Showing 24001 words to 27000 words out of 39630 words

Chapter 9 - WANE YARO !! BOOK COMPLETE BY NASRULLAH.pdf

29 Jul 2025

4260

zai warke.

★★★★★

Bayan gari ya ƙara waye wa, yanzu misalin ƙarfe 8am dai-dai na safe.

Doctor Sani, bai tafi gida hutu ba, da safe bayan ya gama aikinshi na dare.

Tafiya ya ke yana taku ɗai ɗai, da ya zo dai dai bakin ƙofar ɗakin, Saudat ita da mijinta Abban
Sadeeq suke ya tsaya nan baki ƙofar ya gyara shigarshi ya ya gyaran murya.

Shiga cikin ɗakin da suke ciki ya yi tare da sallama, Saudat da Umma idon su biyu sai itama
Saudat da dai ta ke ɗan gyan gyaɗi haka, suka amsa mai sallama, suka gaisa ina kwana ina
gajiya, ba gajiya ya ce, " ya mai jikin suka ƙara ji?, Allah ya basu lafiya ya ƙaro sauƙi ameen,
sanan ya koma kan Umma ya gaidata ya yi mata ya jiki"
Da shi kaɗai amma sai ga wata Nurse a bayan shi tana biye dashi, hannunta riƙe da takardu.

Ya fara gwajejen shi kan Umma ya gama sanan ya amshi takardun hannun Nurse ɗin nan ya
ciccike ya maida mata, sanna ya dawo kan Muktar shima ya diba shi ya taɓa jikin yaji akwai ɗan
ɗumi amma ya yi mamakin rashin tashin shi haka da wuri, haka da ya gama ya ciccike takardun
ya mai da ma da Nurse ɗin nan.
Sanna ya bata wata karamar paper ya ce, " ta rubata mishi number ta akwai wasu magungunan
da za,a siyo, idan ya koma office zai rubuta sai ya kirawo ta, ta zo ta amsa.

Ta amshi takardar ta rubata mai ta bashi, ya na amsa ya ce, " Allah ya basu lafiya, ya ƙaro sauƙi
ya sa kuma kafaffarane, ni zan tafi sai anjima, yauwa Umma Allah ya ƙaro sauƙi zan tafi" sanna
ya fice tare shi da Nurse ɗin.

Yacna fita babu daɗewa sai ga kiran wayarshi, bata ɗauka ba acikin ɗakin ba, ce ma Umma tai,
" bara naje na karɓo takardar magungunan ga kiranshi na gani"

" Ok sai kindawo "

Tana fita tayi nisa da ɗakin ta samu ta ɗaga kiran, ya fara mata maganar banza.

Ta ce mai, "Ƙaramin ɗan iska kawai wallahi ni nafi ƙarfin kayi amfani dani saboda haka ka shiga
tai tayinka domin ko ita rijia ba wurin wasa yara bane"

Uhmm ƙaramar yarinya ce,naga alama har yanzu saboda haka naga da alamun kamar kin
manta ɗaukar danai miki bara na turomimki sai kallah in yaso shima mijin naki ko da zuwa gobe
ne, zai san hakan"

Banza wawa kawai jakin banda kai daƙiƙi ne kamun sharri kuma harkake iƙirarin za nuna mai
video, zai karɓu wurin mijina, Am thank God bcos harda hotonka kaima ciki, kuma ni alamuna
bai nuna ina son hakan ka ke mun video ba, ba ra zana ce mana ka ke mun, saboda haka ka
gama kurarinka da wani abu, duk naka bazai hana yin komai ba.
Ji hakan da ya, yi da ga gareta ya zuciyarshi tai sanyi muƙut ya haɗiye miyau, ya ɗan numfasa
ya ce," mu zuba ni da ke "












Share
Comments
Fisabilillahi
07055852908
★★★★★★★★★★★★★★
[2/24, 3:15 AM] NASRULLAH ✍️: *WANE YARO*


BY
NASRULLAH

®
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

*♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/

*Sadaukarwa*
*Gareki*
```Maman haneef```

️1️⃣7️⃣

"Ya ki ka ga kalar ta kuna? Idan kin isa kisa shi ya tashi mana " " uhmm Allah sarki masu iya
magana suna cewa, ta yaro kyau take ba ta ƙarko, rai da rayuwa, rayawa da kuma macewa
dukkanin su suna hannun Allah s.w.t mai kowa mai wahidul ƙahar saboda duk wani maƙirci
daka shirya mun insha Allah kanka zai koma a sannu" ta ja wani tsaki mtssww....
Lallai ne yarinya wuyanki ya isa yanka, naga alama saboda haka duk wani jiji da kai da ki ke
zan cire miki shi, sai ki shiga tai tayinki kuma ki maza kizo office nawa ina jiranki"

Ya kashe wayarshi ya saki tsaki, "mtswww aikin banza kawai yarinyar nan ko uban wa ma ke
faɗa mata magana tana gaya mun oho? A suffarta ba zata iya aikata hakan ba, nasan ta za tai
taushi tiɓis shiyasa na tayata, ashe ba haka ba, ruwan dafa kaina na ɗebo"

Tsaye ya ke bai kai ga zama kan kujerar ba, daman ya na zuwa ciki ya rubuta magungunan ya
gama sanan ya ɗauko wayarshi, ya kira numberta.

Saudat tafiya ta fara lokacin da taji ya kashe kiranshi. Kai tsaye office nashi ta nufa, mai da
wayarta cikin “ya ƙaramar jakar dake hannnunta, ta cigaba da tafiya tana wasa da hannunta
har ta kawo office nashi a haka, tana wasa da hannunwanta.

Tun ɗazun ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai kawai da komowa yake wuri ɗaya, yana cizan
yatsanshi, irin abunan ya yi bala'in ɗaure mai kanshi!....

Saudat tana bakin ƙofa ta tsaya, ƙara gyara hijab nata tayi dakyau, ko ina na ilahirin jikinta
inda surarta ta bayyana ya gyara domin ma kada ma ya ƙara hango wani gun ya sake haɗiye
miyau domin ƙwalelenshi.

Sakin fuskarta tayi sanna ta kama hannun ƙofar office nashi, ta murɗa tare da sallama, ya amsa
mata sanna ta shigo ciki ta mai da kofar ta rufe.

Doctor Sani, wanda ta shigo ta tarar dashi ciki tunani, sai faman cizan yatsa ya ke yana zuwa
wuri ɗaya yana dawowa, ganinta yasa ya saki fuskarshi murmushi ya yi mata.

Cikin ranta ta ce, "uhmmm aikin banza harara a duhu kaji dashi dai idan kayane ka kai su
mtswww"

Gaishe shi tayi sanan ya ce mata, " haba ke kuwa ki saki fuskartaki manah" ya faɗi yana
murmushi.

Hmmm ta ce, "Bashi ya kawo ni ba, kawai ka bani abunda zaka bani ni na tafi, wanan kuma ya
rage naka" tana faɗin haka ta balla mai wata harara wanda harsai da razana.

"Ok badamuwa ai gashi kizo ki amsa" ya miƙo mata takardar da hannunshi.

Zuwa tai tana taku ɗai ɗai tana qani yatsina baki ta amsa ce mishi tayi,

"Waɗan nan magunganan wanda ka rubuta, sune z,a siya?"

"Eh sune"

"Ok ba matsala bara naje na siyo na barka lafiya sai anjima"

"Ina kuma zaki bamu gama magana ba?"

"Koh wacce maganar, daman muke, wanda ni bansaniba?"

"Hmm wato wani zubin wallahi ke “yar rai nin hankalince, amma bakomai karki damu a sannu
zan cire miki shi"

"Allah koh? Sai kai maza ai mugani"Mtssww

"Hmm toh shikenan tunda haka kika ce? Kije ki siyo maganin ki dawo, sai na nuna miki yadda
za,ai Amfani dashi"

"Ok toh"

"Shikenan yanzu zaki iya tafiya"

ta ja tsaki, mtswww tai wucewarta, fitowa tai daga ciki office nashi, tana lallai ma mutuminan bai
da hankali naga alama amma ni ce kilah, zan zama wacce zata gyara mai halinshi.

Anan cikin harabar akwai chemist haka nan, ta je ta siyo magungunan, ta dawo nan ofishin
nashi, ya bashi ledar maganin ya amsa ya na dariyar mungunta.hahahahaha

Cikin ranta ce wa tayi, "ka dai kayi kagama wallahi mtswwww"

Da ya amshi magungunan wanda suke a cikin baƙar leda, ya ware su wuri biyu wanann Umma
ɗayan kuma ma na mijinta ne.
[3/1, 8:44 PM] NASRULLAH ✍️: *WANE YARO*


BY
NASRULLAH

®

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

*♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/

*Sadaukarwa*
*Gareki*
```Maman haneef```


️1️⃣8️⃣

Saudat tana tsaye tana jin abunda yake cewa, kallonshi ta ke da idanunta, zuwa can ta balla
mai wata uwar harara, ta saki tsaki mtswww. Cigaba da kallonshi ta ke ta ce,
"Uhmmm naji nace sauran me kuma ya rage?"
Budar bakinshi ya ce, "bansaniba ai ko bakomai tunda nace miki have a seat, is better ki zauna
kiji mai zance koh?"
Cikin sansanyar murya ta ce, "Please doctor ba zama nan nazo yi ba, kawai nazo ne kaban
abunda nake da buƙata, da ga lokacin da ka sallameni shikenan tafiya ta zan, ba zama nazo yi
ba pls idan hakan ya ɓata maka rai kayi haƙuri, ba wai nayi da biyu ba ne ba ko wata manufa
kawai ina kare mutuncina ne, da kuma martabata" "Ke kin isa ki gayama mutane magana, ina wata martana da kima da mutuncin da ki ke magana
ki ke da su?"
"Ai ko ima da su da ko banda su bazaka ganni ba haka har niyyar abunda kaso na amince
maka ba ka aikata a gareni ba, kai karan kanka! Kasan da cewa bakin rijiya ba wurin wasa yaro
bane ba saboda wanan rijiyar ta damaka ta shanye, idan ma baka sani ba kasani kamin ƙaranta
wane kai Yaro!, haka zalika sama tayi ma Yaro nisa kamar yadda nima nai maka nisa, Wane kai
Yaro ɗan ƙaramin alhaki" Yatsanshi ɗaya yasa cikin bakinshi yana ciza tare da yarfewa yana
faɗin, "ke ki kalli tsabangen idanuna, ki kalle ni ki ce mun ni ne Yaro?"
"Emnah an faɗa maka ance ɗin kai Yaro ne kai abunda zakai ƙaramin mara kunya kawai daga
anzo nai man taimako wurin ka sai ka nemi ka cin ma mutane mutunci, ko ance makakowa irin
kane ɗan iska?"
"Lallaima ni ne yaron naki tunda haka ki ka ce ni kuma da banci mutuncinki ba yanzu ne zanci
mutun cin naki" ya taho da zafinshi tare da jefar da ledar maganin wuri ɗaya, cikin zafin rai da
ya nufo inda ta ke tsaye domin ko xama ba tai ba saboda ta ce mai wallahi ita ba zata zauna a
wanan tsinannan office ɗin nashi ba. Ta ce, "matso wallahi kana zuwa inda nake kana taɓa ni nima zan rama, kuma idan maganar
cin mutunci ka ke, wallahi sai da muci mutuncin juna amma badai kaci mun zarafi ba kaci bulus
na kyaleka ba wallahi" itama tuni ta murtuke fuskantar ta ɗaure.

Doctor Sani, bai kai ga
ƙarisawa inda take tsaye ba, jin tayi wanan furucin hakan ya dakatar dashi daga ƙarisowa inda

take, sannan ya numfasa yana faɗin, " Wallahi!...Wallahi!... Wallahi!.... Kinci darajar ke matar
aure ce, amma da wallahi yanzu nan babu abunda zai hanani banci mutuncinki ba" ya faɗi haka
cikin rawar murya da alamun shima ya tsorata da lamarinta.
"Karyar banza kawai sai anyi magana ka ce kai babbane, matsoraci kawai ragon maza, ko mata
maza ne ma oho?" ta faɗi haka ta tun tsure da dariya hahahhahahah. Da alamun ya razana
sosai da al'amarinta, nishi yake yana numfashi ƙirjinshin bugun uku-uku ya fara, kafin kace me
zufa harta tsatstsofo mai a jikinshi ya fara gumi arce, rashin gaskiyar shi ya fito fili, gaskiyarta ta
bayyana a fuskarta ƙarara.
Cikin fuskar rashin gaskiya da borin kunya ya ce, "Zan ƙyaleki ne kawai bai dan bazan iya
aikata abunda na faɗa miki ba, kawai sai dai dan cikin lokaci ɗaya naji tausayin ki a rai na
wanan shine dalilin kawai da zai sa nake ƙyaleki"
"Mtswww aikin banza kawai wai tsusayi na hahahahahaha, dan Allah karkaji tausayina idan ma
kaji ka dena ka aikata abunda kai niyyah mana" ta na gama faɗin haka ta ciro wuƙa ciki hijab
nata ashe da ta fita taje siyo magani, ba iya harabar asibiti taje ba har waje ta fita daga ciki
Asibitin ta ce mai, "Wallahi burin da nai kana ƙarisowa inda nake ka taɓani zan yanke ka da
wuƙar nan" ta mai nu ni da ita, ganin haka da ya yi kuma hannunta riƙe da wuƙa wacce ta fito
mai da ita, tunda dai tsakanin mafarauci da da abun hari suke tsakanin junansu a halin da suke
ciki, jikinshi ɓari ya kama sai faman wuri wuri da idanuwanshi ya ke, sannan ya tsaya ya ƙare
ma wuƙar nan kallo sosai ya ganta da kyau.

Cikin rawan muryar doctor Sani yana faɗin, "Tototoh shikenan (kamar zai barbara)tunda abun
da haka ya zo,ni na fasa abunda na ce zan aikata akanki kemah saboda haka ina mai roƙonki
pls ki mai da makaminki na janye muradina akanki.

Ta ce, "Wane yaro daman ni nasan da cewa, duk wani cicciko baki da ka ke na banza ne babu
abunda zaka iya"
"Naji dai maganar ta wuce yanzu zoki zauna na gama abunda zan haɗa miki nai miki bayani na
baki"
"Au bakaji ba kenan abunda na faɗa maka da farko kenan cewar ni bazan zauna a wanan
wukaƙantaccen office ɗin naka ba"
Ce mata ya yi, "I'm sorry pls badan ni ba dan Allah na ce, kuma ai yanzu da manufar ɗazun da
ta yanzu ba ɗaya ba"
Yana gama faɗin haka shima ya koma kan kujerar shi ya zauna, ganinshi da tayi ya yi sanyi,
yasa ta haƙura ta janye ƙudirinta akan ba zata zauna ba.

Saudat ta taho cikin fara'a sakin fuskarta tayi, sannan ta ƙarisa gaban teburin shi ta akwai
kujera ta zama mutane idan sun zo su zauna, itama nan ta zo ta zauna, kallonta ya yi suna
haɗa idanu da ita ya yi maza ya sunkuyar da kanshi ƙasa, diban da zai kawai ashe ɗazun yana
cikin zafin rai da zai nufo inda take, ashe ba kan teburin dake gabashin ya ajeta ledar da
magungunan ke ciki ba ƙasa ya jefar da ita akwai waɗanda suke cikin kwalba amma duk sun
farfashe kwalebanin, ganin haka yasa ranshi ɓaci.

Ya ce mata, " I'm sorry ɗazun ashe ledar ƙasana je fata ki hakuri bansaniba, amma bara na

kirawo Nurse sai na aiketa ta siyo mana wani buɗar bakinta tace, "Oky ba matsala" ya ɗauki
wayarshi ya kirawo Nurse.

Jim kaɗan suna cikin office ɗin shi da Saudat hira kawai suka kama suna hira abunsu, kamar ba
sune wanda ɗazu suke ca-car baki ba, haka dai sukai ta hira, suna cikin haka kwatsam sai ga
wanna Nurse ɗin daya kirawo ta zo nan tatsaya bakin ƙofar nashi tana knocked buɗar bakinshi
ya ce mata, " Yes come in" sannan ta buɗe kofar ta shigo ko da ta shigo ta ci ka raɓa da Saudat
a ciki, gabanta ras ya bata duk da dai bata san meke faruwa ba a tsakaninsu tana jin a ranta
cewa akwai abunda ke faruwa ko kuma yake shirin faruwa.
Tana shigowa ta gaishe da su sannan ta ce ma doctor Sani gani nazo kamar yadda ka umarta,
Doctor Sani jin haka yasa ya samun pieces ɗin takarda ya rubuta mata sunan maganin da zata
siyo mai ya bata, sannan ya ce mata wanan maganin zaki siyo mana awaje.





Nasrullah ✍️✍️✍️✍️
[3/4, 8:43 PM] NASRULLAH ✍️: *WANE YARO*


BY
NASRULLAH

®
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

*♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/

*Sadaukarwa*
*Gareki*
```Maman haneef```


️1️⃣9️⃣

Nurse ɗin ta amsa takardar ciki ladabi da biyayya, sannan ta fito daga cikin office ɗin nan ta
barshi shi da Saudat a cikin office tare suna hira ta barsu.

Cikin hikima Doctor Sani ya cigaba da satar kallonta sunayi suna hira, idan suka ɗan haɗa
fuska Doctor Sani murmushi yake mata.

Hira ta fara daɗi, tuni Saudat ta fara mancewa da abunda ya faru a tsakaninsu, ta fara sakin
jikinta dashi.

Haka suka cigaba da hira tana ma Saudat daɗi sosai, shiru ta mai tana sauraronshi tana jin
abunda yake cewa, kwatsam suna cikin haka again sai ga wannan Nurse din ta dawo daga inda
aka aiketa siyo magani. Kamar dai ɗazun da farko bata kai ga buɗe ƙofar ta shigo ba, nan ta
tsaya bakin ƙofar tayi knocked karo na biyu, sannan ya ce, "come in" buɗe kofar tayi ta shigo ta
zo dai dai bakin teburinshi ta miƙa mai sir gashi, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login