Showing 69001 words to 72000 words out of 90697 words

Chapter 24 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull.txt

24 Nov 2024

3988

gari an sake kawo masa bayani akan ɗayan daya buƙata. Sai dai abin baƙin ciki shima layin na taƙaitaccen lokaci ne kamar wancan, ba kuma a taɓa kiran wani da shi ba. Nasara ɗaya da suka samu itace na shi wanda yay register ɗin layukan duk mutum ɗaya ne. Kuma a lokaci ɗaya yayisa. Sun saka a nemo musu shi a duk inda yake. Hakama abokin masu napep an samu nasarar cafkosa a safiyar yau. Bayan kamar awa biyu da kawosa police station ɗin aka kaisa office ɗin d.c.o kamar yanda ya buƙata. Sai da ya gama masa kallon tsaf daga sama har ƙasa kafin ya tura masa hoton Samraah dake gabansa.
“Kasan wannan?”.
Ya faɗa kansa tsaye idanunsa ƙyam akan saurayin. Hoton saurayin ya ɗauka ya kalla na kusan sakan talatin, ɗagowa yay ya kalla d.c.o sai kuma ya rissinar da kansa yana ɗan jinjina kai. “Nasanta ranka ya daɗe. Sam-G ake kiranta, tana gabatar da shirin matasa kuma ina ɗaya daga cikin fans nata da shirin baya wuceni ta redio ko shafukanta na sada zumunta musamman YouTube da ake ɗora shirin, nakan je na kalla videos ɗinta”.
Kai d.c.o ya jinjina masa da faɗin, “Masha ALLAH. Minene sana'ar ka?”.
“Direban napep ne yallaɓai”.
“Kozan iya sanin ranar goma ga watan nan kana ina? Da ga shida na safe har zuwa ƙarfe takwas?”.
Jimm yay irin na mai son tunano abu. Har kusan minti ɗaya sai kuma ya ɗago yana girgiza kansa. “Na manta yallaɓai. Saboda kwanakin sun ja da yawa”.
“Uhhm yayi ƙyau” d.c.o ya faɗa yana kallon yaronsa. “Azo da yaran nan su duka”.
Kai yaron nasa ya jinjina cikin girmamawa. Fita yay babu jimawa sai gashi ya dawo tare da samarin farko da aka fara kamawa. Yanda suke kallon saurayin haka yake kallonsu. Duk da babu duka ko zagi da akai musu zaman waje ɗaya da ɗan karan Dauda yasa duk sunyi wujiga-wujiga dasu....
“Kasan waɗan nan?”.
“Eh yallaɓai na sansu, su duka abokaina ne. Tare ma muke harkar napep ɗin ma.”
“Kace ka manta mi kayi ranar goma ga watan nan da safe ko?”.
“Eh yallaɓai a gafarceni”.
D.c.o baice dashi komai ba. Sai abokinsa ya kalla ya ce, “Kai tuna masa”.
Kai tsaye abokin nasa ya ce, “Kazo ɗakinmu ni da ƙanina bayan sallar asuba dan gari ma bai gama haske ba. Kace na baka makulin mashin ɗin Imran zakaje amso saƙo tasha kai taka tayar na gareji dan naka babur ɗin ya samu matsala tun jiya sai barinsa ma kayi ya kwana a gareji kan yau zaka kai musu tayoyi da zasu canja maka. A gaban ƙanina Isa akai komai kuma”.
Da sauri ya dafe kansa ya ce, “Tabbas anyi haka Salisu. Tabbas abinda ya faɗa gaskiyane yallaɓai, amma a gafarceni inada yawan mantuwa ne wlhy. Na amshi mashin ɗin, abinda nace kuma zanyi naje nayi da shi”.
“Masha ALLAH haka muke son ji ai dama. Ina ka kai yarinya to? Sannan waye ya sakaka kidnapping ɗinta? Ko raɗin kanka ne kawai?”.
“Ya salam kidnapping kuma? Ni banyi kidnapping kowaba ranka ya daɗe. Duk wanda ke tare dani kuma yasan wannan ba aikina bane ba inada sana'a. Taya ma kuma na rasa wanda zan ɗauka sai Sam-G”.
“Ƙarya kake yi, a waccan ranar ba gareji kaje da napep ɗin abokinka ba Yakasai kaje layin gidan su Samraah. Kai zaman jiranta na kusan mintuna talatin da huɗu. Zata iya yiwuwa kasan dama zata fito a lokacin ne. Dan haka tana fitowa da shirin tsaida abin hawa kazo ka ɗauketa. Ka tsaya a dai-dai fita anguwar ta titin bayansu gaba ɗaya. Ka cire wayarta da facemask da eyeglasses ɗinta ka ajiye saboda maybe kana tunanin za'a iya ganeka ko kuma wanda ya saka ka aikinne ya baka umarnin yin hakan. Ɗan saurayi ban kawoka nan dan ka raina min hankalina ba. Amma kana da zaɓi guda biyu. Fitomin da komai a yanda yake dan ka samu sassauci ko cigaba da raina min hankali na saka ka faɗa ta dole wanne ka zaɓa?”.
Ɗan jimm yay na wasu sakanni, sai kuma ya sauke numfashi da faɗin, “Zan faɗa maka gaskiya yallaɓai.......


🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟


Cikin fisgar zaren da suka ɗaure min ido naji sun warwaresa. Har sai da na ɗan ciza lips saboda yanda naji zafi, amma dai na dake ina mai buɗe idanun nawa a hankali, dan zan gama da ogansu ne sannan na dawo kansu shegu masu suffar bakaken aljanun kan kuka. Sosai gabana yay masifar faɗuwa dan kai tsaye idanuna akan mutumin dake zaune cikin kujera yay crossing ƙafafunsa idanunsa a tab.. dake a hannunsa suka sauka. Ga wani daddaɗan ƙamshinsa da ya cika min hanci da gauraye falon gaba ɗaya. Fuskarsa ciɗin-ciɗin kamar bai taɓa sanin abinda ake kira dariya ba ko saƙon wani bala'i ya riskesa a yanzu. yauma akwai kitso a kansa guda biyu rak da suka zanu tamkar an zana a takarda dan zaka rantse ba hannu ya kitsasu ba, sai farin sirrin gilashi da ya zauna masa ɗaram a fuska tamkar an haliccesa da shi ne. Yatsunsa biyu ya ɗan juya, da sauri sangama-sangaman samarin nan da suka rakoni da bindiga duk suka fice aka bar abokin cin mushen nasa kawai. Sai lokacin ya ɗago ya zuba min cat eyes ɗinsa. Kallon ido cikin ido mukaima juna. A take naji ciwon marata na neman dawowa sabo fil, ba shiri nai saurin duƙar da kaina ƙasa zuciyata na wani kalar masifaffen bugu kamar zata faso ƙirjina ta fita. Amma cikin ƙarfin hali na murguɗa masa baki bayan na saukar da idanun.
Shima janye nasa yay cikin yanayin isa da ƙasaita. “Sit!” ya faɗa a daƙile yana maida kansa ga tab ɗin tasa. Duk da na gane dani yake banyi abinda yace ɗin ba har sai da yaronsa ya sake maimaita min a ɗan tsawace. Ta ƙasan ido na hararesu su duka, kafin na kai zaune saman lallausar kujerar falon, amma sai yaron nasa ya daka min tsawa da mun nuni da wai na zauna ƙasa. (Munafuki ɗan baƙin ciki) na faɗa a raina, a zahiri kam hararsa na sake yi sannan nayi yanda yace na zauna ƙasan carpet ɗin da ko makaho ya laluba yasan ya haɗu. Jikina na ɗan takure a waje ɗaya, na tallafo ƙafafuna duka da hannayena biyu idanuna na kallon carpet ɗin. Sai da kusan mintuna uku suka sake shuɗewa babu alamar zai sake magana, sai kuma a cikin daƙilalliyar muryar nan tasa ya ce, “Wa kike ma aiki a kaina?”.
Sosai tambayar tai matuƙar bani mamaki, har takai na ɗago na ɗan kallesa. Amma a mamakina bama ni yake kalloba, wasu files ne a hannunsa yan rubutu a ciki ya ajiye tab ɗin yanzu. A hankali na maida kaina na duƙar, nima sai da na kwashe wasu sakanni kafin cikin siririyar muryata da yanayin gafara na bashi amsa, “Ni nafi ƙarfin yima kowa aiki ai, dan ni ma ɗin gayyace”. Shiru baice komai ba, dan haka na cigaba da ƙunƙuni ƙasa-ƙasa batare da tunanin zasu ji ni ba. (Ni ai nafi ƙarfin aiken wani, sai dai zuwan kai da kai. Dan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE ai. Idan kuma baka san haka ba kaje kayi bincike. Ashe ma matsoraci ne, tunda har baka iya fito na fito sai ta YAƘIN SUNƘURU...)
Harara yaron nasa ya zuba min. Kafin cikin kakkausar murya ya furta, “Hattara dai ƴammata. Dan ba'a ado da furuci wani lokacin takobin yanka wuyan mai shi yake zama. Nan ba gidan jarida bane, fadar SARKI ce mai cikakken iko kike.”
Murtanin harar nima na maida masa ƙasa-ƙasa. Sai dai na gagara iya cewa komai saboda yanda ogan nasa ya tsareni da shegun kaifafan idanunsa na maguna. Tsahon lokaci falon shiru, yayinda tuni ya janye idanun ya maida ga abinda yake yi. Sai zuwa can a wani irin daƙile ya furta, “A duk sanda wani ya nema shiga min hanci nakan ji farin ciki da mazantakar fyatosa. Shiyyasa abinda yafi birgeni a duniya sune mutane irinki masu taya business ɗin da bai shafesu ba. Well ba tabbatar miki da ni waye yasa nasa a kawoki nan ba, dan inada tarin ayyuka na kai da kai matuƙa. WAYE YA AIKO KI WAJENA?”.
Takaicin maganganunsa yasa bamma san sanda na furta, “Umarnin kaina nake bi ni, na kuma faɗa ai”.
A harzuƙe yaronsa ya katseni da faɗin, “Be careful ƴammata. Walƙiya ba tana nufin ado ne kawai ga sararin samaniya ba. Takan zama gargaɗi ga ma'abota shagala ne. Jirgin ƙasa duk ƙawatuwarsa a hanyarsa kawai yake iya tafiya, saɓanin hakan faɗuwar baƙar tasa zaiyi ta yanda ko kufansa bazai moru ba balle ma'abota shiga cikinsa. Ki dinga bambance tsakanin sama da ƙasa a duk lokacin da kikai tunanin hawa tsani da tunanin taɓa rana ko farin wata. Dan batun wanda zashi sama ya taka leda zance ne kawai irin na masu iya magana.”
Baki na laɓe tare da watsa masa harara ta ƙasan ido. Cigaba yay da faɗin, “Kina da zaɓi biyu, bada abinda ke hannunki ki koma ki cigaba da rayuwarki cikin salama, ki kuma sakama ranki baki taɓa ganin komai ba a wacan ranar, ko nuna taurin kai ki dawwama anan har ƙarshen numfashinki, kin buƙaci 500m an baki rabinsu, amma ke kin kasa cika naki alƙawarin duk da an tabbatar miki idan kin bada za'a baki sauran 250m ɗin. Ke kin san kuwa dawa kike tare ana?”.
Yanzu kam sosai na ɗago a razane matuƙa, tare da wurga masa hararesa dan naga yama fi ogan nasa zaƙewa. A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?........✍️






_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_




.......A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?. Aikin naku ya wuce kisan kai da kidnapping harda sharri kuma. Lallai tatsuniyar gizo da ƙoƙi kenan young man, kasan kuwa gaibu ce dan hikimace kawai irin ta masu iya zance da rubuta hikayoyi. Idan har ka yarda ba'a mutuwa a dawo, to ka ɗauka abinda duk yake a hannun Samraah Gwarzo mallakinta ne ita kaɗai, ko a mafarki bazan taɓa cinikayyarsa da wani ba. An gaya maka nima faƙiriyace bana neman na kaina ne da zan zauna neman a bani fansar kuɗin jinin mutane akan video?. ALLAH ya sawwaƙe, Banyi lalacewar baƙar tasa ba ai, banga kuma wata dukiya da wani zai tara taja hankalina ba dan nima dai kasuwancin nan inayinsa. Ɗan jarin nan na dubu ashirin da ake rainawa na tara wataran sune zasu koma miliyan dubu ashirin ɗin. Dan haka kuma nema wanda ya amsa kuɗinku tun wuri amma ba ɗiyar Abdul-wahab ba. Idan kuma kaine ke yawo da hankalinsa ka faɗa masa gaskiya inma dan kaga baya jin Hausa ne, oho can dai muku matsalarku ce ma wannan dai. Dannni idan har Yaya Musaddiq da Mansoor na numfashi a duniya na maka alwashin nan da kwana takwas iyanzu ina can a tsakkiyar dangina suna shagalin taron bikin aurena tare da ni, yayinda ku kuma zaku kasance a police station kuna amsa tambayoyi”.
“Yaro bai san wuta ba sai ga taka”. Yaron nasa ya faɗa
“Babba bai san yaro ba sai ya latsa”.
Na bashi amsa nima a kausashe ina sake balla masa harara kamar manyan idanuna da ke nuna yanayin bana jin daɗi zasu zubo ƙasa. Juyawa nai shima ogan nasa zan hararesa sai naga ya zuba min ido kamar wanda yay zurfi a tunani. Ban fasa hararar tasa ba, dan haka na maka masa kawai na ɗauke kai ina ƙunƙuni ƙasa-ƙasa (Garama ku sakan tunkan kuja a saka sunanku cikin jerin manyan ƴan ta'addan duniya dan wlhy tona muku asiri zanyi ni babu ruwana).
Tsawa yaron nasa ya daka min alamar ya jini, duk da na tsorata amma mai kicin-kicin da fuska naƙi nunawa. Kuma bakina bai bar motsin ƙunƙuni ba. Wani shegen murmushi ogan nasa da tun maganar farko da yayi bai sake nuna yama san da zaman mu a falon ba ya saki. Tare da lumshe idanunsa cike da salo luuuu ya kuma buɗesu a slowly warrr. Batare da ya sake furta komai ba ya miƙe abinsa ya nufi wata hanyar gilashi data mamaye kusan bango guda na falon har kana iya hango ƙyawawan korayen ciyayin dake ta waje da ga nan, fita yay abinsa cikin wani irin takun mazantaka da nuna ƙarfin iko.....
Wata ƴar siririyar dariyar da yaronsa ya saki ta sakani kallonsa. Ya rumtse hannunsa tare da nuna babban yatsar hannunsa kasa👎 yana wani ɗaure fuska ya furta, “Lallai na tayaki jaje ƴammata. Dan kin taro babban match da baki da defenders balle ƴan kallo. Tunda har kika bari boss ɗina ya taya wannan wasan sai kinyi dana sanin da sai tafi biliyan a cikin koguna biliyoyi. Dan shi giwa ne baya WAIWAYE. Sannan zaki ne ba'a gaba da gaba da shi. Ki jira TAKUN FARKO na wasan kawai, tun anan zaki raina kanki.”
Baki na laɓe nima, tare da watsa masa harara. Cike da tsiwar ƙarfin hali na ce, “Shi kaɗai ka sani da dukkan salonsa. Abinda kuma ni zan iya sirrina ne, kaga kenan tsakanin ni da shi ba'asan maci tuwo ba sai miya ta ƙare a wasan. Dan haka ina baka shawara tunda kaine abokin sharrin nasa. Ka gaya masa da gaggawa ya maidani inda kuka saka aka ɗakkoni, idan ba haka ba, wlhy sai kunyi dana sanin shiga sabgata. Dan zan ajiye muku tarihin da bazaku sake gwada cutar da wani ba bayan ni. Koda kuwa kasheni kukayi fatalwata bazata barku ku zauna lafiya ba. Dan nasan abinda kuka iya kenan kashe mutane kuyi tsafi da jininsu ko”.
Dariyar kularwa ya saki da faɗin, “Irinku dama boss yafi buƙata a wasa. Kema shaida ce tunda a gabanki ga faɗa da bakinsa. Tunda kin shirya game ɗin ga fili ga mai doki, ni dama nawa shawara ce. Kuzo ku maidata inda kuka ɗakkota”. Ya ƙare maganar ƙarshe cikin ɗaga murya. Baima gama rufe baki ba sai ga garadan ɗazun sun shigo kuwa..
(Tofa, Samraah miya faru kuma bayan hakan?).
Humm Bily komai ma ya faru, dan zan iya ce miki a wannan gaɓar ma ne labarin ya ɗauki dai-dai saitin inda kowa ya kamata ya fahimci raunin daya taɓani da kuma nasarorin dana samu. Dan komai da kika ji a baya dai-dai yake da sharar fage. Konace shimfiɗar labarin. Amma kundinsa wannan gaɓar itace SHAFIN FARKO. An maidani ɗakin da aka fiddoni kamar yanda yaronsa ya bada umarni. Da ga haka ban sake ganin kowannensu ba. Sai dai ana kawo min abinci sau uku a kowanne rana. Kamar yanda na kasance a kulle a wancan gidan nan ɗin ma hakanne. Sai dai akwai masu tsarona anan, kuma na nan sun ma fi nacan firgitarwa. A ƙuntace nake matuƙar ƙunci, ga ciwon jiki dana zuciya. Ga kewar ahalina data masoyi. A kowane cikar minti ɗaya na agogo sai na lissafa sauran daƙiƙun da suka rage na cikar ranar aurena. Hakan yasa a duk sanda tunani ya nema fasan zuciya zaki sameni ina karatun Alkur'ani ne. Ina jin sauƙi sosai a raina, bayan na koma yin salla ma Alhamdullah na sake rungumar ibada ta. Dan akoda yaushe cikin kaima UBANGIJINA kukana nake. Ina kuma jin yaƙinin zai karɓa min.. Zakisha mamaki idan nace dake maganar da yaronsa yay na cewar na buƙaci su bani 500m kuma sun bada 250 a cewarsu ban wani sakata a raina ba. Danni a nawa wautar kawai sun faɗane bisa raɗin kansu da son min barazana ne dan na basu abinda suke son, dan haka na cigaba da harkar gabana kawai na manta da duk wani gargaɗinsu balle zuciyata ta fara min wani hasashe mai muhimmanci daya kamata ace nayi, ban san rashin yin shine zai zame min babban kuskure ba kuwa. Dan da'ace nayin maybe da abubuwa basu kasance a wani matsayi daban taɓa tsarama kaina ba bisa ƙaddarar rayuwa. Karna cikaki da zance muje zuwa dai.....


💞☞💞☞💞☞💞



“Ranka ya daɗe zan faɗi gaskiyar abinda ma sani. Sai dai yanda ka fahimci al'amarin sam ba haka yake ba. Wlhy wlhy duk abinda zan faɗa maka shine gaskiyar abinda ya faru. Tsoro ya hanani faɗar gaskiya tun ma a farkon fara case ɗin. Amma na gwada yin hakan tun sanda naji zancen ɓatar Sam-G da kuma kama Salis da akai. Ni bani na saceta ba, hasalima ban san ita za'a ɗauka ba. Wanda kuma ya ɗauketan wlhy ban san kidnapping ɗinta zaiyi ba. Kamar yanda na sanar ma abokina Isa da gaske na amashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login