Showing 24001 words to 27000 words out of 38686 words

Chapter 9 - GAYYA CE! completed by Fatima Alaramma Alaramma.pdf

21 Jul 2025

2581

wasu maganganu masu narkar da zuciya, har falon suka ƙara so suka
zauna.


Suan ta hira, daga baya ta tashi ta shige bedroom ta haɗa masa ruwan wanka, har d'aki ta kai
shi ta taya shi rage kayan jikin shi sannan ya shiga wanka, ta fito masa da kaya marasa nauyi na
barci, sannan ta fito. Ta ƙarah shirya komi, ta koma d'akin tayi sa,a kuwa ya fito, ita ta taimaka
masa ya shirya sannan suka fito falo. Kai tsaye daining suka wuce sukayi lunche sannan suka
dawo falo suna hirah.
A yan zu sosai take nuna wa mijin ta soyayya shima kuma haka. Yau kima bin watan su biyu da
aure kennan.

Kwanciya ya yi kan cinyar ta ya mike ƙafarsa kan kujera, suna pesing juna,

"My dear".


"Na,am my Husband".


"Jibi idan Allah ya kai mu zamuje Kano nida Dad din Jamala da Jamal wani Company ne suke
neman ma,aikata shine zamu ko Allah zai sa a dace tun da kinga ba,a zama da sana'a ɗaya
yanzu.

"kwabe fuska tayi ta ce my Husband amma ba kwana za kayi ba ko?"

"Eh in sha Allah bazan kwana ba".

"Tom my Ubangijin ya baku nasarah da albarka, Ubangijin ya kai ku lpy ya dawo daku lpy."

"Na gode my love ina jin dadi addu'ar ki a gare ne, Alhmdllh na gode wa Allah da ya bani mace
kamar ke, ina alfahari samun ki a Rayuwa ta, my Noor".

"Tayi murmushi ta ce na gode".

"Yawwa gobe su jawahir da jamla zasu zo ko?".

"Eh haka suka ce min".

"To Allah ya kai mu rai da lpy, gaskiya zanji dad'i, sbd sau biyu na taɓa baki a gidan nan.


"Karki damu idan yaya Farouk ma ya dawo zasu zo shi da, Jamal".


*Washe gari*

Karfe 11:00am sun gama komi abinci suka shirya masu kalah kalah, tuni Fatima ta Farah kiran
yaya Jamal wai har yanzu bai je dauko su ba. Ya ce sai 11:30 in sha Allah zaije.

Karfe 11:50 am suna gidan jalil, Fatima tayi farincikin ganin su duk da shi Jamal bai shiga
gidan ba, amma ta leko ta gaida shi. Kasan cewar ma motar jalil ta samu matsala sai kawai suka
wuce tare bayan sun gaisa da su.


Sosai Fatima ta rungume su tana ƙara mamakin lamarin gaskiya ku yan biyu ne, suka saka mata
dariya.

Kayan ciye ciye ta kawo masu kalah kalah da lemo ka daban daban. Ta baje masu a gaban su,
idan da abun da kuke buƙata kuyi magana kunyi, suka ce ba sa bukatar komi. Tace ai kun san

gidan talaka sai hakuri suka saka dariya "au nan ku talakawa ne, ce war jamla". Fatima ta ce eh
mana, sukayi dariya.


Hira suke yi sosai, inda Fatima su ke ta yi da jamla wai Fatima ba zata ce wata jamla Anty ba, ita
kuma jamlah ta ce ai kece babba kuma ko ba komi gaba kike dani fa.

"Kai yau she ma zan girme ki ce war Fatima".

"A'a wllh kin girme ni".

"nifa 20 nake cewar Jamla".

"Eh Nima ma 21 ne fa".

Nan ma jawahir ta ce nima 20 nake.
Wannan kennan.

Har yamma suna ta pics da videos, da sukayi sallar magriba suka taya ta aiki karfe 8:00 dif sukayi
mata sallah ma, cike da kewar su, da kuma tarun Alkairai dan mutum ce mara ruwa Jamal ya
dauke su, Jamla ya farah sauke wa sannan suka wuce gida shida jawahir.


Typing

GAYYA CE!
*Free page*




*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana
mai albarka, godiya ta musamman*



✨✨✨

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina
rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.

✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun
sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma
Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya
littafin, ina alfahari da ku ges nagode.





PG 2️⃣1️⃣&2️⃣2️⃣



................. Ko da suka k'arasa gidan ba su wani bata lokaci ba kowa ya ya shige d'akin shi inda,
sukayi yiwa inna da Babba da suke falo sallama.


Sbd ya sanar da su da zasu yi tafiya gobe idan Allah ya kai mu, za suje Kano su da Dad.

Bayan Jamal ya yi wanka ya kirah Jamla ya ke ce mata ya gajiyar hadi da mata godiya, suka ɗan
taɓa hira sannan sukayi sallah ma sakamakon a gajiye yake.


Haka ita ma Fatima da jalil duk sun hira su sun masu ya suka je gida.


*Washe gari*

7:30 dai dai jalil ya sauke Fatima a gidan su, sbd baya so ya barta ita kad'ai tun da bai san yadda
tafiyar zata kasance ba.

Wannan shi ne zuwan ta gida na biyu bayan wanda sukayi da jalil bata k'arah zuwa ba sai yau.

Sosai ta rungume shi ta dinga jerumasa addu'a, tare da masa fatan alheri, sannan ta fito daga
motar tana ɗaya ma shi hannu.

Kai tsaye gidan su ya wuce ya dauko Jamal sannan suka wuce gidan dad.


*Labarai*

Motoci su wane su Jamal su ke hawa.

Shi dai jalil lokacin da mom Fatima ta bashi dukiyar ta domin ya yi mata kasuwanci da ita, ta
kuma dorah shi kan wata harka duk wata harka ta ta shi ne ta dauki mota halak malak ta bashi.

Shi kuwa Jamal Babur ne da shi da ya siya da halak din shi da yake sana,ar funichace.

Idan kuma ka gan shi da muta to ta Jamla ce ya hau, kuma baya hawanta sai dad ya aike shi ko
zai karbo mai wani sako, ko zai kai Jamla makaranta.



*Cigaba labarin*
*Kaduna*


Tun daga wannan rana Jawad sai yaje gidan Mamy dan ganin halin da take ciki, ya kan bata
lokaci a wajen su na hira, musamman idan papa baya nan

Yau ma kamar kullum ya shiga ya same ta zaune, ya gaida ta sannan ya shiga tambayar ta ko
mai yake da mun ta.

"Ta ce ba komi my son" kawai yau tun da na tashi gaba na keta faduwa na rasa dalilin haka wllh.

"Bakomi Mamy na karki damu in Sha Allah Alkairai ne, haka Ammy ma ta faɗa mun".

"Yawwa dama ina san zan je gaisuwa"

"To Mamy na yau she zaki je".

"Yan zu haka a shirye nake kawai drive nake jirah".

"Tom mamy fito na kai ki mana, Anjima naje office din tun da baki ma papy zaiyi daga Kaduna
nasan har mun dawo basu zoba".


"Tom shikenn na gode my son."

Da kan shi ya kai ta gidan mutuwar sai gararan biyu suka dawo gida, tana ta masa godiya ya ce
ba komi.

Kai tsaye gidan ya shaga yayi wanka ya sake shirya wa sannan ya fito falon Ammyn sa.

"Ammy yana ji gidan sai kamshi ya ke ne?".

"Eh girme kasan dai papy zaiyi baƙi da ga Kaduna kuma ma sun sauka suna Company yan zu gida
zasu wuto".

"Ammy to ina papy yake, dama yau be fita ba? ".

"Eh bai fita ba wai bayajin daɗi ne "

"Tom shikenn bari na shiga na duba shi".

Tuni su Jamal sun sauka a Company papy Amma a bun da basu fahimta ba shi ne, suna zuwa
Dad ya basu wata hula ya ce su saka wadda iyya idan su ake gani, suna ta mamakin abun duk da
sun san dad bazai taɓa cutar da suba.


Sun huta a Company inda daga bisa ni wani yazo ya dauke su suka wuce gidan papy.

Wani abu da yake bashi mamaki idan Jalil ko Jamal ya yi magana sai yaji tamkar yallabai Jawad
ne.

Yana sauke su comput din gidan, drive ya juya yace su cire abun su mai da cap din su, hakan
kuwa sukayi ba musu.


Dad ya kirah papy ya ce gamu a gidan ya ce bari Jawad ya zo ya shigo da ku.


Gida ne mai matukar kyau da tsaruwa k'atan gida ne, wannan da iyya girman sa abun mamaki
ne sai wasu man yan bishiyo da suka zagaye gidan ta ko ina, batun na faɗa maku kyauwun sa da
girma sa bata lokaci ne.


Wasu kuje ru dake gyefe suka Zazzau na suna jiran mai tafiya da su din ya k'araso.

Jamal da Jalil sun ci wata farar shadda wadda ta masu mugun kyau, ga sabun fuskantar su ya
kwanta luf, sai wani shek'i ya keyi.

Papy na sauke wayar Jawad na shigowa, nan take ya masa baya ni. Kawai ma sai suka fito
tare.

Da yake sun ɗan juyawa kofar baya hakan bai basu damar ganin junan su ba, har suka k'araso
gurin gaban su naɗan bugawa dad ya dafa Jawad suka juyo a tare!!.


Suna kallan junan su, ya yin da jikin papy ya dauki rawa, ya tafi suuuuu zai fadi su Jamal suka
rik'o shi, tuni Jawad ya yi suman tsaye.


Jawad kallan su yake yi inda suma shid'in suke kallah, kallan jikin su suka din ga yi dan ganin
wani banbanci amma basu hango shi ba.


Da 'yar suka k'arasa falon papy, papy ya rungume su ya kasa sakin ko ɗaya daga cikin su yana
jin wata kaunar su na ratsa shi, ko ba,a faɗa masa ba yasan wadandan 'yayan shi ne, kawai sai
suka ga hawaye na bin idon shi suka rungume shi, suma hawaye na bin nasu idon, Jawad ma ya
k'araso ya rungume su wannan kennan.


Sun dade a hakan kafin su saki juna papy ya dinga shafasu wanda har yan zu ya kasa furta ko
uffan.

"Kwai sai yace ku tashi mu shiga ciki".

Ta dakin aka bude wata kofa suka shiga babban falon gidan, suna shiga falon "papy ya farah
kiran Ammy Ammy!! Ki fito kiga ikon Allah.


Ammy ta fito jiki na rawa sai ta daskare a wajen da tayi tuzafi da su Jamal. Da gudun ta ta
k'araso falon ta rungume su ta na fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

Jawad ya tsaya yana kallon su.


Har kasa Ammy ta kai, tana kuka mai tabba zuciya suka rike ta, sosai suna jin kukan nata har
cikin zuciyar su. Tabbas ko ba,a faɗa masu ba wannan mahaifiya ce, uwa wandda tasan ciwan
ɗan ta, sosai suka dinga kuka ajikin ta ba kuma wanda ya yi kokarin hana su.
"Ammy ya isa kokan haka ce war Jawad dan Allah Ammy na ki bari kadda kiyi ciwan kai".
Sai lokacin Ammy ta tsagayta da kukan sannan ta shiga shafa fuskokin su hawaye na anbaliya a
kan fuskar ta.

"Jamal ne ya dauki hannun shi ya kira kan fuskar Ammy, Ammy na dan Allah ki dena kukan nan
ba gamu ba, a gaban ki, Ammy ba zamu taba barin ki ba, dan Allah Ammy ki maida komi ba
komi ba, kinji.

Sosai taji daɗin yadda Jamal ɗin ke gogye mata hawayen.

Sai kuma ta mike ta shiga cikin ta shiga kawo musu abinci, da kayan tsaye tsaye, suna taya ta
daukowa ita da su Jamal har suka gama.

Cikin sanyin murya ta ce kuje kuci abinci nasan zuwa yan zu kuna jin yinwa sosai.

"Jamal ya dafata ya ce to Ammy na".

Nan suka shiga cin abinci, duk kan nun su Jawad ne ya kirah Mamy bata daga ba ya ce yasan
maybe barci take yi amma bari ya karah kiran ta yana kiran ta kuwa ta daga"my son dama yan zu
zan kira ka barci nakeyi ne sai yan zu na tashi naga kiran ka.
Mamy bebyn papy bata nan ne, eh bata nan amma nasan tana hanya in sha Allah.
"Tom mamy ki shigo yan zu ana neman ki".

"Tom shikenn gani nan Allah yasa lpy".


Dad ya yi shiru tausayi Ammy da papy ne ya gama kama shi tabbas waɗan nan sune iyayen su
jalil to amma su waye su inna.
Rashin wanda zai amsa masa tambayoyi da ne yasa ya yi shiru ya cigaba da cin abinci shi wanda
ya yi masa daɗi ba kadan ba.

"Papy ne ya kalli dad ya ce bani da abin da zan biya ka da shi Alhaji Bashir Allah ina mata fatan
Alkairi a rayuwar ka data iyalan ka, tabbas iron ku suna da wahala na gode da dawai niya.

"A'a papy ni banji dawainiya da su Jamal ba asalima sune sukayi da ni. Zasu baku labarin da kan
su na sani.

"Amma papy kana nufin ba kada wasu 'yayan bayan Jawad.

"Eh babu ".
Sai 'yar ɗan uwan na, guda daya sai ɗan uwan na.

"To amma ina ɗan uwan na ka? Da yar tasa? .

"Yaje Abuja ne, sai zuwa anjima zai dawo kuma bana so na kira shi ne nafiso yanzo ya gani da
kan sa.

"Yar tasa fa, dad ya kuma jefa mashi tambaya. "

"Ta je unguwa amma yan zu zata shigo".


mamy ce tayi sallah ma ta shigo d'akin, bakin ta ya tsaya cak sbd abun da idon ta ke gani, "my
son wadan nan su wane haka, Mamy na ki shigo ya tashi ya shigo da ita ya ce ki zauna sannan
ya ce 'yan uwa na ne Mamy amma ban san komi game da su ba.


Su kuwa tunda suka ga Mamy suke kallan kallo dajuna, ba wanda ya iyya bayyana komi a kan ta.
Sobda zahirin kallon da suke mata, na wata fuska ne da suke tare da ita.


Nan take suka shiga basu labarin a hannun wadan da suke da kuma rayuwar da sukayi har zuwa
yan zu da Jalil ke da auran Fatima.

Ammy tayi farincikin da auran sosai tana ta addu'ar Ubangijin ya sa da rabo a tsakanin su zuwa
yan zu, Ammy Allah take ruko ya nuna mata Fatima taga gata a wajen ta.


Misalin ƙarfe 4:00 na yamma Dad ya yi masu sallah ma ya ce zai wuce gida sai bayan kwana biyu
kuma, Zai dawo.

Shima jalil ya ce zai bishi ko dan sbd iyalin shi, amma Ammy ta fashe masa da kuka ta ce dan
Allah kar ya yi mata haka dan Allah kada ya tafi ya barta daga nan Dad ya tafi, sannan ya ce nan
da kwana biyu zasu dawo shi da su inna da sauran su.

Amma shi jalil take ya kirah Fatima ya sanar da ita kwana zaiyi, nan fa ta dinga masa rigima da
'yar ta hakura da niyar gobe zata taho Kano in sha Allah, ta shirya komi drive zai zo ya dauke ta,
tayi farincikin sosai sbd ce mata ya yi sun samu aikin.
Sun dade sosai suna hira daga bisani sukayi sallah ma.

Ranar haka suka wani cikin farinciki, hatta Mamy jin daɗin ta yaƙi boyuwa sai kiran jalila take a
waya tana ce mata tayi sauri fa ta dawo.

Jawad ya ce Jamal ku tashi muje kuyi wanka ku huta, suka mike suka bishi sai da suka zo daidai
saitin Ammy suka matso daf da ita suka sakar mata kiss a gishi, musamman Jamal yana matuƙar
jin Ammy ta sa a ran shi.


Ba wani bata lokaci suka shirya cikin kayan Jawad sannan suka dawo falo, lokacin har an kirah
magariba dan haka suka wuce masallaci baki dayan su suka sa papy a tsakiya.
Tun da aka shiga Masallacin ake kallan su, da matukar mamaki wasu na tambayar papy yana
basu amsa da ya'ya na ne.

Fuskar papy ta kasa dena murmushi sbd wanzuwar 'yayan shi a tare da shi, daga nan suka wuce
gidan.


Suna shiga falon sukayi karo da abin da ya tayar masu da hankali, wato Jalila cikin matukar
mamaki Jamal ya ce Jamla ya yin da Jalil ya ce jawahir!!!. Mai ya kawo ki nan?




Typing


GAYYA CE!
*Free page*




*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*

https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana
mai albarka, godiya ta musamman*



✨✨✨

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina
rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login