Showing 15001 words to 18000 words out of 90697 words

Chapter 6 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull.txt

24 Nov 2024

3974

Nai saurin riƙe hijjab ɗin ta gaba na yaga shi sannan na juyo ina sauke numfashi da ƙyar. Baby ce tsaye tana faman huci kamar mai shirin dambe. Na mata kallon sama da ƙasa kafin cikin mamaki na ce, “Lafiya kuwa baiwar ALLAH zaki shaƙeni kamar wadda ta ci miki bashi? Are you okay?”.
“A haukace nake dan uwarki. Kuma kaɗan ma na miki, wataran idan na shaƙeki har sai kin daina numfashi zan ƙyaleki. Dan haka ina mai gargaɗinki in har kina son ranki ki fita a sabgar Mansoor wlhy. Ki kuma bar ganin ya kawo kuɗi da sunan na aurenki, wlhy sai dai in bana raye hakan zata kasance. Dan yanda ban samesa ba kema baki isa samunsa ba jaka kawai ƴan karoro a gidan mutane mai ƙwacewa yaran gida samari su mayya”.
Murmushi kawai na saki mai faɗi dan wlhy ni dariya ma ta bani da tausayi. Bance mata komai ba nai shigewata ɗaki na barta tana ɗuran zagi kamar ba dare ba. Zuwa can kuma naji kamar maganar Abba sama-sama ita kuma tana kuka. Baki kawai na taɓe na gyara kwanciya dan so nake nai barci sosai kodan abinda zan tunkara a gobe in ALLAH ya kai mu. Sai dai duk da haka kamar kullum sai da na tashi nai ƙiyamullaili dan ya riga ya zame min jiki tashin a kullum, sai dai idan banda lafiya, amma ko prioud nake saina farka....


*_DAMA ACE....._*


(Dama ace) kalmace mai harshen damo. Zaɓa mata gurbi a nawa labarin shine cigaba da nutsuwar saurarensa. Kamar kullum yau ma sai da nai duk ayyukan gidan kasancewar nasan yau ɗin Mum a cike take da haushina. Hatta shi Abban ban san a wane matsayi ya ɗauki auren nawa ba. Dan daya dawo da ga sallar asuba na gaishesa sama-sama ya amsa min ya shige ɗaki abinsa. Ga Baby a gefe da marasa kunyar ƙannenta su Bibaa da Nabil. Shiri na nayi kamar yanda na saba, dan baƙin dogon hijjabin jikina har jan ƙasa ma yake. Ban biye ta maganar MD ba, na kawo kuma face mask na saka kamar yanda na saba shima baƙi, na ɗaura sirrin farin eyeglasses ɗina da har ana iya ganin ƙwayar idona fes. Sai ƙamshi dake fita a jikina mai daɗin tsiya na humra da turare. Yaya shike sayamin turare da duk wani nau'in kayan kwalliya na mata. Hatta kayan ciki da suturu shine ke saya min. Hakan yasa banjin ƙyashin duk sanda salary na ya shigo account na tura masa su gaba ɗaya a account ɗinsa batare dana cire ko sisi ba a ciki. To idan na ajiye mizanyi da shi. Duk wani abinda nake buƙata baya gazawa wajen saya min. Idan abin yayi ya shigo zaka sameni a layin farko cikin masu sakashi. Da harda Baby yake saya, amma ta ce masa yama bar wahala bata so. Koda ta faɗa ɗin bai daina saya ba. Sai da yaga bata sakawa sannan ya daina. Hakan kuma baya hanashi bata kuɗi akan ta saya abinda take so. Wannan kam sukan amshe ita da uwarta kuma baza'a sayi abin kirki ba kuɗin zai gantale. Hatta da data sakara Yaya sakamin yake da credit, sai daga baya ne ma Mansoor ya amshesa wannan. Dan haka Yayanmu kallon uba nake masa ba yayaba wlhy, dan ya share mana kukan maraici tuni sai dai na kewar iyaye da bazai taɓa gushewa ba ga ƴaƴansu. Amma ta ɓangaren rayuwa komai Alhamdullah.
Kamar yanda Yaya Musaddiq yay alƙawari shine ya ɗaukan a mashin ɗinsa da yasha wanki sai ɗaukar ido yake. Office ya kaini inda su Mansoor ke jirana dan da motar office zamu fita. Ba sauran abokan aikina ba hatta da Mansoor ƙuri yay kawai yana kallona cikin nuna mamakin ganin hijjab dana zuba har yana sharar ƙasa. Amma sai yay murmushi tare da kashe min ido ɗaya alamar yaji daɗin hakan da nayi. Nima murmushin nayi kawai na ɗauke kaina ina mai gaishesu. Duk suka amsa min da kulawa. Sai Davido ne ke magana akan shigar tawa. Ban tanka masa ba na shige mota abina na zauna batare da na yarda na kalla inda MD yake ba ko sau ɗaya, dan gaisuwa ma kaina a gefe nai masa. Naci sa'a dama sun gama loda komai dama ni suke jira. Kulsoom ma na ciki ita. Kusa da ita na zauna muka gaisa, sai gasu suma sun shigo. Da farko Mansoor na kula kusa dani yaso zama. Amma ganin yanda na koma jikin window muka saka bags ɗinmu a tsakkiya yasa shi haƙura ya zauna kujerar gabanmu, sai lokacin na ɗan saci kallon MD, yay kicin-kicin da fuska sai mazurai yake. Ƙasa nai da kai ina kwasar dariya, ɗan son banza an shirya ganin banza. To bata samu ba ai, sai a tafi wata tashar.......✍️








_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_






........Tun kafin mu fice duk sun cika motar da hira, ni dai ban saka musu baki ba face ma bitar questions ɗin dake rubuce dan karna kwafsa. Dan a nawa shirin ina son masa tambayoyin ne batare da takarda ba. Duk da ma dai har cikin waya na kwashesu gudun samun matsala. Lokaci ɗaya naji motar ta ɗauki shiru, kamar zan basar sai kuma na gagara hakan, dole na ɗago domin ganin abinda ya sakasu nutsuwa haka. To nidai banga komai ba face uban cinkoso na ababen hawa da titin ya samu tamkar ba safiya ba kuma weekend. Da ƙyar drivern mu ya kutsa ya samu wajen parking ma. Haka muka firfito kowannemu na bin katafaran ginin da kallo. Dan sai yanzu na fahimci abinda ya saka su yin shiru ɗazun. Gini ne da akayisa da wani kalar zallar gilashi mai garai-garai ta gabansa. Ga wasu manya-manyan symbols da hoton motoci masu shegen ƙyau da mashina irin na masu kuɗin nan. Da manyan haruffan baƙi an rubuta *_MAASH_*.
Tako ina jami'an tsaro ne, hakan yasa komai ke tafiya a nutse duk da alamu ma sun nuna duk wanda ka gani a inda motarmu ta samu damar shigowa to ba ƙaramin mutum bane, ko kuma dai yana da izinin zuwa wajen. Dan zuƙa-zuƙan motocine na nunama tsara. Yaku bayi kuwa na daga can tunkushe a titi an hanasu shigowa (🤥😞😏). Dan ƙa'idar sai ka nuna invition ɗin nan zasu bar motar ka ta wuce. A ƙafa muka cigaba da takawa saman lafiyayyen titin da aka ɗauka tun daga babban titi har zuwa cikin companyn. A dai-dai katafaren gate ɗin ma dai sai da muka nuna invition ɗin. Sannan akai searching namu aka tabbatar da bama tare da komai sannan muka shige bisa rakkiyar wani jam'i. Da alama wajen zaman ma a tsare yake kenan. Bazaka tabbatar da Companyn mugun ƙato na gaske bane sai ka shigo ciki. Ashe ta gaban duk wasan yara ne da ado kawai. Duk girman harabar an gyarata da uban decorations mai matuƙar ƙyau da ɗaukar hankali. Hakama an tsara kujerun zama cike da birgewa. Da ga can gefe abincine aka jera irin dai na taron ƴan gayun nan, dan ga masu zungura-zunguran hulinan nan irin nasu o,e a kitchen sun jeru kamar ƴan cocin yarabawa (😂lol). Mune ƴan jarida na farko da suka fara isowa, hakan ya mun daɗi, dan koba komai mun samu sits ɗin gaba a inda aka tsara domin ƴan jarida. Tuni su devido sun dasa camaras namu kuwa a inda komai bazai wucemu ba. Zuwan namu kamar ya buɗe ƙofa ne, dan sai ga mutane da ƴan uwanmu ƴan media nata shigowa a nutse babu wata hayaniya ko kace nace. Tun shigowarmu kuma tuni mun fara nuna komai live kamar yanda contract ɗin yake. Dan haka kusan komai daya fara da tushe kai tsaye ana fara ganinsa ne daga gidan tvn mu. Ni dai har lokacin ina a zaune dan ba'azo kan aikina ba. Kafin cikar awa guda waje ya gama cika taf da manyan mutane. Muryar mc kawai ake ji yana sanar da isowar manyan baƙi, sai mu kuma ƴan jarida dake namu bayanin domin gidajen tvn mu kai tsaye. Goma dai-dai dake tabbatar da duk wanda ake buƙata a wajen ya iso hatta da gwamna da sarki ma aka sanar da isowar mai gayya mai aiki. Wato *_Awwab El-Mu'azz Maashi_*. Tsitt wajen ya sake ɗaukar shiru kasancewar dai-dai nan zuƙeƙiyar baƙar mota da irinsu shugaban ƙasa kawai nake gani a ciki ta shigo. Ta gefe da gefenta da gabanta da bayanta kuwa wasu irin murɗa-murɗan basumadayen garada ne da gani kasan ba bugun Kano bane sai dai Lagos ɗin dan bamu da masu irin wannan suffar gaskiya😞. Su duka riƙe suke da bindigu kai kace zasu iya hana mutuwa ɗaukar wanda ke'a cikin motar ne😏. Har tsakkiyar filin motar ta shigo, inda mutanen dake a cikin motar bayansu suka fito a lokaci guda su huɗu. Mace ɗaya maza biyu. Wanda ke mazaunin driver ne ya buɗe booth da hanzarinsa ya ɗakko carpet maroon mai shegen ƙyau an rubuta *_Maash_* a jikinsa da golden mai ɗaukar ido. Yayinda macen baturiyar ta iso da sauri sauran mazan biyu a gefe da gefenta. Daka ganta kaga cikakkiyar baturiya. Duk tsaye sukai a ƙofar motar kowa cikin nutsuwarsa da kamewar girmamawa abin zam mamaki. (Humm jama'a MANDA fa duniya ce😜). Kusan minti ɗaya cif muna zuba idon ganin abinda ke faruwa kafin wanda ke gefen damar matar nan ya kai hannu jikin handle ɗin ƙofar ya buɗe tamkar mai gudun tashin yaro a barci. Wasu sakanni goma aka sake kwashewa kafin wani almurin baƙin takalmin haIf cover shoe mai adon golden ya sauka saman maroon carpet ɗin a hankali. Sai da aka sake jan wasu sakannin kamar uku sannan ɗayar ƙafar ma ta sauka baƙin wandon suit ya bayyana. Sannu a hankali sauran gangar jikin ma ta fito. Kaf wajen har masu ji da mulkin da kuɗin babu wanda bai bi wanna halitta da kallo da ga ƙasa zuwa saman ƙyaƙyƙyawar fuskar mamallakin jikin ba. Tsaye yake gam akan tsahonsa na tsayayyen namiji da babu ko ranƙwafawa. Suit ɗin jikinsa da basai an zauna ɓata lokacin lissafin kuɗin da suka lashe ba sun masifar zauna masa da tabbatar da shi a matsayin jaruminsa mai gara kan naira ta yanda duk yaso bisa damar da ALLAH ya bashi. Komai na jikin nasa baƙine, sai ɗan adon takalminsa da ta kasance golden da neck tie.. ɗinsa shima golden mai azabar ƙyau. Kamilalliyar fuskasa ma'abociyar kamewa da tsare gida ko nace baƙin hali a tsuke, sai kwantaccen gashin kumatunsa siriri daya zagaye bakinsa zuwa haɓarsa tamkar an zana ba biro. Yau ɗin ma dai akwai ɗan kunne ɗaya manne a kunensa, hakama zanen tattoo ɗinsa mai fuskar lion na nan zaune daram. Saɓanin hoto yau gashinsa ne a ɗaure kamar yanda mata ke parking sai dai shi nashi acan ta ƙasa ya ɗauresa har yana ɗan sauka jikin rigarsa dan babu kitso yau. Wanda bai sani ba tuni yake sakashi a jerin larabawa. Babu mai ganin idanunsa kasancewar sakaye suke a cikin eyeglasses mai masifar ƙyau daya ƙara fidda taswurar halittar ƙyawun hancinsa daya zauna ɗaram kan fuskarsa. Kafin kace mi tuni ƙamshinsa ya baje wajen kai kace mu namu turaren baida tasiri ne ko Companyn da suka wallafo namu basu iya zaɓar ƙamshi ba. Kai jama'a akwaifa ƙyawawa a duniya. Idan kaga wani sai kaga kamar ka yanka kanka ka ɓoye wuƙar ƙawai. Bily karfa ki zata wannan bayanin da nake zayyano miki a kansa ya wani birgeni ne. Mtsowww ko kaɗan..
Gaba ɗaya yaran nasa sake kame kansu sukai cikin nuna tsantsar girmamawa a garesa. Karan farko na ɗan taɓe baki takaici kamar zai halakani. Shike nan a wannan rayuwar in har kana da dukiya ka zama saraki ko mai mulki?. Kai wani abun ma da ake maka ko kai mulkin ba lallai ya samu ba. Dibi dai wannan mutumin yanda yake wani busar isaka da shan ƙamshi fuska tamm kamar wanda aka aikama saƙon mutuwar tsoffinsa.
Cikin isa da bajinta, a slowly tamkar wanda ake ɗauka a faifan video yay wani kalar haɗe hannayensa duk biyu a waje guda ya ɗagasu sama alamar gaisuwa wa duk jama'ar wajen. Kusan kowa dake wajen sai da sukai yanda yay ɗin idan ka cire gwamna da sarki. Sai ko ni ƴar balaja'un ku da saida Khulsoom ta zunguran amma na fuske naƙiyi, sai ma laɓe mata baki da nai na sake maida idanuna dake cikin glasses kansa ƙurr kai kace nice camara ɗin ma. Har inda aka tanada domin zamansa a tsakkiyar sarki da gwamna yaran nasa sukai masa rakkiya. Sai da ya zauna sannan suka koma ta bayansa suma duk suka zauna.
Isowar tasa ta saka taron fara motsawa yanda ya kamata. An fara da gabatar da addu'oi kafin gwamna yay bayani mai birgewa a matsayin uban taro, dan ya nuna jin daɗinsa da farin cikinsa matuƙa game da wannan cigaba da aka kawo jiharsa, yana kuma fata da kira ga wannan shugaban kamfani akan idan har yaranmu sun cancanta yana roƙon ace sun zama mafi rinjaye da zasu samu aikinyi a ciki, yana kuma fatan ALLAH yasa kamfanin ya zamewa Kano dama arewacin ƙasar alkairi baki ɗaya.
Kowa yaji daɗin bayanin gwamna. Dan zaka tabbatar da hakanne a fuskokin jama'ar dake a wajen ma. Sai sarki shima dai a matsayin uban taron. Sosai jawabansu suka ƙayatar suka kuma birge shima ɗin dai. Dan yayi kiranye sosai ga masu arziƙinmu da su shigo su kafa cibiyoyin kasuwancin a arewa domin matasanmu su samu aikinyi, hakan da zasu dingayi zai rage mana raɗaɗin rayuwa da ake ciki a wannan ƙarni. Zai kuma ƙarama matasan himma da nisantasu da ga shaye-shaye ko ɗaukar makamin da bai dace dasu ba a matsayin neman abincinsu ko zaman banza a bakin tituna mara amfani. Idan kuma har masu arziƙi suka cigaba da janye jikinsu da dukiyoyinsu da ga arewa to lallai watarana sai an wayi gari kowa ya zama abinda ba'a so. Idan kuma hakan da ba'a fata ta kasance ba arewan kaɗai ba, hatta su ma kudancin da wasu maƙwaftan ƙasashe zata shafesu, suma kuma ta nakasasu kamar yanda muma muke a nakashe yanzu. Bayan waɗan nan bayanan wasu masu muhimmanci ma sun sake biyo bayansu kafin shi ma ya miƙe........✍️


_(🤭Ni dai nace faɗi gaskiya dai Samraah bama son kwana-kwana😜 idan Yaya Maash ya miki ne sai ai miki hanya🥱, dan kunsan bana ni gaskiya ƴar team Yaya Maash ce. Mu dama muna gidan kuɗi babu kwana-kwana🤣👌. Saura naji wani yace kwaɗayi🙄dan ɗan uwanmu ne Ya Maash ɗin na jini🤯, ai gwajin jini kuma a gani🤥😌)._






_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_






.......(Kutumelacy). Na faɗa a zuciya lokacin da yay sallama da wata jarumar muryarsa cikin yanayin mazantaka da nuna kamewa tamkar wanda akama dole, dan hatta lips ɗin ma da ƙyar yake motsasu. Bayan an amsa ya cigaba da miƙa saƙon gaisuwa da sannu da zuwa nan ɗin ma dai a fiffisge alamar maganar ta zame masa dolene ko kuma gayune ko kuwa girman kai irin na masu hannu da maiƙon kaza oho masa. Ga wata hausarsa da ta gama gurɓacewa da harshen ƴan kudanci ko nace harsuna da yawa dan tamkar ba cikakken bahaushen da akace an haifa a gari irin Kano ba. A wata gaɓar ma hausar ƙwace masa take sai dai ya kwakuso turanci ko faransanci ya maka a wajen ya kuma fuske ya cigaba da jawabinsa. Kuga wani ɗigimi, da dai a turancin ya tsaya da yafi, to waye ya wani iya faransanci anan?. Koda yake ban sani ba tunda naga taron duk nasu ne na masu jiki duk chocolates. Haka dai ya haɗa jawabin mintuna uku da ƙyar yana faman mana haɗin gambizar yaruka uku a lokaci guda da kai hannu saman kai ya murza tabbacin dai maganar ta dole ce a garesa. Hummm duniya makaranta, yo ALLAH na tuba su mu kuma indai zance ne ai ko akkun farkon ƙarni ta sama mana lafiya, duk da dai nima sai naso nake nawa surutun. Amma dai na ƙara ilimi, tunda naga yayin ƴar jan ajin nan ake da fidda zance ɗaɗɗaya billa sake kame kaina zan dingayi tunda ban sani ba ko nan gaba nima na kuɗance. Yo Bily abin ai na ALLAH ne, bafa zaune nake kurum ba daga aikin jarida sai na gida. Ina ƴar sana'ar sai da hijjabai da takalma duk da jarin bai wuci na dubu ashirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login