Showing 27001 words to 30000 words out of 39630 words
amsa ya ce mata, " Please thank you, zaki
iya tafiya shikenan"
"Ok sir thanks, na barku lafiya"
Ta buɗe ƙofar ta fito nan ta barsu ciki Doctor sani, ya buɗe ledar data siyo mai maganin ta
bashi, domin ko bai dibawa ba kawai dai yasan har indai ance ɗin ansamu to shine ilai kuwa
shine ɗin ko da ya diba, yasa hannunshi ya ɗauko maganin duk ko wanne ya ci roshi cikin
ledarshi ya gama zana musu dosage na shan maganin sanan ya yi mata ƙarin bayani ya haɗa
mata ya mai da mata shi cikin leda ya bata. Miko hannunta tayi ta amsa cikin fara'ah fuskarta
cike da annuri, ta mai sai anjima zata tafi kenan Doctor Sani ya dakatar da ita.
"Shikenan kuma sai ki tafi ke kaɗai kuma ko wada escort naki baki so? Haba ke kuwa ni da ke
ba faɗa muke ba mun shirya, mai zai hana nazo nai escort naki zuwa can kinga sai ma na sake
diba marasa lafiyan naga?"
Kallonshi tayi ta ce, "Hmm Okay to please sorry, yi haƙuri na shafa'a kuma bugu da ƙari yanzu
bansaniba ko za kai wani aikin ba, shiyasa kawai na ce na tafi da kaina tunda dai ba wani abu
bane ba"
"Don't mind duk da haka ko aikin ni dai idan kin bani dama ina son nazo mi dai nayi escort naki
pls kimun wanan alfamar" ya faɗa yana rokonta.
" Alright ba matsala na maka basai ai ta kaimu ga haka ba, wanda ya neme ka da abota to
masoyinka ne"
"Nagode Allah da ki ka gane hakan, keta musamman ce"
"Uhmm kamar ya dai, banda, tsokana fa?"
" Nima ba tsokana nake ba"
"Shikenan Allah yasa da gaske ne"
"Hmm ki dena tantama a kai na Allah ya riga da yasa hakan"
"Allah ko saurin me ka ke ne?"
"Shikenan bazan sauri ba"
"A'a ni dai amma mamakin abu ne nake samun canji farat ɗaya haka"
"Haka ne daman kisan shi yadda al'amarin Allah yake"
"Ƙwarai kuwa da gaske"
" Yauwa ko kefa kinga ya kamata mu wuce mu tafi, saboda naga alamun idan muka tsaya wasa
wasa hakan zai ci mana lokaci sosai"
"Ok Bismillah ko mu tafi" tana faɗin haka ta wuce gaba ya biyota a baya suka tafi.
*WANE YARO*
BY
NASRULLAH
®
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]
*♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
*Sadaukarwa*
*Gareki*
'''Maman haneef'''
️2️⃣0️⃣
Suna cikin tafiya, Saudat tare da Doctor Sani, Saudat wayarta ce ta fara ringtone dibawan da
zatai ashe ƙawarta ce farhat ta ke kiran wayarta. Suna cikin tafiya ta tsaya murmushi tayi cikin
ranta tana faɗin, "humm ƴar banza ƙawata sai yanzu kenan aka tina dani!" Sa hannunta tayi ta
danna ta ɗauki kiran nata.
Tana ɗauka kiran tasa wayar a kunnanta kenan, ƙawarta farhat tayi mata sallama, "Assalamu
alaikum" Saudat ta amsa mata da, "Ameen Wsalam" farhat ta cigaba da faɗin, " Y kk ƙawata
lafiya kuwa na jiki shiru bayan munyi da ke kuma zaki kirani ki bani bayanin magani akan
abunda kikaji naji ki shiru dafatan kina lafiya? Allah yasa hakan Ameen"
Saudat shiru tayi tana sauraronta ta ce, "Humm ke dai kawai ƙawata bari wani hanzari ba gudu
ba, yanzu haka ma muna asibiti ne Mai gidan nawa dashi da Mamanshi ba su da lafiya shiyasa
ma ki ka ji ban kira numberki ba, magani abun ba'ah magana kuma ba,ah cewa komai, domin
ko kuwa naji daɗin maganin nanki sosai matuƙa, basan ya ma zan misaltamiki ba"
"Ayyah Allah sarki sannu, wallahi ƙawata har naji tausayinki ya fara kamani, abun kamar ya miki
yawa ace kina jinyar mutum biyu a asibiti"
Kemah dai wallahi kin faɗa, ba'a cewa komai domin ko gajiya akwaita sosai, kin ganni nan tun
jiya da daddare nake a cikin asibitin nan hankalina a tashe,ba ni ce nasamu dama dama ba sai
yanzu da muke maganar nan da ke"
"Ayyah Allah sarki,ƙawata karki damu Insha Allah zasu samu lafiya,ke ma kuma ubangiji Allah
ya ƙara miki juriya da haƙuri ya baki ladan aikin da kikai"
"Ameen dai"
"Ƙawata bani labari nasha"
"Uhm ƙawata kenan? Wanne labari kike son na baki banda na asibiti, amma akwai labarin da
zan baki, yanxu ina cikin busy but later we 'll talk Insha Allahu"
Murmushi ne ya bayyana a fuskarta ta ce, "Alright bakomai tawajena na sanki baki da matsala"
Uhmm itama tayi murmushi buɗar bakinta ta ce, "Godiya nake tawajena bara mutsaya daga nan
haka, insha Allah wen Am free zakiji ni" tana gama faɗin haka sukai sallama ta kashe kiran.
Doctor Sani, da ke gefenta tsaye yana jiranta ta gama wayar su tafi, ganin da ya yi ta gama
wayar buɗar bakinshi ya ce mata, "Saudat" ta ce, "Na'am" tambayarta ya fara yi yana faɗin,
"wacece wanan kuma kuke waya da ita?"
"Oh wallahi in faɗa maka wata ƙawata ce nan"
Ya ce mata, "Ok nagane muje ko"
Saudat kallon shi tayi, kana tayi murmushi tana faɗin, " kamar akwai magana a cikin bakin ka?"
"Uhmm ni kuma, a'ah ko ɗaya"
"Nasha ai ko dai kasanta ne?"
"In banda abunki daga jin voice mutum na kuma shikenan sai ka gane waye shi?"
"Emnh Doctor ya ka ke wata magana? Ƙwarai kuwa da gaske zaka iya"
"Kawai dai kin faɗa ne but, nidai ban aminta da hakan ba"
"Ok shikenan tunda haka kace"
"Hakan ne mah ai"
Hmm cigaba da tafiya su kai tare, suna hira tsakanin junansu, haka dai har suka ƙarisa ɗakin da
aka kwantar da su Abban Sadeeq shi da Mamanshi.
Suna zuwa bakin kofar sukai sallama sanan, daman Saudat ce gaba ta sa hannunta ta kama
hannun ƙofar ta murɗa ya buɗe sanna ta shiga daga ciki Doctor Sani ya biye da ita a baya.
Shigowarsu kenan da su kai, su ka tarar da Abban Sadeeq ya farka, yana ganinta ta shigo
buɗar bakinshi ya ce mata, " Ohhh Honey kindawo kenan welcome, daman yanzu nan ina
farkawa na diba naga banganki ba sai momyna na tambayeta tace mun ai kin tafi amso takarda
ki siyo mana magunguna.
Saudat tana shigowa tai arba da Abban Sadeeq suka haɗa idanu huɗu dashi, farin ciki ne ya
baibayeta, rasa ma abunda zata ce tayi, kafin ta ce komai tayi magana dafe ƙirjinta tayi, ta ɗan
ja numfashi ta numfasa.
Ta ce, "Alhamdulillahi rabeel Alameen Tsarki ya tabbata Allah s.w.t Ubangiji talikai" ta cigaba da
cewa tare da ɗaga hannunta sama, "Ya Ubangiji Ya Allah ina tawassali da sunayenka tsarkaka,
ina ƙara gode maka bisa ni'imar da kamun da kasa mijina yadawo cikin hayyacinsa, Ya Allah ka
ƙaro musu sauƙi shi da Mama" tana gama faɗin haka ko rufe bakinta ba tai ba, suka amsa da
Ameen suma Ameen.
Mama Buɗar bakinta ta ce, " Daughter Saudat ubangiji Allah Ya yayi ma rayuwa albarka"
Ta amsa da "Ameen suma ameen Mama" da ga nan ta ɗaga fuskanta da Abban Sadeeq su ka
kalli juna su kai murmushi, Abban Sadeeq bai kula da Doctor Sani ba sai daga baya sanan ya
lura dashi.
Suka gaisa sanan ya miƙo ma Saudat ledar maganin nan take ya ƙara mata bayani ya maimaita
mata yadda za,a basu maganin ta amsa tana murmushi,bai gusa ba nan take ta ba ko wanne
yasha sanan ta mai da ledar ta rufe.
Budar bakin Doctor Sani ya ce, " kinga yanzu tun an basu magani sunsha sai ki nemo musu
abunda ɗan an jima can kaɗan zasu tashi su ci."
"Ok in dai dan ta wannan ne ba matsala"
"Alright ni zan wuce ko sai anjima su kuma ubangiji Allah Ya basu lafiya ya ƙaro sauƙi"
"Ta amsa da ameen suma ameen nagode sosai da kulawarka agaremu jazakallahu khair"
"Karki damu ai babu komai yiwa kaime shi musulmi ɗan uwan musulmi ne, kunan dikkanin ku
ƴan uwana ne"
"Hakane abunda, shikenan bara nazo nai escort naka saboda naga kamar wuce waza kai koh
yanzu?"
"Eh, amma da banso ki wahalar da kanki ne, ina son ki tsaya nan tare dasu ki basu kulawa
kawai is okay"
"No, karka damu indai wanan ne sun samu nidai kawai muje nai escort naka karka damu"
"Alright ba wani abu, I'm agreed with u hundred percent"
"Even me too dear"
"Wow!..I really appreciate to heard dat from u"
"No bakomai ka canci lamar yabo da girma ne shiyasa"
"Allah koh?"
"Emnh ƙwarai kuwa da gaske"
"Hmmm na amince amma nidai pls nan ma is okay kawai ki koma,ki cigaba da kulawa da su
Allah ya basu lafiya"
"Ameen suma ameen Nagode Nagode Nagode jazakallahu khair, basan da wannan kalar baki
zan gode maka ba"
"No nasan da haka, kawaiki barshi bakomai wallahi."
"Uhmm karka manta da cewa shifa yaba kyauta tukuici ne hakane?"
"Eh hakan ne kuma"
"Toh ka gani ba"
"Hakane"
"Pls I'm begging you dear to come back nd take with dem"
"Naji but ko dai nai maka wani abune baka so na sani shiyasa ka ke yi kamar kana korata"
"Ni dear ba wai haka ba ne ba, amma kidai koma da ga cikin, later zamuyi magana"
"Alright byeee sai na jika"
"Okay shikenan byeee"
*Nasrullah✍️*
07055852908
*WANE YARO*
BY
NASRULLAH
®
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]
*♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
*Sadaukarwa*
*Gareki*
'''Maman haneef'''
️2️⃣1️⃣
Shikenan toh naji kuma na amince, zan tafi kamar yadda kace mun, buɗar bakishi cewa yayi,
"yauwa ko kefa kin gani, maza ki koma nima sanan zan wuce na koma office ɗina" ta ce " Toh
shikenan ai babu komai babu sauran wata damuwa kuma" tana gama faɗin haka tai murmushi,
ta kama hanya ta juya zata koma cikin ɗakin da take jinyarsu Abban Sadeeq aciki.
Ganin haka cigaba da kallonta yayi, har sai da ya ga ta koma ta shiga ɗakin baya ganinta sam
ko alamunta sanan shima ya gyaɗa kanshi ya ɗan murmusa ya cigaba da tafiya zuwa office,
shima yanzu yadda yake tafiyar da alamun sauri yake yi ya manta sam yayi late.
Mamanshi tana can gida tana jiran dawowarshi gida, tasan dai duk lokacin da ɗanta yayi Night
Duty asibiti to ranar da sanyin safiya ya ke dawowa gida, amma yau kash!...Saɓanin haka ko
meke shirin faruwa? Har yanzu dau bai kai ga dawowa gida ba,Mamanshi tsayawa tayi tsuru ta
zurawa ƙofar falon nata idanuwa ko zata ga dawowarshi, taji kafiya meke faruwa ne ya yayi late
wurin dawowa?.
Ɓangaren Saudat kuwa haka ta koma cikin ɗakin, ta tararda Abban Sadeeq shi da Mamanshi
suna hira, alamun hira tai daɗi sosa ko wanne ka kalli fuskanshi zaka ga alamun fara'ah atattare
dashi.
Kallon da tayi musu, ta gansu a haka abun yayi matuƙar faranta mata ranta sosai, ba ƙaramun
burgeta hakan yayi ba yadda ta gansu, Ɗa da Uwa suna hira abun gunin ban sha'awa.
Gashi batan son abunda zai katse musu hirarsu da suke, gashi kuma yana da kyau tayi musu
sallama, rashin hakan ba daɗi sam ace mutun yazo wuri baiyi ma mutanan dake wurin sallama
ba.
Hakanan dai ta daure, ta ciccije bakinta, ta numfasa hannunta na saman chest nata breathing
deeply tayi, zuwa can kallonsu tayi tai sallama, suka amsa mata.
Kana ta shigo daga ciki, ta samu wuri ta zauna tana faɗin, "hira kuke kenan?" Har suna haɗa
baki suka ce mata, " Eh Wallahi hira muke, daman ke ce abokiyar hirar toh kuma gashi kin raka
Doctor Sani kina mai godiyar abubuwan da yayi mana na alkhairi, cigaba da cewa yayi ƙwarai
kuwa da gaske hakane nima naji daɗin ganin haka da nai Allah yayi miki albarka matata, kallon
juna sukai tayi murmushi, ta ƙariso bakin gado ta kamman hannunshi ta riƙe tana murmushi tare
da kissed nashi.
"Honeyna ai duk saboda kai ne da kuma momyna, shiyasa nayi hakan, saboda sam bana son
na rasaku, saboda kune ni bana jin zan iya rayuwata muddin idan baku, kun zama mun wata
duniya wacce a cikinta nake rayuwa kuma na ke komai na, muddin ba wanan duniyar to nima
bani.
Abban Sadeeq cewa yayi, "Hmm ki dena faɗar haka, ya ke kyakykyawar matata, ba ma hakan
zata faru ba insha Allahu, ako da yaushe zamu kasance tare dake domin kasantuwar farin
cikinki hubbyna a wannan kyakykyawar fuskartaki.
Murmushi tayi tana faɗin, "Wow Masha Honey ina alfahari da kai, ina sonka idan ina tare dakai
kana sani farin ciki da nishaɗi, kana ɗebe mun kewata duk kasa naji bana da sauran wata
damuwa lokacin da muke tare, kai ne fatilar ganina madubin zuciyata kai ne na bawa amanar
rayuwata a hannunka makusancin ruhina.
Kama hannunta yayi yana kissed nashi, tare da lumshe idanu yana faɗin, "Insha Allah zan kula
dake sosai, zan baki kulawar da wani ɗa namiji bai taɓa bawa wata “ƴa mace ba"
Yana rufe bakinshi tace, " Allah yasa hakan hubbyna" ta tashi daga inda ta ke zaune, tayi kissed
nashi agoshinshi muah!.. muah!... muah!...
Mama ko da ke gefensu tuni Bacci yayi awon gaba da ita,daman jia ta daɗe bata samun bacci
ba, lokacin da Saudat ta dawo hayyacinta, hankalinta ya komo jikinta kunya ce ta ka mata, ƙasa
tayi da kanta saboda ta tuna ɗaki ɗaya suke tare da Mama.
A hankali cikin satar kallo ta ɗago da kanta sama, ta ɗan waiga baya ta diba ko Mama tana
kallon duk abunda suke, ko da ta diba gani tayi Mama har bacci tuni ya kwashe ta, ji kake ras
gabanta ya faɗi, hannunta tasa aƙirjinta wanda ke bugun uku-uku ta ɗan numfasa, sanan ta saki
ranta tana murmushi.
Abban Sadeeq kuwa, yana sane da Mama bacci ya kwasheta shiyasa ma ya biye mata. Yana
kallonta mood ɗin data shiga, yi yayi kamar bai lura da ita ba, zuwa can tambayarta yayi,
"tawan? Meke damunki ne naga kin ɗan shiga wani yanayi"
"Humm kai dai bari wallahi, in fada maka har gabana ya faɗi karkaso kaji yadda naji ƙirjina
namun"
"Ayyah! Allah Sarki, meyasa hakan?"
"Tunawa nayi da Mama kilah tana kallon mu duk abunda mukeyi, da kuma abunda muke cewa"
Duk da dai Abban Sadeeq ba wata cikakkiyar lafiya ya cika ba yana gadon asibiti ne, amma
hakan baisa shi ya fashe da dariya ba, kallonta yayi yana faɗin, aini ina sane wallahi tayi bacci
shiyasa ma na biye miki.
Duk da dai ya mata dariya bataji haushi ba ko ɗaya, hasalima murmushi tayi tace, " shikenan
naji sai kayi shiru karka tada mana da Mama, daga bacci ka ga dai Maybe bata samu hutu ba
sai yanzu shiyasa ma nake tunanin haka"
"Alright hakan ma dai-dai ne" zai shiga cigaba da magana ta hannunta ta rufe bakin nashi, tasa
hannunta abakinta tana shiiiiiiiiit, sanan yayi shiru ya haƙura da maganar da zai.
Haka yayi shiru bai ƙara cewa komai ba, hannunta dake bakinshi yasa haƙoranshi cikin salo ya
ɗan cijeta, ka ga sauri cikin zafin nama ta cire hannunta tana fadin wai...wai... Tare da yarfe
hannunta alamun zafin cizon.
Zata fara mai kukan shagwaɓa yace, "tsaya wannan ne?" Ya taɓa bakinshi tace, "Eh shine"
Humm!...yana murmushi yasa hannushi yana bugun bakin nashi, cikin wasa tace, "nidai a'a ba
haka ba nake so ba"
" To kamar ya kenan kike so nayi"
" Shikenan tsaya bari na nuna maka" ta tashi ta matso daf dashi sanan tace, "kulle idanunka
masoyi"
Yana rufe idanunshi, sai dai kawai yaji ta kwanto kanshi, da jikinta ba duka ta sakarmai nauyinta
ba, tasa bakinta cikin nashi tana tsotsa, shima haka yayi da yaji saƙon kai tsaye ba shiri buɗe
idonshi yayi tare da dafa kanta cigaba da mai da mata martanin tsotsar bakin da ta ke mai yayi.
Nishi kawai suke suna tsotsar bakin juna, yayi da taji zai kaima breast nata capka, ta riƙeshi
tare da kama hannunshi, sannan ta cire bakinta ta tashi ta koma inda take zaune kan kujera ta
zauna, nishi kawai take.
Shima hakan Abban Sadeeq nishi kawai yake yana lumshee idanu, ba ƙaramun daɗin hakan ya
fara ji ba, sai gashi lokaci ɗaya kuma ta katse musu jindaɗin.
*Nasrullah*✍️
07055852908
*WANE YARO*
BY
NASRULLAH
®
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]
*♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
*Sadaukarwa*
*Gareki*
'''Maman Haneef'''
️2️⃣2️⃣
Murmushi yake yana tafiya fuskarshi cikin fara,ah a tunaninshi tarkonshi ya kama kurciya, ashe
bai san dawar garin bah Saudat shigo shigo take mai ba zurfi, koda Doctor Sani ya koma cikin
office nashi kasa zaune tsaye yayi