Showing 27001 words to 30000 words out of 90697 words

Chapter 10 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull.txt

24 Nov 2024

3979

a social media. Kasan dai kisan kai ba abune mai sauƙi ba. Musamman ga mutum irinka sananne mai tarin magauta da masoya tako ina. Na baka awa arba'in da takwas. Idan kunne ya ji jiki ya tsira._*


Ya jima bai motsa da ga zaman da yay a lallausar kujerar ba ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayinda bayansa ke kwance jikin kujerar kansa a sama kaɗan. Yanda yay biris ɗin sai ka ɗauka baima ji ko fahimtar abinda PA ɗin nasa ya karanto masa bane ba sam. Yaja kusan minti uku PA nata kai kawo kafin yaja wani irin huci ya furzar yana mai buɗe idanunsa da suka sake wani irin garai-garai ai nahin suffarsu ta idanun mage na sake bayyana a fili. Zaune ya tashi da ƙyau, sai dai a nutsensa yake abin mamaki. Goran ruwa dake a Centre table ɗin ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa. Sai da ya shanyesa tas sannan ya jefar da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na biyu yana sake nutsar da kansa, sai kuma kamar wanda ya tuna ya dubi PA ɗinsa. “Ina buƙatar duka cctv footage na company a daren nan?”.
Cak Hayatu ya tsaya da ga kai-kawon da yake, sai kuma jiki a sanyaye ya ce, “Sir ka manta mun duba sanda muka shiga kafin faruwar abun amma basayi duk an kashesu”.
“Hakane, amma kamar na kunna ukun farkon nan.”
“Yes yes tabbas kuma hakane fa Sir. Wlhy sai yanzu na tuna. Aiko ko wanene wannan zaici ubansa.” baima jira umarnin ogan nasa ba ya fice da sassarfa tamkar zai kifa ƙasa duk kuwa da dare ne a lokacin. Dan kusan sha ɗaya ma ake nema, saboda bayan an tashi a taron company sun bu sarkine kamar yanda ya buƙa. Bayan sallar magrib suka bar gidan sarki, maimakon gida suka wuce wajen wani abokin harƙallarsa dan haɗuwar ta sirrice, sai goma saura suka nufo gida. Gashi yanzu ana harar sha ɗaya da wasu mintuna.


Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga falon ya nufi bedroom ɗinsa. Tamkar mai hasashen ganin wani abu sai da ya gama kalle kowacce kusurwa da lungu da saƙon na ɗakin sannan ya kai zaune a bakin katafaren lafiyayyen gadon. Sabon gida ne fil dan yau ne ya fara shigarsa. Anyi aikin gininsa tare da Companyn nasa ne. Bai cika son zaman hotels ba a rayuwarsa sai in har ya zama tilas a garesa. Ta wani ɓangaren kuma gorin mutane akan kullum yana cika bakin shi ɗan Kano ne amma ko gida baida a arewa ma gaba ɗaya ya sashi ginin wannan gidan da ko makaho ya laluba yasan an kashe kuɗi. Dan yanda companyn ya haɗu shima gidan haka ya haɗu matuƙa.
Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane. Abubuwane kawai suke masa kai-kawo a rai da suka faru a wannan yinin. Kallon komai yake tamkar wani film ba zahiri ba. Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba. Amma na yau ɗin na musamman ne. Dan duk sunzo masa a bazata. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan. Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba?. Amma dai bari ya jira P.A ɗinsa da sakamakon da yake buƙatar gani kafin ya tsara komai akan mizaninsa. Da ga haka ya miƙe yana mai fara zame kayan jikinsa domin shiga wanka...


Yaja tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe ash color sabuwa dal. Dan yanda take wani maski-maski zai tabbatar da hakan. Ƙaramin towel da a hannunsa ya kai kan jiƙaƙƙiyar sumar kansa mai tsaho data kwanto masa a fuska sosai, hakama ta bayansa kai kace bai haɗa jini da babaƙen fata ba balle ma har a kirashi da suna bahaushe. Tamkar ba shi kaɗaine a ɗakin ba. Fuskar nan a tsuke babu alamun rahama a cikinta. Duk da tun fitowarsa wayarsa ke tsuwwa alamar kira na shigowa, yay biris da ita tamkar bai ji ba. Sai ma ƙoƙarin nufar ƙaton mirrorn dake a ɗakin yayi abinsa. Tuni Hayatu ya shirya masa kayan shafe-shafensa a mirrorn, dan zaiyi kamar 1week ne a cikin Kanon kamar yanda yake fata. Hand dryer da aka ajiye a saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, sumar tasa ya fara busarwa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala gyarata alamar ya riga ya saba da hakan. Kafin ya ɗan shafa mansa sama-sama tare da sprays masu shegen ƙamshi kala har biyu sannan ya nufi doguwar wadrobe data cinye bango guda. Ta farko kawai ya buɗe, anan ko yaga kaya kusan kala goma duk ƙananu, sai ƴar akwatin da yazo da ita da suit kala uku a ciki. Yasan kayan dake a shiryen duk aikin Hayatu ne. Batare da yace komai ba ya ciri farin pyjamas mai shegen ƙyau da laushi, sai boxer shima dai sabo. Tsaf yay shirinsa tare da sake komawa gaban mirrorn yay sabon wankan tsadaddun turarurrukansa na barci da ƙamshinsu ba'a magana kamar ba dare ba. Tsaki yaja a hankali yana hararar wayarsa da ke cigaba da tsuwwa babu ko ƙaƙƙautawa. Ya san mai kiran nasa, dan ita kaɗaice take karya dokarsa akan hakan. Duk wanda ya sanshi yasan yanada doka a akan kira, dokar kuwa itace in har kamasa kira 1 bai ɗaga ba ka bada mintuna kamar biyar sannan ka sake. Idan nan ma aka samu akasi bai ɗaga ɗin ba to ka haƙura kawai, idan shi ya samu lokaci zai iya ya kiraka, idan bai biyo ba kuma ka ɗauka kiran naka baida muhimmanci ne. Wayoyinsa duk a hannun Hayatu suke. Wannan ce kawai yake riƙewa saboda Ummien sa. Gaban gadon ya ƙarasa in da ya yasar da wayar, cikin ƙara ɗaure fuska ya ɗauka dan yana son ta barsa. A daƙile ya kai wayar kunensa sai dai yaƙi cewa komai. Sai da yaja kusan sakan hamsin ya ce, “Thanks”. Kawai yaja bakinsa yay shiru. Kasancewar bai sauke wayar ba zai tabbatar ma da har yanzu magana ake daga can, dan sai wani yamutsa fuska yake da sake tsuketa kamar mai jin warin mai maganar. Kusan minti biyu ya sake furta, “Zanyi barci”. Daga haka ya yanke kiran gaba ɗaya. Wayar ya wurga a saman gadon tare da jan tsaki mai ƙarfi ya haye gadon yay kwanciyarsa. Kai kace ma baida wata damuwa a rayuwa. Sai da yay addu'oi barci sannan ya lumshe idanunsa. Kafin wani dogon lokaci ya fara sauke numfashi a hankali alamar yayi barcin.....




●´⌓`●●´⌓`●●´⌓`●


Duk yanda nagaji na kasa barci. Sai faman juye-juye nake abubuwa na dawo min tamkar yanzu suke faruwa, dan ma ƴar wayar da mukai da Mansoor ta ɗan sani ƴar nutsuwa. Ganin ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa na tashi na ɗaura alwala. Salla na farayi, sai da na kwashe kusan awa ɗaya da rabi sannan na zauna ina istigifari. Kamar a mafarki naji wayata na verbration. A gogo na kalla, ƙarfe biyu da kwata. Mamaki ya kamani, dan ko Mansoor baya kirana a wannan irin lokacin, kuma ma ai munyi waya duk da dai yace zai sake kira video call amma bai kira ba, ganin lokaci haja yasa ban damu ba. Dan duk tsawon wayarmu baya wuce daga tara zuwa goma. Jin an sake kira bayan ta katse na yunƙura na ɗauka. Abin mamaki Mansoor ne. Ɗagawa nai hankali a tashe, a tunanina ko wani abu ya samesa. Amma sai naji yaymin sallama cikin taushin murya. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sannan na amsa masa.
“Dama naji a jikina zaki iya kasa barci, kiyi haƙuri Yaya ne ya ɗauke hankalina shiyyasa ban sake kiran ba. Haba Babie dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan. Ai ko ke kika aikata laifin nan sai haka”.
Numfashi na sauke a hankali. Cikin sanyin murya na ce, “Ni ban kasa barci ba fa, na farka ne kawai”.
“Uhhm yau kuma halin daba naki ba kika aro, to ai bai miki ƙyau ba dan baki iya ƙaryarba tunda ga harshenki yana rawa”.
Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, sai kuma nakai kwance ina faɗin, “To amin afuwa gashi na kwanta. Amma kaima miya hanaka barci?”.
“Saboda mahaɗin zuciyata batayi ba”.
“Humm”. Na faɗa kawai ina murmushi. Shima ina jiyo sautin nasa murmushin. Mun ɗan yi shiru na wasu sakannin kowannemu na sauraren saukar numfashin ɗan uwansa. Kafin ya katse shirun da cewa, “Kin sanarma Yaya Musaddiq abinda ya faru ko?”.
“A'a”.
“Miyasa?”.
“Kawai dai”.
“Aiko Babie ya kamata ya sani. Dan ko zamu iya ɓoyema kowa shi banda shi. Maybe ma ya ƙaremu da shawara ai. Dan wlhy har yanzu ni kaina duk a kulle yake”.
“Hakane zan sanar masa gobe in sha ALLAHU. Amma ni dai dan kaƙi ta nawane. Hukuma kawai ya kamata mu miƙawa ai”.
“Baƙi naiba Samraah. Ina son ki fahimci wani abu. Mutumin nan fa ya wuce duk inda kike tunani a ƙasar nan. Yanzu koda mun miƙa video ɗin nan ga hukuma kina ganin zasu hukuntashi ne. Ko kin manta yanzu a ƙasar nan tamu KUƊI ne ke magana ba GASKIYA ba. Shi kuma ALLAH ya bashi su, Samraah Maash fa zai iya juya Africa a tafin hannunsa ta yanda yaso bama Nigeria ba. Ke hatta da ƙasashen masu jajayen kunnuwan yanada ƙarfin faɗa aji sosai fiye da yanda kike tunani ta wasu fannoni. Sai dai su banbancinsu damu zasu iya hukunta duk wani mai laifi koda shi wanene? Amma a ƙasarmu ba haka bane. Ko wanda bai kama ƙafar Maash ba zai iya shallakewa in har da kuɗi. Kiyi haƙuri dai mu nema mafita mai ɓullewa. Mu kuma samu jajirtaccen ɗan sandan da zai iya yin duk abinda ya dace batare da kuɗi sun iya tankwarashi ba saboda gaskiyarsa. In dai Maash ne bazamu ƙyalesa ba sai an ƙwatoma mutumin nan hakkinsa”.
“ALLAH ya tabbatar to. Na kuma gamsu da bayaninka.”
“Masha ALLAH dear, yanzu dai zan shigo gobe in ALLAH ya kaimu ki biyo Yaya Musaddiq gareji mu haɗu acan dan ina so mu tattauna da gaggawa mu nemo mafita kafin Maash ya farga. Saboda babu yanda za'ai ace babu camaras a wajen nan duk da Companyn bai fara aiki ba sai Monday”.
Sosai zancensa ta ratsani dan har sai da na tashi zaune dingangan. Amma na gagara cemasa komai saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri........✍️



_Tofa masu karatu yanzunne fa ainahin wasan zai fara. Dan da alama mun gama sharar fage zamu tafi mataki na biyu a labarin. Wa kuke tunanin ya rubuta saƙon nan? Sannan karku manta a cctv footage fa Samraah za'a gani. Shin ko itace dai ta rubuta saƙon? Ko kuma wani yaji sanda take faɗama Mansoor yay amfani da damar? Ko kuwa ba ita kaɗaice ta gani ba? Shin minene dalilin Maash nayin kisan nan ma wai? Wanene aka kashe?..... Kai kai kai cakwakiya ce fa iya cakwakiya a labarin nan. Amma dai ina son jin amsoshinku a comment section. Yau har masu laɓe su fito inba haka ba gobe babu posting sai bayan salla🚴🚴🚴._






_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_




.......*_WASHE GARI_* kamar yanda na saba na tashi nai ayyukana da sauri-sauri. Ana idar da sallar asuba nai wanka. Breakfast ɗin Yaya Musaddiq na ɗauka na nufi kai masa kusan bakwai da rabi. Nako samu har ya kammala shiryawa. Tunda na shigo yake bina da kallo, basai nace komai ba nasan ya gama fahimtar yanayina ne. Amma sai na dake. Sai dai ina gaishesa maimakon amsa min tambaya ya jeho min. Baki na buɗe zance babu komai yay saurin ɗaga min hannu da faɗin, “Karma kimun ƙarya. Faɗamin mike damunki?”.
A hankali hawayen da nake riƙewa suka silalo. Nima babu shiri na silale ƙasa ina mai fashewa da kuka. Duk abinda ke a raina tun jiya ne ya samu damar fitowa. Kafin ma ya sake cewa da ni komai na shiga faɗin, “Yaya kisan kai yayi. Da idona na gansa yana zare wuƙa a jikin mutumin ga jini face-face. A kunnena naji yana faɗin akai gawar wani anguwa a ajiyeta.....”
A cikin matuƙar tashin hankali ya katseni jikinsa na rawa. “Waye wai? Ki min magana a buɗe Samraah Please wa aka kashe waye kuma yay kisan?”.
Maimakon bashi amsa sai na miƙa masa wayata kawai. Amsa yay da rawar jiki. Yana ko dannawa da video ɗin ya fara cin karo dan ni bana sakama waya password sam. A matuƙar birkice ya ɗago yana kallona tun a fara kallon video ɗin. Idanunsa a warwaje na shiga razana ya furta, “Samraah Maash fa?”.
Kaina na jinjina masa da sauri ina faɗin, “Shi yaya! shi! Mutumin nan azzalumi ne bana kirki bane kamar yanda duniya ke kallonsa. Zata iya yiwuwa ma kuɗin nasa bana ALLAH bane na jinin mutane ne”.
Tuni zufa ta wanke Yaya Musaddiq. Cikin tashin hankali ya ce, “Bayan ni wa kika faɗamawa?”.
“Mansoor ne kawai Yaya. Tun jiya nace mu kai ma hukuma video ɗin amma ya hana. Shine ma yace na baka ka gani dan mu haɗu da shi a gareji mu tattauna”.
“Gara daya hanaki Samraah. Dan dole wannan al'amarin na buƙatar nazari. Maash ba anyhow mutum bane da dokar hukuma zatayi tasiri akansa cikin sauri. Inaga yanzu ba zama zamuyi ba tashi mu wuce. Bara na kira Mansoor ɗin ya fito shima gara muyi abinda ya dace da wuri tun kafin ya bar garin nan. Dan bai zama lallai a sake samun irin wannan damar ba duk da naji ya amsa miki wai kiyi hira da shi. Ga gari nan duk ya ɗauki zance harda masu faɗin ba haka kawai kikaje masa ba akwai asiri saboda yanda ya amsa ɗin babu musu a gaban duniya. Amma ni zuwa yanzu na fara zargin akwai wata a ƙasa kam, bana raba ɗayan biyu ya ganki sanda kike ɗaukar video ɗin nan, ko kuma ta cctv, dan Company kamar nasa dole asamu camaras tako ina”.
Idanu na waro sosai na matuƙar mamaki, Yaya Musaddiq ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. “Samraah duk mai hankali dolene ya gane akwai dalilin Maash na amsa miki gayyatar da kikai masa cikin sauƙi. Dan bazai taɓa zama ya amsa miki bane kawai saboda kin jera masa tambayoyi. Kai ina dolene ma ya ganki fa, ya barki ne kawai bisa dalilinsa, sannan yazo a bainar jama'a ya amsa zaiyi hira dake, hakan na nufin akwai wani abu da yake ƙullawa”.
Sosai na zubama Yaya Musaddiq ido, dan tabbas zancensa yasa na fara dawowa cikin hankalina yanda ya kamata. (Humm you are vary smart girl) kalmar daya fara ambata a kaina kenan. Tabbas wannan mutumin terror ne na gasken-gaske. Shin mi yake ƙullawa? Dan dolen dole akwai abinda ke ransa kamar yanda Yaya Musaddiq ya faɗa. Kai ina buƙatar ganin ma program ɗin jiya gaskiya.....
“Kinga tashi muje, ba lokacin tunani bane yanzun”. Yaya Musaddiq ya faɗa cikin katse mun tunani. Miƙewa nai babu musu, dan basai na koma cikin gida ba dama....





🤙❤️🤙❤️🤙❤️


A ɓangaren Maash asubar fari ya farka, da ƙyar ya iya tashi saboda gaɓɓansa duk ciwo suke masa. Ruwa ya fara watsawa ya fito a gurguje ya kimtsa cikin wando da rigar polo. Koda ya fito su Hayatu suma har sun fito zasu wuce massalacin. A tare suka fita, bayan an idar da salla bai koma cikin gidan ba yace ma Tijjani ya fito da mota zasu je wani waje. Da sauri Tijjani ya shiga ciki, babu jimawa ya fito da mota, suma guards ɗinsa suka fito. Komai baice ba Hayatu ya buɗe masa baya ga shiga, shi kuma ya shiga gaba kusa da Tijjani. Jihar Jigawa suka nufa, a wani ƙauye dan akwai business ɗin da zai yi a wajen. Duk da dai da farko bai wani ɗauki abin da muhimmanci ba, sai da zasu je massalacin nan ne Hayatu ke sanar masa mutumin da zasuyi kasuwancin ya kira, kuma yana son suje da wuri ne.
Yinin ranar guda a Jigawa suka cinyesa. Ko abinci bai sakama cikinsa ba garama su su Hayatun. Sai Black tea kawai yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login