Showing 36001 words to 38686 words out of 38686 words

Chapter 13 - GAYYA CE! completed by Fatima Alaramma Alaramma.pdf

21 Jul 2025

2578

kuwa my wife kin sani a matsala
kinga abun da tamun kuwa dan Allah kayi hakuri yanzu kira ta, har 3 miss call ya yi take daga wa.
Fatima da kanta ta kira ta amma taki daga wa.
Tayi murmushi karfin halin sannan ta ce ka barta zuwa gobe.

Yau kwana biyu da faruwar hakan ko ya zo gidan baya ganin ta, yau da kan shi ya taka ya shiga
d'akin ya yi sa,a kuwa d'aki a bud'e ya ke. Tana kwance idan ta a rufe, ya k'arasa inda take ya
zauna ita kuwa tana jin shi tayi masa banza.

"Jalilah nasan idan ki biyu ba barci kike ba ina san kifad'an laifin da ɗan uwan ki ya yi dan yace
yana sanki, jalila auranki fa nace zanyi bawai nai manki nayi da sab'on Allah ba dabar kike gudu
na."

"Na sani yaya Jalil amma da wane ido kake so Anty ta kalle ni kasan wani irin muradi take dashi a
kai na? Kullum burin ta na haifi 'yayan wanda ita da hannun ta zata raine su." Dan Allah yaya Jalil
mu hakura da batun nan, ina sanka amma bazan iyya auren ka ba." Ta mike zata fice ya riko ta

tafad'o jikin shi, jalil Fatima ta amince da auren ki kece kadai yan zu naje jira hatta papy da papa
sun san da Maganar.

"Tom shikenn kaje zanyi tuna ni, sai kuma naji tabbacin daga Aunty."

Ranar kuwa kasa barci jalila tayi tana ganin kamar batayiwa Aunty Fatima adalci ba.

*Washe gari*
10:20Am a gidan tayiwa Fatima sbd farincikin Amin ce war jalil. Kai tsaye dakin ta ta wuce ta
shiga tana shiga suka haɗa ido Fatima ta sakar mata wani murmushi ta ce Amaryar mu, jalila tayi
karasa da kanta.

Fatima haka ta tabbatar mata da amincewar ta akan auren su, sannan ta dinga ce mata kin san
yadda yake sanki da kaunar ki, tun tana jin kunyar ta da haka harta saki jiki tana mamakin
Fatima.

Papy ma aranar ya kira su ya ambaye su suka ce sun Amince ce.

Daga nan papy ya dauki kafa Shida abokan da Babba mijin inna suka je wajen Dad dan nema wa
Jamal auren Jamal dan papa da Mamy sun ce sun bar masu ita duniya da lahira.
Dad ya yi farincikin abu daga nan aka tsaida biki wata daya ( one month) .

Nan suka kawo kudi duba dari biyu suka bayar suka karba tare da saka albarka.

Shima jalil da Jawad suma anka karba kuɗi aka tsaida rana kamar tasu Jamal.

******Fatima ma taje gida suka shirya koma mom ta karah shirya ta sannan ta dawo gida
tamkar Amaryar sbd tasha gyera wajen mom.

Anata shirye-shiryen biki ne saura sati daya papa ya dawo duk ya zama abu tausayi haka ya
dinga ne man yafiyar 'yayan na shi da 'yan uwa na shi.
Haka ya dinga ne man gafarar Mamy ya ce ba komi ta yafe masa.

Ranar juma'a kuwa aka shaida daurin Auren,
Jawad da jawahir

Jamal da Jamal

Jalil da jalila

Alhmdllh daga nan suka wuce dasu sabon family Hause din su da aka gina harda su papa da
papy da su kwanan su 5 da tare wa gida na Alfarma.




✍️✍️✍️
*GAYYA CE!*

*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ


*Sadaukar kar wane ga iyaye na da 'yan uwa na 'yayan Alaramma baki d'aya ina alfahari da su*



✨✨✨

Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina
rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.



✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun
sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma
Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya
littafin, ina alfahari da ku ges nagode.




PG 3️⃣1️⃣3️⃣2️⃣


Fatima da Amarya jalil kuwa baka gane su sbd sunyi kwalliya iri ɗaya hatta sutturah duk iri
ɗaya suka saka babu bambanci, ko laifema da ya tashi iri ɗaya ya yi ma su.

Jalil ne ya haɗa su a falo duk ya musu nasiha da a girmama juna sannan suka tashi ko wacce
ta shiga dakin ta.

D'akin Fatima ya shiga ya kawo mata wasu manyan ledoji sannan ya zauna gyefen ta ya jawo ta
jikin shi, a kunnan ta ya shiga faɗa mata wasu maganganu wanda Nima ban samu damar ji mai
duke tattauna wa ba, amma da alama tana jin dadin zance nata dan sai murmushi ta ke, da kan
shi ya bata jougut ta sha da ɗan naman ya haɗa mata ruwa wanka, ya ce ta shigo ya mata "tace
a'a kayiwa amarya, kaje haka kartayi fushi ya ce a'a sai kinyi barci zan tafi". Tana fitowa ta
taddashi a zaune rike da rigar bacci mai shegen kyau, haka ya taimaka mata ta shafa mai masu
dad'i da kan shi ya saka mata rigar barcin ya dauke ta cak sai kan gadon, ya kwantar da ita ya
lullubeta da wani tamtausan bargo ya barshi shafa gashi kanta, sai da yaga tayi barci sannan ya
zuba mata kiss mai zafi a lips din ta sannan ya tufa mata addu'a ya kashe mata wutaya fita daga
d'akin.

Abun da bai sani ba Fatima na jin shi, tana jin fitar sa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

Koda ya koma bangaren jalil zaune ya same ta tayi tagumi, ni kuwa nace Allah sarki baiwar Allah
ta shigo gidan wata. Shi kan shi Jalil yana yin da yagan ta sai ta bashi tausayi a hankali ya k'arasa
dan bata ma san ya shigo d'akin ba, ya janye hannun ta dake fuskantar ta ya jawo ta jikin shi ya
haɗe ta da kirjin shi, sai kawai tayi ƙasa da kan ta.
"A hankali ya fara magana kin gani da jira na ko my love" kiyi hakuri kinji pulet din da ya shigo da
su ya jawo batare da ya sake ta ba ya jawo ledoji da ya shigo da su da cups nan ya shiga ciyar da
ita bata wani ciga ta daure kan ta, daga nan suka shiga ibadojin su sosai ya tambaye ta abun
daga addinin Alhmdllh kuma ya samu, daganan ya kuma masu addu'a sannan ya umarci ta da
taje ta kwanta, sai da ya gama al,amuran sa sannan ya shirya kan shi cikin kaya irin na jikin ta ya
koma ya kashe wutar d'akin ya kwanta kan gadon ya jawo ta jinkin shi, ya fara antaya mata wasu
abubuwa masu wuyar fassarawa a rayuwar ta wanda bata taɓa cin karo da su ba, ni kuma na
wuce gidan Jamal dan ganin mai ke faruwa.

Suma dai a hakan na tadda su dan da Alama sun duniyar mabanbanciya daga nan nayi masu
sallama na wuce gidan su Jawad.

Ina shiga bakin kofar wata karah da naji Jawahir tayi ne ya sani daka tawa a wajen na koma gidan
su Ammy.


Ammy ce gyefen papy fuska ɗauke da farincikin "tace papy kaga hukunci Ubangijin ko,
Ubangijin ya wanzar damu cikin farincikin.
Wannan hajin in sha Allah dukkan nin mu zamu wuce Makkah dan yin ibadojin mu. Kuma harda
Babba da inna in sha Allah.

*Washe gari*
Jawahir kwance gaba ɗaya jikin ta a mace ya ke bata da wani sauran kuzari Jawad ne ya shigo
yaga yana yin ta, ya kawo mata tea ta sha kad'an da hawaye wani na biyu wani, can dai da yaga

abun nata ya yi yawa sai ya ce tashi suke hospital shi ya taimaka mata ta saka hijabi sannan ya
dauke ta har cikin motar suka wuce hospital din da yake aiki.

Yana parking ya ga motar Jamal da yake hawa amma baiyi magana ba sai ya shige kai tsaye
officer din mama Rabi ya wuce ta. " Gaida mama Rabi ya yi fuska a sake sannan ya ce mama ta
faɗa maki abun da yake damunta tun da ni ƙaramin doctor ne ta rainani" .
"A'a yau she zata ce haka nayan kana ɗaya daga cikin waɗan muke ji dasu a
Hospital din nan, aka ce min tun dazu ka shigo ina fita nace gaskiya ba kai bane ɗan uwan ka ne,
shima ya kawo matar sa ba lfy tana officer din mama jummai tana mata dinki".
"Ya ce eh shine Allah ya bata lpy.

Ita ma dai haka Jawahir abinda bata so ba sai da aka yi mata dinki sbd tasha wahala sosai a
wajen Jawad.

Ita kuwa baiwar Allah jalila shida kan shi ya kullah da ita, kuma ya gyerah ta ya gasa mata jiki.

Fatima ma abinci ta kawo mata na musamman da Farfesun kayan ciki taci sosai dama da yinwa
ta tashi.

Sukuwa su Jamal da Jawad wuni sukayi a Hospital da 'yar aka sallame su suka dawo gidan dan
basa son kowa ya sani amma su Ammy time din da suka zo gaida su bayan su dawo daga
Hospital suka fahimci akwai wani abu.

Fatima da yamma ta ce wa jalila ta ƙarah gasa jikin ta ta kuma bata wasu magungunan wanda
zasu taimaka ma ta.
Ita dai jalila sai kunyar Fatima ta ce ji amma ita Fatiman komi yi take tsakanin da Allah.

*Bayan wata daya*
*After one month*

Tuni su Fatima da jalila suka bi mijin su suka koma Ingilan ya cigaba da karatun sa. Amma gabaki
dayan su ya hana su karatu ya ce indai shi zaiyi suma suyi to mai ne amfanin nasan.
Fatima da jalil zama sukeyi na amana gaba ɗaya sun hade kan su suna kyautata mijin su
bayayi ayuwar su gwanin sha,awa.


Shima Jamal ya dawo Ingila din amma gidan shi da ban inda kuma ya ke karatun shi, shida matar
sa.

Jawad kowa yana gida Nageria tun da suka dawo daga honeymoon yana cigaba da kulla da
company wanda a yanzu ya zagaye ko ina a Afrika.

Papa kuwa yan zu bashi da komi a rayuwar shi sbd biyan tara da ya yi amma duk da hakan papy
bai rage shi da komi ba.
Amma a yanzu shi kunyar shigar sa mutane ma yake yi sbd kowa yasan yana kallan shi da abun.


Watan su biyur da auren fatima da jalila suka dinga wani irin ci ga kuma barcin ya rasa mai ke
damun su, yana kai su Hospital aka tabbatar masa da sunada cikin watanni biyar duk kan nin su
zukaga farincikin wajen jalil.
Sai dai Allah ya ingan ta.

Da wa watan da ya wuce Jamal ya kira shi yake faɗa masa Jamal na dauke da ciki.

*Bayan wata hudu*
A yanzu suna shekara karshe, kuma sun kammala jarrabawar karshe dan haka a gobe ne zasu
koma gida Nageria shida matan sa da kuma su Jamal.

Dama Ammy nata faɗan wai a dawo mata da 'yaya su haihu a gaban ta.

Washe gari da wuri suka wuce Nageria a jirgin Jamal nata tsokanar Fatima sbd cikin nata yafi na
kowa girma.

Ko da suka koma ba karamin tarba suka samu daga Ammy da Mamy ba daga nan zuwa dare
kowa ya wuce gidan shi sbd papy ya ce baza,a hana su matan su ba gwara idan sun haihu su
dawo gida gaba ɗaya.

Washe gari da safe jalil kasa fitowa tayi ko falo Fatima ce tayi karfin halin zuwa d'akin na ta dan
tambayar ko lafiya.
Tana zuwa take sanar mata da bata da lpy sosai ga wani ciwo da mararta ke mata, daga nan
Fatima ta kira Jalil ta sanar da shi ai kuwa ba shiri ya taho.
Sosai Jalil ke murkususu na azaba, Fatima sai jera mata sannu takeji duk da ita kanta wata
azabarce take cin ta sai gume takeyi duk da AC da ke d'akin.
Kafin Jalil ya k'araso Fatima tafi jalila gala baita Ammy ce tayi sallah ta ta shigo daga baya Mamy
ta shigo ita ma ta duba Fatima nan take ta gane haihuwa ce har kan beby ma ya tahu, su Ammy
suka taimaka mata sai ga kyakkyawar beby boy nan take wani ciwon ya kuma tashi sai ga wani
kan ya taho beby boy shima daidai nan kuma Jalil ya yi sallah ma ya karbe ɗan da ke hannun
Mamy.
Sai da ta dan huta sosai sannan suka shiga gyera ta, ita kuwa Jalil tuni ta neme ciwo ta rasa taga
tashin hankali dan tayi kuka ba adadin.

Zukaga farincikin wajen jalil da Jawad Jamal papy da papa Ammy da Mamy har mom ma da aka
kirata aka sanar da ita.
Farouk kuwa kamar ya yi tsintsiwa sbd yana san yara.
Musamman ma da aka saka wa yaran sunan Abubakar da kuma sunan Dad din ta.
Zukaga farincikin wajen mom da Farouk wai an musu karah.
Sai ake ce wa yaran Ajilan da ejilan.

Satin Fatima biyu da haihuwa Jalil ta haihu a she wance karun juyi ne kawai.
Ta samu kyakkyawan yara mata 'yan biyu zukaga farincikin wajen jalil.

Satin jalila ɗaya da haihuwa su Jawahir da Jamal suka haihu duka yara mata amma ita Jamal duk
maza ne. Ranar suna kuwa yaro daya yaci sunan Dad Ahmad shi kuma dayan yaci sunan Babba
wato Muhammad an yiwa jawahir karah.
Dad kuwa ya kashe kuɗi sosai a wannan haihuwa ya kumayi matuƙar farincikin da karramawar
su a gare shi.

Dan wani lokaci papy da kan shi yake zuwa ya dauko 'yayan Dad suyi huta a gidan sun saba sosai
da su papy da papa.

Jawahir kuwa sunan Ammy da Mamy aka sakawa yaran zukaga farincikin wajen su mamy.


*After three years*

Rayuwa ta yuwa sosai su Jawad sun kuma Company papy da aiki baki d'ayan su dan gaba ɗaya
sun hakura da zaman kasar waje sun zauna cikin iyalan su da iyayen su.

Duk kannin su sun karah haihuwa yarah sunyi wayo ma.

Sai dai a cikin wannan shekaru abubuwa sun karo masu dad'i da marasa dadi cikin su harda
rasuwar inna da Babba wanda suka rasu a aikin hajin da suka je gaba ɗaya su.

Yara sun girma tuni sun fara zuwa makaranta da kuma kaunar junan su.

Fatima da jalila kuwa baka gane 'yayan ɗaya daga cikin su sbd hadin kai da soyayyar junan su.

Doctor Adam ma yau shekara shi ɗaya da rasuwa kenan.

Shi kuwa Papa banda istigifarri babu abun da yake yi sai tuba ga Allah da kuwa kulawa da matar
sa da ɗan uwan sa .

Rayuwa tayi daɗi sosai abubuwa sun canza ga karin dunya da tarin 'yaya ga kuma wanzajjen
kwanciya hankali da family ɗin Su papy.


TAMMAT BI Ahamdullah .

Alhmdllh Alhmdllh Alhmdllh nan na kawo karshen wannan book Ubangijin kuskure da nayi
acikin sa ka yafe mun. Albarkacin Annabin mu Muhammad Rasulullah ( S A w)

Ku biyo ni cikin littafi na na gaba
Tauraruwa Ahali

And
Ciwo A Zuciya
Book masu sanya kuka da zubar hawaye.

Taku har kullum Fatima Alaramma Alaramma .
09163774774
Ga mai bukatar tambaya ta wani abu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login