Showing 45001 words to 48000 words out of 90697 words

Chapter 16 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull.txt

24 Nov 2024

3983

Cikin taɓe baki na ce, “In dai ba mala'ikan mutuwa ne zai zo ba kuma dai Usman ai shirina yayi”.
Dariya ya sanya ƙasa-ƙasa. Ni kuma na cigaba da duba takardar hannuna. Goma da mintuna hamsin da biyar dai-dai Tsanyawa ya shigo yana sanar mana gasu nan tafe shi da MD. Sake kimtsawa kowa ya shigayi, banda ni kam, dan ko motsi banba daga yanda nake zaune balle na cire idanuna daga takardar dake a hannuna. Duk da face mask dana saka bai hana turarensa dukan hancina ba. Wannan dai fitina da yawa take, nikam bana rabe muku ɗayan biyu shima turaren na jinin tsafi ne shiyyasa yake danne ƙarfin duk wani turare idan mai shi yana waje. To nidai gaskiya ba yafewa zan ba, dan nawa kamfanin turaren suna iya nasu ƙoƙari suma. Jin yanda ɗakin yay tsitt kamar babu mutane yasa takaici sake kume ni. Chewing gum PA ɗin nan nasa ne ya fara shigowa, dole ne a kirasa chewing gum saboda koda yaushe dai yana manne da shi. Kusan a tare suka shigo da MD, sai wani rawar jiki yake da ƙanƙan da kai abin takaici. Duk wanda ke a zaune miƙewa sukayi, banda ni da takaicin MD ya sani ɗauke idona da nake musu kallon ƙasa-ƙasa da ban san mike faruwa ba. Ashe su Usman da ke zaune a inda nake duk sun tashi wai domin girmamawa.
“Samraah!”.
MD ya kirani ƙasa-ƙasa, banji ba dan haka Usman dake tsaye ta gefena ya ɗan bubbuga kujerar. Da farko sharesa nayi, dan nazata surutunsa ne ya tashi, ganin ya cigaba na ɗago ina harararsa. Idanunsa ya ɗan rumtse cikin yanayin matse fuska tare da mun nuni da MD ƙasa-ƙasa. Sai lokacin na lura da kallon da MD ɗin ke mun. Kowa na ɗakin nabi da kallo, ganinsu duk a tsaye shi kaɗaine zaune a inda za'a gudanar da program ɗin PA ɗinsa tsaye a kusa da shi ya ɗan ranƙwafa yana nuna masa abinda ke cikin tab ɗin hannunsa ya sani miƙewa batare dana sake kallon MD ba na ce, “Sorry Sir”.
Kansa kawai ya ɗan girgiza da mun nuni da can ɗin. Komai ban sake cewa ba na wuce inda zai kasance nawa mazaunin. Kujeru ne guda biyu kacal suna ɗan facing juna kaɗan, sai table a gabansu an ɗaura glass cup guda biyu masu ɗauke da ruwa, sai dai an rufe su da ɗan ƙananun fai-fai. Ta ƙasan ido na ɗan kallesu dan koda na zauna ban tanka musu ba ban kuma cire face mask ɗin fuska na ba. Yau ma dai suit ɗinne jikinsa milk colour, rigar ciki, belt da takalmansa ne kawai suka kasance coffee. Sai wani almurin agogo dake hannunsa da duk da ban san kuɗin agogo ba a kallo guda zaka san ba'a sayesa da kuɗi kaɗan ba. Dan coffee fatarsa ma kawai ka kalla kasan ba'a magana. Yau ma babu kitso bai kuma ɗaure gashin ba. Ya sakesa ne kawai baya ya sakko masa har akan kafaɗa kaɗan, akwai kuma coffee ɗan kunne ɗaya a kunnensa na dama yau ma ya manna. Sannan babu neck tie, maɓallan ma rigar cikin ta sama a buɗe suke.... Umarnin cire face mask ɗin fuskata da aka bani ya maidoni hayyacina. Cikin taɓe baki na janye idanuna dake cikin eyeglasses daga kansa ina yin abinda akace ɗin, dan lokacin fara gabatar da shirin yayi. Shima PA ɗin nasa wajen ya bari, yayinda ɗaya daga cikin abokan aikina ya ƙaraso gabansa, cike da ladabi ya maƙala masa abin magana a jikin jacket suit ɗinsa. Nima miƙomin yay na maƙala a jikin hijjab ɗina. Sai da aka tabbatar mun gama kimtsawa sannan aka ɗora camara a kanmu. MD ne cikin yanayin marairaicewa yay mun alamar na ɗan saki fusakata, jinai kamar na hararesa, amma na dake kawai cikin basarwa. Kamar bani ba, tuni yanayina ya koma zuwa sauƙaƙa fuska, sai da na kalla camara naima masu kallo sallama tare da gaisuwar barka da wannan lokaci da musu albishirin shiryawa tsaf domin ganin babban kamun da wannan shiri yayo musu yau a bazata sannan na juya garesa a yanayin jan class ɗina na ce, “Assalamu alaikum ranka ya daɗe”.
A hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa min da “Wa'alaikissalam” cikin muryar nan tasa a daƙile. Bazaka taɓa fahimtar kallona yake ko ba hakaba, saboda akwai eyeglasses mai duhu a idonsa. Yinai kamar ban damu da abinda yay ɗin ba nima, na cigaba da faɗin, “Wannan shiri na maka barka da zuwa, tare da nuna farin ciki matuƙa na cika alkawarin amsa gayyata a cikinsa a lokacin da kowa baiyi zato ba. Na tabbata hatta masu kallo ma zasu kasance cikin farin ciki maybe ma harda mamaki. Amma dai barkan ka da zuwa”.
Nan ma a takaice ya furta, “Barka. Tare da fatan alkairi ma kowa”.
(Ɗan rainin hankali) na faɗa a zuciyata. A zahiri kam na ce, “Masha ALLAH. To masu kallo, zan iya cewa duk sai ku sake matsowa gaban akwatinan talabijin naku, masu rediyo su ƙara sauti domin ji daga bakin babban baƙon namu.” Sake juyowa nai garesa ina faɗin, “Ko zamu iya sanin cikakken sunanka ranka ya daɗe?”.
Cike da wani salo da sake harɗe ƙafafunsa da yay crossing cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Awwab El-Mu'azz K/Mashi. Sai dai Maash akafi sani”.
“Aiko nasan masu kallo zasu so sanin minene ma'anar Maash ɗin nan ranka ya daɗe?”.
Sai da ya bushi iska na wasu sakanni sannan yay wani ɗan murmushin gefen baki, a taƙaice ya ce, “Kwanar Mashi ne ainahin sunan tushena kenan, abokai suka maida shi Maash tun ina secondary school, daga nan kawai ya zama ana kirana da shi”.
“Uhhm Masha ALLAH. To ko zamu iya sanin wanene Maash a takaice. Dan wannan amsa ce da mutane suka jima suna son ji daga bakin ka amma basu samu damar hakan ba?”........✍️






_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_








_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_






_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_




.......Ɗan jimm yay kamar bazai amsa ba, sai kuma ya kai hannu ya shafa ƙasunbarsa. Duk da glasses dake idonsa sosai nake jin kaifin idanun nasa yanzu kam a kaina. Amma sai na basar. Cikin yanayin rashin mafita da gurɓataccen harshensa ya bani amsa yana gwamutsa hausa da turanci sai na gyara masa ma wani lokacin.
“Awwab El-Mu'azz shine Maash. Asalin ɗan jihar Kano girman Lagos. Karatu zuwa matakin masters, wasu courses sun biyo baya duka dai a fanin kasuwanci. Ɓangaren karatun addini ma Alhamdullah. A yanzu haka business man”.
“Masha ALLAH. A yanda dai kake bayanin zabbirgewa, da daɗin saurare, sai dai a zahirance kafin aga Maash a haka nasan ansha gwagwarmaya bata wasa ba. Tare da ƙalubale kala-kala. Shin yaya ma akai ka fara kasuwanci?”.
“Business tamkar logo ne na family ɗin Ummie na. Kusan zan iya cewa na gada ne daga wajenta. Dan tun ina mitsitsi na nake ganin yanda take tsaye akan ƙafafunta ita da mahaifinta, grand father ɗin a kenan, sai hakan ya zaburar dani tashi akan wannan burin, kuma Alhamdullah yanzu an cimma buri. Batun ƙalubale kam ga duk wani rai mai numfashi koda bai tashi da nufin motsawa ba sai an fuskanta, amma Alhamdullah komai ya zama tarihi, dan ko yanzu haka an cimma burika da yawa harma da waɗanda ba'a tsara za'a cimmawa ba”.
“Gaskiya ne to Alhamdullah. Kafin yanzu Maash na kiran kansa ne kawai da suna bakano ɗan arewacin Nijeriya, sai dai mutane na ƙorafe-ƙorafe game da ko gidan kiwon tsuntsaye bai taɓa samarwa a arewacin ba duk da yanda ALLAH ya baka damar baza harkokin kasuwanci a duniya. Sannan ko cikakken Hausa ma bai iya ba. Shin ko Maash nada wani dalilin hakan?”.
“So babu wani dalili gaskiya. Kawai lokacin yin hakan ne baiyi ba, amma yanzu yayi ai gashi mun fara. Za kuma mu cigaba da yi in sha ALLAHU. Batun yare kuwa kowane ɗa kan fara tashi ne da yaran mahaifiya. Kasancewar mahaifiyata ba yarenta bane yasa na samu rauni a kansa, amma nasan ko yanzu zan iya fafatawa da kowa a kansa”.
Dariya maganarsa ta ƙarshe taban. Amma sai na dake na ce, “Kai ashe kace mu sake shiri bayan Companyn ƙera motoci akwai wasu ire-iren sa tafe ma kenan?”.
“Haka muke fata a cikin tsare-tsaren mu.”
“ALLAH ya cika buri”.
A saman lips ya amsa min da “Amin”.
“Mi ya ja hankalin Maash buɗe katafaren Company irin haka a Kano da ba'a taɓa zato ba? Sannan ko Maash zai iya dawowa da rayuwarsa garin Kano gaba ɗaya?”..
“ALLAH ya rubuta anan ɗin ne za'a samar da shi. Idan ALLAH ya ƙaddara hakan kuma game da dawowa ɗin mizai hana”.
“Ko Maash nada aure?”.
“A kasuwa yake”.
“A saka tallarsa kenan ko za'a samu wacce zata saya?”.
Fuska ya ɗan tsuke. A ɗan daƙile ya furta, “Ba'a gaji dani a gidanmu ba ai”.
(Wama zai so ka ɗan rainin wayo) na faɗa a zuciya. A fili kuwa sai na murmusa kawai na cigaba da faɗin, “Miyasa Maash baya son hira da ƴan jarida duk da suna ƙoƙarin ganin anyi hakan kodan tarin masoyansa da matasa irinsa da ake fatan su kallesa matsayin madubinsu?”.
Shiru yay baice komai ba, kusan minti ɗaya sannan ya furta, “Nothing”. A daƙile.
Nima a karan farko na ɗan kafesa da idanuna dake cikin glasses mai haske, dan sam ban gamsu ba. Amma sai MD dake bayan fage yay min nunin na barsa. Jinai kamar na dalla musu harara su duka. Amma na dake na cigaba da faɗin, “Wane kalar kaya Maash yafi so?”.
“Kowanne”.
“Abinci?”.
“tuwo”.
Wani kalar ɗan waro manyan idanuna nai waje a kansa. Shi kuma ya ɗan ɗauke kai cike da basarwa. Nima sai na ɗan basar ɗin kawai. Na cigaba da faɗin. “Wace shawara zaka bama matasa irinka dake tasowa?”.
“Su zama masu jajircewa, juriya akan duk abinda suka sa gaba, dan kayi karatu ba dole sai kayi aiki ba. Dan ka fara business ba dole sai kayi kuɗi kamar ƙyaftawar ido ba. Ka kasance mai Gaskiya akan komanka, neman zaɓin ALLAH da haƙuri akan halak duk ƙanƙantarsa. Ka kuma zama mai tarin wadatar zuci, dan in babu wadatar zuci ko zaka cika duniya da dukiya zakaita jin baka gamsu ba ne. Shaye-shaye baida wani amfani face maida matashi bayan baya a cikin al'umma. Shi iskanci ba'a koyansa, kowa da kake gani zai iya yi, zama mutumin kirki shike da matuƙar wahala, sai mu faɗama kammu gaskiya kafin duniya ta faɗa mana”.
“Masha ALLAH muna godiya da wannan shawara. Minene buri, ko nace shirin Maash na gaba?”.
“Maash nada tarin burika da shirye-shirye masu yawa da shi kansa bai san adadi ba. Amma manya daga cikinsu a dai yanzu sune samar da companys da zasuna fitar da abinci kowane nau'i in sha ALLAH. Zamu fara tsara komai a yanzu haka, muna fatan kuma zuwa ƙarshen shekarar nan komai ya zama ready”.
“Ko zamu iya sanin a ina wannan babban project ɗin zai kasance?”.
“Duka anan arewa ne in sha ALLAHU. Amma sai lokacin yayi za'a sani”.
“ALLAH ya cika buri”.
“Amin” ya amsa a taƙaice.
“Mi Maash yafi so a rayuwarsa?”.
“My Parents”.
“Miye baya so?”.
“Cin amana”.
“ALLAH ya hanemu zama masu fuska biyu” na faɗa a yanayin kalma mai harshen damo ina ɗauke kaina daga kansa. Juyawa nai ga camara, fuskata ɗauke da ɗan murmushi na ce, “To masu kallonmu, gadai hira ta kwararo cike da daɗi, sai dai lokaci ya mana tsiyar tasa. Amma zance ku zama a cikin masu fatan wataran Maash ya sake zama a wannan kujerar domin amsa muku tarin tambayoyin dake a ranku da bamu kawo a wannan dandali ba yanzu saboda ƙarancin lokaci. Amma dai, ko a hakan ma mun gode, dan ALHERI TV ta kafa babban tarihi”. Sake juyawa nai garesa, na ce, “Ranka ya daɗe mun gode sosai da cika alkawari. Muna fatan ALLAH ya maidaka gida lafiya. Zaka iya yin sallama da masu kallo suma”.
Hannu kawai ya ɗaga yana mai sakin murmushi kaɗan ya ce, “Fatan alkairi”.


Ana ɗauke camara daga kammu ya wani sauke numfashi mai ƙarfi yana furzar da shi tare da jan siririn tsaki. Yinai kamar ma ban san da shi a wajen ba. Dan kafin ya tashi tuni na miƙe ni ina ɗaukar ruwan da aka ajiye mana da babu wanda yasha nabar wajen. Ban tsaya a ɗakin ba na fice gaba ɗaya. Office ɗinmu na koma. Bayan kamar mintuna sha biyar sai ga su Asiya sun shigo. Baibayeni sukai su duka har Usman da Khalid. Kowa na jinjina ƙoƙarin da nayi. Tare da nuna zumuɗinsu na fatan zuwan randa za'a saka shirin wa kowa dan su sake kallonsa a tsanake. Murmushi kawai nai musu nidai bance komai ba. Aikinmu muka cigaba dayi, har lokacin sallar Azhar yay muka fito gaba ɗaya. Bayan idar da salla kamar yanda muka saba na haɗu da Mansoor. Fita mukai restaurant ɗin kusa da ma'aikatar tamu cin abinci kamar kullum. Kusan a tare muka shiga da wani saurayi shima fuskarsa da fase mask. Bai mana magana ba bamu masa ba, kowa ya nema wajen zama ya zauna.
Munci abincinmu cike da nishaɗi muna ƴar hirarmu. Bayan mun kammala muka fita. Mun koma office kan ayyukanmu. Banfi zaman mintuna biyar ba sai ga MD har cikin office ɗinmu Harun biye da shi. Duk miƙewa mukai domin girmamawa a garesa. Fuskarsa ɗauke da murmushi yay mana alamar mu zauna. Shima ya zauna a kujerar dake facing ɗina.
“Sannu da ƙoƙari jarumarmu”.
Ya faɗa idonsa a kaina. Sosai na waro nawa idanun dan mamakinsa. Kasa haƙuri nayi sai da na furta, “Jaruma kuma Sir, sai kace wata ƴar Film?”.
“Ba'a Film kawai ake jarumta ba Samraah. A yau kinyi namijin ƙoƙari ƙwarai da gaske. Na tabbatar duk randa aka saki wannan hirar taku wa masu kallo ba ƙaramin tada hazo zatayi ba. Domin Maash yayi abinda bai taɓa kwatanta yi ba. Da ace kuma zan iya babu shakka sai na tambayesa ko miyyasa ya amince mana?. To amma ina, yana da wata irin kima da girma ga kwarjini mai saka shakkar koda kallonsa ne. Kin cancanci a kiraki kallabi tsakanin rawuna. Kuma in sha ALLAHU a dalilin wannan hirar zakiga babbar karramawa wa wannan gida dama duk wanda suka taimaka a ɗaukar shirin”.
Tafi su Khalid suka shiga yi cikin ihu. Yayinda MD ke faman washe baki shima cikin nuna a nishaɗi yake. Ni dai na tsaya kawai ina kallonsu ne galala. Su dai murnarsu kawai sukeyi basu bi takaina ba, Asiya ce ma dai na ɗan ga yanayinta ya canja, da alama abinda suke ɗin bai mata ba, ko kuma zantukan MD ne suka zafeta oho mata. Sallama MD yay mana ya fita. Ni dai na sauke ajiyar zuciya kawai. Yayinda Ruƙayya ta rungumoni. Duka na kai mata kaɗan, ta sakan tana dariya bayan ta ja min hanci. Babu shiri nayi murmushi nima. Ruƙayya nada kirki sosai. Sannan halayenta na matuƙar burgeni. Shiyyasa a wasu lokutan sai naji kamar nace ma Yaya ya nema auranta dan ALLAH su sasanta. Amma ina tsorom halin maza kada yace bata masa ba. Duk da dai nasan babu wani namiji da zai kalli Ruƙayya yace bata masan ba. Dan ƙyaƙyƙyawar yarinya ce sosai. Tana da haske gata ƴar duma-duma abinta. Itama ta taɓa gaya min mahaifiyarta ta rasu a wajen haihuwarta. Kuma ita kaɗai ta bari, hannun kishiyar uwa ta tashi. Duk da bata fito ta faɗa min duka matsalarta ba na fahimci bata jin daɗin zaman gidansu, sai dai haƙurinta yasa bazaka taɓa gane hakan ba kai tsaye sai in har itace ta faɗa maka.......✍️







_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
















*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login