Showing 15001 words to 18000 words out of 102125 words
Chapter 6 - KISHIN MATA part Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx
ka bada hakʼuri sannan kace ka maidata...!ʼʼ
Caraf mami ta cafe tace''Ai wallahi koya bada hakʼuri ba komawa zatayi ba sai lokacin da muka so...ʼʼ azuciye Daddy ya kalleta yace''wai ke Amina meyake damunki ne..?ya zakice bazata koma ba shin kece keda iko da ita koni..?maza shiga ciki kibar maza suyi magana...ʼʼ
Tsoki tajah sannan ta shige tana gunguni,daddy ya dafe kansa cike da takaicin yadda ta dizgashi gaban surukansa,Mukhtar shi kansa ji yayi tamkʼar ya rusa kuka ko zaiji sanyi aransa,su baba haruna kuwa sai jinjina rashin mutuncinta suke,suka sake tabbatar da cewa lallai kam biri yayi kama da mutum,halayenta ne kaf yʼar ta kwasa,Shi kanshi Gidado aransa yace''Ashe halayenki ta kwaso tsaf...ʼʼ
Daddy yace''Don girman Allah kuyi hakʼuri kunsan shaʼanin mata sai ahankali,badamuwa yarinya zata koma dakinta ayau dinnan basai gobe ba..ʼʼ har ya mikʼe zaibi bayanta sai Gidado yayi hanzarin dakatar dashi yace''Daddy karka matsa mata don Allah abi komi asannu kuma ahankali,ni abunda yasa na saki Hafsa ba don komi bane illah fusatani da tayi,ta nunamun cewa ban isa da ita ba tare da yiwa matata da sauran yanʼuwana gorin haihuwa........ʼʼ
''Yo! Kujimun zancen banza fa toh kʼarya tayi..?nace kʼarya tayi..?su dʼin ba juyayyu bane..?ka gayamun yaʼyan da suka fito daga tsatson mahaifiyarka acikinku akwai wanda ya haihu ne...?baka ma gode Allah cewa Hafsa ta aureka ba tare da nuna damuwa akan rashin haihuwar taka ba..?ita wancan wahalalliyar ita taga zata jure zama dakai ammh Hafsa dai bazata koma gidanka ba,dama kaddarace ta hadaku kuma kaddarar ta rabaku,alhamdulillah naji dadin hakan sosai,akarshe ina mai shawartarku daku hanzarta binciken mahaifiyarku don ina tuhumarta akan cewa dasa hannunta acikin rashin haihuwarku dukah....ʼʼ
Gabaki dʼaya kallonta ake cike da mamaki da alʼajabi,ashe da Daddy ya korata ciki labʼe ta musu,afusace Gidado ya mikʼa jikinsa na mugun shaking with running tears yasa hannu ya ciro wata farar takadda ya isa ga daddy ya mikʼe mishi yace''Daddy kuyi hakʼuri ga takaddar Hafsan ammh kamar yadda na fada afarko ayanzu hakan ma ina kan bakana ne donni nagartaccen mutum ne wanda baya tabʼa canza maganarsa,i always stand by my words,idan Hafsa ta hankalta kuma taga zata iya cigaba da zama dani da lalurar da mahaifiyarta ta zayyano toh ina maraba da ita...ʼʼ da rawar jiki shima daddy yasa hannu ya karba,kafin yayi magana tuni Gidado yasa kai zai bar falon ana kiranshi ko waigowa beyi ba,dasauri Aliyu da sagir suka bi bayanshi,Baba Haruna da Baba munniru suma suka mikʼe afusace suka sallami daddy suka fito,dasauri daddy da mukhtar suka bi bayansu ammh ina ko sauraransu basuyi ba,
Afusace daddy ya koma ciki yana nuna mami da yʼar yatsa''Amina saʼarki daya ni ba irin mazajen nan bane masu daga hannu su daki matayensu ba,daʼace ni irinsu ne da ayau kin yabawa aya zakinta,ammh kije ni _*BILYAMINU AHMAD NA SAKEKI SAKI DAYA*_ sakamakon cin mutuncin da kikawa surikaina kuma surukanki,idan kinje gidanku kya musu bayanin hakan....ʼʼ yasa kai ya shige,
Mukhtar dasu Hafsa da suka fito suka shiga nanata kalmar innalillahi suna kuka gami da fadin'' haba Daddy haba Daddy meyasa kaima ka biyewa zugin shaidanʼʼ mami kuwa zubʼewa akasa tayi tana birgima har daddy ya dawo falon ya cillar mata fara takadda yana fadi cike da dacin rai''Amina na gaji da zama dake,ayau hakʼurina ya kʼare ga takaddar sakin nan arubʼuce sannan kuma gana yʼarki wanda mijinta ya bayar abata....ʼʼ ya fada yana sake cilla mata wata farar takaddar,su Hafsa sai kuka suke rusawa har Mukhtar,
Daddy ya shige ciki ya kulle kansa yana kuka,sam Allah be hadashi da mace ta gari ba,haka ma yaʼyansa ukun duk babu na kirkin gara gara Mukhtar yana da hankali sosai kuma baya biye biyen mata,shidai barshi da shaye shaye,
Can mukhtar ya nufi Hafsa ya shigeta da bugu yana fadin''shegiya yʼar iska ai duk kece kika jawo aka saki mahaifiyarmu kuma wallahi tun wuri ki dau damarar bautuwa acikin gidan nan,billahi azimu Hafsa babu tausayi ko rangwame atsakanina dake...ʼʼ kuka yaci kʼarfinsa ya cigaba da bugunta harsai da tayi laushi........
*********
Bayan fitar Aliyu ya samu Gidado yana dukan mota iya karfinsa hadda shuri yana kuka gami da fadin''Yumma why..?ni dama na dade ina zargin dasa hannunki acikin rashin haihuwar yaʼyanki sabida tsanar da kike nuna mana musamman ni tayi yawa ammh shiru kawai nayi don aganina bazaki tabʼa iya aikata abunda nake zarginki akai ba,Yumma meyasa kika hana mana haihuwa...?wani laifin ne mukayi miki da muka cancanki girman hukunci makamancin wannan...?you need to ans my question Asap....
Ya fada yana kokarin bude driverʼs side,Aliyu wanda ya gama jin zancensa shine yayi saurin dakatar dashi yace azuciye''kai Gidado meye haka..?shin kayi hauka ne..?meyasa kake kokarin barin maganganun matar nan suyi tasiri ne acikin zuciyarka..?
Azuciye shima yace''Aliyu ka rabu dani ai gaskia ta fada,itace mutum na uku data fadamun wannan maganar,sauran da suka gayamun ban tabʼa daukar zancen serious ba ammh ayau na dauki na mamin Hafsa don ina ji ajikina mahaifiyata tana da hannu agame da rashin haihuwata da sauran yanʼuwana....ʼʼ
Girgiza kai Aliyu yayi shima din zuciyarsa ta shiga zarginta ammh sai ya daure yace ahankali''plsss Gidado ka binne maganar nan kar kowa ma yaji don ba gaskia bane ni ban yadda ba....ʼʼ kafin yace wani abu sai gasu Baba haruna sun fito rai bace tare da sagir wanda ya koma dakko agogonsa daya manta dashi,babu wanda yace da wani kala har aka isa gida,Jamila sai kiransa take tayi awaya ammh ya kasa dagawa,can ta kira Sagir shine yake fada mata cewar ta kwantar da hankalinta mijinta nanan tafe nan bada jimawa ba,
Sanda aka zayyanewa Tsoho labarin abunda mamin Hafsa ta fada sosai ya fusata ainun don kusan zan iya cewa baʼa tabʼa soya ransa kamar yau ba,sai jeka ka dawo kurum yake tayi ana kallonsa kowa ya zubawa sarautar Allah ido da kuma jiran irin hukuncin dazai yanke,Yumma kuwa sai kuka take ta sharbawa tamkʼar ranta zai fita ji da tayi na ashe mutane zarginta suke akan dasa hannunta agame da rashin haihuwar yaʼyanta,Gidado ma kin bari yayi ya hada idanu da ita,zukatan wasunsu suma din suna zarginta ne,Tsoho ya daga murya ya soma magana cike da zafi''Jibi idan Allah ya kaimu ina son gabaki daya zuriʼar tsoho manya da kanana,na nesa dana kusa kowa ya hallara agidan nan,abuga asanar da kowa cewa akwai gagarumar meeting din gaggawa,zan nunawa matar nan cewa baʼa wulakanta zuriʼar Tsoho sannan kuma azauna lafiya,saina tabbatar dana sa ta jishi ajinin jikinta daga ita har yʼar tata...................ʼʼ
_*kuyi hakuri pls hidindimu sunsha gabana ne kwanan nan,ku sanya mahaifina cikin duʼaʼinku yau yake cika shekaru goma cif da rasuwa*_
_*1 extra free page remaining purchased by Nanarh Ayeesha,insha Allahu daga gobe pages din Nanarh ya kare don haka maza garzaya kiyi register da 200kacal don samun cigaban wannan littafin mai cike da kitimurmura,hajiyata ki sani koda kudinki saida rabonki*_
_ku nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._
*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...
07065481260..Ko kuma 09069067488
_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_
*🍃KISHIN MATA🍃*
🍃🍃🍃
_mai dauke da salo na daban🤙..!_
*♟
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT
WɾƖTҼɾ
ى
ASSɷ
*✍
*NA*
_*HAFNANCY LURF💕*_
_*[Hafseesee]*_
_*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_
*#An_Intense_Jealousy_Story*
_*💫BABI NA BAKWAI..🤚✌*_
!.....Su Gidado an afka cikin romantic moment dake itama Hafsan tasan takan harka don wani irin rikitashi tayi wanda har ya nemi fita cikin hayyacinsa,lallai ya yadda kowacce mace tana da nata baiwar dakuma salon tafiya da imanin dʼa namiji,mikʼewa tayi daga jikinsa taja hannunsa zuwa gado sai mamakinta kawai yake ganin yadda ta fishi zakʼewa da abun ammh kuma yadau alkʼawarin bazai tabʼa tauye mata hakkʼi ba,cire hijjabin tayi ta jefar akasa sannan ta kwanta asaman gadon daga ita sai wannan shara sharar night gown dʼin wanda ta daura masa zani akai sanda zatayi sallah,ammh ayanxu haka tun ah first scene😄 dʼin aka watsar dashi can akasa,
Albarkatun kiʼrjinta ne suka sake turning dʼinsa on,da sauri ya shiga kokʼarin kwafe rigar tou alokacin ne Baddo ta hau bugun gate babu gaggatawa kuma har ransu sunji wannan bugun,wani irin dogon tsaki ya saki yana maida rigar cike da annoyance yace''wai uban waye haka ne zaizo gidan mutane da fresh morning dʼin nan ya hau bugun gate tamkʼar mahaukaci thereby disturbing our peace..?ʼʼ
Ya nufi transparent slide door na dakin don dubawa,yana isa be bʼata lokaci ba yasa hannu yayi sliding kʼofar ya fice da sassarfa,sabida sauri be ankara ba ya bige da wani flower vase kuma sosai ya bugu don har ransa yaji azaba,dukʼawa yayi yana shafa 'yar yatsar data bugun cike da tausayin kanshi yake fadin''ouch! so painful..wallahi diz person must pay for all,na farko distracting my romantic moment and secondly ansa naji rauni,,tou billahil lazi dakwai kura kuma sai mutumin nan yayi ruwaaaa,Allah dai yasa ba wanda nake jin kunyarsa bane...ʼʼ ya ida maganarsa tare da mikʼewa yana dingishi,sai ciccije lips yake don azaba,dara daran idanuwansa ne suka sauka akanta ah saʼilin da securities suka bata hanya ta shigo rikʼe da kafcecen basket wanda yayi mata nauyi ahannu,kallonta yake cike da mamaki don beyi zaton itace zai gani ba as the arrogant gate knocker dʼin,tuni yaji wani irin mugun tsanarta ya sake mamaye zuciyarsa,like seriously he doesʼnt like the gal,saida ya bari ta kutsa kai cikin makeken gidan sosai har ta kawo tsakiya sannan ya doka mata wani gigitacciyar tsawa yace''K...! so dama kece wannan arrogant gate knocker dʼin?kece kikayi distracting peace na mutanen enviroment dʼina harma kika sa ni naji mugun rauni don son ganin useless human being dʼin ashe duk kece?arasa ma wanda zaʼa aiko gidana sai ke _*'YAR ISKA?'*_ Iʼll make sure dat ur death look lyk an accident today...ʼʼ
Fitsari ne kawai ya rage bata sakar ba ah wando sabida tsabar tsoronsa,ashe duk fushinsa da take gani wasa ne akan wannan dake shimfidʼe saman fuskarsa,sai dana sanin shigowa gidan take,tuni wasu hawaye masu dumi suka wanke mata fuska,daga kai sama tayi tana kallonsa jingine da makariyar benen waje ta bʼangaren Hafsan,tace cikin kʼaryewar murya''Sir...plssss..ka..kayiii hakʼuriiii ba..bazaann...saaake...ba...ʼʼ
Ko sauraronta beyi ba ya dubi wani security dake tikʼar dariyar wannan dramar yace dashi''kai Emmanuel sako mata chief don nasan shi kadai kurum ya isheta..ʼʼ ya bada order in a vocal tune expressing angriness,wanda aka ambato da Emmanuel ya dauke dariyarsa at once,cike da tausayi yace''Sir plsss dnt take it too far ka yafe mata,releasing chief will be very dangerous....ʼʼ wani wawan kallo ya watsa masa wanda ya kusan tarwatsa hanjin cikinsa yace in high degree of annoyance''U ar very stupid,kai ne zaka gayamun yadda zanyi?toh sannu ubana Alassana,,come on will you release the dog ko kuwa ka zabʼi ka rasa aikinka ne?ʼʼ
''Am sorry sir..ʼʼ ya furta tare da saluting dʼinsa sannan ya nufi cage din karnukan gidan wanda ke awani bʼangaren gidan ah bʼoye,Baddo kuwa tunda taji ya ambaci dog,taji gabanta ya hau bugawa dasauri sauri akan nada,ta shiga nanatawa in a low pitch ''Dog?D..o..g?..
Juyawa tayi taga wayam babu Emmanuel,haba sai kawai ta fashe da gigitaccen kuka tana fadin''Anku Emma don Allah karka sakeshi kuyi hakʼuri...ʼʼ ta dubi Gidado wanda ke kokʼarin danne dariyar dake neman cinsa tace in a vibrating tune''Ham..maaa don..Allah...ka...yafemun...ka..tuna..fa..ni..kʼanwarkace....ʼʼ
''Will you kip shut?ni banda kʼanwa yʼar iska...ʼʼ
Hafsa nacan kwance saman gado tana mai takaicin katse mata romantic moment dʼinta da akayi wanda ta dadʼe tana mafarki da dokin zuwansa,har kwallar bakʼin ciki ta zubar tsabar haushi,tuni kawai taji ta tsani wannan stranger dʼin tun bata ganta ba,tana son ta tashi taje don taga fuskar bitch dʼin ammh cikinta dake azabar murdʼawa don shaʼawa ya hanata motsawa,magungunan mata datasha ne ke cin ubanta anan,sai juyi take akan gadon rikʼe da cikin tana ciccije lips tamkʼar zata hudashi,Hakikʼanin gaskia Hafsa jarababbiyar macece wacce sam batta iya controlling kanta,tun awaje ta gama rabawa samari dandanon zumarta tsabar jarabar tsiya,Allah ne dai kawai ya kaddara auranta da Gidado wanda besa andau tsawon lokaci ba akayi aurensu,yana kʼiran wata can da yʼar iska bayan ga shahararriyar yʼar iskan nan acikin gidansa wacce bata kawo mashi mutuncin kanta gida ba,Jameelah tasan da wannan bakʼin tabʼon na kishiyar tata acikin binciken data gudanar,don haka Hafsa tana cikin ruwaaaa jamaʼa😅
Tsoki taja sanda taji muryar Baddo na bawa Gidado hakʼuri,dakyar ta mikʼe azuciye tana fadʼin''shegiya tsinanniya Allah yasa ya bari karnukan su yayyaga yʼar banzan,haba wani irin rayuwa kenan wai ace kishiyar gida bata barka ba haka kishiyar wajen ma bazata barka ka shakʼata agidan mijinka ba,wai meyasa ni rayuwar aurena yazo da badluck ne?ʼʼ ta rushe da kuka kan ta nufi inda yake...
Beji zuwanta ba sai jin saukar hannayenta yayi ta zagaye wuyanshi dasu,runtse idanu yayi cike da takaicin halayenta iri iri masu cike da abun mamaki,yanzu kunya anjima kuma akasinta,kallonta ya sauka akan damn cute face dʼin Baddo wacce take shirin tserewa ganin Emmanuel na tahowa dawani kosasshen police dog mai buzu buzun jiki,dogon halshensa awaje yana juyashi alokaci dʼaya kuma yana barking,
''Release...ʼʼ ya bawa Emma umarni,da sauri ya cikashi,Gidado ya daga murya yace da trained dog dʼin''Chief here is ur morning meal today so enjoy...ʼʼ ya furta yana nuna mishi Baddo da yatsa karen ya kada kai tamkʼar yaji abunda yace,da gudu ya nufeta adaidai lokacin Jameelah ta fito arudʼe jin ihun Baddo,
Baddo ta jefar da basket dʼin abinciccikan tana ihun neman ceto,sai ga kular toasted sandwich ya budʼe,,duk slices dʼin suka watse akʼasa,haka ma kular smashed chicken and ground beef cabbage sauce ya watso kasa har yadan bʼata mata kaya,flask dʼin kunun gyadʼan ne kawai ya tsira baʼayi asararsa ba,wani entrance door ne ta hango da gudu ta nufeshi,karen kuma hankalinshi ya koma kan special dishes dʼin da suke watse akʼasa,da sauri ya koma wajen yana lashe halshensa gami da karkadʼa bindinsa,Sai data kai kusa da Jameelah ta kamo hannunta sannan hankalinta yadan kwanta,ta kamo hannunta jiki na bʼari tace tana hawaye''Anti...jami..plsss..help..dnt allow..the..dog..to..harm...meʼʼ Duk jikin Jameelah yayi sanyi,ta daga ido sama zuwa part dʼin Hafsah zuciyarta na suya,tana hadʼa ido da Hafsan sai Hafsan ta dadʼa kankame Gidado don Jameelar taji haushi hadda wani kashe mata ido dʼaya gami da sakin shuʼumin murmushi,Gidado yayi wani wurgi da hannayen Hafsan ah saʼilin daya farga da abunda Chief keyi,he's really enjoying his dishes😀
''Waddafuck!!! wata sabuwa inji yʼan caca,breakfast dʼinmu ne haka chief keci hankali kwance?ʼʼ sai gani yayi karen ya karkadʼa masa bindi,afusace ya juyo har yana buge Hafsa yabi ta dakinta don sakkowa kʼasa ya samu Baddo,ahaukace yake fadin''This gal issay witch kuma wallahi sai ta girka mana sabo kafin ta tafi....ʼʼ
***
Acan waje kuma Kasim duk yabi ya gaji da jiran fitowar ita Baddon,agogo ya duba yaga 7:35am,jan dogon tsoki yayi yace''wai ni meya tsayar da yarinyar nan aciki ne?nifa tamun sauri na gaji da zaman mota kar basir ta kamani....ʼʼ ya ida maganarsa tare da kwantar da jikin seat ya kishingida yana mai lumshe idanu cike da takaici,sai furzar da iska yake lokaci zuwa lokaci idanunsa akan kofa,kuma sosai yake jin some noises na tashi kamar ackin gidan ammh heʼs not sure..
Janyota yayi daga jikin Jameelah tare da sharara mata wawan mari yace cike da tsanarta''Breakfast dʼin namu ne kika watsar akasa haka kare naci?toh billahil lazi sai kin mana sabo kafin ki tafi...ʼʼ ita marin ma be dameta ba kamar yadda yace sai ta girka musu wani,ta zaro idanu waje tana kallonsa,tun kafin tayi magana yace''Yes *MUBEENAH* you heard me right sai kin sake girka exactly abunda kika kawo mana kika kuma barar...ʼʼ wani sabon mamakin ne ya sake lullubʼeta jin ya ambaci ainihin sunanta abunda be tabʼa yi ba,sai taji duk duniya babu wanda yafishi iya kʼiran sunan hatta da waʼenda suka radʼa mata shi basu kaisa ba,
''Sahibu haba meye haka ne kake yi?which kind of wickednes is diz?meh yarinyar ta maka ne?
Jameelah ta fadʼa in high degree of annoyance,yatsa yasa ya datse lips dʼinshi yace''shhhhhhhh!yimun shiru anan tunda ke baki ga abunda tayi ba tou ni na gani don haka babu ruwanki sheʼs my sister...ʼʼ sai alokacin Hafsa data fito tasan cewa ai Baddon kʼanwarsa ce,ta maimaita''Sister?ammh ai ban tabʼa ganin fuskan nan acikin zuriʼarsu ba...ʼʼ
Wani sashin zuciyarta yace''In banda abunki yadda zuriʼarsu take da yawan nan kila harki kʼare rayuwarki agidanshi baki gama saninsu ba...ʼʼ
Angode ma ta sanyo hijabinta,ta ballawa Jameelah harara tana fadin''Munafuka.....ʼʼ ahankali ta fadʼa don kar yaji,daga kafadu Jameelar tayi tace itama ahankali''Dallah malama matsa baki duk wari babu tsafta,,na kaiki ah iya hadʼa munafurcin ne?ai duk inda munafurci yake toh tsuliyar na wajen...ʼʼ wayyo Allah hakika kalaman Jameelah sun soya ran Hafsa don kadan ya rage ta fasa ihu don haushi,ashe Gidado na jinsu shiru ne kawai yayi musu,ganin kar abun ya zamo rikici yasa duk ya tsawatar musu tare da basu umarnin komawa ciki,Hafsa taja tsaki ta soma shigewa kan Jameelar tabi baya,ya maido da hankalinsa akan Baddo yace''Tunda kinki ki gayan wanda ya kawoki toh muje ki duba abunda kika barar sannan mu shiga ciki ki girka yunwa suke ji...ʼʼ ya ida maganarsa tare da kamo hannunta tana tirjewa,tace cikin kuka''Toasted sandwich ne sai kuma smashed chiken and ground beef cabbage sauce da kunun gyadʼa ammh shi be zubʼe ba,sai dai kuma don girman Allah kayi hakʼuri ban iya ba...ʼʼ
Sakin hannunta yayi ya shiga binta da kallon mamaki,can yace yana murmushin takaici''haba dai wasa kike ko Mubeenah?ʼʼ
''Wallahi Hamma da gaske nake ban iya girkin zamani ba...ʼʼ ta furta tana