Showing 33001 words to 36000 words out of 39630 words

Chapter 12 - WANE YARO !! BOOK COMPLETE BY NASRULLAH.pdf

29 Jul 2025

4051

gefe gado inda ta saba zaman gefen Abban Sadeeq,kamar kullum
yanzu ma haka can take zaune hira suke suna ma juna murmushi, ko da 1pm tayi rana aka kira
sallah karfe ɗaya Saudat tashi tayi tashiga toilet tayi tarki sannan tayi alwaka ta fito can harabar
masallci ta fita akwai msallacin mata nan taje tayi sallah data idar shine ta dawo ɗakin da take
jinyarsu abban Sadeeq, tana dawowa shima Abban Sadeeq ya shiga bathroom yayi wanka ya
tsarke kake jikinsa domin yadda zaiji daɗin jikinsa kwana 2 kenan babu wanka jikinsa, sanan
shima ya gama wankan yayi alwala ya fito masallacin maza dake harabar asibitin shima ya fita
yaje yayi sallah ya idar sanan ya dawo inda su Momy da Saudat suke.

Har yanzu Momy bata farka ba baccin nata yayi nauyi sosai, Abban Sadeeq shi da Saudat hira
suke tsakanin junansu mai ban daɗi gunin ban sha,awa idan ka gansu abun saiya birgeka.

★★★★★

Washe gari da safe Mama idonta biyu harta farka daga bacci yau batai bacci ba kalar na jiya,
Saudat da Abban Sadeeq zaune suke kan kujera suna shan tea da donut, itama haka Momy
tana shan ruwan tea zallah babu komai sai madara kuma bata haɗa da komai ba, haka take

shanshi tana gasa bakinta akwai zafi sosai domin ita daman can tana son abu mai zafi sosai a
rayuwarta.

Gama shan su tea ke da wuya, Saudat tayi ma Abban Sadeeq magana zata ga doctor kan a
maganar ko mawarsu gida yau,Abban Sadeeq ko da ta faɗa mishi haka bai ce kata komai ba
face, yayi mata murmushi yace, "Eh badamuwa tashi muje tare nima nayi excersice" Saudat ko
da taji haka tuntsurewa tayi da dariya tana faɗin, " Momy pa? Waye zai kula mana da ita
kenan? Idan mu dukan mu mukatashi muka tafi ko kuma tana buƙatar wani abu? Waye zai
mata kenan pls dear ka tsaya anan naje nadawo kaima ɗin nasan ɗangwalolo ne jikinka ba
wani kwari ke da....." Tana cikin faɗin haka batai auneba sai dai ji tayi an muntsuleta ajikinta zafi
wayoooo ihu zatayi, saurin da yayi ya rufe bakinta nata yasakata shiru, itama ganin datayi ga
damar ramawa tayi hannunshi abakinta ta ganna mai cizo a yatsanshi hankali cikin salo, dariya
taka mayi tana faɗin ɗaya da ɗaya kenan zai yinƙura yatashi ta jawoshi tana faɗin yi hakuri
karkasa jinya tadawo baya nashiga ukuna...

Ko da jin haka ce mata yayi, " lallaimah yarinyar nan nine kike cema ɗangwalolo wato ma na
zauna karna dawo da jinya ba mai kike ɗaukata ne wai? To bara kiji wallahi ko tseren gudu
zamuyi sai na wuceki Allah ina faɗa miki saboda haka ki denamun wani gani²...."

"No!.. ni duk ba wannan ba yanzu Abunda nake so dakai duk da naji ka samu sauƙi sosai, ina
son katsaya kai da Momy pls naje yanzun naje na dawo insha Allah yanzu zanje na dawo, ba
wani jumawa zanyi ba" tana faɗin haka shikenan yace mata, " alright bakomai kije sai kindawo
nima ba zuwa zan ba amma ki sani ni ba ɗangwalolon da ki ke cewa bane" tace, " toh naji,
koma menene dai ai zanu haɗu anjima zan tester ka naji hakane.." ta faɗi haka tare da ɗaga
mai gira, tashi tayi zata fita cikin ɗakin, jin haka da yayi tayi magana yana kallonta suka haɗa
idanu ta ɗaga mishi gira ga kuma kato ɓarar datayi ɗaga hannunshi yayi ya dafa kanshi yana
fadin a'uzibillahi, ko da ya kalli inda Momy take gani yayi hartayi bacci shayin nan data mai zafi
har sakata bacci, Momy dake kwance bisa gadonta na asibiti wani bacci ne mai daɗi ya
kwasheta sai baccinta take abunta bata san abunda ke wakana ba...

Tuni ashe Saudat ta lura da Momy tayi bacci, shiyasa take sakin magana iya son ranta, wanda
shi Abban Sadeeq bai lura da hakan ba sam kwatakwanta, ko da ya diba inda Momy take
gefensu kenan yaga tai bacci girgiza kanshi yayi yana mata nuni da hannunshi yana faɗin "ke
koh? Tom!..." Sannan ta wuce ta fita cikin ɗakin tana faɗin kamar da gaske zaka iya wani abun
kirki, ta tuntsure da dariya ta wuce ta cigaba da tafiyarta.

Abban sadeeq samun wuri yayi bakin gadon asibiti da yake kwance ya ɗan kishin giɗa kafin
masoyiyarsa ta dawo su cigaba da hira tsakanin junansu, zuwa can Saudat bata dawo ba,
Momy ta fara juye juye sai gashi ta tashi ko da ta farka gani tayi ɗan tane kaɗai buɗar bakinshi
tace mai, " Wanan yaron bakai bacci ba?" Ko da jin haka ce mata yayi, " Eh Momy ban kwanta
ba muna zauna ne da Saudat muna hira, shine ta tashi taje taga likita akan maganar sallamar
mu muje gida yau" kasa kunnenta tayi tana sauraron shi tace, " Allah sarki baiwar Allah yarinyar
kirki, mutuniyar arziki ubangiji allah shiyi mata albarka, ka gani ko mai sunan Babana yarinyar

daman ni kaina na yaba da hankalinta shiyasaka ma na zaɓa maka ita matsayin matar da zaka
aura, Alhamdulillah gashi kana yau kaima kana ganin hankalinta da natsuwarta da sanin ya
kamatanta daman ni na yaba da hankalinta nasan kuma tunda akazo nan asibitin take ta
ɗawaini damu koh?" Ya amsa mata da " Eh Momy Hakane wallahi ni kaina ina ganin ƙoƙarinta
da kuma jajircewarta akan hakan, Allah yayi mata albarka ni kaina nasan da cewa nayi sa,ar
samun matar aure wacce ta fahimceni nima kuma na fahimce ta sosai.." Momy ko da taji haka
murmushi tayi, yayi da farin ciki mara misaltuwa ya mamaye birnin zuciyarta.

Momy ɗaga hannuwanta tayi sama tayi tana faɗin, " Alhamdulillah! Alhamdulillah!
Alhamdulillahi! Nayi matuƙar farin ciki da jikin haka sosai daga gareka, kullum addu,ata itace
ubangiji Allah ya haɗe kanku ya ƙara muku son da kaunar junanku ya baku zaman lafiya ya
kuma kawo muku zuri,ah ɗayyiba" tare suka ɗaga hannu suna faɗin ameen suma Ameen.





Nasrullah ✍
07055852908

  *WANE YARO*

    
               BY
       NASRULLAH

®
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

     *♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
        
              *Sadaukarwa*
                   *Gareki*
           ```Maman Haneef```

                ️2️⃣5️⃣

Bakinta ɗauke da sallama Saudat ta shiga cikin office ɗin, bayan tasha tafiya cikin asibitin tana
neman office ɗin doctor ɗin, sai da ta samu wata nurse tayi mata kwatance office nashi ko ince
ta kawo ta office ɗin, tayi mata godiya Saudat, sanan ta juya ta tafi.

Tana shiga ta samu doctor sai faman tunani yake, cikin ranta faɗi take, "ko tunanin me yake
oho?" Sannan ta sake mai sallama ko baiji ba ne, ko da jin haka ya amsa mata yana faɗin, "
have a seat cikin fara'ah" wannan ba doctor Sani ba ne, saboda yau ba shine ke da duty ba
abokin aikin shine, ko da tashiga cikin office ɗin shi ta taras.
Zuwa tayi ta zauna kujerar dake gaban teburinshi, suka gaisa sanan ta mishi bayani ko da ya
diba ya gani, eh lallai babu matsala za,a iya sallamarsu sannan ya rubuta takadda ya bata tayi
sign sanan yace taje ta biya kuɗi anan asibitin shikenan zasu iya tafiya, tana amsa ta tashi ta
fita kai tsaye taje ta biya kuɗi ko inda Abban sadeeq yake bata je ba, tsabar murna da farin ciki
zuwa tayi ta biya kuɗin Abban sadeeq ganinta da receipt kawai yayi suna cikin magana suna
hira da Momy kwatsam sai gata tadawo cikin fara,ah kai daga ganin fuskarta kai kasan akwai
wata kasa domin idan ka kallin fuskarta zaka ganta alamun tana cikin murna da farin ciki...

Bakinta ɗauke da sallam tashigo cikin ɗakin, suka amsa mata suka haɗa ido da Momy, Momy
tayi mata murmushi ko ganin haka Saudat itama murmushi tayi mata sanan Momy tace, "mu
daughter sannu da dawowa" ta ce, " Yauwa Momy sannu harkin farka kenan Allah sarki, ya
kuma ƙarfin jikin ai insha Allahu yau ɗin nan xamu wuce gida gama takardar na amsa mana
kawai da mun kintsa yanzu zamu wuce gida..." Ko da Momy taji haka hamdala tayi tare ɗaga
hannunta sama ta faɗin, "Allah Nagode maka masha Allah" ko da ganin haka Saudat ta saka
Momy farin ciki da wannan maganar tata, tahowa tayi gadon da take kwance ta zauna kusa da
ita gefen gado, tana ƙara karfafa mata guiwa cewar, "Momy ki kwantar da hankalinki insha
Allahu zaki samu sauƙi sosai especially ma idan muka koma gida zaki samun natuwa ki samu ki
huta sosai ki sakata ba kamar nan na cikin ta kura koh Momy?". Ko da Momy taji haka farin ciki
tayi tana Murmushi suka kalli juna tace, "my daughter Allah yayi miki albarka" ameen suka ce
atare duka su ukun har suna haɗa baki.
★★★★★
_________________________Yanzu misalin 2pm kenam na rana Abban Sadeeq ya shiga toilet
na asibiti yana wanka, ita kuma Saudat bayan sun gama hira da Momy tashi tayi tana haɗa
musu kayayyakinsu wanda zasu wuce dasu gida saboda yadda tafiyar zatayi musu sauri, Momy
ko jikinta akwai ɗan saura ko zata samu tayi wanka bisa dukkanin alamu sai ankoma gida.
Abban Sadeeq bai ga gama wankan ba Saudat ta ciro mai kayan sawanshi wanda tazo mai
dasu, tashiga cikin toilet ɗin ko kunyar Momy bata jiba, ai ko tana shiga goganka ya ganta sukai
ido biyu da ita kasa haɗiye miyau yayi sai da ya cakumota jikinshi hankalinshi ya kwanta, duk
da jikishi akwai kunfar sabulu tana ƙokarin kwacewa amma takasawa tayi, buɗar bakinta cewa
tayi, "Saurin me kake? amma kasani kafin nan Momy tana can tana jirana awaje, mekake son
nace mata idan ta ganni na daɗe daga zuwa kawo maka kayan da zaka canza na daɗe ban fito
ba waccw amsa kake son na bata?..." ba shiri Abban Sadeeq jikishi yayi sanyi ya saketa, rasa
mai zai ce mata yayi ko haƙuri zai bata oho?....

MUJE ZUWA DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA?......





Nasrullah ✍
07055852908


  *WANE YARO*

    
               BY
       NASRULLAH

®
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

     *♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
        
              *Sadaukarwa*
                   *Gareki*
           ```Maman Haneef```

                ️2️⃣6️⃣

Binta da idanu yayi yana kallonta zuwa can sai yayi tunanin bara ya ɗauko towel ɗin da zai
amfani dashi ya goge mata jikinta dashi, haka ya ɗauko shi ya goge mata kunfar sanan ta kama
hanya ta fita daga cikin toilet din ta barshi nan bai cigaba da wankan ba...

Ko da Saudat ta fita tana ɓoye-ɓoye jikinta, Momy kallon da zatai Saudat ta fito cikin toilet ɗin,
ta lura akwai abunda ke faruwa Momy bakinta kasa haƙura yayi, sai da tayi magana tana faɗin,
" my daughter lafiya naga rigarki duk rigarki ta jiƙe?.." sunkuyar da kanta tayi sannan tace mata,
"Momy tsautsayi aka samu ina shiga ciki Momy santsi ya kwasheni na zame shine na faɗi ƙasa,
sai yaya ganin haka ya amshi kayan daga hannuna, Allah yasa su basu faɗi ƙasa ba, ya ajesu
sanan ya ɗauko towel ya goge mun jikina shine na fito hakan yasaka kika jini shiru..."

Momy tace, "Subhanallahi sannu kace shiyasa naji shiru ya jikin dafatan dai akwai dama² babu
inda ke miki ciwo ko zafi?"ta ce, " Eh Momy lafiya kalau nake jina, kawai dai lokacin dana faɗin
ne nakejin zafin sosai amma yanzu na dena jin kamar ma ban faɗin bah!.." ta faɗi haka tare da

sunkuyar da kanta ƙasa.

Kunyace ta kamata sakamakon ƙaryar da taima Momy, shiya saka itama ta sunkayar da kanta
ƙasa saboda kada dariya ya ƙwace mata tashiga uku, Momy ta ɗauka ba gaskiya ta faɗa mata
ba hakan ya saka tayi kasa da kanta ilai kuwa hakan ke da wuya dariya tazo mata hakanan tayi
ta kanta ƙasa Momy batasan ma anayi ba, da ta gama tazo ta cigaba da aikin da take na haɗa
kayayyakinsu.

Bata daɗe da fitowa ba daga cikin toilet ɗin, sai gashi shima Abban Sadeeq har ya gama
wankan shima ya fito sanye da kayan da Saudat ta kai mai cikin toilet ɗin ajikinsa.

Shi ma haka yafito kanshi ƙasa yana jin kunyar Momy, ko da Momy ta lura da hakan tasan
akwai wata ƙullalliya ƙasa, dole duk da ta ganshi ko buɗe baki batayi ba balle kuma tayi mai
magana ta kawar da kanta.

Ɗaga kan dazai ya lura da cewa momy ba shi take kallo ba, duk dai akwai kunyar abunda ya
faru, mantawa yayi da hakan kawai yayi gyaran murya ya ce, "ma har na fito ko kemah zaki
samu kije kinyi wankan?.." yana gana faɗin haja tace mishi, "A'a mai Sunan Babana karka
damu zanyi wanka amma ka bari sai mun ka gidan mu sannan" tana faɗin haka tai shiru sa
bakinta bata sake cewa komai ba, shima haka bai ƙara cewa komai ba shiru yayi mata saboda
bai son yaga suna jayayya da mahaifiyarsa, "Shi Abban Sadeeq mutum ne mai matukar
girmama na gaba dashi da kuma biyayya ga iyayansa especially ma momynsa baison yaga yayi
abunda zai ɓata mata ko cusa mata wani baƙin ciki, saboda a hakin yanzu babu wani wanda
yake da shi indai ba ita ba sai kuma iyalanshi idan Allah ya kawo, duk da dai baisan da cewa
yana haihuwa ba" kwatsam Saudat da Abban Sadeeq shi na zaune kan kujerar asibtin sai
faman danne dannen wayarshi yake lafiya ta samu,ita ko Saudat kamar baiwa sai faman tiƙa
aiki takeyi, Momy tashi tayi, "Bismillahi" su dukansu Saudat da Abban Sadeeq hanzari sukai
suka kallo inda Momy take, domin gani abunda ke faruwa sai gani sukai momy tashi tsaye bisa
guiwoyinta ta fara tafiya, ko da suka buɗe suka tambayeta "Momy ina kuma zaki" sai da tayi
murmushi sannan tace, " ina son zagawa ne shiysa naji na fara jin karfi ajikina shine na tashi da
kaina" saudat sauri tayi tace, "Alhamdulillah Allah mungode maka, amma duk da haka ai Momy
da kince nazo na tamaki ki tashi" sake murmushi tayi tace, " a,a. Daughter naga ai kina aikine
shiyasa karka na tsayar dake" tana rufe bakinta ta cigaba da tafiya sakamakon ta tsaya basu
amsar tambayarsu yasaka ta tsaya da tafiyar, shi ko Abban Sadeeq nashi kawai ido bai ce
komai ba, cigaba da danna wayarshi yayi sai kallon screen na wayarshi yake yana sakin
murmushi, ko da saudat dake aiki ta lura da hakan cikin zafin nama, ta tashi ta fisge wayar zata
online ya hau yana chat, ko da ta amshi wayar ta diba gani tayi game yake sannan ta saki
fuskarta.

Abban Sadeeq binta yayi da idanu ko da ya lura ta diba abinda yake buɗar bakinshi cewa yayi, "
I'm sorry dear pls ba wani abu nake ba kawai dai ƴar game ce nake, ba chat ba nasan kishi kike
akaina, toh ayi haƙuri" kallonshi tayi cikin fara,h tana murmushi tace, "kana son na baka
wayarka?" Cikin sauri ya amsa da, " eh" tace mishi, "sai kayi murmushi sannan kuma ka

sumbace ni agoshina da kumatuna sanan" kallonta yayi tareda yi mata murmushi mai narkar da
zuciya, sanan yace, "matso kusa bbyna nayi kissed wannan lallausar kumatun naki" faɗin haka
yake tare cizar leɓenshi yana karkaɗa harshenshi yana taɓa labban bakinshi, Momy ko tashi ga
cikin toilet ta zaga bata fito ba, Saudat tana matsowa ta kashe idanu tare da lumshe su, sanan
Abban Sadeeq ya sumbaci goshinta kamar yadda tace, sauran kumatu zai mata bakinshi ya
sauka kan kumatunta kenan sai ga Momy ta fito daga toilet ɗin data zaga, bata ƙarasa fitowa ba
ko da ta fito tsayawa tayi bakin kofa bata shigo ba tana kallon ikon Allah murmushi take, sanan
tayi musu gyaran murya cikin sauri Saudat ta raba jikinta da nashi sanan tace, " ungo
wayar"tana murmushi yasa hannunshi ya amsa, sannan Momy tazo ta wuce su ta koma inda
gadonta yake, momy tsabar itama bata son su haɗa idanu komawa tayi tana kallnlon can gefen,
suma dai haka kamar ita ɗin kunyar junansu suka koma suna bugu da ƙari ga kuma kunyan
Momy sun san dai ko ba duka ba Momy taga wani abu ko ba yawa dai.

Saudat da Abban Sadeeq satar kallon junansu suke suna dariyar ciki, basu barin sautin dariyar
ya fita waje domin basu san Momy tasani, jim kaɗan Saudat ta kammala haɗa komai da komai,
sannan suka fara ɗaukar kayayyakin suka fara saka su cikin mota tunda babu wanda zasuyi
musu aikim dolene sune nan zasuyi aikinsu da kansu.
Ana cikin kai kayayyakin ne Abban Sadeeq ya fara fidda nishi sama sama ganin haka saudat
tace," rago kawai" cikin tsokana tacigaba da faɗin, "pls ka barmun ɗaukan kayan ji nayi duka da
kai na kaji pls zo nan ka zauna ka huta ko kuma ma ka kwanta pls" ta nuna mai seat ko bed ya
zaɓi wanda zaiyi dai hutun zai ko baccin....







Nasrullah ✍
07055852908



  *WANE YARO*

    
 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login