Showing 15001 words to 18000 words out of 38686 words

Chapter 6 - GAYYA CE! completed by Fatima Alaramma Alaramma.pdf

21 Jul 2025

2580

biyu da aka fasa auran Fatima,
sunata tattaunawa daga baya kanin mahaifin na su ya tafi shi kan shi ya rasa maka ma.


Wani sabon hawaye ne suke zuwa kan kuncin mom nan da nan hankalin su ya k'arah tashi, Jamal
ne yace mom dan Allah ki dena wannan kukan komi zai daidai ta da izinin Allah.

Fatima ce ta she go falon idon ta ya yi jajur duk ya kunburah, gaba ɗaya ta basu tausayi.

Gaban Jalil ta tsaya cikin kuka ta ce yaya Jalil kaga abun da kebi ya yi mun ko, ta kuma fashe wa
da sabon kuka.


Komawa tayi ta rungume mom suka fashe da sabon kuka kowa ya kasa furta komi acikin su.

Mom ce ta dago murya na rawa tace Jalil, "na,am. Mom sai kuma tayi shiru, tashi yayi ya koma
inda take yace ina jinki mom.

"Dan Allah jalil kayimin wata alfarma mana, dagowa ya yi jikin na rawa yace. Ina jinki mom.

Dan Allah ka auri Fatimah!!!

ka tausaya min nida 'yata kaji tausayi na. Tana kaiwa nan ta kuma fashewa da kukan.


Gaba daya jin shi da ganin sa sun ɗauke shida Jamal, hatta Farouk abu ya bashi mamaki dan bai
taba zatan haka daga gare ta ba.


Innalillahi wainnailaihiraju,un!!! Abun da suke furtawa shida Jamal kenan.
Kuna ganin zai amince da wannan auren.

Typing


GAYYA CE!
*Free page*

*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana
mai albarka, godiya ta musamman*



✨✨✨

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina
rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.



✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun
sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma
Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya
littafin, ina alfahari da ku ges nagode.





Pg 15& 16

...................................Jamal ne ya yi karfin halin dagowa yace mom dan Allah ki dena wannan
kukan babu matsah ya Amince da auren fatima ita ma ai k'anwarmu ce bata da wani bambanci
tsakanin ta da jawahir a wajen mu.


Shi kuwa jikin jalil har wani tsima yake yana kallan ɗan uwan na shi ido cikin ido amma ya hana
shi Magana.


Mom ta Farah ma sa gdy da saka albarka.

Jamal ya ce bakomi mom ai duk ɗaya ne. Shi kam Farouk ma ya kasa magana sbd gaskiya bai so
hakan daga mahaifiyar tasa ba.

Bayan mitina 10 kowa ya yi shiru a d'akin ba wanda ya ke cewa kowa komi, kowa da abin da yake
zargawa cikin zuciyar shi.


Jamal ne ya yi karfin halin magana yace mom sai zuwa safe idan Allah ya kai mu, zamu tafi gida,
zamu shigo da wuri dan tattauna wa.


"Tom shikenn Ubangijin ya kai mu goben rai da lpy Mom ta faɗa.

Farouk hannu kawai ya miƙa masubata re da yace komi ba, sukayi musabbaha sannan suka fita.


Koda suka koma gida basu wani b'ata lokacin ba suka sanar da inna da Babba ya ji dadin yadda
Jamal ya karbe lamarin inada shi jalil ya kasa furta komi. Kuma Ababba ya ce Allah ya sanya
alkairi da albarka. Suka kiran mom aka k'arah tattaunawa, inda ta musu godiya ba iyyaka.


shi kam ranar jalil da Jamal, basu rontsa ba.

Ban garen Fatima ma basu rontsa ba dan kwana tayi tana kuka. Yarin ya mai ilimin ta, da ajin
ta, da kyauta. Amma yau ita akeyiwa wani tayin auren ta har ana haɗa shi da Allah , amma ya
zatayi kowa da kaddarar shi. Ubangijin ya sa hakan ne yafi mata alkairi.

Washe gari da sassafe su Abba da wan baban su jalil suka je gidan, suka tattauna na. Ina aka
tsaida daurin aure kamar yadda aka saka karfe 10:00 na safe. Alhmdllh sunyi farincikin da
wannan auren sbd dangin su Fatima muta nan kirki ne.



Asalin su Fulani Rano ne mahaifin finsu da mahaifiyar su, kuma duk kan nin su y'an uwan juna
ne, Baban su Farouk Alhaji Abubakar shine aiki ya kawo shi garin Kaduna daga nan ya zauna a
garin shida matar sa mom Hauwa sun haifi yarah y'an biyu maxa sune Farouk da Abubakar sai
Fatima. Sun girma inda suke Farah karatun su Abubakar yana ɓangaren doctor inda Farouk yake
business. Shekarun su Ashirin a duniya mahaifinsu Alhaji Abubakar ya rasu, inada ita kuma
Fatima tana da shekara bakwai a duniya. Bayan rasuwar mahaifinsu da shekaru biya shima Abubakar ya fara ciwon wata shida ya yi
sannan ya rasu wata ranar juma'a . Inda ranar ta zama ranar baƙin ciki, Farouk kuwa sai kulleshi
akayi a d'aki har ciwo ya yi sannan daga baya ya samu sauki.


Daga nan ya hakura da duk wani aikin shi ya koma na Abubakar. Wannan shi ne kaɗan daga cikin
tahirin su Farouk.

*Asalin labarin*

Washe gari karfe 9: 00 tayi dai dai amma angu yana kwan ce da'yar yake juya jikin shi.



Inna da Jamal ne suka shigo d'akin. Kwance yake ya kalli samma idon shi a rufe amma da alama
ba barci yake yiba.

Gyefen shi suka zauna, A hankali inna ta riko hannun shi ta kirah sunan shi a nutse ya bude idon
shi badan ya ce komi ba. Ta fara magana jalilu ina san kasan wani abu shi bawa da kake gani
kowa da kallah jarrabawar shi. Yarin yar nan mutuniyar kirkice haka zalika iyayen ta dan Allah
kada ka basu kunya a matsayin ka na wanda suka Amince maka har suka baka yar su badan duba
matsayinka ba , nasiha kalah kalah take yi masa a haka har ya gamsu ya kuma karbe kaddara.


"Inna tom yan zu tashi kaje kayi wanka ka shirya, nagd wa Allah da ya nunan wannan rana zanyi
surukai, suka saka dariya gaba ɗaya.



Karfe 10:00 Aka shaida daurin Auren Fatima Abubakar da jalil Ahmad kowa idan ka kalleshi
zaka hango farincikin a tattare da shi musamman Farouk da mom, shekam ango ba,a gane shi
shida Jamal dan ko wanne amsa wa kawai yake yi, inda da aka samu sauki aka shiga gidan dan
gaisawa da iyaye da Amarya.


Sun gaida mom da mutanen biki.

Sannan suka yi sama babban falo dan ganawa da Amarya da k'awayen ta tom da Farouk ya faɗa
mata ga sunan gaban ta ke bugawa dan batasan da wane ido zata kalli yaya Jalil din ba.

Inda su kuma kawa yenta suka ishe ta da zasu ga angon da ake boye musu kawai sai tayi
murmushi.

Suna zaune anata tsokanar shi yana dariya, dan tuni ya saki jiki ba yasan ya nuna mata komi ko
mita ne su fahimci wani abu da ga gare su.


Duk mazan abokan nan nasu duk abokan Farouk ne sai mai hoton da Tahir ya dauko wanda zai
wa Amarya da ango pic and videos.


Sallah su ce ta tsayar da hirar tasu, suka ne me guri suka zauna, ita kuwa kan Fatima a kasa tayi
masifar kyau gashi sai wani kamshi take yi.

Su Hafsah ne suke tambayar Fatima wane ango murya kasa kasa dan jalil da Jamal suke kallo
dan sun san dai acin su ne.


Tahir ne ya farah addu'a sannan aka shiga magan ganu. Hafsah ta dago tace wa Farouk wai yaya
Farouk ina angon yake ne.


Farouk suka saka dariya ya ce Amarya ta nuna maku Ni bana gane su, Nan fa kowa ya ce haka
ne.


Ta sar da Fatima sukayi sannan jalil da Jamal suka tashi suna suna fuskantar ta aka shiga video
ana cewa ta nuna shi. Wanda ita kanta tasan karya take yi tayi hakan, dan bazata iyya ba dan
bata gane suba. Amma sbd karta yarfa kanta a hankali ta Farah tafiya zuwa gaban su. Mai pic ya
ce ki tsaya kiji zaki rungume mijin naki ne kinga ne ta daga mashi kai.

Tafiya take tana kallan su suma ita suke kallah amma tafi gazgata Jamal ne a matsayin jalil da
Jamal ya fuskanci shi take nufa sai ya daga mata girah batare da kowa ya an karah ba aikuwa ta
faɗa jikin Jalil nan fa guri aka saki dariya. Shima haka ya rungume ta a jikin shi yana sakar mata
murmushi mai k'ayatarwa, ya farah mata magana a kunne kinyi matukar kyau matata ked'in ta
dabance my love kin hadu sosai, na godewa Allah da ya bani ke a matsayin mata, my love.
Ubangijin ya wanzar da zaman lafiya a tsakanin mu mata ta.

Duk jikin ta ya yi sanyi tabbas tayi sa,ar miji, ga kuma wata nutsuwa data shiga jikin ta lokacin
ɗaya.


Hatta Farouk sakin baki ya yi yana kallan su, inda kasan wasu masoyan da suke farincikin
mallakar junan su. Kai Alhmdllh ko yan zu nasan yar uwar zata samu farincikin a wajen jalil.


Tom a dago haka masoya. Cewar Tahir da Hafsah.

An sha pics cikin burgewa da nuna kaunar juna Alhmdllh inda su Hafsah da su Khadijah da
sauran 'yan matan wajen suke ta nuna wa Jamal sosai yana basarwa.



*Kano*

Yau she ne ranar karin haihuwa Jawad sanda shi kan shi ya sha,afa da ranar sai da safe ne yaga
MTN sun turah masa sakon sannan ya ankarah, amma shi a nashi lissafin wannan bata zama
wata muhimmiyar rana a gare shi ba, dan Rayuwarsa ce ke tafiya. Dan Allah ya kirah mai gadin
Company yace zai turah masa da kudi dan Allah ayi abinci a raba sadaka.

Ubangijin ya k'arah masa shekaru masu albarka, amma ba tare da ya faɗa masa manufar
hakan ba

Ya kashe wayar ya cigaba da harkokin gaban shi.


Jalilah ce ta shigo dakin fuska dauke da farinciki tace yaya Jawad murnar karin shekara, kallan ta
ya yi fuska ɗauke da murmushi yace au murna ki kemun.


Itama murmushi tayi ta ce wish you rayuwa mai albarka and mace ta gari da 'ya'ya masu
albarka .


Dan jan kuma tun ta ya yi sannan ya ce ngd my dear sister. Tare da ke my dear ya bani mace ta
gari mai kamar ki da kyawun zuciya irin ta ki. Axuciyar sa yace ba irin ta mugun mahaifinki ba.


*Kaduna*

An shirya komi Alhmdllh kuma a yau ne Amarya zata tafi dakin mijin ta.

Kuma Alhmdllh Amarya a yanzu hankalin ta ya kwanta dan yadda Jalil ke nuna mata kulawa
Alhmdllh.

Mom ce ta kirah jalil da Jamal ga Fatima ta ce, jalil ina k'arah godiya gareka da karamcin da
kamun jalil Ubangijin ya saka maka da mafificin Alkairi. Sai dai ina san amarya ta tare yau a gidan
ta da izinin Allah, idan kana ganin babu wata matsala? "Mom gaskiya akwai matsala gidan da
muke ginawa nida Jamal bamu kammalah shi ba amma idan ba damuwa akwai na kusa da shi da
aka gama zan kama hanyar shi sai mu zauna kafin na kammala nawa in sha Allah".


"Tom ma sha Allah Ubangijin ya sanya alkairi da albarka a auran ku my son. Ina da gida amma na
fiso ta kasan ce a naka saboda, hakan shine zata k'arah sanin darajar ka". Fatima kiyiwa mijinki
biyayya dan Allah kinga dai halaccin da ya yi mana.


Jamal ya dago da kanshi ya ce dan Allah mom mubar wannan maganar komi ya wuce fa banda
tada zance.


Haka kuwa akayi wa a ranar aka kai kayan Fatima. Da dare kuma aka kai Amarya dakin ta. Cikin
saka albarka iyaye da 'yan uwan ta. Tayi kuka harta barwa Allah.


Shima b'an garen jalil ya sha addu'a da saka albarka iyaye.

Sannan kuma su Jamal da abokan su suka fito raka shi gidan shi. Har sun fito Jamal ya koma ya
dauko wata k'aramar jaka yasa a bayan mutar suka tafi.


Bakin gidan sukayi parking ko da suka shi gidan shiru da alamar ba kowa a cikin gidan sai
amarya.

Madaidaicin falo ne mai dakuna biyu a cikin shi sai kicin. Ko wanne d'aki da ban d'akin cikin shi,
gidan ne madaidaici kuma mai madaidaicin kyau amma ya tsaru.

Sukuwa zama sukayi kan wasu kyawawan kujeru wanda kana ganin su kasan da kudi aka siye su.

Jamal ne ya tabo jalil ya ce tashi kaje ka kira Amaryar mana dare fa yanayi karka manta ba
kwana zamuyi ba.

D'akin da ke gaban shiya shiga wanda yana saran ganinta aciki, Amma bai same ta ba, sai kuwa
tsayawa ya yi yana kallon wani k'ayataccen bedroom mai matukar kyau ga wani kan shi mai
daɗi da yake ratsa shi.

Fitowa ya yi sannan ya shiga daya dakin bakin shi dauke da Sallah. Ta amsa mashi a nutse
gyefenta ya zauna sannan yace ki taso ana jiran mu a falo ta tashi ya rike hannunta cikin salon
soyayya yana faɗa mata magan ganu masu dad'i har suka k'arasa falon fuskarta a k'asa sannan
kuma a rufe.


Nasiha da addu'oi suka masu sannan suka masu sallah ma tare da aje masu manyan ledoji
wanda ko biyar dinsa babu acikin wannan kayan.

Ya raka su bakin kofar gida Jamal ya jawo ɗan uwan na shi ya shiga yi masa nasiha da rikon
amanar da aka bashi ya gamsu sosai sannan ya rungume shi hawaye na bin idon shi dan wannan
ita ce ranar ta farko da zasu taɓa kwana ba tare ba, wannan shine lokacin na ɗaya.

Shima rungume shi ya yi zuciyar shi tayi rauni yace kaje yanzu kaga suna jarah na. Kai ma kuma
jiran ka tare kabarta ita kad'ai.


Sallah ya yi musu sannan ya wuce gidan cike da kewar d'an uwa shi.


Kayan ya shigar mata dasu, basu wani b'ata lokacin ba suka Farah ci komi shike bata tare da faɗa
mata dad'ad'an malamai har suka kammala. Sannan suka yi alwala sukayi sallah . Nan ya shiga
tambayar ta abinda ya shafi addini tana bashi amsa yaji dad'in yadda ya sameta da ilimin.


Sannan ya shiga hira da ita, tana kwance a jikin shi, ta kanyi murmushi idan ya faɗi wani abu, da
ya fahimci tana tsoran shi yace kije ki kwanta sai da safe. Ta meke zata kwanta yace ki ragye
kayan jikin ki dan Allah, Sai dasafe ya fice, ta sauke ajiyar zuciya.

Typing


GAYYA CE!
*Free page*

*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana
mai albarka, godiya ta musamman*



✨✨✨

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina
rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.

✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun
sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma
Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya
littafin, ina alfahari da ku ges nagode.





PG 1️⃣7️⃣& 1️⃣8️⃣



Ranar Jamal kasa barci ya yi gaba ɗaya ya rasa mai ke damun shi. Yau hatta jamla ta sa ya kasa
waya da ita. Ga kuma barci daya kaura ce wa idon shi, dan haka kawai ya yi alwala ya tada sallah
yana yiwa ɗan uwan na shi fatan kasan ce cikin farinciki, sbd a zahiri gaskiya yana matuƙar
kaunar ɗan uwan sa, sbd yadda yake mashi biyayya koda kuwa baya so.


Washe gari

Ko da asuba da Fatima ta tashi bata ga jalil ba, hakan kuma bai bata mamaki ba, sbd tunda
sukayi sallah ma bata karajin motsin shi ba.

Da asuba ne data tashi taji mutsin shi da alama masallaci yaje.



Amarya da sassafe ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wata shaddar wadda tasha aiki, ba karamin
kyau tayi ba. Duk da dama Fatima kyakkyawa ce bata da makusa.


Koda ta fito falo bata gan shi ba dan haka ta shige cikin.


Dubawa ta fara yi a nutse ta samu kayan da take buƙata, nan take ta daura musu tea da dankali.
Ba wani lkcn ta bata ba ta kammala, ta koma kan gidan ta gyerah shi tsaf sannan ta shiga dakin
da yake dan har lokacin ba mutsin shi. Kwance ta tarar da shi yanata barci cikin nutsuwa, a
hankali ta k'arasa bakin gadon ta zauna tana kare masa kallo, duk da jikin shi a rufe yake fuskar
shi ce kawai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login