Showing 78001 words to 81000 words out of 90697 words

Chapter 27 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull.txt

24 Nov 2024

3986

duk wani makircin masu makirci ƙarfin addu'a yayi tasiri dan gashi UBANGIJI ya dawo da ita gida a lokacin da magauta wannan aure basu so ba. Kuma in sha ALLAHU babu fashi ranar juma'a iyanzu tana nan da igiyoyi uku a kanta”.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Mansoor ya sauke yana mai lumshe idanunsa. Yayinda Mamyn sa tai ɗan murmushi kawai. Hakama Dad ɗinsa da su Kawu Lurwanu duk murmushin sukayi. Attahir kuwa mintsinin Mansoor yayi yana kashe masa ido ɗaya cike da tsokana. Hakama ƙannensa Islam da Sakeena dake zaune kusa da Samraah duk murmushin sukayi. Aiko Mum kamar zata haɗiyi zuciya, amma dai ta danne tana murmushin yaƙen itama kamar kowa. Abba ma baice komai ba, da ga ƙarshe ya wayance da an kirasa a waya ya fita yana amsawa. Yaya Musaddiq ma a hankali ya dinga sakin ajiyar zuciya jijiyoyin kan nasa na saki sannu-sannu, dan koba komai amsar da Gwaggo ta bama Mum ta fanshi duk wani ɗaci da fushin daya yunƙuro masa. Ni dai kaina a ƙasa ina satar kallon Yaya Musaddiq, zancen Gwaggo ya sakani jin kunyar kowa dake ɗakin musamman ma family ɗin Mansoor. Dan dama tunda suka shigo ban sake yarda na kalli kowa ba. Ko magana da ƙannensa ke mun ƙasa-ƙasa ɗan murmushi kawai nake musu. Lokacin sallar magrib kowa ya watse. Iyayen Mansoor da ƙannensa suka wuce. Hakama Mum da su Kawu Lurwanu Yaya Musaddiq ya tafi kaisu masauki. Shi dama Abba tun wayar nan daya fita bai sake dawowa ba. Su Baby kam har yanzu ban gansu a asibitin ba. Dan ko Abbas dake matsayin babbansu bana jin yama zo dubani, koma basu san na dawo bane oho, koda yake da wuya ace hakan ta kasance gaskiya.
Daga ni sai Gwaggo Gudidi aka bari, sai bayan sallar isha'i ne Yaya Musaddiq da Mansoor suka dawo. Babu jimawa da shigowar tasu sai ga d.c.o da yaransa guda biyu. Sun nuna jin daɗinsu na ganina garau yanzun, dan doctor ma yace zai sallaman da safe tunda banda wata matsala a tare dani, sai rashin ƙarfin jiki na allurar da suka min, tun ma a daren yay niyyar sallamata Mansoor ya ce a barni sai washe gari dai na sake jin ƙarfi da kuzari. Mun gaisa da su suka jajanta min kan abinda ya faru. Kafin d.c.o ya tabbatar min dana kwantar da hankalina na kuma basu haɗin kai mutanen nan ko su waye su sai sun kamasu an hukuntasu.
Amsa masa nai kawai da kaina dan nasan abinda yake faɗar bamai yiwuwa bane ba. Wani ma idan nace ga wanda yay kidnapping ɗina cazai ƙarya nake yi. Su kuwa koda ma sun san gaskiya babu abinda zasu iya yi ɗin kamar yanda yake faɗa. To shi hatsabibin aljanin ma zai basu wata ƙafane da zasu gane shine, dan magana ta ALLAH al'amarin mutumin nan ya fara sakani a firgici, dan bana jin na taɓa cin karo da makirin mutum, hatsabibin gaske da ko tsoro bazaka taɓa karanta a yanayinsa ba irin wannan mutumin. Ga shi yayta wani shan ƙamshi cikin gadara da karfin iko kai kace shike mulkar ƙasar. Ta wani ɓangaren kuma ina buƙatar rayuwar ƴan uwana. Dan wannan mutumin babu shakka zai iya aikata abinda ya faɗa koma fiye da shi tunda na gani da idona sanda yake zare wuƙa a jikin wani. Ga kuma abinda Nurse ɗin nan tace, a duk inda muke yana biye damu ƙafa da ƙafa. Zan kare rayuwar ƴan uwana kamar yanda yay min barazana, sai dai fa idan yasan wata baisan wata ba. Nayi alƙawarin saina ƙullama rayuwarsa tarkon da bazai taɓa iya kuɓutar da kansa ba. Dan saina tabbatar masa da *_TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE_* da ƴar Abdul-wahab Gwarzo yake magana. Nashi kuma wasa ne, bai san mi ake kira kaidin mata ba sai na tabbatar masa.....
Taɓanin da Yaya Musaddiq yay ya sani dawowa hayyacina firgigit. Cike da kulawa ya furta, “Tunanin mi kike anata magana Samraah?”.
Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, sai kuma cikin sanyin murya na ce, “Ba komai Yaya. Kuyi haƙuri”.
Baki ya buɗe zai sake magana naga ɗan sandan ya masa alamar ya barni. Shirun kuwa yayi, suma sai sukai mana sallama akan zasu wuce. Amma an ajiye ƴan sanda biyu domin tsarona gudun abinda zaije ya dawo. Godiya Mansoor da Yaya Musaddiq da Gwaggo suketa jera musu, ni dai bance komai ba face zamewa na kwanta kawai. Dan a ganina bani ke buƙatar ƴan sanda ba Yaya Musaddiq da Hafizzullah ne. Tunda idan sake niyyar saceni yay nikam nasan abune mai sauƙi a garesa. Nama fara zargin bayan Nurse likitan ma nasa ne. Kai kowama dake asibitin kallon yana da alaƙa da shi nake yanzu. Sai dai ban san ta yanda zan fito na faɗi hakan ba kuma a fahimta a kuma gaskata ni.....


💢💢💢💢💢💢💢


Agogon dake bangon ɗakin ta sake kallo a karo na barkatai, sai kuma ta ja sirrin tsaki. Ɗagowa mijin nata yay ya kalleta. Ganin yanda ta ɗauke kai gefe ya sashi faɗin, “Lafiya kuwa kike Safina?”.
Kanta ta ɗan girgiza, cikin nuna damuwa ta ce, “Ba komai. Yaron nan ne dai al'amarinsa ya fara bani tsoro. Kalla agogo maganar ɗaya ake na dare amma har yanzu bai shigo gidan nan ba. Hakan na nufin a asibitin zai kwana ko mi?”.
Agogon ya kalla shima, sai kuma ya ɗauka wayarsa batare da yace mata komai ba. Kunnensa ya kai alamar kira yake bayan yay ƴan danne-danne. Ana ɗagawa kuwa bayan amsa sallama ya ce, “Ɗan uwanka bai dawo gidan nan bane har yanzu Attahiru?”. Ɗan jimm yay alamar saurare. Sai kuma ya janye wayar batare da ya sake cewa komai ba. Kallonsa Mamy tayi cikin ƙagara ta ce, “Bai dawo ba ko?”. Kansa ya jinjina mata alamar eh. Zai cigaba da aikinsa a computer ta dakatar da shi. “Ya kuma zaka cigaba da aiki ka dadynsu? Ka kirashi ɗan ALLAH mana muji yana ina”. Kafeta yay da ido na tsawon sakanni. Sai kuma ya girgiza kansa da faɗin, “Mansoor yaro ne ƙarami Safina. Karki manta shirin ɗaura masa aure fa ake nan da kwanaki huɗu. Kinga ko ai yasan abinda yake ko”.
“Nifa gaskiya Daddynsu bana wani jin batun auren nan a raina yanzu. Kuma dama can kaima kasan dan ya nace ne akan yarinyar nan yasa ka zuba ido da kuma dagewa da nayi nima saboda yarinyar ta shiga raina da farko. Amma magana ta gaskiya maganar matar kawunta ta ɗazun ta shigeni matuƙa. Shiyyasa tunda na dawo gidan nan naketa auna abubuwa. Dan zancen abin a duba ne fa, musamman idan muka tsaida hankalinmu muka nazarci komai a yanda yake”.
Idanu kawai ya zuba mata kamar zai cinyeta da su. Itako ta ɗauke kai tana wani kum-kum da fuska tabbacin zancen nata fa tun daga zuciya ne.
“Safina kin san kuwa mi kike faɗa? Kin san fa yanda ɗanki ke matuƙar son yarinyar nan. Idan har a baya na kasa hanashi dake kanki a yanzu mi kike tunanin zan iya? Naga kece kika zaƙe da faɗar ƙyawawan halayyar yarinyar a baya duk da ni na nuna batai min ba. Ina baki shawarar kawai ki bisu da addu'a kamar yanda kika saba tun farko. Maganar matar kawunta kuma ai ba lallai ne ya zama gaskiya ba. Tunda ba'a san wani kalar kidnappers ne suka kamata ba.....”
“Oh amma yallaɓai su Kidnappers ɗin har suna da wani banbanci da juna ne?. Ai duk wanda akace kidnapper to Kidnapper ɗinne kawai babu wani ba rabe a ciki. Na kula yanzu ba gane maganata kake ba, bayan kuma ada ba son yarinyar kake ba, ban san miya canjaka a yanzu ba kuma. Amma dai ka zauna kayi nazari kaima. Wlhy sam babu alamar wahala a tattare da yarinyar nan. Sai ma uban haske da ƙyau data ƙara duk da kuwa sau biyu na taɓa ganinta ido da ido. Amma ai biye nake da program ɗinta duk sati a gidan tvn su.”
Shi kam dai Dad ɗin su Mansoor yama kasa magana. Dan mamaki ma da al'ajabi matar tasa ke bashi yau kam. Sai yake ganin kamar ma ba ita ba. Irin wannan kafiya haka har ina kuma. Anya kuwa ba wani ne ya zugata ba?. Bashi da mai bashi amsa. Dan haka ya girgiza kansa kawai yana ƙoƙarin manyan abubuwan dake ransa tare da haɗiyesu a zuciyarsa da ga shi sai UBANGIJINSA. Gudun damuwarta saboda tanada hawan jini ya sashi sassauta nasa yanayin, cike da kulawa ya ce, “Tom naji zanyi nazari kamar yanda kika ce in sha ALLAH. Kuma zan yi bincike. Shima ɗan naki bari na taɓasa a waya. Ki kwanta ki huta kema”. Kafin ma tace wani abu ya ɗauka wayarsa ya fara ƙoƙarin kiran Mansoor........✍️




_Tofa wata sabuwa masu karatu🥱_




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_




......Yana kai wayar kunnensa dai-dai nan ma yake jin horn ɗin motar Mansoor ɗin da ƙarar buɗe gate. Wayar ya sauke tare da ajiyar zuciya ya ce, “To Alhamdullah gashi can ma ya dawo ai. Sai ki kwantar da hankalinki
Ajiyar zuciya Mamy ta sauke kuwa. Ta yunƙura zata miƙe Dad ɗin ya zuba mata ido. “Ina kuma zaki?”. “Zanje na duba shi ne mana. Kofa abincin dare baici ba. Kasanshi kuma da abinci, inba tsaresa akai ba ba wani son ci yake ba”.
Kai Dad ɗin ya girgiza. Sai kuma ya ce, “Uhm kinga Safina zauna Please”. Babu musu ta koma ta zauna. Sake cemata yay “Kwanta sai da safe. Tunda dai Mansoor ba jariri bane balle kice baki gama rainonsa ba.” tasan halin mijin nata dan haka bata sake magana ba kuma. Sai dai zuciyarta gaba ɗaya tana akan son sanin a wane hali ɗan nata yake ciki. Amma tunda yace bazata je ba to bata isa fitarba kuwa. Shima dai hankalinsa ya sake maidawa ga aikinsa bai sake bi takanta ba kuma. Ga shi ya haɗe fuska dan bama ya son tace zata roƙesa ko ta takura masa da batun auren Mansoor ɗin kuma.....



💞🌟💞🌟💞🌟💞


Washe gari kamar yanda doctor ya faɗa aka sallameni. Gwaggo Gudidi taso wucewa da ni can Dawanau gidanta amma Yaya Musaddiq ya roƙeta kan ta barni na koma can gidan ɗin. Tunda har Mansoor yayi magana kan baya son a ɗaga bikin nan a yanda yake koda na kwana ɗaya ne kawai ayi a wuce wajen. Ya kamata kuma muje can gidan Abba a ƙarasa komai daya kamata kada halin Mum ya dameta. Badan Gwaggo taso hakan ba ta yarda.
Tarba muka samu babu yabo babu fallasa da ga Mum. Hakama su Baby na zaune a falo amma babu wanda yay min sannu ko nuna farin cikin dawowata garesu. Sai auta ne ya tsillo da gudu ya ruƙunƙumeni. Duk da miskilancin yaron sai da ya furta, “Adda nayi kewarki. Adda Bibaa tace kin mutu bayan sake ganinki ba ashe ƙarya take min”.
Murmushi kawai na masa tare da shafa fuskarsa. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “Ta mutu kuma? To in ALLAH ya yarda ba yanzu ba, mu bazamuga mutuwa ba sai alkairi nan da kwana huɗu. Ke kuma baƙin halin naki sak na uwarki dai ashe, da wani shegen goshinki kamar jirgin tsallake ruwan bagwai”. Ta ƙare maganar tana nuna Bibaa data tura baki gaba zomomo. Na zata Mum zatayi magana. Sai naji shiru ta dai sake tsuke fuska. Ni dai sai ma na yunƙura na nufi bedroom ɗinmu dan so nake na ɗan watsa ruwa ko zanji daɗin jikina. Yanda na tadda ɗakin kaca-kaca sai da ƙirjina ya buga. Abu sai kace turken dabbobi. Wai ni yaushe Bibaa zatayi hankali ni Samraah. Na jima tsaye zuciyata cike da takaici ga ƙyanƙyami dan bazan iya zama a ɗakin ba. Dole na juya na fita cikin ƙarfin hali da son ƙarfafa kaina. Har yanzu duk suna a falon, Gwaggo Gudidi tai saurin faɗin, “Ya kuma kika fito Samraatu lafiya dai ko?”.
Kaina na jinjina mata a yanayin rashin ƙarfi jiki, cikin yamutse fuska na ce, “Gwaggo zan ɗakko kayan shara ne ɗakin yayi datti ina jin ƙyanƙyami”.
Dukansu sai da suka ɗago suka kalleni. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “To kaji kuma wani sheɗancin kuma, yanzu duk waɗan nan zagada-zagadan ƴan matan uwa wa ƴan matan amarya a gida ashe hotiho suke. Yo ni dama tunda na shigo naga gidan yamun wani harmutsai a ido nasan ana ƙwaɓa hauka dan har bashi-bashi da tsami-tsamin dauɗa nake shaƙowa ma. Yanzu ke Julaila kike ko mima oho miki bayan koyama ƴaƴanki rashin kunya abinda zai taimaki rayuwar tasu ma kin tauyesu basu iya ba. Komai kun tattara akan marainiyar ALLAH. To wlhy ba mugunta kikai mata ba idan ma ke haka kike tunani, su waɗan nan da kike gani ƴan hutu a gabanki su kika kashewa rayuwa, dan su zasu gurji kan ubansu nan gaba kaɗan. Zaku ma ki tabbatar da hakan ke da su ranar da tusa ta ƙarewa bodari, ɗiya mace bata iya komai ba ai bata cika mace ba wlhy, babu kuma namijin da zai juri zama da ita, idan ma ya haƙura ya jure dan yanada kuɗin biyan wasu suyi to bazata taɓa daraja a idonsa ba dan wataran ko shine ƙaruna akan kuɗi zai so matarsa ta masa hidima. Kai ai wlhy baki birgeba kuwa. Ashe ma fuggukar taki da ɗaga hanci kamar ƙofar gora na wofine” ta ƙare faɗa a fusace. Bibaa ta nuna da Baby “Ku dan ubanku Imamu ku tashi ku ɗakko kayan shara, ke kuma zoki zauna anan wazai barki kiyi wani aiki kina fama da kanki. Zakiyya ma na hanya gyaran jiki zata fara miki yau ɗin nan dan duk da gaki nan fes da ke ga kuma ƙarancin lokaci bazai hana nasa a kwaskware min ke ba dan kowa ya sake tabbatar da amarya ƴar gata zan kai”.
Sosai Bibaa da Baby ke kallonta ransu a ɓace, sai kuma su kalla Mum da taƙi cewa komai. Tsawa ta daka musu, babu shiri suka miƙe a zabure kuwa. Nayi mamakin shirun Mum dan nasan yanda suke ƴar tsama da Gwaggo Gudidi, rashin jituwar tasu ma ce tasa Gwaggon daina zuwa gidan gaba ɗaya. Amma dai dole a wannan shirun nata akwai ayar tambaya.
Su Baby naji na gani Gwaggo ta turkesu sukai gyaran ɗakin, sau biyu tana maidasu su maimaita wai bai mata ba. Bayan sun kammala sunata zungure-zunguren baki tasa Bibaa ta tattara kayanta ta maida ɗakin Baby. Shima auta aka haɗa masa nasa aka sanda shi ɗakin Mum. Acewar Gwaggo nan sune zasu zauna har sai biki ya tashi. Ni dai dariya ma abin ke ban. Dan Gwaggo Gudidi fitinanniya ce sai dai idan bataso ba zaka ga ta watsar da kai kamar mai shiru-shiru. Halin namu dai na kamanceceniya sosai, ƙila dai ita na gado ma (🤣). Fuu Mum ta tashi batare da tace mana komai ba ta bar falon, mu duka da kallo muka bita, sai dai babu wanda yace komai.


“Mum na shiga ɗaki waya ta ɗauka, sai faman huci take da jan numfashi, kai daka ganta kasan dama danne komai take da ƙyar kawai. Ko sallama balle gaisuwa batayi ga wanda ta kira ɗin ba ta fara magana a hasale. “Mama magana ta gaskiya bazan iya haƙurin da kikace da wannan tsohuwar ba. Kinga daga dawowarsu yanzu tabi ta addabar min yara. Nidai bazan iya ɗauka ba. Wannan plan ɗin naki na fara jin kamar bazan iya juresa ba. Ina dalili yara tun suna ƙanana sun tare min komai yanzu kuma an saka min ƴaƴa a gaba duk da kwacen saurayi da akaima Baby”.
Siririyar dariya akayi mai sauti daga can. Sai kuma dattijuwar murya ta fara faɗin, “Jalila wani lokacin idan kina wani shashancin sai nake ganin kamar bani ce na haifeki ba. Ke matsalarki baki iya ɓoye abu aranki. Shiyyasa tun farko ko riƙon yaran nan nace ki yi na siyasa ta yanda koshi mijin naki bazai fahimci baki ƙaunarsu ko son zama daku ba. Amma ina kin kasa. Yanzu kina ganin matsala ta taso kaso biyu bisa uku na mutane har yanzu ke suke zargi da satar yarinyar nan har da ƴaƴanki. Ko ƴan sandan nan idonsu kema na'a kanki. Amma kin kasa fahimta. Ko shi mijin naki badan mun danne masa kai ba tuni kina ganin bake zai zarga ba ne? Shin wai rayuwa babu siyasa ta yiyu haka ne?”.
“Wai Mama sai kice siyasa, siyasa. Dan kawai ina son na birge wani sai na dinga nunawa wanda bana so so. Nidai a bar wannan maganar, kawai ki faɗa min abinda zanyi na gaba dan na fara ƙosawa da halin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login