Showing 3001 words to 6000 words out of 29806 words
Chapter 2 - IDAN RANA TA FITO Book 3 End Complete Na halima Abdullahi K Mashi .pdf
muke ji sai yanzun Helin ta dora abinci,
kaje ka amshe ta don ka fi tasauri kuma naka yafi dadi."Yasa bakinshi ya dan tsotsi le6enta tare
da cewa.""Na gajiMy Dear,nima in so samu ne in hau cin abinci yanzun."Dukkansu da Turanci
suke magana tun zuwan su k'asar ba sosai suka cika yin Hausa ba."Ta ce,"To kaje ka taya
tamana."Ya sake manneta a jikinshi."Basma ke da Husna ya dace ku koyi dafa abincu fa,
musamman ke Hunsa in ni na jure baki sani ba ko wanda za ki aura ba zaya jure ba.""To kuwa
Brother in ba zaya jure ba sai dai ya yi ta cin Indomie."Dukkan su suka sa dariya."Ya ce,"Na
tuna Dady fa ya yi aure."Husna ta zaro idanu.""Aure kuma Bros?""Uhmhm!Ba a dai daura ba sai
ranar Jumma'a."Ta ta6a baki, Basma kuma ta ce,"Budurwa?""Yarinya ce amma ta ta6a
aure."Husna ta ce, "Ni kam Bros ka ce mishi ya hkr ya dawo da Hjy.,Ganin yadda ta 6ata rai
tamkar zata yi kuka sai ya ce,"Tozan shawarce shi amma kin san ba lallai bane ya yarda."Husna
ta ce," In ma ba zaya dawo da ita baya hkr da auren ya auro karamar yarinya ta raina mu?"
[29/09 9:29 am] Inna: 13.Dariya Husna ta bashi, ya dai gano cewa kishi ne ke damun
Husna. Waton tana kishin mahaifiyarta."Dady bai isa ya zauna haka ba tukunna batare da
wadda zata dafa mishi abinci ba."Ta zum6oro baki."To baga kuku ba?""To in mun yi waya zan
fada mishi, ko kuma ki kira shi ma."Ta ce,"A'a kai ne zaka fada masa don ya fu jin
maganarka.""To zan fada, ki ka ce in ce mishi kina gaidaAntynmu ko?"Husna ta sake turo
baki.Basma tana dry tana kalon fuskar M.B, ta sumbaci wu yanshi tare da cewa.""Honey kana
k'ara kunna Husna ko?"Helin ce ta katse su da cewa"Ta shirya musu tebur."Shi kam M.B ya
kanci abincin Helin ne kawai don yunwa, amma ba wai don dadi ba, su kuwa su Basma har da
santi.¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤Ranar Juma'a kuwa bayan an tashi daga Sallar Jumma'a aka daura auran
Alhj Tahir da Amaryarsa Fatima, wadda aka fi sani daNana, kuma a ranar ne ta tare a gidanta
wanda yasha gyara tare da cana dukkan Ma'aikatan gidan.Rayuwa sosai su Dady suka shiga
Shimfidawa shi da Nana, lallai namiji damaan ce namjin yana tsufa ta wani gefe ya kuma lkcn
karfinshi ke kara zuwa ya dinga jin shi tamkar saurayi.Nana zata shaida hakan.14.Ni kam ina
nan zaman jiran miji har an sa kimanin wata 6 ni da Baba ya ce nan da wata 3 har an kara 3 ga
matsi da nake fuskanta daga gurin Baba Gaje fiye da da.Ga Hinde tunda ta haihu aiki ya karu
gurina, wankin kashi, goyon yaron mai suna Zubairu, du in da zani dashia baya, ko talla har ma
wani lkcn ya ki uwarsa sai ni.Binto ma ta haihu 'yarta budurwa sunanta Jamila, matar Ado ma
tana nan da nata cikin.Shi kuwa M.B baya son zuwa Najeriya ne sbd batun auranshi da Jidda
wanda kusan shi ne ya janyo ma kansa, amma in ya yi wani tunani sai yaga kamar bai yiwa
iyayanshi da ita kanta yarinyar adalci ba, inya san ba zaya iya ba me ya kai shi cewa za ya
yi?"Koda yaushe cikin saka wannan lmr yake, daga karshe ya tattara lamuranshi ya mikasu ga
Mahaliccinshi, duk abinda ya faru da shi ya yarda daga Allah ne kuma zai amsheshi hannu
bibbiyu
[29/09 9:32 am] Inna: 15.Cikin haka kwatsam sai gashi aiki ya taso mishi daga gurin aiki
an tura shi Najeriya, alissafin shi aikin zai dauke shi tsawon sati 2amma an bashi sati 4, don
haka sai ya yi tunanin yin amfani da damar ya cika alkawarin da ya dauka duk da dai Lagos aka
tura shi aikinki.#NIGERIA!Ya sauka Najeriya a Abuja, watanshi 9 kenan rabonshi da kasar.Ya
sake hawa wani jirgin don zuwa Lagos. Cikin taimakon Ubangijinshi a kwana gomaya kammala
aikin shi, ya nufi Kano.Kafin ya bar Lagos din sai da ya hada lefenshi tsaf,a kwatuna ne guda
biyar da dan karamin su cikon na shida.Ya bi jirgi ne zuwa Kano sannan ya yi shatar mota zuwa
gidansu, kafin ya karaso ne ya kira mahaifinshi ya sanar dashi cewayana shigowa yanzun nan
don ya iso Kano din.Dady ba ya gida amma ya kira Nana yashaida mata zuwan dan
nasa.Lokacin da yashigo gidan bayan ya sallamimai tasi, 'yan aiki suka kwashi kayansa zuwa
ciki.da salla,a ya shiga falon, babu kowa ya sake yin sallma tare da zaunawa kan kujera.Ta fito
tana sanye da atamfa 'yar Ingila da bakin hijabi a kanta.Kyakkyawar mace mai cikar mutunci, da
fara'a ta tare shi tare da cewa "Kai ne tafe?"Ya yi murmushi."Ni ne Anty."Bata samu matsala ba
don bata baringidan babu abinci.
[29/09 11:21 am] Inna: 16.Nan ko ta shirya masa abinci kan tebur ta zo ta ce"To Bello ga
abinci fa sai dai Allah yasa kana cin rin shi domin namu ne na gida."Ya ce,"Anty kenan, ai ni na
fi son komai nawa inda zai yiwu in yi amfani da na gidan ba ma abincin ba."Ya ci gaba da
cewa,"Ba mu gaisa ba sai batun abinci." Ta ce,"To ai zamu gaisa tunda gida kazo."Tuwo ne na
shinkafa da miyar shuwaka, yaci tamkar kar ya koshi don dadi, ya jima baikoshi haka ba. Yana
idar da sallah Dadynshi yanashigowa.Ya dubi mahaifin nashi da murmushi cikin tsokana."Dady
kai ne kayi k'iba haka?"Dariya suka sa har Nana.Dady ya ce,"Aikin Antunka kenan, cika miniciki
take yi da kalolin girkinta."M.B ya ce,"Na lura don nima na shaida haka.""Yaya ya zo babu su
Husna?"M.B ya ce,"Ai ya zo Lagos kuma ya kammala aikin.""Allah ya taimaka,ina fata dai ka
taho da shirin ka na zuwa kauye, don Babanka Maigari da kansa ya zo kwanaki don jin yanda
ake ciki, na kumatabbatar masa da ka iso da sati guda za a soma biki."M.B ya share zufar da ta
feso mishi, sannan ya dubi mahaifinsa.""Kayan can lefe da shi na taho."Dady ya ji dadi tareda
cewa Allah ya yi masa albarka.Shi kuwa ya ce,"Anty Nana ki duba duk abinda babu sai a zuba,
sannan a yi mata dunkunan kayan da za da zai samu duka." Ta ce,"To, sai dai a raba ma
Teloli."Nan ta shiga dubu kayan.Rantsattsun lesuna ne da shaddodi da kuma atamfofi duk na
karshen kudi, takalma da gyalulluka zuwa after dress ba a magana.
17.Anty Nana ta yabakaya, sannan ta ce, "Sai kayan shafa zuwa kayan ciki irin su siket." Ya
ce,"To Anty sai ku shiga kasuwa, yarinyar dai k'arama ce ina tunanin ba ta wuce sha shida zuwa
sha bakwai ba."Anty Nana ta ce, "To za'a siyo. Sai batun dunkunan a dinka duka?""A dinkesu
kawai don can ba su da wasu Teloli."Dady ya ce,"Haka ne."Bayan sun gama wannan babin sai
Dady ya ce,"Ka sanar da Basma kuwa?""A'a sai nan gaba saboda wasu 'yan dalilai."Haka da
dare sundawo daga Sallar Isha'i su da Dadynshi suka samu abinci kusan kala 4, kowanne
dai-dai cin mutum uku. Nan fa M.B ya shigaruwan ido ya ma rasa wanne zai ci, nan ya ci
wannan ya ci wancan ga kunun aya da kwakwa da dabino, ga so6o.Ya dubi Nana ya ce,"Anty
Nana ina ma a nan nake."Duk suka saka dariya.Abinda ya k'ara birge shi da matar mahaifin
nasa shi ne, yanda take matukar girmama shi da yin tsantsam da duk wani abu da tasan zai
sosa masa rai.Cikin dare yana kwance gefensa na da tunanin Basma yake yi wadda ba su dade
da gama waya ba yanzun.Yana son ta bayason abinda zaya sosa ranta. Yana tunanin ranar da
zata ji ya sake aure ba tare da ta sani ba.,Gashi ta yarda dashi duk wata gaskiya ta ba shi, tana
makutar sonshi.Ya tuna sanda zaya taho, rungume shi tayi tana kuka, kuka sosai da kyar ya
sha kanta dama kwana biyu kafin ya taho ya shiga kasuwa da su sun siyi duk wani abu da za
su bukata kafin ya dawo., Ya basu mota ya kuma ce baya son suje ko'ina sai Mkrnt, ya tsorata
su da cewa kada su ga ba ya nan sucanza dabi'u ya saka abinda duk inda suka je za ya mishi
bayani.
18.Duk sun yarda musamman Basma wadda ta tuna abinda ya faru baya. Ya yi murmushi da ya
tuna yanda suka tsorata tare da rantse mishi cewa ba za su canza ba.Ya janyo filo ya rungume
yana me tuna lallausan jikin Basma tare da kamshinta, kanta ya soma sanin wacece mace, don
haka baya wasa da ita. Ma'ana baya son abinsa zai sosa ranta, nashi ganin tafi dukkan wata
mace a bayan kasa.Cikin kawana 2 duk wani abu da lefen ke bukata ya kammalu, hatta
dinkunan.Ya jinjinawa Anty Nana, don ta tsaya tsayindaka don ganin komai ya hadu.Sajan Sani
ne ya ja motar zuwa Garkosukadauki wasu daga dangin mahaifinsa, sannan suka nufi kauyan
su Maigari.Gidan Maigari suka sauka, sun ci sun sha sannan suka kuma dunguma zuwa gidan
Amarya.¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤Ni ina zaunebutu- butu gidin murhu ina yiwa Hinduwa dimamen
tuwo, ga danta a bayana yana ta kuka hancinsa dam da majina, sai muka ji tsayuwar
motoci.Babana ya fito ya tare su tare da yi musu sannu da zuwa.Sajan ya shaida ma Baba
cewa lefena sukakawo, tabarma Baba ya amso nan makotanmu shi da kanshi ya shigo ya
same su tsattsayemutan gidan sai kallonsusuke yi.Baba Gaje ce ma ta zo tana baje jayayan
hakoranta tana cewa,"Sannunku bayin Allah, daga ina?"Sai kuma ta hango matan Maigari nan
taketa nufi gurin su tana cewa,"Lafiya?"A'a wai na ce lafiya?"Kafin su yi magana Baba ya shigo
da tabarma nan suka amsa suka shimfida suka zauna
19.Ya ce,"Gaje kawo ma baki ruwa."Da yake bata san dalilin zuwan su ba, nan ta nufi dakin
Jama'a don aron kwanon sha, sbd Baba Gaje dai bata da abin kanta.Bayan ta kawo musu ne ta
nufo inda ni ke ta zubamin rankwashi iya karfinta har sai da na gigice tare da cewa,"Tashi a nan
uwar kallon tsiyakada ki sa su amai da wannan warin naki."Na mike na nufi cikin daki." Daga
ciki ina jin lkcn da matan suka shaida ma su Baba Gaje cewa lefen Jidda suka kawo. Gaje ta
fiddo da dukkan idanunta waje tareda cewa," Wacece me wannan sunan, kunanufin
Kuluwa?"Suka ce,"Eh."Ta ce,"Kunyi 6atan kai, ina ga dai Kuluwar gidan Me jakai ce."Matan
Maigari suka ce"Ta nan gidan ce ba 6atan kai muka yi ba.",Da saurita iso dakin ta janyo ni zuwa
gabbansi."Kun ga fa irin tamu Kuluwar, wane mahaukaci ne zai ce yana sonta?Koko Birni suna
matsalar Kuluwa ne ba su da masu sunan.
20.Baba ya yi tsaki sannan ya ce ma bakin "Toan gode muku."Matan Maigari tare da sauran
bayin Allah da suka zo tare dai mamaki ya hana kowa magana.Suka mike suka ce,"To su
daikan za su tafi."Baba ya kawo kudi ya ba su ya ce,"Ga tukuici."Suka ce ba za su kar6a ba, ya
ce,"Su amsa ai haka ake yi, sannan suka amsa.Suna fita nan fa Baba Gaje Faifan bala'i wato
ita muguwa ce har da za a dinga 6oyemata abu?"Lallai kuwa za a ja da ita.Yau kam sai ta ji
dalilin da za a 6oye mata auran Kuluwa, ko ba ita ce ta haife ta ba ai ita ce taci kashinta ta
kuma ci fitsarinta. Saiyau naga fushin Baba inda ya ce,"Karya ki ke Gaje!"Ya bugi kirjinshi "Ni
nenan na ci kashin Jidda na ci fitsarinta, ke tauye ta ki ka yi tare da bautar da ita kin manta
ne?"Ta ce,"Haka ka ce?""Eh,na fada."In ji Baba.Ta rasa me zata ce, sai ta zari mayafinta ta yi
gidan Dija.Tana shiga tarushe da kuka tamkar waddaaka ce mata uwarta ta mutu.Dija ta taso
tana sallallami, tana fadin."Kawalli me ya faru?"Cikin kuka riris take sanar da Dija cewa,"Ashe
batun auran Kuluwa gaske ne?"Dija ta dafa kirje tare da cewa,"Kai haba?"Gaje ta ce,"Wallahi
kuwa, ga lefe can an kawo Adaka ce kusan guda 6 ban ma ta6a ganin irin ta ba."Dija ta
ce,"Wanene kuwa mijin?"
21.Gaje ta ce,"Ina zansani?Ni dai ba ruwana da harkar su kayan su ma ba dai dakina ba, kuma
ko zan tafi tsirara ba dai su zauna lafiya da mijin ba."Dija tasa hannu ta dafe mata baki tare da
cewa,"To sarkin shirme an ce miki ana fadane, batun ki ce ba ruwanki da biki bai ma taso ba,
kin san halin kauyan nan ba su iya tsegumi ba.Yanzun a zaga gari da ke ace kina bakin ciki, yi
kokari ki danne in yaso 'yan bori na sun ishe su.Za mu sa su turo musu Aljannu su hana su
zaman lafiya,ko ya dinga ganinta a Dodo kin gani dole neya sako ta."Gaje ta ce,"Kin kawo
shawara, sai dai Allahyasa na iya dannewa, in ga wannan Bakin cikin."Dija ta ce,"Za ki iya
mana muje gidan yanun sai ki nuna cewa kin zo ne ki gaya min mu zo muga kaya daga nan sai
ki aika duk Jama'a su zo su gani, ki nuna murnarki ki danne komai."Sai ga su sun dawo kafin su
dawo ma gidanya soma cika nan kuma aka rasa yanda za a bude akwatuna.Sai da aka aika
gidan Maigari sannan aka zo aka bude.Ba Baba Gaje ba, hatta Dija ta ji bakin ciki kayan, gashi
matan Maigari sun dawo su ne ke daga kayan saboda sata, dankunne da sarkan ma ba su bari
kowa ya ta6a ba, sun dai nuna suka ce daham ne dashi za sutafi.Cikin abin da bai fi sa'a biyar
ba lbrn kayanaurena ya zaga har makotan kauyan sun soma samun lbr.Wasu da yawa da yawa
in za su yi kwatancena kucakar gidan Wanzamai sukece min, shi yasa ba a sha wuya gurin
gane ni ba.Dija da Baba Gaje cikin daki suka tara ni sai na gaya musu wanene mijin, na dinga
rantsuwa kan cewani ban san shi ba............
[29/09 11:22 am] Inna: 21.Hinduwa kuwa kuka ta kwana yi wai Baba ya samo min miji a
birni ita ya k'i samo mata.Hakan ya k'ara d'aga hankalin Baba Gaje dama akwatunan shagonsa
suke kwana ta ce d'akinta ba guri. Sauran matan gida kuwa suna tsoranta.Matar Yaya Auwalu
ma har da had'a ni da Allah wai in fad'a mata ko wanene mijin, wallahi ba zata sanar da kowa
ba, na ce nima nan bn san shi ba, k'ila ma nakashsshe ne, ta ce haba?"Na ce Allah to in ba
haka ba wa ki ka ga zaya aure ni?Nan kuwa matar Auwalu ta je ta sanar da su Baba Gaje cewa
mijin nawa nakashasshe ne, wai ta lalla6a ni na gaya mata.Nan kuwa zance ya shiga yad'a gari,
kai wasu ma har cewa suka yi K'ila dai irin 'yanshan jinin nan ne da yake ana cewa suna yin
amfanin da Mahaukata, to wai ya ganniya zata Mahaukaciya ce.Babana ya tafi ya sanar da
dangin mahaifiyata ya ce da wan mahaifiyata ya dace su zo don kula da kayan aurena da aka
kawo, ya dawo kamar yau washe garinsuka zo."A lkcn Baba ya 6ulo da shagonsa ta cikin gida
aka kulle k'ofar waje.Nan dangin mahaifiyata suka zauna, hakanya dad'a k'ona ran Baba Gaje
don dai Dija tana tausarta."A na sauran kwana 3 daurin aure Baba Jummalata tsafe min kai, ni
kaina na tsorata da irin kwarkwatar da ke zuba dagakaina, kalkashin suka sa suka wanke min
kaina sai naji tamkar an cire min kayan nauyin nedaga kan nawa.Ana saura kwana 2 daurin
aure Baba yaje suka sayo min kayan d'aki, ranar ce kuma aka saka ni a lalle.23.Gidan k'anwar
su Babanmu muke zaman lallan, itama a tsorace ta amshe mu don duk 'yan gefen Baba Gaje
ne. Kawaye kuwa har da wadanda ba su ta6a min magana ba, duk sun zo sun shiga bikina.
Ban san abokan ango ba bare in dago ko wanene Angon nawa, komai da Angawaye za su
baiwa Amare daga gidan Maigari akekawo shi.An saba kajin alibidi guda 2 ake kawowa, sai ga
nawa guda 10. Kai komai nawa ya fita daban, ana gobe daurin aure mijin nawa yaaiko da
buhunan shinkafa 'yar Gwamnati da Rago tikeke, tun lkcn aka yanka shi aka shiga suya, miya
aka yi ranardaurin aure da safe kuma tyn Asubahi aka girka shinkafa.Wani abin alfahari ba a
ta6a yin wani taro a k'auyanmu kamar na aurena ba, ko lkcn nadin Sauratar Maigari taron bai
kai wannnan ba.Motoci daga birni 'yan daurin aure ga su nan.Bayan an daura ne kuma aka
shiga cin abinci, suma angawayan sun zo da abincin cikin wani d'an abu ga kuma lemon kwali
da na roba.Suka yi ta ba Jama'a kowa sai sambarka dahamdala, mata kuwa ba na kauyan
namu ba hatta da na wasu mak'otada kauyan namu sun lodi abinci.Sai dafawaake ana ba
Jama'a, ku ce min ina Baba Gaje lkcn???24.Tana nan daki ta kasa fitowa don
damuwa,kawayan ta suna tausarta, in sun fito waje kuma suyita yi mata dariya tare da cin
abincinsu gamida kaiwa gidajansu.Dangin uwa ba su da na 2, sune suka tsayatsayin daka a
bikin matan gida ma in tana d'aki su fito suma susa hannu in kuma ta fito sai su koma
daki.Mutanan k'auyen mu ba su girgiza ba sai da aka gama d'aurin aure suka ga wanene
Ango.#MuhammaduBello Tahir,yana sanye da shadda danya ,mai ruwan k'asa 'yar ciki da
malun-malun, ya murza hula Minsta itama mai kalar shaddar Haka nan takaliminshi duk in da ya
ratsa k'amshine ke tashi.Na ya durkusa gaban su Baba wanda shima ya yi wankan farar shadda
malun-malun aska tara itama daga Angon nawa ya kawo masa, ya gaishesu Baba ya gabatar
da shi gurin abokansa da wan Mahaifiyata, da kuma sauran 'yan uwansa.Duk sun sha mamaki,
da kyar suke iya furta Allah ya sanya alheri.Shi kuwa nanya cika su da kudi, shi da su Ado suka
yi masa rakiya zuwa cikin gidanmu don gaida dangin mahaifiyata.Kafin su karaso tuni lbr ya iso
cewa ga Angon nan shigowa, tuni mata suka shiga baza idanu don ganin wanene
Angon.Tsohon ne ko nakashasshenne??"25.Lokacin nima ina zaune cikin d'akin da dangin
mahaifiyata suke zaune, sanye nake cikin leshi ruwan d'orawa na rufa gyale fari, ni kaina samun
kaina da faduwar gaba lkcn da Sayyada 'yar wan mahaifiyata ta shigo tana cewa wallahi ga
Angon ya shigo, mutane suka bisu da kallo