Showing 33001 words to 36000 words out of 52544 words
Chapter 12 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Jidda s Mapi.txt
yayi bacci kafin itama tayi.
_washe gari_
Bayan sunci abinci Bilal yace "jiya baki tambayeni maganar danace zamuyi ba meyasa?"
Minal tace "yaya na manta ne"
"Okay dama maganar da zamuyi itace, meya sameki a ido har kika makance?"
Shiru Minal tayi batayi maganaba.
Bilal yace "karki min karya ni mijinkine bai kamata kib'oyemin sirrinki ba"
Hawayene yafara fita a idanun Minal, cikin kuka tace "yaya Bilal koda nafad'a maka bazaka yadda ba, abune Wanda jinshi yafi rashin jinshi Alkhairi"
Bilal yace "idan kika fad'amin gaskiya baki b'oyemin ba ai kin fita a hakki, damuwana ne idan nayadda damuwana ne idan ban yadda ba"
Minal tace "yaya na Makance ne sabida kai!!!"
Sabida ni kuma beauty? Tayaya?.
Cikin kuka Minal tace "yaya Daddynka ne da Alhaji Nura suka tura awatsa maka Acid a ido, nikuma lokacin naje nabaka hakurin Manja Dana watsa maka a Riga, shine najiyosu, washe gari naje domin in fad'a maka Amma bansan inane garden naku ba, shine garin nemanka suka watsamin Acid d'in kuma naga fuskarsu, Hafeez kaninka kuma yana nemana da fasikanci nikuma naki yadda dashi shine yakemin barazana akan zai kasheni, ita kuma Madina ina jinku kuna hira da ita a bedroom amma muryanta kad'ai nakeji, Hajiya babba kullum saita zagi iyayena shiyasa na tsani gidanku, kuma koda mun koma Nigeria bazan iya zama a gidanku ba gara na zauna da Mahaifiyata, dama ta sanadiyyarka na makance gashi kuma ta sanadiyyanka na warke, kaga 1-1 kenan ko?"
Bilal manyan idanunshi ya zuba mata kamar maye, yanaji idan ya bud'e bakin shi to dole saiya sume sabida yanda zuciyarshi take bugawa, janyota jikinshi yayi ya matseta sosai, idanunshi suna fitar da hawaye.
"Beauty da gaske Daddy ne yakeson ya nakasani?"
Minal tace "nifa ban fad'a maka Dan kaje kafad'a mishi ba,tom"
Bilal kuka kawai yakeyi kamar karamin yaro, Minal yabata tausayi sosai A hankali tafara rarrashinshi, tana bubbuga bayanshi, kwantar da kanshi yayi akan cinyarta zuciyarshi a cakud'e hankalinshi a tashe, A hankali yace "Minal narasa iyayena da kanwata wacce nafi sonta fiyeda komai, ta hanyar Accident, Na tabbata ba Accident bane kawai akwai abinda aka shirya kuma da yaddar Allah saina gano ko menene"
Minal dukda Haushin Bilal datakeji Dan yana zarginta da fasikanci, hakan bai hanata tausaya mishi ba, itama kuka tafara tana lallab'ashi, saida yaga tafara kuka sosai kafin ya danne zuciyarshi yayi shiru.
Ahaka sukayi sati d'aya a India, acikin satin idan suna kwance yagwada nemanta, saita fara mishi kuka, a haka zai hakura ya kwanta wani lokacin yayi ta mata nasiha akan duk matar data hana mijinta hakkinshi tana cikin tsinuwar Allah da mala'ikunshi har wayewan gari, ita kuma Minal saidai tace mishi Allah ya yafe mana baki d'aya.
A haka harya gaji ya kyaleta.
Kamar kullum yauma Minal ta takurashi saiya fita da ita yawon shakatawa, da kyar ya yadda Dan yanzu har haushi take bashi nakin Amincewa dashi.
"Wanka tayi da sabulunta me kamshi, kwalliya tayi had'i da tattare gashin kanta ta kitsashi waje d'aya, d'an kunne red tasa da warwaro red, Jan bakinta ma red colour, wani dogon Riga baki jikin anyi adon da red beat tasa, hannun a yanke kad'an kad'an, jan gyalle me beat baki tasa, zuwa wajen Dressing mirror tayi ta tsaya tana kallon kanta, wani murmushin daya bayyana dimple nata tayi, Glass na Bilal tagani half face baki ta d'auko tasa a idonta, " Wow shine abinda tafad'a lokacin dataga kanta jikin mirror"
Turare me kamshi ta d'auko ta fesa duk jikinta dashi, zama tayi akan stool tana jiran fitowar Bilal.
Bilal ne yafito daga wanka d'aure da towel babba sai karami kuma yana goge kanshi, tsayawa yayi turus yana kallonta.
Minal kuma ganin yana b'ata musu lokaci yasa ta sakko daga kan stool d'in cikin takunta na kasaita ta nufi wurinshi, karb'an karamin towel d'in tayi tafara goge mishi jikinshi,
Tana gamawa taja hannunshi zuwa wurin dressing mirror, Lotion nashi ta d'auko ta Murza a hannunta, a hankali tafara shafa mishi duk jikinshi.
Tana gamawa taje wurin wardrobe ta d'auko mishi wani Riga red colour da wando black sai picab ma red, zuwa wurinshi tayi cikin shagwab'a tace "yaya gashi kasa kar muyi dare"
Bilal shima cikin shagwab'a yace "kisamin mana Beauty".
Sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunyar maganarshi,
Ganin ta sunkuyar da kanta kawai yayi murmushi, yaje yasa kayan data zab'a mishi, picap yasa idan ka ganshi kamar shima ka sace ka gudu (Ammafa Minal tafishi kyau, bari na gudu kafin team Bilal su rufeni da duka).
hannunta yariko yace " kinyi kyau Beauty"
'Dago kanta tayi a hankali tace "ai ban kaika ba yaya"
Murmushi yayi yace "har kin fini ma, muje ko?"
Minal tace "ka manta Abu biyu"
Yace "mena manta beauty?"
Wurin dressing mirror taje ta d'auko agogo da turare tazo wurinshi, hannunshi takamo ta d'aura mishi agogon ta fesa mishi turare me k'amshi,
Bilal sai kallonta yake har taje ta ajiye ta dawo.
Hannunta yariko suka fita zuwa cikin garin India domin bud'e ido,
Wani wurin shakatawa me kyau Bilal ya kaisu,
Daga ganin wurin zakasan na masoyane sabida wani grass Capet dake shimfid'e akasa, sannan kowani round kujeru bibbiyu ne akai, sai gefe kuma akwai wani Ruwa me kyau da d'aukan hankali,
Minal ce taga wasu suna siyan Ice cream, da Sauri tace "yaya zansha Ice cream"
Bilal yace "dawani bakin?"
Karamin bakinta ta turo tace "da wannan mana"
Yace "bud'e mugani"
Cikin shagwab'a ta bud'e mishi bakinta,
Dariya yayi yace "bakinnan yayi karami dashan ice cream"
Kuka tafara mishi tace "ni wallahi saika siyamin"
Yace "sorry banda kuka muje in siya miki".
Share hawayenta tayi tace " to"
Bayan sun siyo ice cream ne suka dawo wurin ruwan kafafuwansu sukasa a cikin, Minal tanashan ice cream nata, shikuma Bilal sai kallonta yake tayi.
Kallonshi tayi tace "kai bazaka sha ice cream bane?"
Bilal yace "zansha mana idan kin bani"
Murmushi tayi ta d'ibo a spoon tace "haa"
Bud'e bakinshi yayi tasa mishi,
Tace "yaya yaushe zamu koma gida?"
"Sai ranar da kika yadda dani".
Minal tace "wani irin yadda kuma Yaya Bilal?"
Lumshe idanunshi yayi a hankali yasaukesu akanta, sunkuyar da kanta tayi sabida bata iya jure ganin cikin idonshi, kwarjini yakeyi mata bana wasa ba,
A hankali yace "nafison mu koma Nigeria kinada katon ciki".
_✔ote & comment_
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
*Jiddah S Mapi*
Page 31....
*wannan shafin na sadaukarwa 'yan Makauniya ce Fans group 1 idan kunga dama kada kubawa 'yan group 2 su karanta, sai yanda kukayi dashi Ur Comments make my Day*
Minal maganarshi ba karamin kunya yasata ba,
Kanta ta saukar kasa tace "yaya nifa ba sonka nake ba, kawai inayi maka magana ne sabida babu Wanda zanyi hira dashi a kasar nan".
Bilal yace " da gaske kike?"
Gyad'a kai tayi alamar eh.
Bai sake cewa komai ba, wayarshi yaciro yafara latsawa,
Minal sai shan ice cream nata take kota kanshi bata karabi ba, tana gamawa tace "yaya zanci pizza".
'Dago kanshi yayi baiyi maganaba sai idanu daya zuba mata, Kawadda kanta tayi itama batace komai ba,
Saida yagaji da kallon nata kafin yace "zakici pizza ko?"
Minal tace "Eh".
Yace "OK muje in siya miki tinda kin bani ajiyar kud'i, keda bakya sona ai bazaki so abin hannuna ba".
Turo baki tayi tace " dama can badan Allah kake siyamin Abu ba"
Bilal yace "Eh na yadda".
Har suka koma gida babu Wanda yayiwa wani magana,
Minal haushin Bilal takeji dan yaki siya mata Pizza, ta b'angaren Bilal ma haushi take bashi Sabida tace bata sonshi Abun ya kona mishi rai matuka.
"Har dare babu Wanda yayiwa d'an Uwanshi magana kowa yana fishin, Minal ce tashiga toilet tayi wanka had'i dayin Alwala, towel ta d'aura tafita sai kumbura take kamar zata fashe,
Mai tashafawa jikinta tasa rigan bacci light purple silk ce gaban da tsagu sai mad'aurinshi daidai waist, d'aurewa tayi tasa night cap ta haye gado tayi kwanciyarta ko juya baya batayi ba,
Shima Bilal yana gama wankarshi yayi Alwala dama sun saba idan zasu kwanta sai sunyi Alwala, mai ya shafa yasa singlet da wando dogo na bacci shima silk ce, hayewa gadon yayi shima ya juya bayanshi, Minal tana jinshi tayi likimo kamar tana bacci, jin saukar numfashinta alamar tayi bacci ne yasashi juyawa wajenta ya janyota jikinshi yayi Addu'an bacci ya shafe jikinshi da nata, Minal ji tayi kamar ta sauke mishi duka tsaban haushi, Ace mutum sai girman kai kamar yafi kowa, magana ma yaki yayi mata tin d'azu sabida yana ganin idan yayi mata zata rainashi, Amma yazo ya rungumeni kamar 'yarshi haka tayi ta surutunta har bacci ya d'auketa.
Cikin dare Minal ce ta tashi da ciwon ciki sakamakon Period nata dayazo, tashi tayi ta zauna tanata kuka tana rike da cikinta, Bilal cikin bacci yaji kamar ana kuka, Mikewa yayi yaga Minal rike da ciki yace "Beauty meya sameki?"
"Cikina" shine iya abinda ta iya fad'a,
Bilal ne ya riketa yace "sannu daidai Ina yake miki ciwo?"
Minal bazata iya magana ba, hannunshi ta riko tasa a daidai maranta, a hankali yafara shafawa yana cewa "sannu".
Minal lumshe idonta tayi a hankali take samun relief,
Bilal ganin tana jin dad'in hakan yasa ya kwantar da ita a hankali yana shafa mata cikin, sautin kukanta ne ya ragu,
Hannunshi ya zame yace "ko nakira doctor ne?"
Da sauri tariko hannunshi tamayar kan cikinta alamar yaci gaba a hankali tace "Aa banason Allura".
Shiru kawai yayi.
Bai samu bacci ba har sai kusan Asuba, ita kuma Minal tuni tayi bacci.
_washe gari_
Minal ta jima da tashi Amma batasan yanda zata mike ba sabida tayi staining, har bedsheet d'in ta b'ata, Bilal jin ta tashi yasashi mikewa yace " beauty ya jikin naki?"
Cikin jin kunya tace "da sauki"
Bilal yace "me zakiyi yanzu?"
Batace komai ba sai kallonshi take, Bargon ta tattare ta rikeshi waje d'aya, Bilal ya lura da yanda take b'oye bargon sai kawai ya wupce a hannunta, da sauri ta mike zata kwace sai kawai yaga yanda tayi staining ta b'ata jikinta, sai yanzu yagane meyasa taki tashi, d'aukarta yayi cak yakaita toilet, cikin bathtub yasata tareda kunna shower wanka yayi mata ya d'auke towel ya d'aura mata, kanta a kasa har yakaita kan gado, Always ya d'auko ya mika mata yace "tashi ki gyara kanki"
Minal ji take kamar kasa ya tsage ta shige ciki tsabar kunya,
Turo baki tayi tana hararanshi,
Ajiyewa yayi yawuce toilet da bedsheet d'in ya wanke tareda kayan data b'ata.
Ita kuma Minal tana gama sawa ta rufe kanta a bargo har bacci ya d'auketa.
A haka har sukayi kwana Uku Bilal yana bata kulawa, wani lokacin idan yayi mata Abu ta gode mishi wani lokacin ta harareshi.
_bayan kwana Uku_
Minal ce zaune a kasa tana kuka, shi kuma Bilal ya juya bayanshi yana latsa waya, cikin kuka tace "wallahi saika maidani wajen Umma, Bazan zauna a garinnan ba, ai tunda mun gama abinda ya kawomu saimu koma kasarmu".
Bilal baice komai ba,
Ganin ya rainata dayawa yasa ta mike zata wupce wayar, fizgota yayi tafad'a jikinshi a kunne ya rad'a mata "wato raini yafara shiga tsakanin mu ko?"
Tsaki taja ta kawar da kanta, Bilal ganin harda tsaki take mishi yasa yaji ranshi ya b'aci da sauri ya tashi ya cire kayan jikinshi, Yayi Off na wutan d'akin dimm light ya kunna Minal ganin haka yasa tafara bashi hakuri, bai saurareta ba yafara cire kayan jikinta, ganin da gaske yake yasa tafara kwace kanta, da karfi Bilal yafara kissing nata, Hannunta yarike da iya karfinshi, Minal tana bashi hakuri Amma yaki ko saurarenta, (A lokacin nikuma na sulale nabar d'akin.
Sai can najiyo ihun Minal acikin d'aki daganan ban karajin motsinta ba).
Bayan wasu Minta Bilal ne kwance yayi rub da ciki, hankalinshi har yanzu bai dawo jikinshi ba, gani yake kamar mafarki ne, "Fyad'e" shine abinda ya furta a hankali ya kuma cewa "no ba Fyad'e badai ai matata ce"
Shi kad'ai yake magana shi yake kara baiwa kanshi Amsa.
Minal kuma ta dad'e da sumewa Dan ba karamin wahala Bilal ya bata ba.
Wani ciwon kai ne da zazzab'i suka rufe Bilal a lokaci d'aya, Tashi yayi da kyar yana tangal tangal kamar zai fad'i a hankali ya d'auki Minal yayi hanyar toilet da ita, daidai bakin kofa yaji wani jiri ya kwasheshi, Fad'iwa yayi da Minal a hannunshi, saidai ita bataji ciwo ba shi kad'ai yaji ciwo ka kafarshi Dan ya bugu bada wasa ba,
A haka ya daura yakara d'aukanta yakaita toilet yayi mata wanka da kyar shima yayi Dan zuwa yanzu jikinshi har rawa yake.
Towel ya d'aura mata shima ya d'aura yafito da ita,
Minal lokacin ta farfad'o Amma babu bakin magana sai hawayen dayake fita a idonta, akan gado ya kwantar da ita ko mai bai shafa musu ba yaja bargo ya lullub'e su jikinshi yana rawa, kanshi kamar zai fad'o tsabar zazzab'i,
Minal kuma ji take da akwai wuka a gefenta to babu abinda zai hanata ta dab'awa Bilal a ciki tsabar yanda tsanarshi yakara shiga zuciyarta, dama tasan ba sonta yake ba ya kawota ne Dan a gyara mata idonta yasamu dama cutar da ita, A hankali tace "mugu Azzalimi, macuci..."
Da Sauri ya had'e bakinsu Dan bayason jin sauran maganar nata,
Saida yaga tayi shiru bakinta ya mutu kafin ya daure ya d'auko waya yakira wani doctor yace yazo da nurse mace, Sabida yasan dukkansu suna bukatar taimako.
_Nigeria_
Afrah ce tasa Hajiya babba a gaba tana kuka wai masoyinta ya b'ata, cikin muryan damuwa Hajiya Babba tace "haba Afrah meyasa zaki zauna kina kuka sabida b'atan wannan yaron? Dad'in Abinma kina cin Abinci da bakya cin abinci da ban San yanda zanyi ba"
Afrah ce Tace "Hajiya babba kinsan ina sonshi rana d'aya ace ya b'ata? Haba"
Rarrashinta Hajiya babba tayi harta samu tayi shiru.
Gidan Umma kuma kuka ba dare ba rana, "waya sace min ke Minal?" Shine abinda Umma take fad'a idan ta zauna, Madina ce take bata hakuri tace mata in Allah ya yadda zata bayyana, da haka take samun Umma tayi shiru.
_India_
Bayan doctors sunzo anyiwa Minal allura an bata magani Bilal ma anyi mishi Allura da magunguna, dukkansu bacci suke.
Minal ce ta tashi tayita kuka harta godewa Allah.
_washe gari_
Minal tad'an samu sauki shikuma Bilal bai dameta ba sabida yasan yanzu ta tsaneshi yanason saita huce kafin yabata hakuri,
Da Bilal yashiga wanka Minal ce ta bud'e drower ta d'ibe kud'i masu yawa ta b'oye a Jakarta,
Bilal yana fitowa ya shirya a hankali yace "Am sorry ki yafemin"
Minal murmushi tayi tace "ba komai"
Har cikin ranshi yaji dad'in yanda tayi saurin saukowa, peck yagi mata a forehead yafita yana cewa "I will be back soon"
Minal murmushi tayi,
Yana fita ta leka taga yabar Area na hotel d'in ta d'auko mayafinta da Jakarta Wanda ta had'a kayanta tin jiya da dare, ta d'au Makullin d'akin tafice da Sauri.
_✔ote & comments_
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 32...
"Sauri take kamar zata tashi sama, batasan ma ina zataje ba burinta kawai taga tabar Cikin Hotel d'in yanda ko yadawo yanzu bazai ganta ba, tana Cikin tafiya ne ta hango wani majalisa da sauri ta karasa tana gaishesu babu Wanda ya kulata Sai harkokinsu suke, ta gaji iya gajiya gashi bata samu mafita ba, tin safe take yawo a gari babu me taimaka mata ga yunwa ga kishi duk ta Tara, zama tayi a karkashin wata bishiya, har yanzu bata daina jin ciwon jiki ba, kishingid'a tayi tad'an lumshe kyawawan idanunta da Alamun gajiya, jakarta ta ajiye a gefenta ta d'aura hannunta akai sabida tsaro, wani nauyayyen bacci ne ya kwasheta ba shiri, mikewa tayi a kasa tafara bacci".
Bilal kuma wani farin cikine ya zagaye jikinshi ganin Minal ta sakko da wuri, idan ya tuna abinda yafaru tsakaninsu Sai yayi murmushi, jin kanshi yake kamar sabon halitta, wani babban super market ya nufa, kayan bacci na mata masu kyau ya zab'o, da turaruka masu kamshi, b'angaren kayan sweet ya nufa ya d'ebo su Chocolate da oatmilk dasu candy sweet Sai Ice cream saya siya mata sabida yasan tanaso sosai, wani zobe da d'an kunne na gold ya d'auka mata, murmushi yayi azuciyarshi yace "nasan idan tasa wannan she will become like princess".
A takaice zuwa wannan super market dayayi, yayishi ne sabida Minal Dan yanason ya faranta mata kamar yanda itama ta faranta mishi,
Yana gama siyayyan yanufi wajen me kaza, yasiyo gasasshe guda biyu, mota ya kama ya nufi Hanyar Hotel Cikin zumud'in zaije yaga beautyn shi.
"Yana zuwa ya wuce Room 120 Wanda shi suka kama, Murmushi yayi yace "nasan yanzu tana jirana"
Sai de me? Yana zuwa yaga kofar d'akin Rubb da kwad'o, Cikin mamaki yace "kai waya rufe d'akin? Kodai namanta d'akin ne? No Room 120 muke kuma gashi shine wannan"
Ajiye ledojin hannunshi yayi yatafi wajen reception, tambaya yayi, ina makullun Room 120? Mika mishi makullin akayi Cikin mamaki yace to ina Minal taje? Kai baridai na dubata Cikin d'akin, da sauri yaje wajen d'akin ya d'ebo ledojin yashiga,
"Beauty? Beauty?"
Shine abinda yake fad'a nemanta yake acikin d'akin har karkashin gado saida yaduba dasu toilet gaba d'aya Amma ko Alamunta babu, Cikin firgici yafita a d'akin ya nufi wajen reception Yana tambayarsu waya kawo makullin, wata mata ce tayi mishi bayani cewar ai wata yarinya ce takawo Hannunta d'auke da jakan kaya"
Bilal Cikin tashin hankali yace "no no beauty baza kiyi hakaba nasani zaki dawo"
Barin wajen yayi da sauri yanufi harabar hotel d'in da wuraren shakatawarsu amma bai ganta ba,
Zama yayi a bakin get Yana jiran dawowarta.
Minal bacci take Cikin kwanciyar hankali, wasu samari ne sukazo wucewa, Sai sukaga mutum kwance akasa rungume da jaka, zaro ido d'ayan yayi da turanci yace "kai kaga wata fine girl a can?"
Da sauri d'ayan ya juya yaga yarinya kwance tana sharar bacci, juyawa sukayi gabas da yamma sukaga babu me kallonsu, wurin Minal suka nufa d'ayan ya wupce jakar ya bud'e, ganin kud'ad'e yasa yace "guy's yaufa mun fito da sa'a ga kud'i ga kaya"
Tafawa sukayi suna jin dad'i, Minal ce taji hayaniya akanta da sauri ta mike tana laluben Jakarta, ganin samarai guda uku a kanta suna kallonta kuma da Alama 'yan kwayane yasa ta tsala ihu tace "kafa me naci ban Baka ba?"
Gudu take tsakaninta da Allah Samaran suna bin bayanta, mutane suna kallonsu Amma babu Wanda ya kula, Minal ihu take tana cewa "a taimaka min" babu Wanda yakejin yaren Hausa a cikinsu, Sai samaran suce "Ku kama mana ita b'arauniya ce"
Idan mutane sunji haka Sai su kyalesu,
A halin yanzu ta gaji da gudun kafafuwanta sun mutu, daidai wani kwana ne wata mota tazo da gudu, itama Minal da gudu tazo Sai kawai motar ya d'auketa cakk, Minal fad'iwa