Showing 3001 words to 6000 words out of 90697 words

Chapter 2 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull.txt

24 Nov 2024

3993

da batunsa ba bayan Yaya Musaddiq. Koda yake su Baby sun sani, dan nasha jin ma wai ai Baby ta jima tana son shi, sai dai bansan minene ya faru koya katangeta da sanarwa a gida ina soyayya da wani ba, sannan ita bata taɓa tarata da batun Mansoor ba kai tsaye, sai dai tai habaici a wasu lokutan ko shaguɓe, ni kuma sai ban taɓa kulata ba ko nuna na fahimta. Ina zangon ƙarshe na kammala karatuna na fahimci ashe Yaya Musaddiq shike biyamin kuɗin makaranta babu wani scholarship dama. Ya haɗa baki da malamin namune kawai, dan a yanzu haka shima Hafizzullah yana a level 100 a jami'ar Umaru Musa ƴar-aduwa dake Katsina. Shima kuma dai da batun scholarship ɗin nan aka rufe bakunan su Uncle Imam duk da an kwashi tashin hankali sosai fiye da nawa lokacin kasancewar shi Nabil bai samu ya tafi ba har yanzu. Ranar da nasan wannan sirrin nasha kuka a gaban Yaya Musaddiq. Shiko ya dinga lallashina yana murmushi, a ranar ya sanar min da komai bai ɓoye min ba. Dan yace bazai taɓa iya zama bamuyi karatu ba, dan haka ya zaɓi bi ta wannan hanyar domin gina gobenmu. Shiko aikin kanikancinsa ya ishesa in sha ALLAHU. Na nuna masa ban yarda ba, shima dole ne musam yanda zamuyi ya koma karatu, dan kuwa zuwa yanzu yana samun kuɗi sosai, sai dai duk a hidimar gidanmu da karatunmu suke tafiya, dan har yanzu bai tsinanama kansa komai na rayuwa ba irin burin matasa na son gina gida da sauransu, hatta budurwa ma baida ita shi sam. Ya min alƙawarin idan lokacin komawar yayi zai koma in sha ALLAHU.
Alhmdllh na kammala karatu cikin nasara, yayinda na riga Abbas da Baby da suka rigani farawa kammalawa saboda su sun saka wasa a karatun nasu. Bakuma su da niyyar gama school ɗin da alama, maybe sai an korosu su shiga hankalinsu oho, dan gasu nan koda yaushe cikin maimaita shekara suke. Bayan kammala karatuna da wasu watanni Mansoor yay uwa yay maɗaukiya ya sama min aiki a wani gidan tv da rediyo dake tashe a wannan lokacin. Hakan ya saka Yaya Musaddiq farin ciki, yayinda ran su Abba yay baƙi har suka kasa ɓoye hassadarsu a fili musamman ma Mom, dan da farko ma tuburewa tai akan tunda na gama karatu aure kawai ya kamata Abba yay min, wai akwai wani ɗan yayarta ya jima da cewa yana so na. Abba har ya ɗauki zancenta da muhimmanci niko na tibire nace wlhy idan aka aura min shi kashesa zanyi, dan ni ban shirya aure ba sai na fara aiki na. Ganin fa da gaske nake kuma sun san tsurin idona dan randa yaron yazo hira wajena zagin ƙare dangi na masa, hakan yasa Abba ya kashe maganar, sai dai ban san yaya sukai da matar tashi ba a ɓoye, a zahiri dai yace ya kashe wannan batu naje nai aiki na. Amma ya bani nan da ƙarshen shekarar nan na kawo miji. Oho ban wani damu dasu ba na fara aiki na, dan nasan dai inada Mansoor ɗina a hannu. Cikin nasara kafin kace mi na samu karɓuwa, albashina na farko dana biyu dana uku na haɗa da shi na sayama Yaya Musaddiq fili da taimakon Mansoor. Lokacin dana damƙa masa takardun sai kawai ya fashe da kuka. Nima kukan na fashe da shi tare riƙe hannunsa ina roƙonsa dan ALLAH ya daina, shifa uba ne a garemu yanzu, idan bamu masa hidima da abinda ALLAH ya azurtamu da shi ba wa zamuyimawa. Da ƙyar dai mukai shiru dan dama a wajen aikinsa na samesa, gudun kada na bashi a gida wani yaji a ƙwace. Tom Alhmdllh, yanzu dai a taƙaice watanni na shida kenan da fara aiki na, ina kuma matuƙar jin daɗin da nuna kwazo matuƙa. Dan bada ƙwaƙwalwa kawai nake aikin nan ba, harda zuciyata da ƙwanjina gaba ɗaya. Gashi ALLAH ya bani farin jinin mutane, dan tunda na fara gabatar da wani shiri akan matasa shikenan kamar nayi kiranyen masoya, dan da a iya rediyo ne kawai, amma wata guda kenan da fara gabatar da shi a television saboda yanda oganmu yaga shirin ya amsu yana sake jawo hankalin mutane ga channel ɗin tamu sai abin yay matuƙar birgesa. Dan haka aka sake ƙarfafa shirin ta hanyar fiddoshi a fanninmu na television ma, Alhmdllh kuma komai na tafiya fiye ma da yanda akai zato da tsammaninsa.......✍️








_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒐𝒖𝒓_






......A gurguje nake faman shiryawa saboda makarar da naso nayi. Ba kuma komai ya jawo min hakan ba sai sharaɗin girka breakfast ga masu gidan a kullum kafin na fita bisa umarnin Mom bayan gyara ko ina. Ban isa nace bazanyi ba, dan na fahimci hanyar da zata tuzguɗe ɗan aikin nawa take nema. Dan haka na tsarama kaina time table ta yanda bazan cutu ba. Kullum ƙarfe huɗu na asuba na tashi, zan shiga kitchen na ɗaura breakfast. Inayi ina ɗan wasu aikin gyara gidan har na kammala, dana gama na maida hankali ga sauran ayyukan, ALLAH na taimakona kafin ai kiran sallar farko zaka samu na kammala komai, da Yaya Musaddiq ya fahimta ma sai ya zam shima yana tasowa muyi tare dandanan saina kammala nai shiri. To yau an samu akasi ne da alama Yaya ya makara, dan har na kammala bai shigoba, gashi ma har na gama shirina. Nayi ƙyau sosai cikin baƙar abayar dana saka, nai rolling veil ɗin ta da ya sake fiddoni tsamm kamar wata ɗiyar larabawa. A ɓangaren ƙyawun fuska dana jiki babu abinda zance sai Alhmdllh, sai dai ban taɓa jin alfahari ko son yin ɗagawa da wannan baiwar da ALLAH yay min ba. Nakan gode masa ta hanyar suturta kaina da ƙyaƙyƙyawar shiga, dan kullum cikin dogon hijjabi nake da nose mask. Dan ƙaryane kace ka ganni babu nose mask a fuska. A lokacin dazan fara gabatar da shirin nan a sashen tv ansha gumurzu dani a ranar farko dan har hawaye saida nayi saboda ciresa, dole dai na haƙura daga ƙarshe ma toshe idona da eyeglasses sannan na iya gabatar da shirin, a hakanma ina jin kaina kamar ba daidai ba.
Kamar kullum mask ɗina na saka, sai dai yau baƙi ne, yay min ƙyau sosai dan ƙyawawan fararen idanuna masu girma da cikar gashi kawai ake iya gani. Cikin takun nutsuwata na fito, ga wani ƙamshi mai sanyi yana tashi a jikina, sai dai bamai ƙarfi bane, dan sai ka kasance a kusa dani sosai zaka iya jinsa yanda ya kamata. Sauri nake, dan haka bana fatan haɗuwa da kowa na gidan. Sai da na leƙo na tabbatar babu kowa a falon sannan na ƙarasa fitowa. Nan ma da sanɗa na fita, inayi ina waigen bayana. Ban sami nutsuwa ba saida na ganni a waje, na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina sakin murmushi, bag ɗita mai zubin school bag na rataya hannunta guda a bayana, ɗakin yaya na fara leƙawa, sai muka kusa cin karo dan shima yana niyyar fitowa ne.
“Kandala ƴar jaridan Yayanta”.
Ya faɗa cikin tsokana yana mun murmushi. Murmushin nima na mayar masa ina ɗan rufe fuskata da tafin hannuna. Sai kuma na janye ina ɗan ɓata fuska da faɗin, “Ai ni fushi ma nake da kai yaya. Na manta nai maka murmushi ma.”
Cikin dariya ya ce, “Oh oh Tom ayi haƙuri Ƴar ficika, nasan laifin Yaya dai rashin shigowa taya aiki, wlhy jiya na matuƙar gajiya ne a gareji, shiyyasa tunda na samu na kwanta ko juyi banyi ba sai kawai naji ana sallame salla. Dan yau ma sai a ɗaki nayi tawa dan abin kunya”.
Dariya na ƙyalƙyale da ita sosai saboda yanda yay da fuska kamar wani ɗan yaro. Sai kuma na kalla agogo da sake kallonsa. A zabure na ce, “Uhm Yaya zan makara. Ni dai taho muje ka saukeni, dan yau a mashin ɗinka zanje office, ina son na baka wani labari a hanya”.
Babu musu yace min muje, saboda karna makara bai shiga gidan ya gaidasu kamar yanda ya saba ba. Ya kuma san sai yasha masifa akan haka ɗin, amma yafi buƙatar farin cikina. Cike da farin ciki muka bar ƙofar gidan tamkar bamu da wata damuwar rayuwa. Maganar da nace masa zamuyi na fara masa. Ba komai bane face batun fara gininsa, dan ina son a fara ya samu yay aure. Bai dai ce dani komai ba face murmushi kawai har muka isa, a ƙofar gate ya ajiyeni. Har lokacin fuskarsa da murmushi ya kalleni. Sai kuma ya ɗan ja fasali da harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallona.
“Samraah!”.
Ya kirayi sunana da tsantsar kulawa. Amsa masa nai nima da girmamawa. Numfashi ya sake furzarwa da ɗan duƙar da kansa ƙasa kamar mai nazari, sai kuma ya ɗago yana sake kallona. “Samraah inaga ba batun gini ya kamata muyi ba yanzu. Kamata yay ace mu tattali abinda muke samu domin kayan aurenki. Kin girma Samraah, kin kammala karatunki cikin aminci, ga aiki kin samu cikin sauƙi, kina da Mansoor a hannu, a ganina batun aure ya kamata ace kunyi da shi yanzu kafin ma lokacin da Abba ya baki ya cika. Kin san dai halin Mom basai na faɗa miki ba, wannan shirun da kikaga tayi wlhy bazai zama na alkairi ba. Gara mu fiskanci zahiri. Wannan ƙaramin jikin naki yabar kwasarki ba baya kike komawa ba shekaru ne ke ƙaruwa. mutanen wajene kawai suke miki kallon ƴar ƙarama ganinki ƴar ficit. Ni nawa batun mai sauƙi ne, namiji ne ni, konan da shakara goma bazan tsufa da aure ba ai. Ga Hafizzullah yanzu ya fara karatunsa, kamata yay har sai shima ya kammala koda zan yi batun wani aure, sai nake ganin kamar hakan zai fi, ni dama ba wata budurwa ba a ƙasa”. Ya ƙare maganar da zolaya.
Baki na kumbura cikin ƴar shagwaɓa nace, “Yaya ni duk ban amshi wannan ƙorafin naka ba sam. Kadai bari mu samu lokaci mu zauna mu tattauna. Amma batun bazakai aure ba sai nayi ko Hafiz ya kammala makaranta duk baima taso ba. In dai Dan budurwar ce zan maka, amma bazan bari ka cigaba dama waɗan can mutanen bauta ba. Kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Wannan lokacin ya wuce muma yanzu munsan kammu”.
Kansa kawai ya girgiza, nasan kuma ba komai ya sakashi yin hakan ba sai ganin yanda na ƙarasa maganar a hasale. A bayyane fushina da zafin mariƙanmu ya gama bayyana. Maimakon yace wani wani sai kawai yaymin nuni da gate alamar naje ciki. Banyi musu ba nai masa sallama na nufi shiga ciki ina kumbura baki da fiki-fiki da idanu najin haushi........✍️






_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒊𝒗𝒆_




........Ina zama office ɗinmu daya kasance mu biyar ne a ciki Asiya data kasance duk tare muke anan ta shigo da sallama. Ganin takardu a hannunta ya tabbatar min da ba yanzu ne ta shigo ba. Gaisawa mukai farko, kafin ta ɗora da faɗin, “Samraah MD na kiranki kuwa. Ya ce ki maza kuma dan zaiyi baƙi”.
Kaina na jinjina mata batare da nayi magana ba na miƙe ina sake gyara zaman facemask ɗina daya ɗan zamo ta saman hanci. A cikin takuna na nutsuwa da yanga da mutane da yawa ke fassarawa na fito. Duk wanda na gamu da shi nakan ɗaga masa hannu da cewa good morning, wasu sukan ɗan tsokaneni. Sai dai iyakata murmushi kawai dan nifa idan ba kayi dogon zama dani ba bazaka taɓa tunanin inada surutu ba sam. Ban cika yawan magana a ko ina ba sai in nice naga damar hakan. Shiyyasa da yawan mutane ke ɗaukata mai shiru-shiru. Har wasu kan dangantani da hakan da iya yardarsu. Basu sani ba idan aka taɓoni banda ragi banda ragowa sam. Na isa office ɗin MD, bayan nayi knocking sai da nai tsaiwar kusan minti ɗaya kafin ya bani izinin shiga ciki. Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina, dan mutum ne shi mai shegen son kallon mutane kamar zai cinyesu. Cikin son kawar da idanunsa dake yawo a kaina ya ce, “Zauna”.
Zaman nayi a ɗarare nace da shi, “Good morning sir”.
A taƙaice ya amsani da, “How are you?”. Batare da ya jira amsawata ba ya cigaba da maganarsa yana turomin wata ƙyaƙyƙyawar mujalla da wani envelope mai kama da invetion card. Bana ganin fuskar mutumin daya mamaye bangon farko na mujallar gaba ɗaya. Sai jikinsa dake sanye cikin wasu shegun suit sky blue zuwa ƙafarsa dake cikin cover shoes dake wani shining duk da kuwa a hoto ne. Zaune yake a kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya, hakan ya bani ɗan damar ganin hannunsa mai ɗauke da dogayen fararen farata dake riƙe da glass cup da guntun drink ke ciki. Sai zobe guda ɗaya mai ƙyau sosai a yatsarsa...
Duk da baifi a sakanni goma na ƙarema hoton irin wannan kallon ba a ɗan kamar fusace naji gyaran muryar MD a kaina. Saurin gyara yanayina nayi na maida hankalina gareshi, fuskarsa a ɗan ɗaure yana famar yamutsa fuska ya ce, “Ɗauka ki duba”. Ɗaukar nayi, sai dai ban kallaba yanzu na maida hankali garesa da nuna alamar shi nake saurare. Shima sai naga ya ɗan sassauta yanayinsa. Ya nuna ni da faɗin, “Samraah na zaɓoki ne saboda nasan zaki iya. Wannan mujalla ce ta TAURARINMU A YAU data fita jiya. A gaba ɗaya abinda ke cikinta ya ta'allaka ne akan matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ke amsa kuwa a ƙasashenmu na Africa dama duniya a ɗan tsakanin nan. Wato *_AWWAB EL-MU'AZZ._* sai dai kowa yafi saninsa da *_MAASH_* ne. Maash ɗan arewa ne haifaffen garin Kano sai dai mazaunin jihar Lagos. Yana da tarin cibiyoyin kasuwanci a kudancin ƙasar nan dama wasu ƙasashen Africa. Hakama a ƙasashen turawan da larabawa yana da rassan kasuwanci. Amma abin mamaki bai taɓa kafa wani abunsa a arewacin nan namu ba. Hakan yasa mutanenmu sukai masa ca, suke kuma sukarsa akan hakan, har takai suna ƙalubalantar dukiyar tasa musamman idan akai dubi da ƙarancin shekarunsa. Duk da kuwa an san mahaifinsa nada kuɗi, hakama Kakansa sanannen mutum ne, sai dai ko kwatar abinda shi MAASH ɗin ke da a yanzu mahaifinsa bai mallaka ba. Kace nace ya sake yawaita a kansa ne a watanni uku da suka gabata, dalilin bayyanar Companyn sa na jirage dake jigilar mutane daga Nigeria zuwa ƙasashen ƙetare. Domin a farko jirage goma ne ciff suka fara aiki. Sosai manyan gidajen jaridu sun so tattaunawa da shi amma Maash yaƙi bada kowacce irin dama. A duk lokacin da hakan ta taso sai dai a tattauna da P.A ɗinsa. To nadai taƙaice miki zance a yanzu haka bayan ka-ce-na-ce da aka sha yimasa akan gudun arewa da ƙaruwa Mujallar nan ta fitar da bayanan buɗe ɓoyayyen katafaren company da kusan wata uku kenan ana aikinsa batare da mutane sun san na wanene ba a cikin Kanon nan. Company ne na ƙera motoci da babura da abubuwa masu yawa da suka shafi ababen hawa. Irinsa shine na farko a Africa, a duniya kuma na uku. Kuma Maash da kansa zai zo Kano bikin buɗesa. Hakan yasa tunda naga mujallar nan na shiga na fita sai da na samo mana invetion card ɗin shiga wajen, dan hatta ƴan jaridar da zasu halarci wajen a ƙa'ide suke. Dan haka na kwana nazari a daren jiya, na kuma hanga na hango a kaf gidan nan kece nake ganin zaki iya mana wannan aikin, fatanmu kiyi duk yanda zakiyi kisa Maash ya magantu a gaban ƴan jarida karo na farko dan ALLAH. Hakan zai zama ba ƙaramar nasara ba a garemu da ma wannan gidan namu baki ɗaya. Sannan ke a karan kamki ma wata sabuwar ɗaukakace da nike da tabbacin zata zamewa rayuwarki alkairi in ALLAH ya yarda.”
Wani irin nauyi naji kaina yamun, dan haka da ƙyar na iya fisgo kalma ɗaya akan harshena na furta. “Amma Sir kaifa kace bai taɓa yarda yayi hira da ƴan jarida ba. Taya kake tunanin ni zan iya samo wannan nasarar? Yaushe ma na fara aiki, wane matsayi na taka a cikinsa? Ni wacece da zanyi abinda manyan ƴan jarida gogaggu suka gagara yi cikin sauƙi haka?”.
“Ba cikin sauƙi bane Samraah. Sannan al'amarin ba iyawa bace ko kaiwa wani matsayi. Sa'a ce kawai kuma kowa da irin tasa a rayuwa. Nima ba ina ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login