Showing 18001 words to 21000 words out of 102125 words

Chapter 7 - KISHIN MATA part Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

5884

sharar kwalla abun dai gwanin ban tausayi ammh gogan ko gezau beji ba yace''Tou kwantar da hankalinki don yau zaki koya agidan Gidado kuma make sure it taste good if not am gonna skin you alive and for the very last tym kedawa kuka zo?ki budʼe baki kiyi magana don i promise bazan sake maimaita tambayan nan kamar ina bitar karatu ba next thing zakijishi ne ajikinki...ʼʼ

  Baki na rawa tace''Da...Ham...ma..ka.....ʼʼsai kuma tayi shiru

Duk da cewa ya dago wanda take shirin ambatar sunansa ammh sai kuma ya fuske yace''Dawa?ina jinki ai karashe...ʼʼ

     ''Ham..ma..ka..kasimm...ʼʼ ta ida ah matukʼar tsorace tana kallon yadda kalar idanunsa suka sauya,sai can kuma taga ya saki murmushi yace''idan na fahimceki kina nufin tare kuke da abokin cin mushenki ammh sabida shi dʼin isassahe ne shiyasa yaki shigowa ya gaidani ko?fyn jeki kirawoshi,kice masa ina kʼira...start moving kafin nasa chief ya yayyaga mun ke yanzuʼʼ

Ya lura tsoron karen takeji shiyasa taki motsawa,ya bawa securities daketa kallon ikon Allah umarnin maida chief cage wanda ya gama cinye wasted dishes dʼin sai lashe kasa yake,suka kamashi suka mayyar toh asannan ne ta samu kafarta da motsawa

  Har tasa hannu zata budʼe kofa ya kʼirawo sunanta cikin wani kakkausar murya _*''MUBEENAH....!ʼʼ*_

  Da sauri ta waigo tare da sauke kallonta akan serious face dʼinsa yace''karku sake kuce zakuyi tunanin guduwa kinji nace wallahi duk inda kuka shige saina nemoku na kʼwakuloku,sauran abunda zan muku kuma basai na fadʼa ba,don haka kice masa idan yana son cigaba da ganin kansa araye toh tun daga gate ya soma tsallen kʼwado har zuwa inda nake basai na bashi umarni ba,da fatar kinji abunda nace or u prefer the language of dogs?ʼʼ

  Da sauri ta daga kai cike da tsoro tace''naji duk abunda kace basai ka kirashi ba...ʼʼ ta fice da sauri shi kuma ya fashe da dariyar mugunta yace''Saina ci ubanku dukah yau dʼin nan yʼan iska kawai...ʼʼ yaja tsoki tare da duba yadda babbar yatsar kafar damarsa tadan kumbura sakamakon bigewar da yayi dazu........✍!

_ku nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_

_*#KISHIN_MATA*_

_*#2020_NOVEL*_

_*#SALO_NA_DABAN*_

_*IWA🖊*_

*🍃KISHIN MATA🍃*

               🍃🍃🍃

         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT



WɾƖTҼɾ

ى

 

ASSɷ

*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_

           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   

*#An_Intense_Jealousy_Story*

          _*💫BABI NA TAKWAS...✋🤟*_

!....Ah babban falon kowacce ta samu gu ta zauna,Hafsa sai ruwan balaʼi take ta zubawa Jameelah,ita kuwa Jameelar ta bawa banza ajiyarta don bata da lokacinta ta Baddo take,sosai yarinyar ke bata tausayi sannan kuma ta rasa meyasa Gidado ke azabtar da ita haka don kallo dʼaya zakayiwa kʼwayar idanunsa ka hango tsantsar tsanar da yake mata,

  Jameelah dai taga cin fuskar Hafsa na neman yawa don haka ta dubeta fuska ahadʼe tace''wato ke Hafsa na lura idan baʼa ciki da wuta wuta ba toh tabbas bazaki dagawa mutum kafa ba,da kike ganina dʼin nan billahil azimu na fiki dʼanyen kai kawai kʼyaleki nake don azauna lfy ammh na lura kinfi son adunga tashin hankali,Allah Hafsa ki bini asannu don wallahi nasan komi akanki,ina da   labarin irin ababen assha dʼin da kikayi ta aikatawa agari kafin ki auri mijina...ʼʼ

   Gaban Hafsa ne yayi wani irin mummunar faduwa tace cike da fargaba''meh kike nufi?wani abun assha dʼinne na aikata kafin na auri Suleiman?ʼʼ wani wawan kallo Jameelah ta watsa mata kan tace''Biye biyen maza mana ana raba musu dʼandʼanon zumar..ʼʼ ta furta tare da kashe mata ido guda,cikin tashin hankali Hafsa takai hannu ta buga kʼirjinta take fadin''innalillahi ni Hafsa dʼin?wallahi kʼarya kike ina kika samu wannan kagaggen labarin?ʼʼ

    ''Ai kʼarya ma nake miki ko?toh bari shi Gidadon ya shigo zakiyi bayani da bakinki bayan na hadʼa miki bomb..ʼʼ wani miyan tashin hankali Hafsa ta hadʼiye sannan ta tashi dasauri zuwa inda Jameelah ke zaune itama ta zaunan akusa da ita,in a low pitch take mata magana''Jameelah don girman Allah na rokeki ki rufan asiri karki bari aurena ya mutu plsss wallahi ina tsananin son Gidado,daga yau na daukʼar miki alkʼawari insha Allahu ko kallon banza bazan sake miki ba in har zaki rikʼemun amana ki binne sirrina acikin zuciyarki....ʼʼ sai Jameelar taji duk ta bata tausayi sabida ko kadan batayi zaton zatayi laushi haka lokaci guda ba,tagwayen ajiyar zuciya ta saukar sannan tace''Nifa yadda kike ganina dʼin nan bani da matsala,idan har zaki bini asannu mu zauna lafiya toh wallahi tallahi ba Gidado kadai bama babu wanda zaiji wannan batun ammh idan kika cigaba da rawar kai tofa zan fasa kwan ne,don haka tun wuri in zaki canza taku ki canza karkice ban gargadʼeki ba ehe....ʼʼ

   Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kan tace''Shikenan ngd kuma nima insha Allahu zan kiyaye..ʼʼ murmushi Jameelah tayi sannan tace''Good...yanzu dai ki tashi kije kiyi wanka don amarya da gayu aka santa bawai ta zauna hakanan da tsamin jiki ba..ʼʼ sosai kalamanta suka soya ranta Hafsa ammah sai ta dake bata nuna ba tace''Hakane..! bari inje toh nayi ngd da tunatarwa...ʼʼ ta mikʼe tana sake duban yadda Jameelar taci kwalliya cikin atampa holland kai kace ko itace ma amaryan ba ita ba,tuni taji wani irin kishita ya turnuke zuciyarta,

  Jameelah ta bita da kallo harta shige part dʼinta sannan ta saukar da wawan ajiyar zuciya tana fadin''Ya salam..! Suleiman meka dakkowa kanka hakane?macen da aketa ikarin ta iya kissa da kisisinar kenan?Goddd..! Ramlah tun baʼa kai koʼina ba gashi har Hafsan ta soma badake,,tabdi ammh agaskia anji kunya wallahi tirrrr Allah ya sawwake kayan tsami kawai mace duk ba kan gado..ʼʼ ta ida maganarta tare da mikʼewa ta shige part dʼinta don nema musu abunda zasu ci tunda Gidado yasa Baddo yi musu asarar breakfast,akicin ta jingina da kofa tana dube dube don tama rasa abunda zata girka musu mai saukʼi gashi kuma gogan akwai shi da son kʼaryawa da snacks,hakan yasa ba tare da wani bʼata lokaci ba ta auno fulawa don making sausage rolls ita nan aganinta zaifi saukʼi,ruwan shayi ta soma azawa awuta

    _____,,,,,________

Baddo na fita ta samu Kasim jingine jikin mota don ya gaji da jiranta shine ya fito waje,ada yana shirin zuwa kʼwankwasa kʼofar gidan ne sai ganinta yayi ta fito hankali tashe tana kuka sosai,ah rudʼe yace''Ke babe meya sameki kike kuka sannan kuma ya akayi ne kayanki ya bʼace da mai huh...?ʼʼ yayi tambaya looking so confused,amaimakon ta bashi amsa sai kawai ta sake rushewa da kuka take fadi arikice''Ya...yace...ka..kashigo...ʼʼ

  Gabansa yaji yayi wani irin bugawa cikin tashin hankali yace''ke wayace in shigo,shi wa?dallah kizo mu wuce nina gaji da ganin kaina ah kʼofar gidan mahaukacin nan..ʼʼ yasa hannu yana kokarin budʼe murfin motar zuciyarsa na fat fat don tsabar tsoro,yasan tabbas idan ya shiga gidan abun bazai masa kʼyau ba,shi wallahi yama rasa wai wani irin mutum ne Gidado,wallahi daʼace aikin soja yakeyi da yafi matching dashi,haba mutum yabi ya takura rayuwarshi sai kace akanshi ne aka soma neman yʼan mata?

   Baddo ta katse mishi gajeriyar hirarshi da zuciyarsa tace ah matukʼar tsorace''Don Allah Hamma Kasim kar kayi masa taurin kai kazo mu koma ciki tare wallahi duk wani kalma daya fito daga bakinsa Allah har zuciyarsa he mean it,yace idan muka gudu toh kuwa haduwarmu dashi nan gaba bazaiyi kʼyau ba....ʼʼ Ah zuciye yayi saurin taran numfashinta''So whatt...!?to hell with him,,kinga ni na tafi tunda naga ke tsoro bazai barki ki tsere ba,ki koma yaci zalinki ke dʼaya ammh banda Kasimu in naje gida dai ce musu zanyi ance zaki koma zuwa yamma...ʼʼ be jira yaji ta cewarta ba ya fadʼa cikin mota tare da bata key yayi gaba ah tsiyace,sai data ga bʼacewar motar sannan taja jiki ta koma ciki tsoro fal ranta,

Idanunsa akanta ah saʼilin data kutsa kai cikin gidan,sai wurga mata wani mayataccen kallo yake wanda hakan ya dadʼa tsananta faduwar gabanta,tun kan ta karaso yace cikin hargowa''Ina dʼan iskan yake..!?ʼʼ runtse ido tayi tace with a breaking voice''Ya...wuuce...ʼʼ

   ''Whattttt? ya wuce kika ce?ʼʼ ya tambaya cike da mamaki,daga masa kai tayi alamun tabbatarwa,

Yace yana sakin murmushin mugunta''Good...! inason haka! mutum mai taurin kai ba? i lyk dat,,ba damuwa zan nuna masa cewa nida kai biyu aka haifeni,ki gode ke Allah ya kubutar dake don wallahi daʼace kin bishi da punishment dʼinki yafi worse,waya wuce ciki muje ki mana girkin..ʼʼ

Ya fadʼa yana nuna mata hanya da er yatsa,da sauri ta shige ah tsorace.Kicin dʼin Jameelar ya kaita acan ya ganta tana shirin soma kwabʼa filawar,wani gigitacciyar tsawa ya doka mata wanda yatsoratata ba kadan ba yace''Hearthrob meh kike shirin yi?ʼʼ

   Ajiyar zuciya ta sauke tace''kai Sahibu wallahi ni harka tsoratani,meh zanyi in banda breakfast?ko muna da wani abun da zamuci ne ah ajje?ʼʼ

   ''Bayan kinji nace yarinyar nan ne zata mana girki ammh don neman magana shine kikayi saurin shigowa kicin ko?toh tashi ki fita kibar mata kicin dʼin kinji nace wallahi yau da girkin Mubeenah zamu kʼarya da kuma exactly abunda ta kawo..ʼʼ Jameelah na kokarin magana yayi saurin datse lips dʼinsa yace''shhhhhh! juz obey..ʼʼ haka dai Jameelah ta tsame hannunta ta fice cike da tausayin Baddo,ya dubeta yace''na baki juz 1hr ki gama komi if not jikinki zaiyi tsami...ʼʼ

  Har ya juya zai fita sai yaji tace''ban san inda kayan hadin suke ba..ʼʼ ta fadʼa tana matsar kwalla,zuwa yayi ya turo jameelah yace taje ta nuna mata inda abubuwa suke sannan kuma ta taimaketa don kar suci jagwalgwalo,sosai Jameelah taji dadi daya ce ta taimaketa,ya shige dakinta don wanka ita kuma taje don taimaka mata,ran Baddo fari kal ganin Anti Jameelah na taimakonta,bayan ya fito wanka sai ya kʼira can gida ya fadʼa musu cewa zai maido da Baddo anjima ta tsaya taya Hafsa aiki ne,awa dʼaya da rabi suka dauka sannan suka kammallah kuma abincin sun bada good taste ba kadan ba dake Jameelar ma kʼarshe ce ah kicin,Hafsa an ciyo gayu tamkʼar zata gasar kʼyau sai wani shisshige masa take don Jameelah taji haushi,dakyar yabar Baddo ta zauna acikinsu don cin abinci wanda saida Jameelah tayi da gaske kafin ya kʼyaleta,lokaci zuwa lokaci yake jifanta da harara idan har suka hadʼa ido,

Sai misalin sha dʼaya da rabi ya maida ita gida don ayau ne iyayenta zasu koma kano su kʼyaleta tayi hutu anan,koda suka koma gida ko kadan bata nuna musu komi ba,yana ajjeta ya juya ya koma bayan ya nemi kasim ammh be ganshi ba,yace ''ai zamu hadʼu watarana..ʼʼ

  Awajen Yumma Baddo zata tsaya harta kʼare hutunta........

   ______''''''_________

''Azeema kina jina ko?wallahi idan har nina haifeki toh saikin bar gidan mustapha wannan kʼaron,haka kurum kinje kin auri dangin mayu ba haihuwa ba komi,dubi duk sauran yanʼuwansa ma da sukayi auran ba haihuwa,towa ya sani ko mahaifiyarsu ce ke lashe yaʼyan aciki?ʼʼ

  Cikin muryar kuka Azeema tace''Haba Umma wattakullah kiji tsoron Allah,wannan wacce irin maganace kike yi ne haka?zato fa zunubi sannan kuma nina barwa Allah komi don haihuwar awajensa take,in yaso ya bada in kuma yaso yaki azurtawa,plsss umma karku rabani da mijina wallahi inasonshi sosaii...ʼʼ ta ida maganarta tare da barkewa da sabon kuka mai tsuma rai,azuciye umma ta doka mata tsawa''Dallah gafara can shashasha wacce batasan inda ke mata ciwo ba,toh saurareni nan mustapha na dawowa ko baki kʼira kin sanar mana da batun dawowar tasa ba tofa zamu sani don shigowarsa gari da fitarsa ba boyayyen abu bane,insha Allah zamu zo mu tafi dake tare da takaddan sakinki,Azeema ya zama dole kibar gidan mustapha,ga kannanki nan mata duk sun haihaifa ammh ke har yanzu shiru waya sani ma ko dakwai mahaifa ajikinki?kila hatta shi dʼin an rabaki dashi...ʼʼ Azeema tayi saurin yanke call dʼin don bazata iya cigaba da sauraron bakakʼen maganganun mahaifiyar tata ba,ta hadʼa kai da gwiwa tana cizgar kuka tamkʼar ranta zai fita,kusan watanni biyu kenan da iyayenta suka soma matsa mata lamba akan tabar gidan mustapha ammh taki don tana masifar son mijinta,kuma taki gayawa kowa wannan bukatar ta iyayenta hatta shi kansa mijin nata bata fadʼa mishi ba,mustapha ba mazauni bane,shi dʼin SS ne na gwamnar jihar kaduna,don haka be cika zama ba kullum suna kan tafiye tafiye ne,yanzu haka ma bashi agari akayi bikin danʼuwan nashi,

Sake barkewa tayi da kuka tana fadin''Babu shawarar wanda zan nema don kowa cewa zaiyi inbi umarnin iyayena kuma ni inason mijina bazan iya rabuwa dashi ba,Kasim nasan zaka taimakamun amatsayinka na jinin mustapha,tabbas kai kadai ne kawai zaka iya bani hadin kai acikin zuriʼarku....ʼʼ wani sabon kukan yaci kʼarfinta dakyar ta daga hannu sama tace''Ya Allah ka dubeni da idon rahama ka kawo mun mafita da gaggawa gudun karna afka cikin sabonka......ʼʼ

Tana cikin wannan halin nefa sai ga kʼiran mustaphan ya shigo wayarta,bayan sun gaisa yaji muryarta wani iri kamar tana cikin damuwa yace''Habibati ya naji muryarki kamar kinsha kuka?meya faru?ʼʼ saurin waskewa tayi tare da kʼago dariyar dole tace''wallahi babu komi hubbynah kawai kewarka nakeji...ʼʼ

Cike da tausayinta yace''Dnt worry nan da sati mai zuwa warhaka ina jikin matata...ʼʼ ta saki murmushin kʼarfin hali,yace''Ina Zuby take ne..!?ʼʼ

   ''Dazu umma tayi kʼiranta ta tafi gida ammh zata dawo anjima...ʼʼ yana tambaya ne akan kʼanwarta ta uku wacce takan zo ta tayata zama idan baya gari...

  

    _*BAYAN SATI DAYA*_

Tuni su Gidado aka angwance duk da cewa bawai yaji dadin yadda ya samu Hafsan bane ammh dai kawai ya batsar don azauna lfy,wani tafiyar gaggawa ne ya sameshi daga hukumarsu,zaʼaje wani taro ne na yʼan sanda ah garin lagos kuma shine zai jagoranci yankinsu,ana gobe zai tafi ya hadʼa kan matansa ya musu fadʼa sosai akan beso ya dawo yaji ance mishi kaza da kaza akansu,duk suka dau masa alkʼawarin zama lafiya,yace kowacce tana iya kawo wata acikin danginsu ta tayata zama idan har bazata iya zaman part dʼinta ita kadai ba,Hafsa tace zata kʼirawo Nabeelah kʼanwarta,

Jameelah kuma tace Baddo takeson adakko mata,cike da mmki ya kalleta yace''Ki rasa wacce zaki ce adakko miki sai Mubeenah?ʼʼ

  Tace''pls dnt say nooo sahibu inason yarinyar sosaii...ʼʼ ganin yadda ta marairaice yasa yayi naʼam da bukatarta kai tsaye tunda atleast ko ba komi ai tafi mishi Hafsa wacce ta nuna son kai ta zabʼi nata jinin ita kuwa Jameelar ta masa kʼara ta hanyar zabʼar wani nashi...

  Yace mata zaije ya dakkota da safe tunda tafiyar yamma ce zasuyi.........✍

  _*Ku biyoni kuji babban kuskuren da Azeema zata tafka arayuwarta,agaskiya mata muna ruwaaaa shiyasa akace yawancinmu gidan wuta direct😭 mata muji tsoron Allah,diz page is dedicated to all the women all over the globe*_

  _*juz 3 free pages remaining hurry and register*_

_ku nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_

_*#KISHIN_MATA*_

_*#2020_NOVEL*_

_*#SALO_NA_DABAN*_

_*IWA🖊*_

*🍃KISHIN MATA🍃*

               🍃🍃🍃

         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT



WɾƖTҼɾ

ى

 

ASSɷ

*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_

           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   

*#An_Intense_Jealousy_Story*

    _*💫BABI NA TARA...✋✌✌*_

  !.....Kansa akan cinyarta yace''Yumma don Allah ki dʼan mana aron yʼar wajenki man Jameelah ce keson tazo ta tayata zama kan na dawo..ʼʼ kokarin daga kansa tayi tana fadin''Don Allah ni dagani tunda kai bakasan ka girma ba wallahi ko Ramlah dai da take auta batta yin shirmen dakai kakeyi...ʼʼ ta ida maganarta tana mai zuba mishi hararar wasa,murmusawa yadanyi kan yace''Yumma kenan ni abar wannan batun don ke kanki kinsan indai akan kwanciya saman cinyar mahaifiyata ne toh anan bazan tabʼa girma ba,nidai ke nake sauraro shin zaki mana aron nata..?ʼʼ

''Ni duk kabi ka cikan kunni da zancen aro,wai wacece kukeson amaku aron nata ne?ʼʼ idonsa acikin nata yace''Baddo kuke ce mata ko?toh ita nake nufi..ʼʼ

Girgiza masa kai ta shiga yi take fadin''Gaskia bazai yuwu ba salon kaje ka dunga cin zalin yarinya tunda kai na lura dabʼiarka kenan son mugunta,toh bari kaji ko Ramlar ma babu inda zata balle wata Baddo..ʼʼ Ramlah ta bawa Baddo shekʼaru biyu,Ramlar tana da shekʼaru 19 ayanzu haka tana shirin shiga ss3 ne ayayin da Baddo keda 17 ita kuma Ss2 zata shiga,

  ''Haba Yumma ni babu wata muguntar da nake dashi,ni idan baka shiga gonata ba toh babu yadda zaʼayi na shigeka da bugu haka kawai,kima kirata ki tambayeta ko kallon banza ma be tabʼa shiga tsakanina da ita ba balle fadʼa har akai ga batun duka,Yumma in banda abunki ma ni ina ma aka ganni agida bayan tafiya nace miki zanyi kuma zamu kai sati guda acan,plssss Yummina ki mana aronta...ʼʼ

Ya ida magana tare da shimfidʼa mata fuskar tausayi,ajiyar zuciya ta sauke kan tace''Gidado in banda neman magana irin naka inace baga yʼarʼuwatta Hafsa ba,shin bata isheta zama bane saika dauki wata Baddo..?ʼʼ

  ''Haba Yummina ki fahimceni man,kowacce da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login