wani dalili nashi wanda basu sani ba.

What!!! Latif cewar Bilal, no Daddy ban yadda ba Latif bazai taɓa cutar dani ba..... Dakata!!! inji Daddy kai wani irin mutum ne? Baka jin abunda suke faɗane? Ko sharri zasuyi mishi? Aina suka sanshi dazasuyi mishi sharri? Shi kaɗaine aduniyar dazasu tsallake kowa suzo kanshi?

"Kalamun Daddy sunyi matukar tasiri akan Bilal,
Magana yakeson yayi amma bakinshi yana rawa tsabar firgitan dayayi.
ganin haka yasa Daddy juyawa yasaki wata murmushi wanda shikaɗai yasan dalilin yinta.
azuciyarshi yace Yanzu aka fara wasan"

*************************

"Minal tana cikin kuncin rayuwa, babu inda Umma bataje neman aiki ba amma takasa samu, kamar kullum yauma suna zaune acikin gida suna hira Minal ce tace Umma?
Umma tace Na'am 'yata.
Umma inason in fara zuwa BARA.... Bara kuma Minal? Yaushe kika fara son duniya? Meyasa bazaki hakura da halin damuke ciki ba?.

Minal ce tafara zubar da hawaye tace "Umma ya bazanyi bara ba? Kiduba irin halin damuke ciki abinci ma neman gagararmu take, hannayenta biyu taɗaga tace ya Allah ka karɓi rayuwata, Allah kana ganin duk abinda yake faruwa, Allah ka gaggauta ɗaukan rayuwata kafin ta ɓaci gaba ɗaya... Ta karashe maganar tana wani irin kuka mecin rai, rungumeta Umma tayi sukaci gaba da kukan tare gwanin ban tausayi"

"Latif? No... Kodai mafarki nake ne Daddy? Bilal durkusawa yayi agaban Daddy yarike kafafunshi yace Dan Allah Daddy kafaɗan gaskiya Latif ne yake neman hallaka rayuwata? Latif ne ya makantar dani?"

Ɗagoshi Daddy yayi ya rungumeshi yana bubbuga bayanshi yace "my son idan baka gani ai kanaji, kasan dai babu yanda za'ayi mutanennan suce shiya aikesu, may be ma kuɗinsu ne be basu ba, amma insha Allah yau Latif baze kwana agida ba, agidan yari ze kwana sabida yayi kokarin kisan kai"

Aa Daddy kar ayi saurin yanke hukunci, ayi bincike tukunna kar muzo muna dana sani.... Enough! Karka kara samin baki acikin maganarnan, kai Amana ne awajena idan har nazuba ido wata rana kasheka zasuyi, wallahi, Wallahi, wallahi, nayi rantsuwa sau uku kuma nasan muhimmancin rantsuwa, bazan bar Latif da Abbanshi ba dukansu saina kai karansu kotu kuma dolene ayanke musu HUKUNCIN KISA!!! sabida sunyi kokarin kashe ran da babu hakki.

idan kaga Daddy alokacin zakayi zaton babu masoyin Bilal kamarshi,
Bilal gyara glass nashi yayi yaci gaba da kallon Daddy aɓoye, dashike yanzu yanasa baƙin glass irinna makafi.
Yace "to Daddy duk abinda kayanke daidai ne sabida kai amatsayin uba kake awajena, bayan iyayena babu wanda nakeso saikai Daddy,
Na Amince akama Latif amma ina neman alfarma ɗaya awajenka"

Faɗi alfarmar dakake so nikuma nayi maka alkawarin zanyi maka.

"Bilal yace Daddy dan Allah kar ayiwa Latif HUKUNCIN KISA!!! Ayi mishi horo iya abinda yayi niyan aikatawa......


_✔ote comment & share_


✍🏻 *JIDDAH S MAPI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*
MAKAUNIYA CE

Na
Jiddah S Mapi

Page 9

"Shikenan babu matsala zanyi yanda kace. Godiya Bilal yayiwa Daddy daganan Daddy yafita yabar mishi ďakin cikin Farin ciki, kwanciya Bilal yayi yana tunani wannan wani irin jagwalgwalon rayuwane? Lumshe idanunshi yayi me ďauke da Zara Zaran eyelashes dafe kirjinshi yayi sabida wani irin zafin dayake mishi".

Minal yau ta tashi da ciwon ciki me tsanani dama kowani wata haka yake mata dazaran lokacin period nata yazo, kwance take akan katifarta tana murd'e murd'e fuskanta duk yajike da zufa ita kad'ai tasan me takeji idan period nata yazo, tana cikin wannan halin Umma tayi sallama, meya sameki Minal? Umma ci...ci....takasa karasa maganar tsabar azaba ganin yanda take rike cikine yasa Umma tagane me yake daminta, hannunta Umma tarike suka fito cikin gida, zaunar Da ita tayi akan kujera tace zauna anan nahad'a miki ruwan zafi kiyi wanka kozakiji sauki, dakyar ta amsa da to, bayan Umma tagama had'a ruwan tazo tarike hanun Minal ta kaita band'aki cike da tausayi, yawwa Minal tawa yi wankarki ko, har Umma ta juya zata fita taji Minal tace "Umma kitaimaka kimin wankar idanuna basa gani kuma kinsan ina period bansan yanda zan gyara jikina ba, nasan awannan lokacin ke kad'aice zaki iya kula dani yanda yakamata, jin haka yasa Umma taji wasu hawaye masu d'umi suna sauka a idanunta, juyawa tayi takoma cikin toilet d'in tareda rungume Minal suna kuka, ahankali tafarayi mata wankar harta gama ta kintsa mata jikinta suka fito, magani Umma tabata bata dad'eba bacci yad'auketa,
Wasu hawaye Umma ta goge cikin sanyin jiki tafice a d'akin".

" Latif ne zaune a office nashi shida wani manager d'inshi suna tattaunawa akan wasu kwangila dazasu d'auka, tura kofan office d'in akayi batare da excuse ba! police? Cewar latif yes police what happened, are you scared? Cewar wani police yana zazzare idanu,
Meyafaru zaku shigomin office ko excuse babu?
Idan mukaje station zakaji meyafaru amma yanzu ba abunda zance maka sai you are under Arrested!!!
Menayi daza'a kamani? Arasa inda za'a kamani sai a office nawa ai mutane zasuyi zaton sata nayi koba hakaba manager?
No..no..no Mr Latif basai katambayi manager naka ba abunda kayi ai gara Wanda yayi sata, Enough!! Kada ka kara dangantani da b'arawo intact ba inda zanje, baka isaba Mr Latif hasalima bazaka ja da hukuma ba komai taurin kanka,
Haka aka kama Latif mutane sai binsu da kallo suke".

Bilal kanshi yakulle kuma yaji labarin an kama Latif amma babu yanda zaiyi, haka yahakura kullum yana kan bincike amma har yanzu be gano komaiba,
Zaune yake a garden yauma kamar kullum sanye yake dawani Kaya me launin ja da fari bakin glass yasawa fuskarshi Wanda ake kirada half face sandarshi yad'aura akan cinyarshi yana d'an wasa dashi, abun duniya yataru yamishi yawa, yana cikin tunani yaji an rike mishi fuska da Alama hannun mace he kuma yasan baze wuce Afrah bace, cikin wani Bakin ciki dabai tab'aji ba yace Afrah banason rainin wayo ki kiyayeni niba sa'anki bane, shake murya tayi ita adole ta iya yanga tace "yayana ya akayi kasan nice kodai kafara sona ne?" Ranshi ne yayi mugun b'aci, afusace yace ba dole naganeki ba kullum turare d'aya kike anfami da ita tin yana kamshi harya fara wari,
Aduniya babu abinda Afrah ta tsana sama da ace mata tana wari wannan Kalmar tana matukar b'ata mata rai, itama Afusace tace "ai garani ansan turarene kuma Ina ganin komai kai kumafa? Makaho Wanda ze kare a makanta....karki sake kib'ata min rai Afrah idan raina ya b'aci kinsan banida kyau...sai me? Idan rannaka yab'aci adane nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login