Showing 48001 words to 51000 words out of 90697 words
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_
........Tunda suka fito Hayatu ya zuba masa ido ta cikin mirror ɗin gaban motar, dan shi yana zaune ne a kusa da Tijjani driver. A hankali kamar mai ɗan jin shakka ya ce, “Sir ko zamu koma gida ne ka huta?”.
Shiru kamar bazai tanka ba. Sai da ya mula dan kansa batare da ya buɗe idanunsa dake a rufe ba, ko gyara zaman ƙasaitar da yay ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Ba buƙata”. Ya faɗa a taƙaice. Kai kawai Hayatu ya jinjina yana mai haɗiye yawu. Kai tsaye Company suka nufa. Dan akwai zaman meeting da zasuyi sakamakon fara ɗaukar ma'aikata da za'ayi a gobe in sha ALLAHU. Sun samu duk wanda ake buƙatar gani a zaman meeting ɗin yazo. Tunda aka buɗe masa mota kuma ya fita kowa keta ƙoƙarin gaida shi cikin girmamawa. Hannu kawai yake ɗaga musu da bin yanayin wajen da kallo ƙasa-ƙasa. Hatta da turawa da Chaines ɗin da zasu jagoranci aiki a companyn girmamashi sukeyi. Kai tsaye hall ɗin da meeting ɗin zai gunada suka nufa.
Wajene da akai matuƙar tsarawa da ƙawatawa. Sai da ya zauna a babbar kujerar dake tsakiyar dogon tables ɗin sannan suma kowa ya zauna. Ya ƙare musu kallo ƙasa-ƙasa ta cikin gilashinsa ɗaya bayan ɗaya kafin suka fara gudanar da abinda ya tarasu..
★ A matuƙar gajiye liƙis suka bar Company bayan sallar la'asar. Koda suka isa gida sun samu baƙonsa Abubakar yazo. Saboda yanda yake jinsa a takure bai iya ganawa da shi ba ma ya shige bedroom. Wanka ya farayi sannan ya ɗan kwanta. Tabbacin ya gaji sosai cikin ƙanƙanin lokaci barci mai nauyi yay awon gaba da shi kuwa. Bai fito ba sai lokacin sallar magrib, sai da kuma akai isha'i ya dawo gidan. A sannan ne yay ɗan zaman awa guda da Abubakar da Hayatu. Suna kammalawa ya bama Hayatu umarnin su shirya jirgin sha biyu na daren yau ɗin nan zasu bi zuwa Lagos. Hakan ba sabon abu bane a gare su. Dan shi duk sanda abu ya kaɗa masa yinsa kawai yake yi, ko dan jirgin nasa ne na kansa yake hakan oho masa . Tunda ma har aka tsaida time ɗin tafiyar yasan Juliet ita ta sani, amma duk da haka bayan ya sanar da guards da Tijjani su shirya sai ya nufi sashen da take.
Hayatu na gab da shiga falon wayarsa tai tsuwwa alamar shigowar saƙo. Baibi takanta ba ya ƙarasa. A falo ya samu Juliet ɗin tana waya. Ganinsa yasa ta katse sukai maganar da zasuyi ya fito. Shima nasa masaukin ya nufa domin kimtsawa. Duk da dai akwai ɗan sauran lokaci ma. Daga aljihu ya cire wayarsa da nufin ajiyewa sai kuma ya fasa saboda tuna shigowar saƙon ɗazun.
“What!” ya faɗa da ƙarfi, sai kuma ya miƙe da saurinsa cikin sassarfa ya fice. Kai tsaye sashen ogan nasu ya koma. Sallama ɗaya yay batare da jiran izini ba ya afka ciki. Dai-dai nan kuma Maash ke fitowa da ga bedroom ɗinsa kunnen sa manne da bluetooth alamar waya yake yi, yanda ya tsuke fuska matuƙa zai tabbatar maka koma da waye yake yinta bada daɗin rai bane. Kallo ɗaya yay ma Hayatu daya shigo kamar an korosa ya ɗauke idonsa. Cikin kujera ya kai yana wani kalar cije lips ɗinsa. Sai kuma kamar a fusace ya furta, “Nifa ba fushi nake ba Paa. Maganar yarinyar nan kuma nace a barta bana so. Ni ban taɓa cewa ai ina ra'ayin zama da ita ba, kuma ban taɓa cemata ina sonta ba”.
Ɗan shiru yay alamar yana saurare, sai kuma ya sake ɓata fuska a yanayin shagwaɓa ya sake cewa, “Paa Please mana. Understand me.”
Sai kuma ya sake yin shiru. Kusan minti ɗaya ya ce, “Okay naji, amma ni daga nan zan wuce Finland ne, bazan dawo ta Lagos ba. Kwana shida zanyi kawai in sha ALLAH”.
Guntun murmushi ya saki kaɗan, sai kuma a hankali ya ce, “I love you too. Bye ka gaida Ummie da Mamma.” daga haka ya cire bluetooth ɗin yana maida hankalinsa kan Hayatu. Hayatu da dama kamar a ɗofane yake a saman wuta yay wata zabura zuwa gabansa. Cikin rawar hannu ya miƙa masa wayar yana faɗin, “Sir yarinyar nan ce fa ta sake turo saƙo ta number na. Ban san taya ta samu ba, ko yau da mukaje office ɗinsu ne?”.
Komai baice ba ya amshi wayar. Kasancewar da turanci aka rubata text message ɗin yasa ya fahimci komai. Ya jima bai motsa ba ya ƙurama wayar kawai cat eyes ɗin shi, sai dai fuskarsa ta sake komawa wani bala'in kicin-kicin har blue ɗin cikin idanunsa na ƙoƙarin ɓacewa. Hayatu ne ya katse shirun da faɗin, “Wlhy Sir al'amarin yarinyar nan mamaki yake bani, na jima banga mace mai busashiyar zuciya irinta ba. Just small girl ɗin nan wai tasan yin irin wannan ta'addacin haka. Jiba yau yanda take wani basarwa da shan ƙamshi fa. Ni wlhy dan kawai kace a barta ne ai. Amma har ita wacece da bazamu sa a tattaro mana kaf zuri'ar gidansu ba taga ƙaryar tsagerancin nata. Haba ita wacece da zata zauna tana rainama mutane hankali. Kawai na kira Sani a daren nan ya kawo mana ita gidan nan a amshi wayar tata a gabanta mu goge video ɗin sannan mu danƙata hannun hukuma, muda muke da makami ma a kanta, dan biyowa ta bayan gida fa tai akan hira dakai har yanzu ba'a daina cecekuce a kansa ba a media, wani abun ma nasan sai randa aka saki hirar, tabbacin mutane da yawa na asiri tazo da shi wajen har ka yarda ka amsa matan zai sake gitowa”.
Shi gaba ɗaya ma surutun Hayatun saka masa ciwon kai yake. Dan haka ya wurga masa wani kallon da ya sakashi nutsuwa, tare da jan bakinsa ya tsuke. Shiru falon ya sake ɗauka kowa na cuɗawa da kwancewa a cikinsu. Kafin shi ya miƙama Hayatu wayar yana faɗin, “Ba buƙatar mata komai a yanzu. Ina son ganin iya gudun ruwanta. Ka amsa mata da za'a bata 500m ɗin, amma a ina za'a haɗu da ita ta bada recording ɗin”.
“Amma Sir.....”
Hannu ya ɗaga masa, a daƙile ya ce, “Na gama magana”.
Yawu mai ɗaci Hayatu ya haɗiye. Sai kuma ya jinjina kansa cikin girmamawa ya ce, “Okay Sir, in sha ALLAH za'ayi yanda kace. Na barka lafiya”. Daga haka ya juya ya fice. Ta gefen ido Marsh ya bisa da kallo. Sai kuma yay wani kalar furzar da iska yana maida kansa a kujera ya kwantare tare da lumshe idanunsa a hankali. Shi kaɗai yasan mi yake ji a ransa game da yarinyar nan. Ya fahimci lallai bata fahimci a ramin da take neman jefa ƙafarta ba. Amma zai bata lokaci ta gama nata kalar ƙaramin wasan kafin ya fara buga babban game da sai tayi dana sanin saninsa a rayuwarta a kanta. Idan ita ƙaramar ƴar iskar layi ce, zai tabbatar mata shi na duniya ne baki ɗaya, dan ba neman kuɗi kawai ya iya ba harda cin uban duk wanda ya shiga sabgarsa. Ko abubuwan data dinga yi yau duk a rubuce suke a brain ɗin, ya fahimci tanada taurin kai da tsageranci. Duk zai sauke mata su kuwa nan bada jimawa ba.
Ya jima a wajen zaune har Hayatu ya dawo ɗauke da abincin da Sani yayo order. Amma sai yace bazai ci ba. Ya haɗa masa coffee kawai. Umarninsa Hayatu yabi. Ya kawo masa coffee amma ya haɗo da biscuits mai daɗi. Dan yasan waɗan nan sune kalar ciye-ciyen da ogan nasu yafi so a rayuwarsa. Shiyyasa a duk inda yake baka rabashi da kalolin biscuits da chocolates kala-kala masu shegen daɗi. Sabone tun na ƙuruciya ya riga ya kamashi. Sake fita Hayatun yay ya barsa, shi kuma ya maida hankalinsa ga tv yana kallon film ɗin da sukeyi yana shan coffee ɗinsa da biscuit ɗin kamar baya so. Koda ya kammala zamansa ya cigaba dayi har sai da film ɗin ya ƙare sannan ya shige ciki. Maimakon kwanciya bathroom ya faɗa, ya haɗa ruwa mai ɗumi cikin bathtub tare da haɗa kayan ƙamshi kala-kala a ruwan sannan ya shiga ciki. Sai da yay minti talatin cur ruwan na ratsashi da miƙar masa da kowace gaɓa sannan ya fito ya shiga wajen wanka ya ɗauraye jikinsa. Bayan ya fito salla ya fara gabatarwa tare da shafa'i da wutiri sannan ya shiga shiri. Yayi ƙyau sosai cikin shigar tasa tamkar ka sacesa ka gudu. Ga wani uban ƙamshi na tashi uwa kamfanin haɗa turare kamar ba dare ba. Sumar nan tasha gyara daka gansa kasan ya haɗa jini da masu jajayen kunne. Hakama kwantaccen gashin sajensa sai walƙiya yake gashi kwance luf-luf ya sake fidda taswurar doguwar fuskarsa. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata sannan ya fito cikin nutsuwarsa da takunsa na tsayayyen namiji. Baiyi mamakin ganin Hayatu a falon ba. Dan duk inda aka gansa dolene aga Hayatun. Duk da yana jin idonsa a kansa bai kallesa ba. Hakan yasa Hayatu ɗauke idonsa shima a ransa yana kirari wa UBANGIJI mahaliccin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta, gaskiya dole ma aso mai ƙyau, dan ko shi dake a namiji, kuma ana yawan sanar masa shima ɗin ƙyaƙyƙyawane har ga ALLAH ogansa na birgesa. Dan mutum ne daya san hakkin tsara ado. Ya iya tsara saka sutura ta zauna ɗam ya haskata kuma tamkar dan shi kaɗai ake saƙa kaya irinsu. Ganin zai ɗago da sauri ya wuce sumu-sumu zuwa bedroom dan ya kashe komai ya gyara kuma abinda ya ɓata tunda basu san ranar dawowarsu Kano ɗin ba kuma. Suda suke kullum a tafiye-tafiye kamar ƴan sama jannati.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_
.......Kamar ko yaushe yau ma Mansoor ne ya maida ni gida, koda na shiga na samu gidan tsitt. Banbi takan kowaba na shige ɗaki, auta na samu yana barci, ga books ɗinsa a gefensa barbaje alamar homework yake barcin ya kwashesa. Ɗagashi nai na maida kan katifa. Sannan na tattare books ɗin na ajiye masa gefe bayan na duba abinda yake. Yaron akwai brain, inba ni ba babu mai zama damuwar koya masa homework, sai idan Abba. Wani lokacin ma sai kika yayi da kansa kafin ma na dawo, sai dai na ɗan masa gyararraki kawai. Wanka nai ƙoƙarin shiga, sai dai bayin duk an ɓata shi, nasan Bibaa ce zatai wannan aikin ba wani ba. Na rasa mike damun kan yarinyar nan, amma zan koya mata hankali. Tanada ɗakinta ita kaɗai amma tsabar shaiɗanci tace tsoro take ji a can, shine Abba yace ta dawo nan mu zauna wai sai ta ƙara girma. Da farko na ɗauka haka ɗinne, sai daga baya na fahimci Mom ce ta sakata yin hakan dan ta dinga ɗaukar rahoton duk motsina tana kai musu. Tun wani lokaci da naji tana faɗama Mom wayar da mukai da Mansoor nagane hakan. Bayin na sake gyarawa sannan nai wankan. Harna fito na gyara jikina banji motsin kowa ba. Ba'a wani ɓata falonba yau sosai, dan haka na wuce kitchen. Shi kam yana nan jibge da kayan wanke-wanke tun daga kofunan kalacin safe har na rana da sukaci. Kaina na girgiza ina mai jin tausayin Bibaa da Baby a rayuwa. Dan ita Mom gani take gata take musu bata san kashe musu rayuwar take ba, haka kullum da rayuwar take a gidan, idan nai aikin safe na fita babu abinda suke kaudawa har sai na dawo na sake yi, badan nima na zama jan wuya ba abincin rana ma sai na musu na saka a kula. Sai da na nuna musu nima tsagerar kaina ce sannan, shiyyasa kullum basu da abincin rana a gidan sai taliya ko cus-cus ko macaroni, indomie. Sai idan akwai stew ne zakiga sun dafa farar shinkafa. Stew ɗin kuma zakiga dole nice zanyita, Mom taƙi yarda a ajiye mai aiki wai ita kishi, randa nayi aure to naga ubanda zai zo ya musu. Kwanikan na fara tattarewa na wanke, ƙafafuna duk sunyi tsami saboda tsaiwa. Haka dai na daure na kammala na maida komai muhalinsa sannan shima kitchen ɗin na shiga gyaransa. Ƙaramar indomie na dafa guda biyu, na raba biyu naci tawa anan na juyema auta tasa a plate. Har lokacin babu wanda ya dawo, mamaki ya sake kamani da tunanin ina sukaje haka ne?.
Har akai sallar magrib sai mu kaɗai a gidan. Sai bayan an idar Abba ya shigo. Fita mukai ni da auta daya tashi muka gaishesa. Na wuce na kawo masa ruwa na koma ɗaki abina na barsu anan falo. Sun fita sallar isha'i nima zan kabbara tawa naji hayaniyar shigowar su Mom. Banbi takansu ba na tada sallata. Sai da nai har shafa'i da wutiri sannan na fito musu sannu da dawowa. Kaya na tarar barbaje a falon kashi-kashi. Na sakawa dana kwalliya harda na ciye-ciye alamar dai daga kasuwa suke. Ganin hankalinsu baya kaina dan ko gaisuwar ma da kai Mom ta amsa min na juya na koma abina ina mamaki, dan tabbas da kuɗin Yaya na jiya akai wannan sayayyar kenan. Jinai raina ya ɓaci matuƙa, dan haka na fito na wucesu. Yanzun ma hankalinsu babu alamar yana kaina. Ta ihun murnar kayansu suke kawai. Ɗakin Yaya Musaddiq na nufa, yana tsaye da alama yanzu ne yake dawowa massalaci. Ganina rai ɓace ya sashi faɗin, “Jikin ne?”. Kaina na girgiza masa ina kaiwa zaune. Cikin zafin rai na ce, “Wlhy Yaya zancen kuɗin sarƙar nan shirine kawai. Ko kasan matar can yau kasuwa suka shiga ita da ƴaƴan nata gasu can sun baje kaya a falo kamar za'a buɗe kanti. Kasan kuma babu yanda za'ai hakan ta faru Mom ta iya kashe kuɗin sarƙar nan a banza haka da gaskiya ne”.
Murmushi mai sanyi Yaya Musaddiq yay hana kaiwa zaune kusa dani. Cikin sauƙaƙa murya tare da riƙo hannuna cikin nashi ya furta, “Cool down sweetheart. Sune a ƙasa ai. Bakiji shata na faɗin ku gargaɗi mai gina ramin mugunta ba. Ni nasan dama koda an ɗauki sarƙar ma bata kai ta kuɗin data faɗa ɗin ba. Amma ba komai ALLAH zai bamu wasu. Yanzu ma Abba ya bar ɗakin nan”.
“Miya faru ya shigo?”.
Na faɗa cikin mamaki tunda nasan dole akwai dalili. Hannuna ya saki yana miƙewa da ɗan taɓe bakinsa. Ya zare jallabiyarsa ya ajiye sannan ya koma ya zauna dan jikinsa akwai dogon wando da t-shirt fara. “Yazo ya sameni akan wai tunda yaga inada kuɗi ni ne ya kamata na miki komai na aure. Dan shi gaskiya yana a cikin damuwar rashin kuɗi. Saboda hakane ma yaƙi yarda su tsaida rana a randa iyayen Mansoor suka zo. Amma da yasan har inada wannan kuɗin haka aida an kammala komai. Dan haka zai kirasu suzo weekend ɗin nan a tsaida ɗin. Na kuma bashi aron 200k zuwa ɗan wani lokaci zai bani..”
“Kuttt! Amma mutumin nan ko! Wai mike damun Abban nan ne?. Dama ko bai faɗaba waye ke jiran wani abu da ga garesa mtsowww aikin banza. Sannan kuma bashin ka amsa zaka bashi Yaya?”.
Murmushi Yaya Musaddiq ya saki mai haɗe da dariya, sai kuma ya girgiza kansa. “Kai wannan yarinya masifaffiya ce ke wlhy, wanda basu sanki bane kawai suke miki kallon mai haƙuri. Ni ALLAH har ma na fara tausayin Mansoor bawan ALLAH shi gashi da sauƙin halin tsiya”.
Baki na tura ina faɗin, “Kai Yaya nice masifaffiyar?”.
“Ta bugawa ma kuwa a jarida kandala. Wani lokacin da idan kina abu sai naga kamar ma kece Yayar tawa. Shiyyasa Hafizzullah ke cewa da kece Mamanmu da mun shiga uku”.
Dariya na ƙyalƙyale da shi. Na ce, “Masherancine yaron nan ai. Dan ALLAH Yaya weekend ɗin nan muje mu gansa tunda wancan ya shuɗe. ALLAH ina kewarsa”.
“Karki damu zamuje in sha ALLAHU. Dan na kammala masa ma siyayyarsa.”
Cike da farin ciki nace “Yauwa Yayanmu, kuma Babanmu. Yanzu dai yaya mi kacema Abban?”.
Sai da yay murmushi ya ce, “Mizan ce masa kuwa Samraah. Na gaya masa kuɗin dana bama Mom ɗin jiya ne kaɗai dama a wajena, sai abinda ya rage baifi saura dubu arba'in ba nama cire wani abu a ciki na haɗama Hafizzullah provision. Dama na tara wancan kuɗinne dan na basa shi da Mom ɗin su rage hidimar biki. Ga kuma abinda ya faru yanzu. Ina gaya miki sai kawai ya hauni da faɗa. Wai to wlhy sai nasan inda zan nemo wasu kuwa. Dan shi dai baida wani kuɗin yin hidimar nan bai kuma da hanyar samunsu. Inba hakaba kuwa sai dai a kaiki gidan mijin a haka.. inada yake shiga dai bata nan yake fita ba.”
Wata shegiyar dariya na bushe da