Showing 9001 words to 12000 words out of 90697 words

Chapter 4 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull.txt

24 Nov 2024

3975

tabarmar barcinsa, dan koya sayi katifa amshewa Mum take ta bama su Bibaa su kasheta da fitsari ko a bama su Abbas. Kusan sau uku tana yin hakan shiyyasa ma ya bar saya shima. Murmushi yay min yana mai bina da kallo, na ɗan tura baki gaba ina zama a gefensa da ajiye jakar kamar a yanayin gajiye. Yaya Musaddiq mutum ne mai sauƙin kai sosai, da wahala ka iya ganin fushinsa a zahiri. Cike da kulawa ya ce, “Kandala miya faru kuma ake kumbura wannan cat face ɗin?”.
Sake tura bakin nayi da faɗin, “Ni ba komai, yunwa nake ji”.
Ɗan jimm yay yana kallona, sai kuma ya ɗauke kansa da sauke ajiyar zuciya ya miƙe. Rigarsa ya ɗauka ya saka a saman singlate ɗin jikinsa. “Ki jirani ina zuwa”.
Kaina na jinjina masa ina kaiwa kwance a tabarmar tasa. Yana fita na ɗan lumshe idona. Kusan minti huɗu ina a haka sai kuma na miƙe zaune. Jakar tawa na jawo gabana, tare da zuge zip na ciro mujallar nan da MD ya bani ɗazun. Yanzu kam kai tsaye na zubama mujallar ido, sosai nama mutumin kallon ƙurilla a karo na biyu, badan baiyi haske dau irin na larabawa da indiyawa ba da tabbas zan iya cewa daga cikinsu ya fito. Dan daga suffar jiki har zuwa ta halitta fuska bai yi kama da ƴan Nigeria ba. Sai dai kuma abin mamaki fatarsa zamu iya cewa irin tamu ce. Duk da kuwa ba baƙi bane wulik, idan ma za'a kira farare za'a iya nunashi mu anan Africa, sai dai kuma farin nashi yasha banban, koda yake maybe camara ce ta maida shi hakan. Sake maida idanuna akan kitson kansa dake ɗaure a tsakkiyar kai kamar wani mace, sai kawai naja sirrin tsaki, banda ƙarshen duniya dai ace namiji da kitso da ɗan kunne. Kai ALLAH ya ƙyauta, inaga dai ɗan daudu ne gaskiya. Dangwarar da mujallar nayi gefe na sake komawa nai kwanciyata. A dai-dai nan Yaya Musaddiq ya shigo ɗakin da sallama. Amsa masa nai ina tashi zaune. Ya ajiye min ledar hannunsa yana faɗin, “Oya tashi kici”.
Babu musu na tashi zaune, ina ƙoƙarin buɗe ledar shima yana kaiwa zaune ya ɗauki mujallar. “Tofa! Ke kuma ina kika samo _Maash_ haka kandala?”.
Baki na taɓe da fara kai lokar indomie ɗina. Kafin na ce, “MD ɗinmu ne ya bani yau wai zanyi aiki a kansa”.
“Aiki kuma?”.
“Eh Yaya, so suke wai nayi hira da shi a ranar bikin buɗe Companyn sa”.
“Kai lallai sun haɗaki da aiki. Amma ALLAH ya bada nasara”.
“Amin” na amsa masa ina sake jin karaya. Sai kuma na kallesa, batare da nasan ya akai bakina ya suɓuce ba na ce, “Yaya amma dai shi ba musulmi bane ba ko? Sannan ba ɗan Nigeria bane?”.
Sosai ya waro idanu waje da faɗin, “Kai! K waye ya gaya miki ba musulmi bane?”.
“To Yaya wane musulmi ne zai zauna ai masa kitso a saman kai ya ɗaure haka kamar wani mace. Ga ɗan kunne kuma a kunne ga tattoo a wuyansa. Sannan kalli idonsa kamar na mage fa. Ni wlhy banji ya birgeni ba abu kamar ɗan daudu”.
Dariya Yaya Musaddiq ya saki yana girgiza kansa. Ya ce, “Banda abinki Samraah dan mutum yayi duk wannan sai a fiddashi a musulunci ko a kirashi ɗan daudu. Wannan abun da kika gani yanzu shine samari suka ɗauka matsayin gayu da wayewa wai, baki ganin kuma shi ɗin mai lokaci ne da duniya ke ji da gani. Idan kuɗi na ɗibar mutum ai komai ma sai ya yi ba komai bane. Sannan shi ɗin kamar ance ruwa biyu ne. Tsakanin kakansa da kakarsa akwai wadda ba ɗan Nigeria ba, anan ma ya kwaso waɗan nan kamannin da kowa ke ganin ba ɗan 9ja ɗin bane ba. Amma asalin mahaifinsa ɗan kwanar Mashi ne ma, Kinga kuwa shi cikakken bakano ne, anan ma aka haifesa shi”.
Baki na taɓe akan maganar yaya ta kusan ƙarshe, sai kuma na ce, “Humm, to ALLAH ya rabamu da irin wannan kuɗin masu mantar da bawa shi waye kuwa. Ni yanzu Yaya yaya zanyi to. Wlhy duk kaina ya gama kullewa fa?”.
“Karki damu in sha ALLAHU zamu samo mafita. Ke dai kawai ki saka a zuciyarki zaki iya. In dai shi ba aljani bane nasan duk taurin kan Maash bazai gagari Kandalata ba ai. Dan itama tauriƙiƙin kantace ga naci akan abinda tasa gaba”.
Dariya na ƙyalƙyale da shi da faɗin “Kai yaya?”
Ya ce, “ALLAH ai nasanki ne fiye da yunwar cikina kandala”.
Nanma dariyar nayi shima yana tayani, tuni Yaya ya mantar dani baƙin halin mutanen gidanmu. Ya kuma bani ƙwarin gwiwa sosai data bani karsashi akan tunkarar wannan aiki da MD ya bani, ban baro ɗakin ba sai da na fara hammar barci....


Washe gari ban ɗaga ko tsinke ba a gidan, dan banma tashi a barci ba sai ƙarfe bakwai. Salla nayi nai wanka nai shirin office nai tafiyata, dan har lokacin babu wanda ya tashi suna can suna barci ana jiran jaka ta gama girkawa a fito a ci. To ai na fisu iya tsiya, dan kamar yanda na saba in har aka gunziga min baƙin ciki a gidan sai na maida murtani. Yaya Musaddiq bai san tsiyar dana shuka ba ya ɗaukeni muka wuce a mashin ɗinsa. A hanya nake roƙonsa wannan weekend ɗin muje muga Hafizzullah a Katsina dan ALLAH idan baida aiki da yawa. Bai musa ba yace min in sha ALLAHU zamuje ranar asabar sai mu dawo lahadi. Sosai naji farin ciki, harma na manta da damuwata balle na sanar masa banyi breakfast ba na gudo yau. Yana sauke ni ya miƙamin 1500. Amsa nayi ina masa godiya da yima iyayenmu addu'ar samun rahama. Daga haka na shige shi kuma ya wuce.
Kasancewar yau inada gabatar da program banfi zaman mintina talatin ba na tashi na fita tare Khalid. Kusan cin karo mukai da Mansoor dake ƙoƙarin fitowa. Baya naja da sauri, sai hakan ya sakani tuzguɗewa na tafi zan faɗi. Kusan tare suka kawo hannu shi da Khalid domin taimaka min, niko nai saurin sake maida jikina baya ta yanda kowannensu bai samu damar taɓanin ba, dan na gwammaci na faɗin kawai. Aiko faɗuwar nayi, na kuma ji zafi sosai, duk da kuwa na fuske Mansoor sai da ya fahimci hakan. Cike da damuwa yakai duƙe gabana tare da sake kai hannu zai riƙo nawa na ɗan hararesa. Murmushi kawai yay ya janye hannunsa yana kaisa saman kansa ya shafa cike da basarwa. Sai kuma ya sake maida idonsa gareni, a hankali ya ce, “Yanzu har kina da damar yin masifa babie. Naga dai hannun ai nawa ne”.
Sake hararsa nayi tare da ɗauke kai ina ɗan murguɗa baki, na ce, “Sai ka bari sai ka biya ai”. Ina kai ƙarshen maganar na miƙe abina. Dariya ya saki mai sauti da faɗin, “Rigimammiya kawai ai saura ƙiris dai, mi kike ci na baka na zuba. Wata uku bazaki ƙaraba sai da igiya uku na ciff a kanki”.
Murmushi kawai nayi ina ɗan murguɗa bakina dake cikin face mask ɗina na wuce na barsu a wajen Khalid na tayasa dariya. Sai da na gaishe da kowa kafin na wuce na ɗan ƙara gyara fuskata gaban mirror, suma su Mansoor sun shigo, dama mu zaije kira ashe. Hakama baƙonmu na yau ya iso tuni, dan haka babu ɓata lokaci aka fara gabatar da program ɗin........✍️








_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕_




.......Yau ma kamar kullum Mansoor ne ya ɗaukeni zuwa gida bayan an tashi. Mun ɗan fara tafiya nake sanar masa aikin da MD ya saka ni. Da mamaki ya juyo yana kallona da faɗin, “What! Dama ke ya bama aikin nan? Taya zai haɗaki da wannan aikin mai wuya bayan yasan wanene wannan mutumin. A tarihinsa fa bai taɓa yarda yayi hira da ɗan jarida ba har yanzu. Kuma karki ɗauka wai ƴan jaridar nan gida Nigeria kawai. A'a har manya-manyan ma irinsu BBC, VOA, Aljazeera da ire-iren su. A duk sanda aka buƙaci hira da shi sai ya haɗa mutane da P.A ɗinsa...”
“Hu'umm, to amma shi miyyasa yake yin haka? Kamar ba wayayye ba? Ko kuma bashi da gaskiya ne shiyyasa yake gudun hakan?”.
“To ALLAH kaɗai masanin gaibu, sai kuma shi da ya barma kansa sanin dalilin. Amma dai wasu na ganin girman kai ne kawai da giyar kuɗi dake ɗibarsa. Dan a yanzu fa shine matashi ɗan kasuwa na biyu a duniya dake juya manyan kuɗaɗe, anama hasashen nanda shekara mai zuwa zai iya zama na farko. Wasu kuma na ganin akwai dai wani babban dalili nashi, dan in har da girman kai ne ai zaiso ƙara bayyanama duniya shi ɗin wanene ta hanyar ƴan media ɗin. Wasu ko na ganin ko dodon tsafinsa ne yace kar yay hakan, kin san dai mafi yawan ƴan kwasuwar nan dake shahara a ƙanƙanin lokaci sai a hankali, shiyyasa ake yawan ɗora musu zargi, ALLAH dai masanin gaibu. Amma gaskiya al'marin dai nasa akwai ɗaure kai”.
“Ƙila to aljanu ne da shi da basa son hira da ƴan jaridar. Ko kuma dai da gasken dodon tsafinne da shi. Dan ni naga yanda kowa ke misalta dukiyar tasa akwai ban tsoro kam”. Na faɗa cikin halin ko in kula. Dariya sosai Mansoor ya sanya, tare da faɗin, “Kai Babie baƙya rabo da wauta ALLAH. Aljanu kuma? Namiji da aljanu? Adai tsaya a dodon tsafin”.
“To inba aljanu ba shi kam ai abin nasa yayi yawa, dodon tsafin ma kuma ai aljanu ne. Yanda yake nuna kansa a matsayin wayayye irin haka ai ya kamata ace an wuce wannan ajin. Amma ni kam in sha ALLAHU sai na sakashi ya magantu, ni halin nasa ma sai ya ƙara min ƙwarin gwiwar tunkararsa.”
Sosai Mansoor ya juyo ya kalleni cikin nuna mamakinsa a fili. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Anya yarinyar nan kin san wanene *_MASH!?_* kuwa? Babu sauƙi fa a ɗaukar wannan alwashin naki. Ni dai ina gargaɗarki da kar kiyi wani abu mara ƙyau dan ALLAH. Idan kin samu dama kamar yanda kowa ke fata fine, idan baki samu ba ba faɗuwa bace. Dan haka be careful sweetie. Kar ki biye ta MD kujerarsa kawai yake yunƙurin saitawa”.
“Karka damu, ni ba wani abu mara ƙyau zanyiba ALLAH. Kuma duk ma tambayar da zan masa ai sai na kaima MD ɗin ya duba. Kaima kuma zan baka ka gani kafin ma na turama MD ɗin har ma Yaya Musaddiq. Kawai dai ina fatan karya masa wannan alfaharin nasa ne”.
Kansa ya jin jina min, ya ce, “To ALLAH ya bamu sa'a, dan zanfi kowa kasancewa a farin ciki ace kece kika karya ɗin kam. Dan har ƙyauta sai na miki na musamman”.
“Tami?”.
“A'a ai ba sai na faɗa ba. Yanzu dai ajiye ma wannan batun. Su Alhajina fa zasu zo wannan weekend ɗin. Dan haka yau ina buƙatar ganawa da Abba yaya za'ayi kenan”.
Da sauri na juyo na kallesa, ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. Kaina na ɗauke cikin jin kunya, sai dai wani irin farin ciki ne ke ratsa ƙashina da ɓargo har ina jin yanda jikin nawa ke rawa. Amma dai nayi juriyar dakewa. Sai dai ban sake cemasa komai ba har muka iso. Tunda ya tsayar da motar na kasa wani motsi, mun kai minti biyu a haka shi kuma yana kallona kamar ya samu tv kafin ya saki ɗan murmushi mai sauti. “Wai kunyar ce dai Babie?”. Sake kauda kaina nayi gefe batare dana bashi amsa ba. Ya saki ƴar siririyar dariya yana ɗan dukar sitiyari, sai kuma ya juyo gareni yana faɗin, “ALLAH ya kaini randa zan cire wannan kunya dai kowa ya huta, dan bazanyi sakaci ba a daren farko zata kama gabanta. Anya baki haɗa jini da fulani ba Samraah”.
Hannu na kai ga handle ɗin ƙofar zan buɗe na gudu sai na jita gam alamar ya saka lock. Kasa sake wani yunƙuri nayi, na kuma kasa juyowa dan har lokacin ina jin kallon ƙurullar da yake min.
“Kayi haƙuri ka buɗemin, zancen ganin Abba kuma ya kamata ka fara ganin Yaya Musaddiq dai first nake ga”.
Sosai ya sauke numfashi mai nauyi, sai kuma ya amsa da, “Okay hakan ma yayi, zan bari to sai gobe in sha ALLAHU na samu Yaya a gareji”. Daga haka ya buɗe min. Wuff na fice abina kuwa. Batare da ko sallama nayi masa yau ba na shige gida, har lokacin kuma ina jin idanunsa a kaina. Ina rufe ƙofar gate ɗin na jingina a jiki ina sauke numfashi, sai kuma na kai hannuna saman ƙirjina da ke bugawa da sauri-sauri. Murmushi na saki kafin na buɗe idanuna a hankali na ɗan leƙa gate ɗin naga ko ya wuce. Sai lokacin naga yana ƙoƙarin yin reverse. Bazan ɓoye miki ba ina matuƙar ƙaunar Mansoor wlhy Bilyn Abdull, soyayya nake masa mai ƙarfin gaske da bama zan iya misaltata ba, dan Mansoor ya mun abubuwa na halacci da dama akan soyayya da bazasu iya ƙirgiguwa ba, na tabbata da aure kawai zan iya masa godiya a kansu amma bada fatar baki ko soyayyar saman titi ba.

Cikin gidan na shiga kamar yanda na saba, sai dai acan ƙasan raina ina ɗan jin tsoro-tsoro. Sosai na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ganin ban samu kowa a falo ba yau. Zuruf na shige ɗakinmu, in da na tarar da Bibaa kawai tana kallo a wayarta. Yanda bata amsa ko sallamata ba nima ban sake bi takanta ba. Wanka na farayi duk da kuwa cikin ƙyanƙyamin bayin nai haka, dan yanda ban wanke ba haka Bibaa itama bata wanke ba, sai ma datti da suka ƙara masa. Gudun kar lokacin sallah ya wuce min yasa ni saka doguwar riga kawai na saka hijjab na tada sallar. Na kai raka'a ta biyu ina sujidar ƙarshe kawai naji saukar duka kaina. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un wata irin azabace ta ratsa ni, amma na daure sosai na cigaba da sallata. Abinda kuma zai baki mamaki ba'a daina dukan nawa ba har na idar. Karo na farko kenan dana ɗaga hannu sama ina kuka da neman sakayya wajen UBANGIJI na, ina ƙoƙarin shafa addu'ar dai dai nan Abba ya shigo kamar wanda aka jeho.
“Haba Jalilah minene haka? Baki da hankali ne tana salla kina dukanta”. Ya faɗa a matuƙar hasale yana riƙe bulalar. Basu ba hatta ni sai da na shiga shock, dan nidai nasan ba yau ne karan farko da Mum take dukana ba a gidan nan. Hasalima ta dakeni a gabansa a lokuta barkatai amma bai taɓa cewa komai ba. Bama ni ba, hatta da Yaya Musaddiq yasha shan duka a wajen Mum, yanzu ne dai ta daina sai zaginsa da baƙar magana. Hakama Hafizzullah, sai dai duk ni na fisu shan wahala kasancewar akoda yaushe ni ina cikin gida a tare da su....
Mum ce ta katse min tunani na, dan cikin hargagi ta hayayyaƙo ma Abba a gabanmu. Idan ni bazata ji nauyina ba ai ya kamata taji nauyin su Babie kasancewar sa na mahaifinsu. Amma ko'a kwalar kwagirinta. Dan sai da takai ya koma bata haƙuri da lallashinta. Ni al'amarin nasu ma sai ya nema fasan kaina dan al'ajabi. Haka dai ya jata da ƙyar suka fice a ɗakin. Harara Baby ta watsa min da faɗin, “Shegiya mayya. To kurwar iyayenmu kur wlhy. Kuma indai Mum ce kaɗan ma ta miki wlhy, bari dai Abban ya fita duk da ma ko yana nan zata iya cigaba da cin ubanki, yanzu ɗin ma ta ƙyaleki ne kawai kiji da wannan tsamin jikin mtsowww makwaɗaitan banza da wofi anzo an cika mana gida an hanamu rawar gaban hantsi”. Daga haka ta fice kamar iska zata ɗibeta. Dan sam Baby bata da wani jikin kirki, ta girman amma na fita cikar halittar jiki sosai, wanda ma bai sani ba sai ya ɗauka nice babbarta. Sai da suka gama zageni tsaf ita da Bibaa suka fita sannan na fashe da kuka, dan illahirin jikina raɗaɗi yake min sosai. Da ƙyar na iya tashi na zare hijjab ɗina, abinka da farar fata wasu wajen ma har sun fashe. Cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeni, haka na kwana ina makyarkyata ga ciwon jiki. Duk kiran da Yaya kemin a waya ban ɗaga ba, har ya gaji ya daina kiran, nasan dai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login