Showing 45001 words to 48000 words out of 52544 words

Chapter 16 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Jidda s Mapi.txt

29 Oct 2025

551

ya cika da hawaye yace "Dan Allah Latif kar kayimin karya don samun lafiyana pls"
Latif yace "ba karya nake ba gaskiya nake fad'a maka"
Bilal ne ya mike yanufi wardrobe passport nashi yafara nema, zauje yayi visa.


"Baby tayiwa Daddy maganar makarantar Minal, Daddy yaji dad'i sosai washe gari akayi mata register a makarantar su Baby, Minal tafara zuwa school rana ta farko harta fara gane Abu, 'yan mata sai zuwa wurinta suke wai sunaso suzama kawaye, Minal sai dariya kawai takeyi musu.

"Bilal yayi visa gobe da sassafe zai tafi Abuja, Latif ne yace "Bilal yakamata fa kabi komai a hankali kada kayi gaggawa"
Harara Bilal ya banka mishi baice komai ba yaci gaba da shirya kayanshi.


_Guy's am seriously busy am trying my best to write in return just expects ur moment.
.well if you won't comments I will not give update...silent readers pls comment....next Update when can't promise am vary busy, Thanks you All_


✔ote and Comments


*Wattpad*

@jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Page 40...

By
Jiddah S Mapi

*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio


~had'a kayanshi yayi ko kallon inda Latif yake bai kara ba, yana gamawa ya Ciro waya ya sanarwa manager cewa kwana biyu bazai zo company ba, Latif da kallo yake kawai yake binshi, shi abun har mamaki yake bashi wai ace Bilal ne ya rud'e akan soyayya haka? "To Allah dai ya kyauta"


"Amma Baby kina ganin karatu da cikin nan zaiyi kuwa?" Minal tafad'a cikin hawaye azuciyarta kuma tanajin Bakin cikin abinda Bilal yayi mata, Baby ce ta share mata hawayen tace "mata nawa suke karatu da ciki? Mata sunfi dubu, meyasa zaki tada hankalinki? Kowa da nashi kaddarar ki godewa Allah daya kawo miki naki ahaka"
Minal rungume Baby tayi tana kuka, Baby bubbuga bayanta take alamar rarrashi, suna cikin haka mommy tayi sallama, ganin yanayinsu ba karamin tausayin Minal taji ba, itama karasawa tayi ta rungumesu duka tana rarrashinsu, saida taga Minal ta daina kuka kafin ta saketa, tace "Daddynku ne yace nakiraku"
Mikewa sukayi dukansu sukabi bayan Mommy, suna zuwa babban falo Minal da Baby suka zauna a kasa inda Mommy kuma ta zauna agefen Daddy, gyaran murya yayi yace.

"Am Minal? Naji sakon da kika tura Baby tafad'amin kuma naji dad'i da kikace kinason karatu, to Amma raina yayi matukar b'aci da ke bakizo da kanki kika fad'amin ba, daidai da rana d'aya ban tab'a d'aukanki bare agidannan ba, dake da Baby duk 'ya'yan cikina na d'aukeku bakuda bambanci awajena, daga yau idan kina bukatar Abu kizo da kanki ki tambayeni karkiji tsoro, nima Uba nake awajenki kinji?"

"Insha Allah Daddy zanyi yadda kace nagode da kulawan da kuka bani, Allah ya biyaku da gidan Aljanna"
Tafad'a tana goge hawayenta da gefen d'ankwalinta.

Daddy yace "Ameen, to kuma akwai wata Alfarma danakeso awajenki, inason kifad'amin gaskiya idan kinaso ko bakya so, inason in had'aku Aure da Hamma Yarda, Wanda asalin sunanshi Abubakar, jikan Innace wacce mukaje wurinta a yola, mahaifinshi ya rasu sanadiyyar cutar Hanta data dameshi, an kaishi kasashe da Dama Amma ba'a dace ba daga baya sai mutuwa da yayi, Abubakar takwaran Mijin Inna ce, anace mishi Hamma Yarda ne sabida takwaran baban babanshine, yayi karatu secondary anan gida Nigeria, sannan yayi University a kasar England, kasancewar yayi karatu a kasar turai hakan bai hanashi riko da addininshi kem kem ba, na yadda da tarbiyyarki sannan na yadda da tarbiyyar Hamma Yarda, na tabbata idan kika Aureshi zakiji dad'i, Za'a bar Auren saikin haihu tukun"

Wasu hawaye masu d'umi ne suka fara bin kuncin Minal, zuciyarta sai dukan Tara Tara take, tarasa ta ina zata fara yiwa Daddy bayanin tanada Aure, gashi sun nuna mata so bana wasa ba, Mommy ce ta katseta tace "Minal idan har bakya son Hamma Yarda kifito ki fad'a mana mu bazamuyi doleba"
Minal dukar da kanta tayi cikin jin kunyar karyar datayi musu abaya, cikin kuka me tsuma zuciya ta bud'e bani da kyar tana har hard'e zance tace

"Ku gafarceni Mommy da Daddy da Baby nayi muku karya tin rana ta farko da kuka bugeni da mota, banyi Dan ra'ayina ba, nayine don in tsere daga sharrin Mijina.....kukane ya kubce mata, tashiga yi ba tsayawa.
Mommy ce ta taso daga kan kujera ta riko Minal tace "me kikeyi haka Daughter? Idan bakya sonshi ai babu dole"
Minal juyawa tayi tana fuskantar Bedroom sabida batason had'a ido dasu, sakamakon karyar datayi musu, tana kuka tace "Mommy inada Aure, kuma ba soyayya mukeyi da Hamma Yarda ba, soyayyan da mukeyi ta 'yan uwantaka ne a matsayinmu na musulmai, kuma na d'auki Hamma Yarda kamar yayana ne yanda Baby ta d'aukeshi, ya zan Baku labarin Mugun Mijin Dana Aura Wanda yayi sanadiyyar makancewata daga baya ya wulakanta ni, babu abinda yake b'atamin rai kamar idan na tuna ranar Aurena da aka kaini gidan mijina, a kasan tyles cikin sanyin AC muka kwanta nida kawata" share hawayenta tayi taci gaba da basu labarin irin wahalar datasha sanadiyyar Mijinta, Abu biyune ta b'oye musu shine Sunan Bilal da kuma sunan Daddyn Bilal.

"Amma wannan Mijin naki yacika mugu Mara imani, Da ace nasanshi to wallahi babu abinda zai hanani kaishi koto, sabida gani nake kamar wa Baby akayi wannan abun" cewar Mommy wacce tun kafin taga Mijin Minal taji ta tsaneshi, da ace zata Ganshi yanzu dasai ta zabga mini duka don ba karamin haushi ya bata ba.

Shiru Daddy yayi yarasa mema zai fara fad'a awannan lamarin, ajiyar zuciya ya sauke yace "shikenan tashi Ku tafi d'aki babu komai Allah yana tare da mai hakuri, sannan shima sai yaga sakayya insha Allah"
Baby ce ta riko hannunta suka tafi d'aki, Minal sai kuka take, Baby cikin muryar rarrashi tace "to miye anfanin kukan? Ni wallahi har naji maza sun ficemin arai, Ai garake ma baya miki maganar Banza, nida Yaya Mujahid kullum daga yace nayi mishi kiss, sai yace nayi hugging nashi, saifa nayi da gaske na had'e rai kafin ya daina, nafad'awa kawayena na makaranta sukace wai duk maza yanzu shine aikinsu koda Aurenki zasuyi sai sunyi miki maganar banza"

"Haba Baby, ai idan kinga namiji yana yi mini maganar banza tofa must of them ba Aure ya kawosu ba iyeyine kawai, sai suce Aurenki zasuyi daganan idan sun samu abinda sukeso sai kiga sun fara sauya miki, idan kuma suka gano keba 'yar iska bace sai kiji sunce gwadaki suke, babu wani gwaji, a lokacin da suke gwadakin da kin yarda wallahi bazasuce gwadaki suke ba, mazan ne yanzu sai an had'a da Addu'a,

*Note*
_('Yammata yakamata mukula sosai da samarin zamaninnan zakiga wani yazo wurinki da niyar Aure sai kiga yafara bijiro miki da maganar banza, idan kika nuna kefa ba 'yar iska bace sai kiga yace wai Dama wallahi gwadaki yakeyi yanason yasan ke 'yar iskace ko mutuniyar kwarai, idan ke wawiyace kuma saiki yadda, sai kiji suna cewa 'yammatan yanzu duk bazawaraye ne, baby bari nafad'a miki they know what they are doing, sunsan me sukeyi, mu kula sosai muyi taka tsantsan, wani Dan cin fuska idan yagama dake sai kiga ya koma wurin kawarki, wanima sai kiga ya Aureta an barki a zero zero, ga rashin mutuncinki ga bakin cikin ya Auri kawarki, maganin karta faru tofa kada a fara)_

_back to business_

Baby ajiyar zuciya ta sauke tace "to ai ina sonshi sosai Minal bari dai nayi istikhara"
Dariya Minal tayi tace "istikhara ana yinshi ne a lokacin da Abu bai shiga zuciya ba, shi istikhara ai Neman zab'in Allah ne, to idan yariga yashiga zuciyarki kinga koda Allah ya nuna mini ga Wanda yafi Alkhairi ke kuma Wanda yake ranki dabanne, bama wannan ba Baby nida tin d'azu gabana sai fad'uwa yake narasa meyasa"

"Wallahi nima hakane Minal saidai kawai muyita Addu'a Allah yasa Alkhairi ne"
Minal tace "Ameen".

_washe gari_

Bilal da Asuba ya d'au jakar kayanshi ya ya nufi airport, saida yashiga office ya kara duba information akan anguwarsu Minal kafin yaje yashiga jirgi, sai Addu'a yake Allah yasa yaga Beauty cikin sauki, sai 8:30Am kafin jirgi ya tashi, cikin minti 30 suka sauka cikin garin Abuja, Bilal fita yayi yashiga restaurant yaci abinci kafin ya kama taxi yanufi maitama unguwar da Minal take, zoben hannunshi yashafa a hankali yace "am coming to you beauty" yayi wani murmushin daya bayyana dimple nashi, fararen hakorinshi ma suka bayyana, rabon da Bilal yayi murmushi tun ranar da Minal ta gujeshi, wayarshi ya Ciro yanda kallon sreen d'in, hoton Minal ne Wanda ya d'auketa ranar a India tana bacci, gashin kanta duk a hargitse ta turo baki kamar wacce zatayi magana, Lokacin tayi mishi kyau bana wasaba shiyasa ya d'auketa photo, manna wayar yayi a kirjinshi ya lumshe idonshi a hankali yace "I miss you"
Saidai wani ikon Allah yana shiga cikin Maitama yaji gabanshi yana fad'uwa har wata zuciyar tace "kodai zuwanka ba alkhairi bane" wata zuciyar kuma tace mishi "fad'uwar gaba asarar namiji"
Dakewa yayi yanata Fad'in innalillahi, har suka iso kofar gidan dayakeda tabbacin shine gidansu domin har numbar gidan saida ya d'auka, Yabiya me Taxi kud'inshi ko canji bai tsaya ya karb'a ba ya juya ya tafi, yana zuwa kofar gidan Me gadi ya tsayar dashi yana mishi tambayoyi, Bilal ganin an rainashi yasashi kutsa kai yana kokarin shiga ciki, Rigimane ya b'arke tsakaninshi da me gadi.

"Minal Baby Mommy da Daddy suna zaune a dining sunacin abinci, kowa yayi shiru sai karan cokala kawai akeji, Minal sanye take da Riga da wando, rigar top ce me ado ajikin pitch color, sai wando daga wait an d'ame sai kasan aka bud'eshi (palazo) ta ta d'aura kanta da bakin d'an kwali Wanda ta taje gashinta ta bazashi a bayanta, ba karamin kyau dressing d'in yayi mataba, musamman yanda ta d'aura black d'an kwali, sai farantakanta ya kara bayyana, Baby kuma tasa wando jins blue da t shirt fari, sai farin picap datasa akanta itama tayi kyau, sai mommy datasa Black abaya da gyallenshi, Daddy kuma shadda yasa da Alama office zaije idan ya gama, kowa yanacin abincine Amma Sam yau gidan yayi shiru dayawa jikinsu duk a mace musamnan Minal datin jiya gabanta yake fad'uwa, Daddy ne ya katse shirun dacewa "Minal da Baby yau zakuje super market kuyi sayayya, nabawa mommynku 50 thousand tabaku, sannan akula banason yawuce yawucen banza, musamman ke Baby nasanki dason yawo kamar kinci kafar kwad'o" Minal ce ta toshe bakinta rana dariya kasa kasa, Baby sai hararanta take ta kasa tana hura hanci, Daddy yace "yi dariyanki Da Karfi My daughter, yarinyarnan yawonta yayi......kafin Daddy yakarasa sukaji hayaniya abakin gate, Gaba d'ayansu suka mike suka fice don ganin me yake faruwa, me gadi suka gani yana kokarin ture wani matashi, Daddy ne yace "kai kai meke faruwane?"

Cakk jinin jikin Bilal ya tsaya da aiki, jin wani murya da bazai tab'a mantawa a rayuwarshi ba, bayanshi a juye, yakasa juyawa yakalli me maganar tsabar yanda wani shock ya d'ibeshi, Me gadi ne yafara yiwa Daddy bayani "wai yace dole sai an barshi yashigo sai kace gidanshi" Daddy yace "barshi mana yashigo malam Yusu, kasan dame yazo?"
Me gadi yace "Alhaji mutanen yanzu ba abun yadda bane"
Daddy yace "kabarshi Wanda ya cuci wani ai kanshi ya cuta bawan Allah shigo".

"Duk maganar dasukeyi Bilal yana jinsu Amma shi yanzu da za'a yanka jikinshi tofa jini bazai fito ba, bai karasa tunani ba yakarajin Muryan daya firgitashi, "Bawan Allah kayi hakuri kashigo, kada ranka a b'aci" cewar Mommy, Baby ce takarasa don tabashi hakuri tana zuwa ta bubbuga bayanshi tace "Dan Allah kayi hakuri d'an uwa ba wulakanci akayi makaba, me gadi aikinshi na lura da wanda zai shigo kawai yayi"
Ganin baiyi maganaba yasata d'an turashi kad'an, Sai gani kawai tayi yafad'i a wurin a sume, ihu tafara tana kokarin d'agashi su Daddy da Minal da Mommy suka karaso, d'agashi sukayi suna son ganin ko wayene, Baby ce ta fad'i ajikin Minal, Minal d'agata tafarayi Amma sai taji tayi Nauyi, Alamar itama ta suma, Ihu Minal ta sake tana cewa Mommy!!! Mommy!!! Juyawan dazatayi sai taga Daddy yana bubbuga Mommy Alamar ta tashi, Minal da me gadi sun rud'e, Ko kallon inda bakon yake basuyi ba, suna takan Mommy da Baby, Daddy zufane yafara keto mishi kota ina, meyake faruwane? Me hakan yake nufi? Daga mutum d'aya ya suma sai biyu subi bayanshi? Minal ce garin d'aga Baby taji ta taka hannun mutum, juyawa tayi tana kallon meshi, a gigice takai idonta kan fuskarshi, jada baya tafara tana girgiza kai, Daddy be ankaraba yaga Minal ta fad'i akan mommy asume, babban rigan jikinshi ya cire, yaciro hulan kanshi yana fifita jikinshi, wuri yasamu ya zauna tsabar tashin hankali yarasa mema zai farayi, Baba me gadi sai zagayesu yake, idan yabi takan wannan yadawo kan wannan, shima yarasa me yake faruwa ".


✔ote & comments

*Wattpad*

_@Jiddah S Mapi_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Page 41...

By
Jiddah S Mapi

*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio

~me gadi yagaji da zirga zirga gashi ba Dama ya d'agasu sabida matane, cikin hanzari ya d'aga Bilal yasashi a gaban mota, Daddy ma yatashi yasa su Baby da Mommy da Minal a mota, suka nufi hanyar asibiti, suna zuwa aka karb'esu hannu bibbiyu, likitoci suka rarrabu akansu suna basu kulawa, Daddy da me gadi ne suka d'an fita domin subasu wuri, Zagaye cikin Asibiti Daddy yafara yana tunanin menene yasa dukkansu suka suma a lokaci d'aya? Share zufan daya fito mishi a goshi yayi, Megadi ne yace "Alhaji zamanin yanzu mutanefa ba abun yadda bane, zakaga mutum simi simi kamar mutumin kirki saika zauna dashi kafin kasan Halinshi, ni Dama tun zuwan yaron bai shiga raina ba, bakaga gashin kanshi ba kamar rumfa"
Daddy cikin dakewa yace "malam Yusuf Addu'a shine babban abinda yakamata muyi yanzu ba wai surutu ba"
Malam Yusuf shiru yayi bai kara cewa komai ba,
Sai bayan Isha kafin su Baby suka farfard'o Abin Mamaki Baby da sunan Yaya Bilal ta tashi, Mommy ma Bilal taketa Ambata, Sai Minal data tashi Tana Hawaye wani nabin wani, ta b'angaren Bilal yana farfad'owa yaganshi a d'aki kwance, a hankali yagmfara bin d'akin da Kallo, murya a toshe yace "Ashema Mafarki nakeyi, to amma inane nan?" Wani doctor ne yashigo yayiwa Bilal murmushi tareda mika mishi hannu suka gaisa, yace "Sannu Kaine Bilal ko?"
Bilal gid'a kanshi yayi alamar eh "ok wad'anda aka kawoku tare suna nemanka, Akwai wacce takeson ganinka acikinsu"
Bilal sai a lokacin ya tuna abinda yafaru sauka yayi akan gadon yace "ka kaini wurinsu"
Doctor yace "kabi a hankali fa"
'Dakin dasu Minal suke Doctor yakaishi, suna zuwa Doctor yayi sallama Bilal ma cikin sanyin murya yayi sallama, Minal ce kwance ta rufe idonta kamar me bacci, Zuciyarta tana mata sake sake da Dama, Jin sallamar Bilal yasata kara runtse idonta, Bilal yana shiga d'akin yaga Mommy tanata kuka, karasawa wurinta yayi da gudu ya rungumeta, itama rungumeshi tayi sosai tana kuka, Baby ma tashi tayi akan gadon da aka kwantar da ita ta rungume Bilal ta baya tana kuka, cikin sheshekar kuka Bilal yace.

"Mommy kuna Raye Dama? Shine kuka gujeni, harda ke Nabeelah? Yafad'a yana kallon Baby,
Mommy ce tarufe bakinshi tace " munyi hakane domin mu kub'utar da kanmu da kuma kai daga zalincin Yayan Mahaifinka, Alhaji Umar, Bamuyi don bama sonka ba"
Baby cikin kuka tace "Yaya bansan kana Raye ba, wallahi ban sani ba" taci gaba da kuka me tsuma zuciya,
"Ina Daddy?" Cewar Bilal.
Lokacin Daddy yashigo yana tsaye abakin kofa yace "gani nan, waye kai?"
Bilal cikin mamaki yake kallon Daddy juyawa yayi wurin mommy yana kallonta sai yaga ta kawar da kanta tana kuka sosai, "Daddy baka sanni ba?"
Daddy ne yace "ina zan sanka bawan Allah naganka dai a gidana"
Bilal cikin firgici yace "mommy kina jin abinda yake cewa"
Mommy batayi maganaba sai kuka, cikin kuka tace "Bilal yanzu ba lokacin magana bane kabari idan munje gida sai nayi maka bayani"
Minal tana jinsu Amma tayi likimo tana jin labarin kamar Almara, kara runtse idonta tayi tana numfashi kamar meyin bacci, Bilal ne yajuya yana kallon inda take idanunshi ne suka cika da hawayen farin ciki ga Minal ga Iyayenshi ga kanwarshi wacce yakesonta sosai, tashi yayi yanufi wurinta, A hankali yariko hannunta yana shafawa, Kwantar da kanshi yayi akan hannunta hawaye sunabin kumatunshi, cikin kuka yace.

"Lalle kin cancanci yabo Beauty, Had'uwata dake ya haifarmin da farin ciki mara d'orewa, Kin Makance ta dalilina, Wanda sanadiyyar haka ni na tsira da lafiyata, Kin had'ani da iyayena, Nagode miki Minal, insha Allah saina zama gatanki a duniyarnan, zan saki farin ciki Wanda bakiyi zato ba, zan maidaki tamkar sarauniya, Zaki fito daban acikin mata"
Minal tana jinshi, Amma tayi mishi shiru, janye hannunta tayi daga nashi, ta juya mishi baya kamar acikin bacci, Murmushi yayi yace "nasan dole kiyi fishin dani, Amma komai zakiyimin zan jure har lokacin da zaki sakko ki kulani"

Baby ce tazo inda suke ta dafashi tace "Yaya matar Aurece fa, kuma kake tab'ata bafa 'yar mommy bace"
Dariya yayi Wanda yafi kuka ciwo yace "Nabeela wannan matata ce"
Waro ido Baby tayi tace "matarka kuma?"
Bai karayi mata magana ba yaje wurin doctor ya tambaya musu sallama, sabida ya matsu yaji meyasa Daddy yanuna bai sanshi ba me yayi mishi, Doctor ne yarubuta musu takaddar sallama gaba d'ayansu, Daddy yabiya kud'in, Kowa ya tashi yana shiri banda Minal dataki bud'e idonta tin d'azu, Bilal ne yaje yana tattara hannun riganshi Alamar zai d'auketa, "dakata" cewar Mommy, cakk ya tsaya yana jinta, "karka sake kasa hannunka a jikinta, tayimin bayanij komai, duk abinda yafaru tsakaninta da Mijinta ta fad'amin, kuma a lokacin na nuna b'acin rai na, sabida haka baza'a toye mata hakki ba"
Tashi tayi taje gefe Minal ta zauna, hannunta ta riko tace "tashi daughter an sallamemu"
Minal ce ta mike don batason tana yiwa Mommy musu, Ido hud'u

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login