Showing 6001 words to 9000 words out of 90697 words

Chapter 3 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull.txt

24 Nov 2024

3991

bane wai lallai sai hakan ta kasance ba. Fata dai nake yi da jin yaƙinin zaki iya in sha ALLAHU”.
Shiru kamar bazance komai ba, kafin kuma na sauke nannauyar ajiyar zuciya. Na ce, “Shike nan Sir zan gwada na gani, ai da gwaji jirgin sama ya tashi sama daga bisa ƙasa. Amma dai bani kaɗai ce zanje wajen ba?”.
Ƴar dariya yayi a karo na farko, cikin tsokana ya ce, “Kada kice min ke ɗin matsoraciya ce mana. Bayan kuma kallon jaruma nake miki. Kallabi a tsakanin rawuna”.
“Humm Sir bazaka gane ba. Irin waɗan nan mutanen da suke jin tamkar ma duniyar su suke mata alfarma ba itace ke musu na basu fili a cikinta ba suna kallon mutane ne tamkar wasu dodannin tsaffi a rayuwa. Dan a kullu yaumin zaka gansu ne zagaye da masu tsaro a kowacce kusurwa ta rayuwarsu. Ni gaskiya bana son ƙasƙanci koda a wajen wanda ya fini ne”.
“Wannan itace ɗabi'a ta cikakken mutum ai Samraah. Duk wanda yasan darajar kansa haka ake so kuma ya kasance. Kada ki damu bake kaɗai zaki je ba. Hasalima ke aikin ki shine gabatar da shirin kawai. Akwai Davido da Mansoor da Khulsoom a tare dake. Yanzu sai kije ki tsara tambayoyin da zaki masa ki kawo min, ki nutsu sosai wajen tsarasun daga nan har zuwa Monday, kinga kinada kwanaki kusan huɗu kenan tunda yau muna alhamis. Kije da wannan mujallar domin duba abinda suka rubuta a kansa. Za kuma ki iya wani binciken a kansa ɗin dai koda ta hanyar yanar gizo ne ko wasu mutane. Hakan da zakiyi ne zai baki damar tsara abinda ya dace a kansa ɗin, dan ina fatan mu zama mune taurarin mako mai zuwa”. Ya ƙare maganar yana murmushi.
Nima dai murmushin nayi, dan ya ba ni dariya. “In sha ALLAHU zanje nayi nazarin Sir. Maybe ma kafin Monday ɗin kaga na tura maka duk abinda na tsara ɗin koda ta WhatsApp ne”.
“Masha ALLAH, ALLAH ya bada ikon hakan. Amma dai baki da matsala kibi komai a sannu tunda nunada kusan kwana goma kafin ranar”.
“To nagode Sir”.
Na faɗa ina miƙewa hannuna ɗauke da Mujallar. Harna fice a office ɗin ina jin idanunsa a kaina. A raina nace (Maye kawai sai dai kaci kanka kasha baƙin ruwa).......✍️






_Tofa masu karatu yaya kuke tunani akan wannan aiki da MD ya damƙama Samraah. Shin zata samu damar haɗuwa da wannan matashi mai wahalar sha'ani mai suna *Maash* ko kuwa?_.




_Idan ma ta haɗu da shi ɗin taya zata iya abinda wanda suka fita faɗa aji da gogewa akan irin aikinta suka kasa?_.


_Shin wai wanene ma *Maash* ɗin nan ne? Minene dalilinsa na gudun yarda ya bayyana asalinsa ga ƴan jarida. Miyyasa yake ɓoye kansa? Minene baya son a sani game da shi ɗin?_


_Duka wannan amsoshin suna a kundin littafin TSUTSAR NAMA... masu iya magana sunce wai ITAMA ƊIN NAMA ce. Kuzo ku mallaki naku domin jin abinda littafin zai zo muku da shi, domin kuwa ƙumshe yake da abubuwa masu ban mamaki, al'ajabi, makirci, soyayya, cakwakiya, zamba cikin aminci, tare da ɗan karan munafunci daga ɓangarori daban-daban._


*_In sha ALLAHU sayen nagari maida kuɗi gida😊😉😉😘😘🫡🫡._*






______________


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙_




.......Zaune na kai jagwaf a kujerar zamana ina dangwarar da mujallar da MD ya bani a desk ɗinmu. Mujallar Ruƙayya ta ɗauka tana faɗin, “Woow kaga wani handsome guy anan. Sam G daga ina haka? Waye shi?”.
Baki na ɗan taɓe kaɗan batare dana amsa mata ba na shiga ƙoƙarin kunna computer ɗin gabana. Itama batabi takan jiran amsar tawa ba ta shiga karanta abinda ke jiki. Wata ƴar zaburowa tai da zazzaro idanunta waje tana faɗin, “Kutt Sam-G wannan ai Maash ne.”
Duk ɗagowa sauran abokan aikinmu sukai suma suna kallonta. Sai kuma suka maido kallonsu gareni kamar yanda take kallona. Ganin na ɗauke kai tamkar bamma san mi sukeyi ba yasa suka sake maidawa kanta tare da miƙewa suka nufeta. Rufuwa sukai akan mujallar suna karantawa su duka huɗun, jin yanda duk suka nutsu yasa na ɗago na kallesu, batare da nace dasu komai ba na warce mujallar a hannun Ruƙayya. Ƴar harara na sakar musu ganin duk yanda suka ɗago suna kallona. “Malamai kowa ya koma kan aikinsa. Kun wani zauna karanta abinda bazai amfaneku ba.”
Ƴar dariya Usman da Asiya da Khalid sukai, yayinda Ruƙayya ta balla min harara. Magiya Usman ya shiga min yana faɗin, “Sam-G Please ki bamu mu ƙarasa karantawa, anya kinsan kuwa wanene wannan na jikin hoton?”.
“ALLAH bazan baku ba kuje kuyi aikinku, mi sanin nasa kuma zai amfaneni da shi da zan damu da so.”
Magiya suka shiga mun nace bafa zan basu ba, dole suka haƙura suka barni badan sun so ba. Sai dan ayyukan dake gabansu. Nima nawa aikin na cigaba dayi batare dana sake bi takan mujallar ba. Haka muka cigaba da aikin gabanmu har lokacin tashi yayi. Tarkacena na shiga haɗawa domin wucewa gida aɗan gaggauce, dan nasan Mansoor na jirana. A karo na farko idanuna suka sauka akan fuskar mutumin dake jikin mujallar lokacin da nake ɗakkota zan saka a jakka. Duk yanda naso kauda idanuna hakan ya gagara, dole nai tsai ina kallon ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Sam a zahirance baya kamanni da ƴan Nigeria ma bare Kano, duk da kuwa muma munada ƙyawawan fiye ma da kamarsa, sai dai kuma yanda hasken fatarsa yake tsaka tsaki dan bai wani yi haske dau ba zaka iya kiransa ko haif caste. Abu mafi ɗaukar hankali a fuskar tashi siririn baƙin gashin daya zagaye kumatunsa har zuwa haɓarsa ya kuma zagayo ta bakinsa ɗan ƙarami kamar ba namiji ba. Sam babu fara'a akan fuskar, sai hasken idanunsa dake a wani irin salo kamar na mai jin bacci. Abin mamaki tsakkiyar ƙwayarsu blue-blue zaiba-zaiba bansan yazan kirashi ba, ataƙaice kamar dai na mage ko masu jajayen kunne oho duk yanda kuka fassara. Sai cikakkiyar girarsa mai faɗi. Sosai na sake waro idanu lokacin da nakai dubana ga sumar kansa. Kitso ne guda huɗu akan nasa a kusan tsakkiyar kan dan ta gefe-gefe an aske sai saisayayyen sabon gashin daya kwanta luf-luf baƙi siɗik. Daga ta bayan kunnensa kam a dai-dai dokin wuyarsa zanen tattoo ne anyi fuskar zaki. Kunensa ɗaya manne da ɗan kunnen stone daketa wani irin sheƙi da ɗaukar ido kalar sky blue mai garai-garai kamar diamond. Wani wawan tsaki da ban san dalilin yinsa ba naja ina mai tura mujallar a bag ɗin. Dan sam nikam abin bai mun ba. Ɗan musulmi haihuwar arewacin Najeriya cikin Kano ne haka tamkar wani jinin yahudawa. Toni wannan tunda ma ba wani kama yake damu ɗin ba sosai ai gara ma a dinga jinginashi da ƙasashen ƙetaran mu bar musu kawai yafi, dan gaskiya aka bincika kam a cikin iyayensa akwai wanda ba bahaushe ba ko nace ma ɗan Nigeria gaba ɗaya. Da wannan mitar na fita a office ɗin, dan kusan ma nice ƙarshe su Khalid duk sun fice.
Horn da Mansoor yayi min ne ya ankarar dani in da yake, da alama dama ni yake jira, dan ina shiga yayma motar key muka fice. Har muka fita a layin da station ɗinmu yake muka hau titi sosai babu wanda yay magana a cikinmu. Sai zuwa can Mansoor ya katse shirun namu da faɗin, “Madam duk gajiyar ce haka?”.
Cikin ɗan yatsine fuska na ce, “Kawai dai”.
Maimakon yaji haushi sai yay murmushi kawai, dan ya fahimci yau ɗin ƴan shiru-shirun ne a kaina. Dan ko ɗazu da muka haɗu dama bawani hira nayi sosai ba. Baiyi fushi ba ya cigaba da jana da hira, tun dai ina amsawa a sama-sama harna ware, dan akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanina da Mansoor. Muna a gab da isa anguwarmu na takalo masa maganar da Uncle yay min akan aure kamar yanda Yaya Musaddiq ya bani shawarar nayi. Kamar wanda ya ɗan razana ya kallan, sai kuma ya maida hankalinsa ga titi da sauri ganin nima shi nake kallo..
“Lafiya kuwa? Naga kamar ka razana?”.
Murmushi ya saki tare da ɗan dubana, sai kuma ya gangara gefen titi ganin yanda duk na wani tsaresa da kallo. Sai da ya kashe motar da ƙyau ya juyo yana fuskantata. Ɗauke nawa idanun nayi daga kansa. Murmushi naji ya saki mai ɗan sauti, sai kuma ya fara magana a hankali. “Dole ne na razana ai Baby, dan farin ciki ne da yazo min a matuƙar bazata. Kema kin san tsahon lokacin dana ɓata ina fatan jin wannan furucin daga bakin ki. Taya yau na jisa ba zanji kaɗuwar farin ciki ba. Ki godema ALLAH ma da ban saki kan motar mun daki fitila ba. ALLAH na gode maka da ganin wannan rana a gareni, ni Mansoor zan mallaki TAURARUWAR MATAN DUNIYA”.
(🤥Ni dai banda ni eh🥱).
Murmushi ne ya suɓuce min, na kauda kaina gefe inayi duk da kuwa akwai facemask a fuskata, harma da eyeglasses dakan ƙara fiddo tsarin ƙyawuna a duk sanda na saka shi. Ganin murnar tashi bazata ƙare ba ga shi lokaci na tafiya murya can ƙasa-ƙasa na ce, “Please ka tada motar nan magrib fa zai yi”.
“A'a Madam, barni na gama murnata dan ALLAH. Mansoor ne fa zai mallaki Samraah Gwarzo. Wani shagalin ma ai sai naje gida hajjaju”.
“To nidai kaini gidan, idan kaje sai ka cigaba dayi”.
Da ƙyar na samu ya tada motar muka tafi, bakinsa baiyi shiru ba har muka ƙarasa. Nidai na sungumi bag ɗina na fice ina cemasa sai da safe.

A falo na iske duk mutanen gidan. Amma babu Hafizzullah da Abbas, da Nabel, hakama Abba da alama bai dawo ba shi da Yaya Musaddiq. Koda yake shi dama Yaya Musaddiq sai kai ma wata baka gansa zaune a falon nan ba. Iyaka ya shigo ya gaida Abba da dare, daga haka ya koma ɗakinsa, abincin gidan ma yakan daɗe yanzu bai cisa ba duk da nauyin kawowa ta dawo kansa badan kuma Abban ya rasa ba sai dan haka Mum ta tsara ayi. Mum ta watso min wata muguwar harara da ta sakani tura baki ta cikin mask ɗina. Batare dana sake kallonta ba nace “Mum good evening”.
“Ko kuma good uwarki ba”. Ta amsa a fusace. Dariya sosai Baby da Bibaa suka kwashe da shi. Sai autansu dake ta aikin homework ɗinsa kamar ma bai san abinda ake a falon ba. Tsawa ta daka min kan nazo. A hankali na nufi gabanta na durƙusa, bamma gama kaiwa ƙasa ba naji saukar lafiyayyen mari daya nema gigitani, dan har eyeglasses ɗina sai da ya faɗi. Idanun kawai na rumtse da ƙarfi, sai dai naƙi yarda hawayen da suka ciko min ido su zubo. A fusace ta ce, “K dan uban uwarki har ni zan sakaki aiki ki tafi sabgar gabanki ki bar min?”.
Karo na farko na ɗan kalleta. Cikin danne kukan dake neman kufce min na ce, “Mum wlhy duk abinda kikace nayi ban tafi ba sai da nayi sa”.
“Oh ƙarya nake miki ke nan ko? Miyar da kika bari akan wuta uwarki ce tai fatalwa ta ƙarasa min?”.
Wani irin rumtse ido na sake yi ina cije lips. Babu abinda kemin ciwo a duniya sama da zagin iyayenmu da Mum kanyi. Kuma in har tayi hakan bana iya daurewa sai na mayar mata da murtani. Yanzun ma hakance ta kasance. Dan cikin kaushin murya da tsiwa na ce, “Mum ai kunsha tubarraki kenan, dan nasan duk abinda zai fito daga Ummie na mai albarka ne, to balle kuma ace fatalwarta, ai nasan albarkar sai ta ninka ma. Bara naje nai salla na sake mata addu'a dan gobe idan zatazo a fatalwar ta dafa mana har abincin ba ƙarasa miya kawai ba”.
Ba Mum ɗin ba hatta su Baby sagade sukai suna kallona. Nikam ko'a kwalar rigata na miƙe tsam. Batare dana yarda na kalla kowa a cikinsu ba na nufi hanyar ɗakinmu ni da su Bibaa, dan Baby tun muna yara tace bazata zauna dani a ɗaki ɗaya ba. Hakan yasa aka haɗani da Bibaa da auta. Nasha wahalar yaran sosai, dan dukkan nauyinsu kaina ya koma, ga fitsarin kwance. Dole nabar musu katifar na dawo kwana ƙasa saman tabarma. Bayan na fara zama budurwa nazata za'ace nabar cikin yaran na koma ɗakin Baby, amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Sai ma wani sabon salon iskanci da ita Bibaa kan min yanzu, wai ita tana takura gaskiya a ɗakin dan munyi yawa. Ban taɓa cemata komai a kan hakan ba dai, dan fatana ma a yanzu Mansoor ya fito kawai ayi auren mu a wuce wajen. Shima Yaya Musaddiq yay nasa Hafizzullah ya koma gidansa ba shike nan ba mun bar musu gidansu........✍️








_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏_




.......Ina shiga ɗaki kukan da banyi ba a gabansu ya kufce min. Ban yarda nai zaman yinsa ba, na zame kayan jikina kawai na nufi bathroom. Tsayawa kawai nai ina kallon bayin raina a matuƙar ɓace. An masa kaca-kaca tamkar banyi wahalar gyaransa ba kafin na wuce. Nasan Bibaa ce tai masa haka. Dan tsabar iskanci har pad data cire guda biyu ta yasar a bayin da pants ɗinta. Inada ƙyanƙyami sosai a rayuwata, dan abu kaɗan ke ɗagamin hankali, shiyyasa ma nake bugar jikina na tsaftace gidan yanda ta kamata batare da jin ƙyashi ba. Hawaye tab da idona na shiga gyaran bayin, sai da na maidashi ƙal na tattara trash ɗin data tarama mutane na fitar. Har lokacin suna a falon zaune suna kallo har Mum ɗin, kai kace basu ji sallar magrib da akeyi ba. Na jima da fahimtar Mum saita gadama take salla, shiyyasa ƴaƴan nata ma dai gasu nan sai a hankali babu wanda ya damu da ibadar. A da Hafizzullah har ya fara ɗaukar ɗabi'ar, sai da na miƙe kansa ni da Yaya Musaddiq tamkar bama ƙaunarsa sannan. Sake zuwa nai na wucesu na koma ciki. Sai da nayi wanka na saka doguwar riga mara nauyi nai salla. Bayan na idar zaman yin karatun Alkur'ani nayi, ban ɗaga a wajen ba sai da akai isha'i, har lokacin kuma ina jiyo hayaniyarsu a falon, sallar dai bazasu tashi suyi ba. Falon na fito na wuce dan ɗaukar abinci na, amma sai na samu wayam. Banyi ƙasa a gwiwa ba na dawo ina tambayar Bibaa. Wani kallon banza yarinyar ta watsa min duk da kuwa na bata kusan shekara bakwai zuwa takwas, dan kwata-kwata yanzu take a shekara ta goma sha uku, a gadarance ta ce, “Kin bani ajiya ne. Ka jimin rainin wayo dan ALLAH mtsowww!!” ta maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Bance komai ba na juya na koma ɗaki, dan hakan da tai na nufin yau banda abinci a gidan tunda na tafi aiki ban kammala miya ba, bayan kuma nayi komai har abinda ba'a sakani ba, miyar ma na barta ne kawai ta gama fidda mai dan karna makara tunda ta soyu. Wajen kwanciyata nakai zaune ina hawaye, dan haka kawai yau naji zafin abinda akai min ɗin duk da bawai yau ɗinne farko ba, amma kasancewar na dawo da yunwa sai abin ya zafeni. Tun muna yara idan Mum ta bushi iska takan hanamu abinci, haka Hafizzullah zaita kukan yunwa dan ni da Yaya Musaddiq mukan daure, ko zaiyi kukan mutuwa kuma bazata bashi ba sai dai Yaya Musaddiq ya fita ya samo masa a waje koda da bara ne, yanzu kam da muka girma idan aka hanamu zai sayo ya jamu ɗakinsa muci mu ƙoshi muna hirarmu. Sai kuma hakan ke ba Mum haushi take kai ƙararmu ga Abba wai muna haɗe kai muyita zaginta a ɗakin Yaya Musaddiq. Wani lokacin Abban kan mana faɗa, wataran kuma ya mata shiru, sai dai ta ƙaraci masifarta ita kaɗai. Ganin zaman bazai amfaneni da komai ba na miƙe ina share hawayena. Ƙaramin hijjab ɗina na zaman gida na ɗauka na saka, na ɗauki jakata dana fita aiki da ita na fito. Suna a falon har yanzu suna kallo, banko kalla kowa ba a cikinsu na fita zuwa ɗakin Yaya Musaddiq. Sai da na ƙwanƙwasa tare da yin sallama ya bani izinin shiga sannan na shiga. Tashi yay daga kwancen da yake a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login