Showing 6001 words to 9000 words out of 52544 words
Chapter 3 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Jidda s Mapi.txt
bata tsoron jikin maza, ace in Aureta Kai inaa"
Latif ne yafara lallaɓanshi harya samu Bilal yadaina surutun.
Yace "yanzu dai katashi kashirya akwai meeting dazamuyi yau ana jiranmu a office kuma idan anyi wannan zaman Zai taimaka mana wajen bunƙasa wannan Companyn"
Bilal ne yace "meyasa baka sanar dani dawuri ba?"
Nima bada wuri suka sanar dani ba, cewar Latif.
Dasauri Bilal yatashi yashiga cikin gida domin shiryawa,
Toilet yanufa sabida yayi wanka.
_Minal_
Ita kuma yau ganin wani faɗa ta tsaya yi a anguwansu har tayi lattin siyan wake,
Sai bayan an gama faɗan kafin ta tafi gida, sauri take taga ta iso gida.
Tana shiga gida Umma tafara yi mata faɗa "haba Minal aina kikahe siyan waken? Tin karfe 9 na aikeki sai karfe 11 zaki dawo? Yanzu kiga kinyi letti har yaushe zaki wanke wake akai markaɗe har ayi alale?"
Minal shiru tayi dan batasan me zatace ba,
Kuma tasan tayi laifi.
Ba magana nake miki ba?
Minal tace "Umma dama su Ummi ne suke faɗa shine nake rabasu ina musu wa'azi"
Dagajin maganar ansan karya take faɗa.
Minal sau nawa zan faɗa miki ki daina sa kanki a RIKICIN UNGUWA (sunan littafin kanwata, Walida S Mapi)
Minal shiru tayi tafara wanke waken
Dasauri take aikin sabida ta tafka letti gashi Umma taki tayata,
Surutu takeyi azuciyarta "yazu garin kallon RIKICIN UNGUWA sai in dawo inyi abu letti, kai gaskiya bazan kara tsayawa kallon faɗa ba,
Tana aiki tana surutu Umma najinta Amma tayi mata shiru.
Dakyar tagama alalen ta girka manja awuta kafin tashirya,
Cikin wani kwano me marfi tasa manjar,
Ɗaukan alalen tayi tace "Umma natafi"
Sai kin dawo cewar Umma.
Bilal wanka yayi da sauri yafito yashafa mai da turare, ya taje gashin kanshi yashafa mai,
Wani Farin shadda ɗinkin Omo yaɗauko yasa da farin hula farin agogo da farin takalmi.
Keyn motarshi yaɗauka tafita aɗakin da sauri.
Wata farin mota kirar marsandi naga yashiga, horn yayiwa megadi aka buɗe mishi get yafita dasauri.
Gudu yake yana Allah Allah ya iso Companyn domin baya taɓa mantawa da maganar Daddynshi akan yakula da dukiyarshi, hakan yasa Bilal baya wasa da harkan Business,
12 cif ya iso Companyn,
Shiga ciki yayi da motarshi,
Daidai lokacin daya fito yana kulle motar, shine lokacin da Minal tazo wucewa, juyawan dazeyi kawai yaci karo da mutum.
Ita kuma Minal tsoro da fargaba yasa tayi saurin sakin kwanon manjar hannunta.
"Kwal kakeji kwano yafaɗi kasa manja yazube jikin Bilal"
Tsaya tayi jikinta yana rawa, manya manyan idanuwanta duk awaje tsabar firgita, ga alalenta ma yazube.
"Mutane kuma sun tsaya sai kallonsu suke kamar sun samu Daɗin kowa lols"
Tin daga sama har kasa Bilal yake kallon kayan jikinshi duk yaɓaci da manja, bfarin motarshi ma duk manja sun ɗila ajiki.
"Bilal tinani yafara me zaiyiwa yarinyan nan?"
Tafiya yafarayi yana isota, ita kuwa sai baya baya takeyi a razane.
Latif ne yafito daga office yaga yanda jikin Bilal yaɓaci da manja ga Minal tsaye a ruɗe yace "yau ake yinta"
Isowa wajen dasuke yayi yace
"Ranka shidaɗe An tanadar maka da wajen zama me ɗauke da farin kuhera you are wellcome"
Yakwashe da dariya yabar wajen,
Abun yasa mutane dariya kowa sai kyalkyalawa yake kamar ba gobe,
Takaici, baƙin ciki, haushi, su suka taru sukayiwa Bilal yawa awannan lokacin.
Minal ce tajuya ta ɗaga skirt nata wanda duk ya ɓaci dazaren da akayita ɗinkawa ta faki idon Bilal ta kwasa da gudu tabar cikin companyn.
Bilal ne yacewa megadi "kai? Karka barta tafita"
Ai Minal tayi gaba sai labari.
Haka Bilal yadaure yashiga motar yabar Companyn rai aɓace,
Ita kuwa Minal gudu tarinka tikawa har gida.
Dagudu tashiga gida tana nishi,
Umma ce ta tashi afirgice tace "Minal 'yata meya sameki?"
Minal tafara kame kame, daga baya tace Umma cikina ne ya ruɗe.
Toiket tanufa dasauri, Umma tana kallonta.
Shikuma Bilal kuka ne kawai beyi ba, jiyayi ya kara tsanar Minal, yau daza'a bashi bindiga ace ya harbe mutum ɗaya babu shakka Minal ze fara harbewa, yatsaneta!
Yatsaneta!
Yatsaneta!
Gudu yake akan titi motarshi duk ya lalace da manja.
Ahaka harya iso gida yakira megadi yace awanke mishi motar.
Shiga cikin gida yayi dasauri, Hajiya Babbace afalo tana kallo,
Bilal yazo wucewa taganshi jiki duk manja ga fararen kaya, dariya takwashe dashi tana tafa hannu,
Wani kallo Bilal yabita dashi idanunshi duk yayi jaa,
Wucewa yayi cikin ɗakinahi yacire kayan jikinshi yace "na rantse ke zaki wanke kayannan".
_Washe gari_
"Daddy ne yashiga ɗakin Bilal yace "yau bazakaje office ba zan aikeka,
Bilal yace to,
Daddy yace bani makullin office ɗin?
Bilal ne yatashi yabashi makullin.
Yau Bilal beje office ba Daddy ne yaje amaikonshi,
Zama Daddy yayi akan kujera yace akira mishi Alhaji Nura.
Alhaji Nura shinee kula da companyn idan Bilal baya nan,
Shi baƙi ne yanada jiki,
Bilal ya yadda da Alhj Nura sosai.
Shiga office ɗin Alhj Nura yayi,
Daddy ne yace mishi "have a sit"
Zama yayi a kujeran dake fuskantar Daddy,
Tashi Daddy yayi yaɗau makulli yakulle office ɗin,
Mamaki ne yakama Alhj Nura.
Daddy ne yayi gyaran murya yace "Am Alhj Nura nasan zakayi mamakin kiranka danayi, kuma na kulle kofa,
Wata muhimmiyar magana nakeso muyi dakai,
Wanda banason kowa yaji dagani sai kai"
Alhj Nura yace wani magana me wannan?
Daddy ne yayi gyaran murya yace "Alhj Nura? Shin kanason kazamo me arziki sosai yanda kowa zai sanka aduk faɗin garin Gombe?"
Meze hana? Cewar Alhj Nura
To wani aiki nakeso muyi amma kasani idan har aiki yayi kyau zan baka kashi talatin nacikin dukiyana,
Idan kuma aiki beyi kyau ba, tofa babu hannuna aciki.
Shiru Alhj Nura yayi yana tunani, sannan yace "babu komai insha Allah Aiki zeyi kyau"
Daddy ne yatashi yana zagaye office ɗin yace "Alhj Nura aiki akan Bilal nakeson ayimin"
Bilal yanada taurin kai,
Babu yanda banyi ba akan yanunamin dukiyar Mahaifinshi Amma sam yaki,
Hakan be dameni ba nace ya Auri Afrah sabida nasan idan harya Aureta to dukiyar namu ne,
Hakan ma yaki yadda"
Yanzu inason ayi mishi abunda zesa yanunamin dukiyarshi dakanshi basai na tambaya ba.
Alhj Nura yace me za'a mishi?
Daddy ne yace "Makantar dashi za'ayi"
Alhj Nura yace tayaya?
"Ta hanyar watsa mishi ACID inji Daddy"
Mutane Biyu zaka nema, zan faɗa maka inda yake zama bayan mangariba, inason awatsa mishi a idonshi kawai shikenan.
Ammafa kasani idan har aka kamasu kada sunana yafito abakinsu.
Domin wanke hannuna zanyi cau incire bakina.
In Allah ya yadda babu wanda ze kamamu cewar Alhj Nura.
Wasu kuɗaɗe Daddy yaciro yabawa Alhj Nura yace "ga wannan karike awajenka nasan zasuyi maka anfani"
Karɓa Alhj Nura yayi jiki narawa yace an gode Alhaji.
Jibi nakeson ayi aikin, a garden nacikin gidana za'a sameshi bayan mangariba,
Akula sosai sanman banason kowa yasan muna tare dakai, karka nunawa mutane kasanni sosai kaji?
To Alhaji,
Akula sosai.
Fita yayi daga office ɗin, dasauri Minal tamatsa abakin Kofar jikinta duk yana rawa,
Ɓuya tayi abayan wani karfe,
Tsayawa Alhj Nura yayi yana juye juye jin kamar mutum abayanshi.
Jikin Minal ne yafara rawa atake cikinta ya ɗibi ruwa,
Addu'a take Allah yasa Alhj Nura be ganta ba,
Dan idan yaganta tasan kasheta zasuyi.
Juyawa yayi yafita a companyn dasauri,
Daka ganshi kasan bashida gaskiya.
"Minal ganin yatafi yasa tafito abayan karfen dasauri, har yanzu jikinta be dena rawa ba,
Sauri take afirgice jikinta yana rawa"
Hanyar gida takama tana addu'a tana sauri,
Nida nazo bada hakuri sai kuma inji abunda yafi karfin kunnena?
Nashiga Uku Allah yasa mafarki nake,
Acid a ido kai.
Afirgice tashiga gida, Umma naganinta tafara tambayanta "'yata meya faru?"
Shiru Minal tayi tana kallon Ua jikinta duk yana rawa,
Hannunta Umma takama suka shiga ɗaki, Kwanciya Minal tayi akan gado har yanzu jikinta be dena rawa ba.
Umma ce tafara tofa mata Addu'a harta samu tafara bacci.
Hawayene yafara fita a idon Umma tana me tausayawa 'yarta.
_✅ote comment and share_
✍🏻 *Jiddah S Mapi*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
(An heart touching story)
*Written by*
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_
*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_
*Page* 5
"Minal bacci take amma zuciyarta kamar wuta har mafarkin abinda taji saida tayi, tinda take bata taɓajin abinda ya tsinka mata zuciya irin wannan ba, acikin mafarkin taga wasu mutane biyu sunje sun watsawa Bilal Acid, afirgice tatashi tana tana cewa idonka! Ka gudu idonka! Zasu watsa maka Acid, dasaufi Umma tashigo ɗakin tana rike Minal, lafiyarki kuwa? Meya sameki? Kodai Jinnu ne? Dan Allah Minal kifaɗamin abinda yafaru ke kaɗai kika ragemin aduniya bayanke banida kowa banason in rasaki Minal kitaimaka kifaɗamin suwaye suke bibiyarki?
Shiru Minal tayi batason tafaɗawa Umma abinda yake faruwa dan tasan Umma bazata barta taɗau mataki ba,
Sharewa Umma hawaye tayi tace ba komai Umma mafarkin abin tsoro nayi shiyasa natashi afirgice, kin tabbata? Cewar Umma
Minal tace eh Umma
To tashi kije kiyi wanka Minal tace to"
_Washe Gari_
6-4-2019 ranar Juma'a shida ga watan Aprilu shekara ta dubu biyu da goma shatara Bilal ne kwance akan makeken gadonshi idonshi alumshe azahiri bacci yakeyi amma a baɗini ba bacci yake ba, tunani yake akan abunda yafaru da iyayenshi da kanwarshi wanda haryau zuciyarshi tanayi mishi wasi-wasi akan wannan hatsari dasukayi, juyawa yayi ahankali yana kallon wani Agogo dake cikin ɗakinshi wanda Daddynshi yabashi tin lokacin yana primary yana daraja agogon sosai, gani yayi har karfe takwas yayi dasauri yasauka akan gadon yayi hanyar toilet, wanka yayi da sabulanshi me kamshi sannan yafito yashafa mayukanshi me kamshi da sanyaya zuciya, wata jar riga yaɗauko wanda aka rubuta Mad over you ajikin da bakin rubutu, sai wani jins nawando dayasa da picap jaa yasa da baƙin flatshoe namaza yaɗauki makullin motarshi yafice agidan.
"Minal kuwa yau wayarta take dubawa kowani bayan mintuna gani take kamar zaman datakeyi na ɓata lokaci ne gashi Umma zataje unguwa yau tahanata fita ko ina
Kuma tasan zuwa unguwar Umma idan taje bata dawowa dawuri
Gashi yaune su Alhj Umar da Alhj Nura zasu cika kudirinsu akan abokin gabanta wato Bilal, duba agogo kawai take idan karfe biyar yayi zatayi tafiyarta acewarta ko Umma bata dawoba
Karfe 5:50 cif Minal tafita agida babu wanda yasani sabida Umma bata gida Mashin me kafa uku takama tayi hanyar company tana zuwa tawuce wajen me gadi tagaidashi ina wuni baba? Yace lafiya lau ɗiyata meya fito dake yau da goshin mangariba haka?
Minal shiru tayi dan tarasa me zatace sai can wani tunani Yafaɗo mata tace Baba dan Allah yau Bilal yazo aikine?
Be zoba cewar baba megadi amma lafiya kike tambayarshi?
Eh dama baba wallahi sonake nbashi hakuri akan abinda yafaru cewar Minal amma dan Allah kokasan adreshin gidansu?
Eh nasani inji Baba megadi G.R.A house Number 3
Tom nagode baba cewar Minal
Fita tayi dasauri takama mashin tace me mashin Hause Number GRA house number 3 zaka kaini amma inason kajirani sabida sauri nake
To badamuwa Hajiya cewar me mashin ɗin"
Shikuma Bilal yau agidansu Latif ya wuni suna hira sai karfe 5:30 yadawo gida, kwanciya yai yaɗan huta kaɗan kamin yatashi yanason yayi alwalar mangariba,
Masallaci yatafi lokacin daya fito Minal dame mashin sunata hira kamar dama sunsan juna kasancewar Minal akwai saurin sabo da mutum masallaci me mashin ɗin yaje shima yabarta awajen, Minal tana zaune agefen mashin ɗin taga wasu mutane guda biyu sunzo zasu shiga gidan Alhj Umar zuciyarta ne yayi bala'in tsinkewa amma kuma saita tuna mutanen dazasu zo ze kasance 'yan dabane su kuma waɗannan da shadda ajikinsu me zafin gaske sannan da wata 'yar karamar jaka ɗayan yarataya awuyarshi da alama abokan Bilal ne
Kallonsu take har suka shige gidan.
Bayan an idar da mangaribane Bilal yadawo yaga mace zaune akofar gidansu amma tajuya kanta ba'a ganin fuskarta kawar dakanshi yayi yawuce gida ko kara kallonta beyi ba,
Ita kuma Minal ganin yashiga gida yasa ta tashi da sauri zata shiga gidan taɓoye lokacin megadi yana masallaci dasauri tashig ciki tarasa ta ina zata farabi acikin gidan Babban gidane batasan ta inane garden da ake faɗaba tsayawa tayi tana tunani taji ance ke!! Me kijeyi anan? Fitsari ne kawai btayi ba awando tsabar ruɗewa juyowa tayi taga wani tsoho da alama megadi ne yadawo, jikinta yana rawa tace dama Latif ne ya aikeni wajen yaya Bilal dajin haka se megadi yace ok ok jeki dataga tatsira sauke ajiyar zuciya tayi tace Alhmdllh dama Baba yacemin a garden kuma bansan gadmrden ɗin ba
Kibi senta har karshe zakiga garden ɗin nima dan ina sauri ne yasa bazan kaiki ba sabida Alhaji ya aikeni, to baba nagode cewar Minal"
Minal senter tabi kamar yanda Baba megadi yace daidai wajen kwana taga wasu 'ya'yan itatuwa kala kala wajen dasanyi sosai sannan yana kamshin fruits lumshe idonta tayi tana mejin daɗin yanayin wajen,
Tana buɗe idonta ahankali ahankali tayi tozali da Bilal zaune kan plastic chair dawata farar center table agabanshi wanda aka cikata da kayan itatuwa dakuma drinks kasancewar inda yake akwai ɗan haske kaɗan yasa take iya ganinshi
Ɓuya tayi abayan wata bishiyar inab yanda zata iya hango duk abinda ze faru.
"Shikuma Bilal kawai yana zaune ne amma sam yau yanajin wajen baya mishi daɗi, karan takun mutane yafaraji abayanshi daya juya sai yaga ba kowa
Waya yaɗauko yakira Latif yace mishi dan Allah Latif kazo akwai wata magana dazamuyi
Ok cewar Latif"
Yana kashe wayar yaji an ja plastic chair dayake zaune akai yana kokarin tashi yaji ɗayan ya rirrike hannayenshi duka biyu,
Gani yayi ɗayan yaciro wani abu a kwalba yana kokarin watsa mishi kafarshi yaɗaga ya buge abun dasauri meshi ya ɗauko ragowan suna kokarin watsa mishine yajuya fuskarshi a dasauri abun yataɓa kanshi ihu yasa sabida zafin dayaji, sukuma mutanen sunaji yayi ihu ɗayan yace yataɓa idonshi?
Dakai ɗayan ya amsa mishi alamar Eh.
Ita kuma Minal hankalinta akan wayarta da aka kira da sabuwar numba jin ihu da Bilal yayi yasa ta tashi afirgice tana kallon meya faru,
Ganin mutanen data gansu ɗazu tayi suna fitowa, dagudu ta iso wajen tana ganin ɗayan ze bugeta tayi saurin rike riganshi tana bugunshi gashi fuskarsu duk sun ɓoye da bakaken abu,
Ganin yarinyan zata tara musu jama'a yasa yaciro ragowan Acid ɗin yawatsa wa Minal a idanu, saurin sakeshi tayi tasa wani irin ihun daya ɗaukin cikin unguwar GRA gaba ɗayanta tace Wayyo IDONA dasauri me mashin ɗin yashigo gidan yaga Minal Kwance tana ihun idonta,
Hanunta yarike yafita da ita dasauri tana ihu tana murza idonta, dasauri yasata amashin ɗin yaja yabar unguwar da ita.
"Bilal kuwa yanajin sunce yataɓata idonshi? Se yayi pretending kamar a idonshi abun yasameshi, yasan cewa wannan shiri ne kuma yaji ihu amma idan yabuɗe idonshi yasan zasu watsa mishi a ido domin alamu sun nuna makantar dashi sukeson suyi, daidai lokacin da mutabe suka shigo gidan jin anyi ihu,
Sukaga Bilal kwance yana murza ido dasauri suka karasa inda yake suna tambayarshi meya faru? Yace Acid a idona sun watsamin shikenan namutu kutaimaka min".
_✔ote Comment & share pls_
✍🏻 *JIDDAH S MAPI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
(An heart touching story)
*Written by*
Jiddah S Mapi
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_
*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_
*Page* 6
"Mutane sun taru makil akofar gidan Alhaji Umar shikuma Bilal ganin haka yasan da haɗin bakin nakusa dashi awannan lamarin kuma yanada tabbacin idonshi suke nema su ɓata, daidai lokacin motar Alhaji Umar yadanno kai cikin gidan, dasauri yafito amotar yana tambaya meyafaru? Wanine acikinsu yace ranka shidaɗe wasu mutanene suka shigo gidannan suka watsawa Bilal Acid a ido, Acid!!! Cewar Alhaji Umar, garin yaya haka tafaru? Wani mara mutuncinne yashigo har cikin gidana yawatsawa ɗana Acid a ido? Lalle kuwa sai hukuma sun shigo lamarinnan saina kulle duk wani wanda yakeda sahanu, haka Alhaji Umar yayita matsifa kamar dagaske Amma acikin zuciyarshi wani irin daɗi yakeji,
Karasawa inda Bilal yake yayi yana zuwa yafashe da kuka yace yanzu Bilal shikenan sun makantar min dakai? Yanzu baka ganin kowa? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un,
Bilal yanajin maganar Daddy abun yabashi mamaki matuka, ganin haka yasashi cewa Eh wallahi Daddy haka Allah yakaddara min zan kare rayuwana amakanta yanzu idaduna basa ganin komai, Bilal yafaɗi haka yana me hawaye, idan kaga yanda Bilal yake acting zakace da gaskene yataɓa idonshi amma shi azuciyarshi yasa kudirin saiyayi bincike alamarin,
Suna cikin wannan halinne saiga Latif yana zuwa yafara tambayar meyafaru? Daddy ne yayi mishi bayanin komai, shiru Latif yayi sannan yace yanzu Bilal baka ganin komai? Bilal yace Latif bana ganin komai kutaimaka ku kaini ɗakina, latif ne yace wallahi saina gano duk waɗanda sukayi maka wannan aika-aikar koda kuwa zan rasa raina ne,
Jin haka yasa zuciyar Daddy tabada wani sauti Dummm yasan idan bincike yayi bincike dolene aganoshi"
"wani irin kallo Daddy yake yiwa Latif, hannun Bilal Latif yarike domin kaishi ɗaki, mutane sunata Allah wadai da wanda suka aikata mishi haka".
"Minal damai mashin kuwa asibiti suka nufa, suna zuwa aka nunawa me mashin ɗakin dazasu samu babban likita, Hannunta me mashin yake rikewa suna tafiya har suka iso office na babban Doctor"
Bubbuga kofar me mashin ɗin yayi daga ciki akace "yes coming"
Shiga sukayi ciki wani bakin mutum ne me jikin gaske yake zaune akan kujeran doctor.
"Meke tafe daku?
Yallaɓai wasu mutanene suka watsa mata Acid A ido shine nace bari nakawo ta aduba karya zame mata matsala,
Shiru doctor yayi yazubawa Minal namujiya can yacewa me Napep ɗin wannan fine girl ɗin aka watsawa Acid a ido? Kai gaskiya banji daɗi ba amma ɗan fita kabamu waje mana"
Fita me mashin yayi a office ɗin wanda har zuciyarshi be kawo komai ba.
Tashi doctor yayi awajen zamanshi yaje dab da Minal yazauna,