Showing 3001 words to 6000 words out of 39630 words

Chapter 2 - WANE YARO !! BOOK COMPLETE BY NASRULLAH.pdf

29 Jul 2025

4050

wani lokaci, bud'ar bakin, Saudat cema k'awarta farhat tayi bani labari, naji kinyi shiru
ne?.

Haba dai ke kam k'awata saurin me kike haka,ina son ki kwantar da hankalinki.

Insha allah, Yau dai kam, Abban sadeeq, tamkar hannunki yake yau sai yadda kika ga dama
kiyi dashi kuma zaki ce na fada miki.

Amma banso ki saurin bashi kanki haka cikin sauki ya kamata, a ce kidan ja,aji kemah tunda
kemah sai da aka shamiki kanshi, ko kuma ince mah sai da kika siyoshi da kudin ki sannan kika
samu kanshi.

Wow k'awata ina yinki gaskiya sosai, shiyasa kike kara burgeni, dad'ina dake kinsan abunda ya
kamata mutum yayi domin ampanin kanshi.

Sam bana dana sanin, saninki acikin rayuwata, a kullum ko da yaushe farin cikin kasancewa
atare dake nakeyi, saboda kalar kwarin gwiwar da kike bani, ina fatan ko wacce mace tasamu,
k'awa kamarki abun murna ne da farin ciki, ina alfahari dake k'awar amana.

Hmm kemah ai haka kike ta musamman awurina, shiyasa dole natashi na mik'e tsaye domin
naga natabbatar da farin ciki a fuskarki, shine hankalina zai kwanta k'awata.

Allah sarki, k'awata karki ji komai, insha allah mafarkin mu zai cika nan ba da dad'ewa ba.


Ameen Allah yasa,
Insha Allah! Inaji cikin raina tunda na taho da maganin nan nakeji araina insha Allah zamuyi
nasara k'awata.

Ameen suma ameen, nima ko da zanfi kowa farin ciki da hakan.

Hakane k'awata, kuma aminiyata, farin cikin kinshine nawa, matukar kikai farin ciki nima daga
lokacin nasan dacewa nayi nasara, domin idan kikai farin cikin tamkar da nima nayi ne abunda
ya sameki ji nake nima ya sameni.


Zan hada k'arfi da k'arfe domin ganin kin samu biyan bukatarki kawata saboda haka, ki dai na
hanzarin da kike shi ba gudu ba!..

Ga maganin da nazo miki dashi, zaki ban labari k'awata insha allah duk wani kuka naki, da
wai-wai yazo k'arshe k'awata.

Insha Allah.
Alhamdulillah masha Allah, Allah nagode maka daka nuna mun wanan rana kuma, insha Allah
itace ranar k'arshen bakin cikina acikin wanan gidan.

Allah sarki, k'awata wato har kinji wani sanyi sanyi aranki kenan, kingashi ba, hankalinki ya
kwanta dai koh?.

Masha Allah
Kwarai kuwa da gaske ina k'awata, ina cikin farin ciki mara misaltuwa, kuma wallahi k'awata.

Basan da me zan saka miki dashi bah, basan kalar godiyar da zan miki bah, bani da abunda
zan baki mai makon abunda kika mun face nace, Allah yasaka miki da mafificin alkhairi, ya
rabaki da sharrin makiyanki, allah ya maida mak'iyanki slippers muyi ta sakasu muna zuwa

banyi muna wanka, Ubangiji Allah Ya jikan mahaifan mu Yasa mutuwa hutuce garesu, idan
kuma tamu tazo ubangiji Allah ka kyautata tamu!..


Ameen suma ameen, kai!.. K'awata naji dadi sosai, gaskiya nagode sosai da wanann adda'ah
taki da kika mun, amma gasky baki da mutunci wato shine ma harda wani cewa allah ya mai
dasu slippers, tana fadin haka tuntsurewa da dariya tayi.

Ita ko saudat, murmushi tayi mata, tana cewa, ai duk cikin farin ciki ne.

Hmm naga alama ai, idan kuma magani ya dara aiki bansan wanne kalar farin ciki za,a bah.

ke dai bari k'awata, ba,a cewa komai wallahi na k'agu ajima da tayi k'awata.


Hmm nidae wallahi na gaji da wanan k'unatar taki, kin manne kin nace kan abu daya wato baki
magana zuwa ajima kalar abuncin da zaki mana, ta ajiman kawai kike.


Emnh kinga laifina?.

Aa banganibah amma da arage zumud'i da yawa.

Kin san maye

k'awata?.

Aa sai kin fada.

Wallahi yau dinan bah, jina nake tamkar wata sabuwar amarya, allah kuwa!.

Gaskiya ne lalai kuwa kyayi zumud'i saboda nasan amarya bazan mata ba, akwaita da zumud'in
daran farko.

Hhhhhhhh hakane kuwa, amma fa ni yanzu zumud'ina yana fi nata ma saboda, ni an lasamun
d'an d'anon dad'in zumace, kuma aka dena bani ita zumar kwatata, kinga ko akwai banbanci
tsakanin motar da take sabuwa da kuma wacce ta kwana biu ana hawanta.

Hakane amma ni dai tsaya ki saurara, in fada miki ko wanne, farhat ta d'auki k'ulli d'aya, tace
mata kinga wannan shine wanda zaki rinqa samai a abun shan shi.

Ta d'auko d'ayan shima tace shi kuma wanan shine naki narage sha,awa ne kamar anjiman
kapin ya dawo kin shirya komai kinga sai kisha naki shikuma idan kika bashi nashi yasha

shikenan kin kunnoshi ke kuma kin kashe taki hankalinki kwance ba ruwanki.

Wow k'awata gaskiya ke fasihiya ce kina da basira sosai akwaiki da dabara, allah yayi miki
baiwa wacce ba ko wacce mace ne da kalarta ba.

Allah koh?.

Kw'arai kuwa da gaske.


Hmm ke kad'ai ce k'awata, kika fahinci hakan shiyasa nake k'ara jinki cikin raina.

Nima haka.

Yawwa dafatan dai yanzu kin fahimci karatun da nai miki dallah dallah.

Kwarai kuwa da gaske na fahimta, ai ko ma ban fahimta ba sai na kiraki ki k'aramun haske akan
abun ballanta mana insha Allah na gane.

Yawwa haka nakeson ji, fatan nasara tare da kuma fatan alkhairi k'awata.

Ina godia sosai.

Sanan ta d'auki maganin ta dank'a mata guda biyun a duka ahannunta.

Cikin fara da murmushi Saudat ta karb'a tayi godia ta nuna farin cikinta da murna.


Wow gasky naji dadi sosai k'awata, Allah yasaka da alkhairi.

Yanzu menene farashin shi kawata?.

Haba dai k'awata' sai kace wata bakuwa ko kuma ince wacce bansanibah, ai yanzu abu
tsakanina dake kyauta ne yiwa kaine kuma nagani, ba fata nake bah, wani abu ya faru ba,
amma watarana kemah kece zaki taimaka mun kamar yadda nima nayi miki yanzun.

Toh kin gani babu zance , wai nawa ne, ki bar wannan zance ma dan Allah.

Shikenan na barta k'awata.

Yawwa ko kepa.

Saudat tashi tayi, ta bar farhat nan zaune cikin parlour, taje ta a je maganin a bedroom nata.

Bayan Saudat tadawo, ta zauka cigaba da hira sukai.

Suna cikin hira,rana tayi sosai farhat, tana ganin haka tashi tayi tsaye, toh ni k'awata zan wuce
akwai wurin da zan biya ba nan kad'ai ba?

Haba dai daga zuwanki shine mah zakice zaki tafi.


Haba dae ke kuwa k'awata aiko na jima ba yanzu nazo ba balle ki fadi haka.

Nasan da haka k'awata, amma ina son ki k'ara zama mudan k'arayin hira, in yaso anjima sai ki
tafi.


Wato bah so kike nabiye miki muyi ta hira ko ke ba ruwanki, babu abunda ya shafe ki, to ni
nawa gidan pa waye zai mun aikace akacen nawa? Kinga dole natashi ma tafi domin naje nima
na samu na karasa ayyukana saboda na miki alkwarine ma k'awata shiyasa, amma da bazan
zo kamar wannan lokacin da nazo miki ba.
Shikenan bakomai, duk da haka ina godia, Allah Ya tsare mana ke.

Ameen nagode, farhat tashi tayi ta dauki jakarta, cemata tayi to ni k'awata zan wuce sai kuma
Allah ya kara hadamu.

Sanan kuma kada ki manta pa da yadda na fada miki zaki amfani da maganin dana kawo miki
ba.

Insha Allah,itama Saudat tashi tayi tamik'e tsaye da niyyar tai mata rakiyya zuwa k'ofar gida.

Nan suka wuce izuwa kofar gida, suna hira tsakanin junan su ficewa sukai daga cikin parlourn.

Sun isa kofar gidan kenan babu jimawa, farhat, tasamu abun hawa, sallama sukai wa, junan su,
sanam farhat aka tuk'ata suka wuce.


Saudat tsaye take nan baki gate tana kallon su har sukai mata nisa bata ganin su.

Bata jima tana tsayuwa ba, ta shige cikin gida.

Komawa tayi tasamu wuri ta zauna tayi shiru, ita kad'ai abunta.

Bacci ne nan parlour, ya dauketa tunda ta fara shi ba ita ba ce ta tashi ba sai 1pm.

Nan ta farka ta tashi tayi alwala tayi sallah,bayan ta idar da sallah shine ta nufa hanyar kitchen.

Domin ta hada musu abunda zasu ci, baccin da tai yasa masa tayi lattin daura musu abunci.

Cikin k'ank'ankn lokaci kafin kace me, har abinci ya kusa sauka yanzu misalin k'arfe 2pm kenan.

Nan Saudat ta d'auko blander cikin kitchen, da take markad'a abubuwa.

Saudat shirin had'awa, Abban sadeeq juice take, ayaba ta dauko sanna kuma ta dauko madara
tasaka ayabar nan da kuma madara, kapin ta fara markad'asu ta dauko maganin da k'awarta,
ta bata tasa aciki sanna ta kuna blander ta fara markad'awa.

Cikin k'ank'anin lokaci abunsha ya kammalu shi abinci ya sauka.

Nan ta shirya komai da komai na kayan abinci ya halarta kan dinitable.

Yanzu karfe 4 kenan dai dai, yumwa takeji sanna ta samu taci abinci ta dawo hayyacinta.


Pls zaku jini shiru zan tsaya a nan


Pls
Share
Comments
07055852908```

*WANE YARO*


BY
NASRULLAH

®️

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]

         _♡F.J.W.A♡_

https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/

️6️⃣

```Saudat, Samun kanta ne, da tayi bayan ta gama cin abinci, yasa ta nufa bedroom nata,
domin ta samun tayi, alwala tayi sallah.

Sanan Saudat tasamu tayi, alwala tayi sallah, bayan ta idar da sallah, zaune take kan nadduma,
d'aga hannunta sama tayi, tana addu,ah ubangiji Allah Ya cika mata burinta.

Kana ta gama ta shafa addu,ah, tayi tashi daga kan naddumar, ta ajeta nan cikin bedroom, nata
inda ta idar da sallah, dawowa tayi parlour ta zauna.

Zaune take cikin parlour, shiru tayi ta zurawa ikon Allah idanu,yanzu misalin 4:40pm kenan
yamma tayi.

Lokacin tayi wanka taci ado tayi matuk'ar kyau sosai abun masai wanda ya gani zankad'aziyya.

Zaune take , alamun bud'e gate taji anayi mai guards.

Cikin hanzari ko Saudat ta tashi tsaye domin taga waye daman tasan za,a rina shine.

Ashe abban sadeeq ne ya dawo daga wurin aiki.


Amma abun yayi matukar bata mamaki, yadda taga bai tab'a dawowa gida akasin 5pm ba,
dai-dai indai kuma ba wani abu ne ya faru bah?.

Cikin ranta tambayar kanta take anyya lafiya kuwa? Wata zuciyar kuma tacs mata ko da yake
bakomai ai daman.

Sauran duka minti nawa?, k'arfe biyar din tayi dai-dai.

Bayan abud'e ma, abban sadeeq gate ya shiga zuwa yayi aje motar a wurin da yake parked
motocin shi.

Yana gama parked nata ya bud'e murfin k'ofar ya fito daga cikin motar had'e da jakarshi, kai
tsaye ya nufa parlourn gidan.

Saudat, ganin hakan yasa wani farin ciki mara misaltuwa ya mamayeta, rasa abunda zatayi tayi
tsabar farin ciki.

Abban sadeeq, bud'e k'ofar parlourn yayi tare da sallama, Assalamu alakaimu.

Saudat tana tsaye bakin kofar cikin fara,a da murmushi ta amsa mai cikin san sanyar murya,
Ameen wsalam habibyna, Oyoyoyo k'arisawa tayi kusa dashi rungumeshi cikin farin ciki da
murna.

Abban sadeeq, ganin wanan bazata haka da kuma wanan tarba haka ta musamman abun yayi
matuk'ar bashi mamaki sosai, hakan bai nuna wani damuwa bah cikin murmushi mai karya
zuciya shima ya bayyana afuskarshi, ba k'aramun kyau yayi ba da yayi murmushi,sanan ya sa
hannunshi d'ayan da babu komai akanta, yana shafa mata liyaliyan, gashinta wanda tai
attached dashi.

Kwantawa tayi akan k'irjinsa, yana shafa mata gashin kanta, ba k'aramun dadi hakan take ji ba.

Bayan sun kwashi wasu Seconds a haka, cikin san sanyar murya tana sa bakinta dai-dai
kunnenshi kamar zata cije shi,budar bakinta ce mai tayi.

Hubby kawo jakar kaje kayi wanka ko,gashi ka gaji allah sarki kasha aiki sosai masoyina,
kasamu kayi wanka kaji dama-dama,kaga sai ka kintsa kazo muci abunci koh gashi can a
dinitable na aje mana, daman kawai kaine nake jiran naga zuwanka masoyina.

Tana rufe bakinta,ta fara sa harshenta cikin kunneshi ta fara lasa kunan cikin salo wani yanayi
da yaji ya fara ziyartashi lumshe idanuwa ya fara yi.

Miko mata jakar yayi.

Ta duk'unna k'asa ta karba.

Sanan ya wuce upstairs, bedroom nashi domin ya watsa ruwa ajikinsa maganin gajiya.

Itama upstairs ta wuce bedroom nata ta hada maganin da k'awarta, Farhat ta kawo mata tasha,
bayan tagama sha, sanna ta wuce bedroom nashi tana jiranshi ya fito daga wanka.

Bayan wani lokaci sai gashi ya fito daga wanka, jikinshi daure da towel.

Daman jiranshi kawai take ya fito ta gyara shi tayi mai kwalliya sosai yadda zai kyau, ta dinga
kallon abunta, acikin gida tana samun nishadi da farin ciki.

Bud'e Sip, tayi Hatta kayan da zai canza idan ya fito sai da ta zab'o mai su taje su.

Cikin qanqanin lokaci ta gyarashi yayi matukar had'uwa sanan kuma ta chanza mai kayan dake
jikinsa.

Yayi matuk'ar kyau sosai, sai ma ka ganshi wani abu.

Sanan bayan ta gama kintsa shi rik'o mai hannu tayi suna tafe suna hira suna kallon juna suna
murmushi ahaka har suka,sauko downstairs nan cikin parlour, Dani table suka nufa.

Ta kaishi wurin zaman shi, ta ajeshi sanan itama ta dawo wurinta zaman ta zauna.


Oh My God!..
Wow dear, delicious cooked nd nice smelling & testing, ashe Abban Sadeeq,ne da ya bud'e
d'aya daga cikin kular dake gabanshi ta abinci, yake ta faman santi tun kafin ya ci abuncin,
ganin yadda ya k'awatu da kayanshi da alamun dai girkin nata zai bata citta sosai.

Cikin san sanyar murya, had'e da shagwaba, budar bakinta cewa mai tayi, Haba daer, abun
kuma harda zolaya tun baka ci bah?.

Hmm..! Dear kenan wanan ai ba zolaya bane bah, I'm serious lokacin dana bude kular nan wani
qamshi da d'and'ano mai dashi naji nasha k'e su cikin hancina hakan ya bani cewar da, alamun
girkin nan mai dad'i ne sosai kuma ga d'and'ano mai dad'i shiyasa na fadi haia ba zolaya bane
ba.
Shin ma wai idan ban dawo gida naci wanan daddad'an girkin naki ba girkin waccce kike so
naci In ba naki ba?.

Allah koh?, toh nagode sosai, cikin fara,a da murmushi mai sanyaya zuciya da sa natsuwa.


Wai kai d'in ne namawa wannan girkin saboda kidin, ka kasance na musamman ne agareni
jarumina kaine sarkin da ke mulki awanna babban fadar birnin zuciyata hubby.

Masha Allah Alhamdulillah dukkanin yabo da godia su tabbataga Allah (S.W.T). Ina cikin farin
ciki sosai mara misaltuwa,nayi matukar farin cikin samunki cikin rayuwata, kedin ta musamman
ce agareni, kuma wannan babbar dama ace agareni,bazan gajia ba insha Allah, wurin ganin na
baki dukkanin kulawa ta musamman ba.
Nai matukar farin ciki da jin haka daga gareka nawan, shiyasa kake kara burgeni kullum kuma
soyayyarka take kara shiga cikin raina.

Amma yanzu bana son ka k'ara cewa komai nawan, abunda nake buk'ata shine kayi shiru
katsaya ka natsu, kaci abincinka inyaso idanuka kammala sai muyi hirar mu, abun mu ko ba
haka ba?.

Eh kuma hakane, tawan gaskiya kika fada.

Bismillah sukai sanan suka cigaba da cin abinci.

Suna cikin cin abinci, Saudat ta tashi tasa mai wanan juice special one,a cup, data hada mishi
d'azu.


Bud'ar bakin Abban Sadeeq!..

Wow kace kuma harda wani Special Juice haka mai kamshin dadi tun kafin kiban nasha, nasan
zaiyi dadi sosai domin naji kamshin shi yadda ya mamaye mun hancina.

Nawan!.. Ka ganka ko!.

Allah sarki tawan!.. Maye kuma ya faru Allah Yasa dai ba laipi kuma na sakeyi ba?.

Haba dai shalelena laifi kuma sai kace wani dan k'aramin yaro, ai kai ka wuce laifi awurina,
kawai dae zolayata kakeyi.

Hmm shikenan indai hakane sai na dena ai.

Saudat, cikin shagwab'a, tace mai, A'a karka dena nawan.

Murmushi yayi mata tare da fadin,Koh meyasa?.

Cikin san sanyar murya da shagwab'a, tace mai, Saboda idan kamun hakan dad'i nakeji ba d'an
kadan bah, idan kuma ka dena zanyi maka kuka.

Sorry!...Please tawan bazan, so hakan ta kasance ba, bani da zabi sai abunda kika zaba shine
zabina.

Wow!.. Nayi matukar farin ciki da jin haka hubby shiyasa kake burgeni nake ji kana k'ara shiga
raina.

Nima haka tawan.

Yana gama rufe bakin shi.

Sai gashi ta mik'o mai,Juice din harta zuba mai, a cup, ta miko mai shi.

Amsa yayi yana murnushu, fuskarshi cike da annuri da farin ciki.

Nawan wanan murmushi haka karka sani narasa inda zansa kaina.

Haba dai hakan ma baizai faru bah insha allah.

Ameen suma ameen.
Allah Yasa.

Abban sadeeq, bismmilah yayi ya fara shan wanan Special Juice.

Wow!... So sweet, very nice and fantastic taste, har wani garshi tawan bakiji yadda naji wani
kalar sanyi araina ba, gaskiya kedinan ta musamman ce, kin sani farin ciki, dukkanin kulawarki
ta allaqa ne akaine tawan, nagode da wanan kulawarki ta musamman agareni.

Haba nawan karka damu wallahi babu komai, kadin nawa ne mallakina, uban "ya"yana idan ban
faranta maka ba waye zan mawa? Idan ban baka abunsha mai dadi ba waye zan ba wanda ya
wuce mun kai?, kaine dai muradin zuciya shiyasa akullum take k'ara sonka.

Abban sadeeq, tsabar dadin juice din, da yaji tunda ya d'aga bai aje bah, sai daya kusa half
cup, sanan ya aje.
Tsabar dadin lumshe idanuwa yake yana ta sumbatun dadi, yana suburbud'o mata labarai,
tana murmushi da dariya.

Haka sukai ta tafiya, yana sha yana mata hira har juice din ya k'are bai lura ba sai da ya daga
yaji wayan babu abunda ya zuba cikin bakin sa, daman juice din zaikai cup

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login