Showing 30001 words to 33000 words out of 102125 words
Chapter 11 - KISHIN MATA part Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx
rufemun baki munafuka ki gayamun uban wanda zai iya barwa cikinsa irin abunda kukamun..?zakizo mun da wani tsamin baki wai am not qualified for marriage toh sannu ke meh qualification dʼin ai naga kin kyankyashe kwai...!ʼʼ
Tuni wuta ya daukewa Jameelah don ta gano cewa gorin haihuwa ce ta mata,wani irin kukan kura tayi ta shako Hafsan tana kukan bakin ciki....
Adaidai wannan lokacin kuma aka iso da Gidado gida......
_*Extra free pages will start counting as from tomorrow buh mind you register is still goin on😜*_
_ku nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._
*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...
07065481260..Ko kuma 09069067488
_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_
*🍃KISHIN MATA🍃*
🍃🍃🍃
_mai dauke da salo na daban🤙..!_
*♟
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT
WɾƖTҼɾ
ى
ASSɷ
*✍
*NA*
_*HAFNANCY LURF💕*_
_*[Hafseesee]*_
_*fans ina matukar godia da nuna kulawarku agareni da jina shiru da kukai kwana biyu har wasunku suka nemeni awaya,wasu kuma sukamun dropping sako ta DM,ina godia kwarai da gaske hadda ma wa'enda Allah be basu ikon kira ba duk ina kaunarku dukah,Allah yabar zaman tare ameen👐*_
_*💍NANARH AYEESHAʼS PAGE..!😘*_
_*💫BABI NA SHA UKU...👐🤟*_
!...Mugun shakʼa Jameelah takaiwa Hafsa ah wuya tana mai kukan bakin ciki,Hafsa ta shiga kiciniyar kubutar da kanta ammh inaa! kʼarfin dan damisa ba daya yake dana zaki ba,Hafsa sai kakari take tana neman ceto,dakyar take iya fadin''Jameelah idan kika kasheni toki sani kema dʼin kashekin zaʼai don arubuce yake acikin constitutional book of law,duk wanda yakashe wani rai tofa shima dʼin zaʼa kasheshin,haka kuma zaki mutu kibar Suleiman da duk wani masoyinki kamar yadda nina kika rabani da nawa masoyan,sannan kuma gari zai dauka cewa kin kashe kishiyarki,mutane zasu dunga tsine miki da kuma laʼantarki,don haka bazan hanaki ba go ahead and killl meee...!ʼʼ ta ida magana dkyar,
Dasauri Jameelah ta hankadata ta fadi saman doguwar kujera,cike da dacin rai take magana cikin kuka''Hafsa idan na kasheki da hannuna meh nayi achieving arayuwa..?bʼacin suna..?shiga wutar jahannama da kuma dawwama acikinsa..?ko kuwa tsinuwar ubangiji da kuma fushinsa akaina..?shin da wanne zanji aciki..?
Girgiza kai tayi hawaye na cigaba da ziraro mata tace''Toki sani ni ba asararriya bace wacce zata koma ga mahaliccinta cike da buhun asara ba,Hafsa zaki mutu ammh insha Allahu bazan zamo sanadi ba,sannan kuma ban tabʼa tsammanin cewa girman jahilcinki har yakai ki dora ayar tambaya agame da rashin haihuwata ba,bazan ce miki banji zafi ba don dalilin dayasa nakai miki shakʼa kenan,naji zafi sosai ammh abunda nakeson ki sani shine,shi rashin haihuwa na Allah ne wanda bashi da magani sai dai adduʼa,idan Allah yaso sai ya bayar,sai amikʼa lamura zuwa gareshi akan ya kawo masu alkhairi domin kuwa yara sukan zamo masifa idan har babu alkhairi,don haka yarʼuwa ni zabʼi na alkhairin nake nema daga wajen ubangijina,idan har dakwai rabo na alkhairi Allah ya gaggauta azurtani da yaʼya masu albarka,idan har kuma babu toh ina mai rokʼonsa daya kʼyaleni hakan babu haihuwar...!ʼʼ
Ta ida magana tana mai rushewa da kuka mai tsuma zuciya,duk da cewa sosai Hafsa ta tausaya mata ammh sai bata nuna hakan ba,ta mikʼe tana zuba mata dirty look gami da fashewa da dariyar kafi mahaukaci ban haushi,Jameelah ta tsaida kukanta tana binta da kallon mamaki,lallai ta yarda babu talauci kamar jahilci,sai datayi mai isarta kan tace''malama ni zancen soki burusunki beyi tasiri akaina ba,abunda kawai na sani shine all of you are barren,ke da wannan sakarar matar kʼaninsa da kuma figegiyar kʼanwarsa dʼin nan surayya take da suna ko..?toh dukanku juyayyu ne waʼenda suka rako mata duniya....ʼʼ
Karaf! acikin kunnen Gidado daya kutso kai cikin falon,gabaki dʼaya suka zuba mishi idanu cike da mamakin ganinshi bayan ya tabbatar musu da cewa zaikai tsawon kwana bakwai acan,ammh dududu yau ya cike kwana hudu,sannu ahankali yake takawo zuwa inda suke fuskarsa amurtuke tamkʼar be tabʼa sanin dariya ba,idanuwansa akan Hafsa wacce tsoro da kuma fargaba ya gama cikata tsaye anan,kamar kace mata arrr ta arce ah guje,babu abunda kake ji sai kʼarar cover shoes dʼinsa masu suffar kifin ruwa,zuciyarsa tamkʼar zata zillo waje tsabar bakin cikin abunda Hafsa ta fadʼa,wai matarsa ce da kanta takewa yanʼuwansa gorin haihuwa,amanta da batun Jameelah tunda kishiyartace,don haka idan ta mata gorin ba abun mamaki bane,ammh shine har zata sako yanʼuwansa aciki..?abune wanda bazai tabʼa karba ba acikin gidanshi..
Jameelah ce tayi kʼarfin halin cewa''sahibu..barka...da..zuwaa...ʼʼ saurin daga mata hannu yayi cike da tsananin bʼacin rai yake fadin''Sauraramun nan...!rike barkanki bana bukatarsa,yanzu so nake kowaccenku ta shiga ciki ta dakko mayafinta ta wuce gidansu taje ta huta saina nemeku,maza nace...!ʼʼ
Kuka sosai Jameelah ta fashe dashi cike da mamaki take fadin''Haba..! Haba..! Sahibu plsss ka dena biyewa bacin rai wallahi saita kaika ta baroka,ban gane zancen muje gida mu huta ba bayan ah iya sanina nan dʼin shine gidanmu,kuma babu wani gidan da muke dashi wanda ya wuce nan dʼin...!ʼʼ
Afusace ya dubeta da jajayen ido wanda yasa hanjin cikinta canza position yace''kuna dashi inajin mantuwa kikai..! Ina nufin gidan iyayenku zaku wuce kubar mun gida yanzun nan har saina nemeku...!ʼʼ
Wani irin shewa Hafsa tayi tace''Billahil azimu saidai ita ta tafi ammh banda ni,Allah na tuba ma yaushe akai auran da har zan soma zuwa gida da sunan matsala..?dududu ma yau kwanakinmu goma sha dʼaya da aure shine zakace in tafi gidanmu saika nemeni...?wallahi inajin dai wasa kake Suleiman,toka sani babu inda zani ruwan daya tafasa ya dadʼe be kʼone ba.....!ʼʼ
Wannan magana tata ya sake fusatashi sosai don dama bata san cewa cike yake da ita ba,murmushin yake ya sakar mata kan yace''haka kikace ko..?ʼʼ
''Eh din haka nace kuma kai baka isa kayi komi akai ba mtssw...ʼʼ ta fadʼa tana girgiza kʼwankʼwaso,shi kuwa runtse idanu yayi jin yadda zuciyarsa ke azalzala tamkʼar ana caccaka masa mashi,can ya budʼe idanun ya saukesu fes akanta yace''Hafsa yanzu kuwa zan nuna miki cewa ni din dʼan halak ne na haifu kuma na isa,,kije ni _*SULEIMAN ALASSANA GIDADO NA SAKEKI SAKI DAYA,IDAN KIN HANKALTA NAN GABA INA IYA MAIDAKI,IDAN KUMA AʼAH HAKANAN ZAKI CIGABA DA TAFIYAR DA RAYUWAR TAKI BABU DAʼA GA MIJI TOH IDAN KIN SAMU WANI KIYI AURENKI....!ʼʼ*_
ba ita kadai ba hatta Jameelah saida gabanta yayi mummunar faduwa,Hafsa ta fashe da kuka gami da zubʼewa akʼasa tana kururuwa''wayyo Allahna na shiga uku ya sakeni bayan ko sati biyu ban cika agidanshi ba,ni meh zancewa iyayena..?Suleiman Allah ya isa tsakanina dakai ban yafe maka da irin wannan tozarcin dakamun ba....!ʼʼ ta sake budʼe wani shafin kukan abun dai gwanin ban tausayi,Jameelah kuwa toshe bakinta tayi jin wani irin uban kuka na neman kufce mata,duba dʼaya zaka mata ka tabbatar da cewa sheʼs in deep shock,sai tunano maganar da yayi mata adazu take,ah inda yace _''Ai bazaki masan na cika zuciyar ba sai kinji kalmar saki ya fito daga bakina tukun...!ʼʼ_
Ah gigice ta dubeshi tana kuka tace''No sahiba plss ka janye sakin don ba ita yakamata ka saka ba niche ya dace ka sakan,karfa ka manta dani dakai mun ajje magana akan hakan,ko kuwa ka manta ne dana ce maka na gwammace ka sakeni da in fadʼa maka wacce ta maka rashin kunya awaya..!?Sahibu ka tuna _*'JAMEELAH'*_ ya dace ka saka ba _*'HAFSA'*_ ba....!ʼʼ
Ta ida magana tana dukan kʼirjinta,dubanta yayi akaikaice kan yace''Ina sane ba giyar mantuwa nasha ba,kuma akan hakan ne yasa nace ki tafi gidanku ita kuma na saketa ne sabida rashin daʼa ga miji don ta nuna mun ban isa ba shiyasa na nuna mata cewa _*DCP SULEIMAN GIDADO*_ isasshe ne ba saʼar wasanta ba....!ʼʼ ya fadʼa yana dukan chest nashi da kʼarfi...
Har Jameelah ta budʼe baki zata sake magana yayi saurin taran numfashinta ta hanyar doka mata tsawa''Karki sake ki kuma magana kawai kiyi abunda ya dace,kije saina nemeki...!ʼʼ dasauri ta juya tana cizgar kuka ta dauki dankwalin abayarta dake yashe akan wani one seater tana shirin yafawa tsabar rudu,
Cikin kakkausar murya yace''Kar ah sake ah fitar mun da wannan ficiciyar mayafin,aje ah sako hijabi ko babban mayafin dazai suturta jiki dakyau don har yanzu amatsayin _*MATAR DCP SULEIMAN GIDADO*_ kike,don haka go in there and get something to cover ur body maza nace...!ʼʼ
Ya fada atsawace yana mai nuna part dʼinta da hannu ba tare daya kalleta ba,hallau mamakinsa take don bata tabʼa ganin mugun fushinsa irin nayau ba,dasauri tabi umarninsa tana kuka ta shige part dʼinta,minti biyu tayi sai gata ta fito jaye da karamin trolley dʼinta,yana ganinta dashi yace''What do you mean..?ni bance ki tafi da kaya ba single dʼinki zaki wuce ga wacce zata tafi da nata akwatin...!ʼʼ ya fadʼa yana nuna Hafsa dake zubʼe akasa tana rusar kuka,ya cigaba''Don haka amayar kuma na baki juz 30secs to do dat...!ʼʼ
Da gudu ta koma tana kuka,ko 30secs dinma bata cika ba ta fito rike da wayarta da makullin motarta tana kuka ta wucesu,harta murda handle dʼin kofa taji saukar amon maganarshi acikin kunnuwanta''For the very last time wacece ta kʼarbe waya ahannunki tamun rashin kunya...?ʼʼ
Kamar bazatayi magana ba ammh sai wani bʼangaren zuciyarta yace kawai ta fada juz to save her marriage,abun kunya ne taje gida tace musu wai sun samu yar matsala ne da Gidado karon farko abunda be tabʼa faruwa dasu ba kenan don ko yajin nan da wasu matan keyi bata tabʼa yinshi ba,
_''*MUBEENAH...!*_ ce ......ʼʼ ta fadʼa with a shaking voice
Cike da tsantsar mamaki yake fadin''Mubeenah kuma..?wacce Mubeenar kike nufi kenan..?
Juyowa tayi tana mai fuskantarshi gami da share hawayenta sannan tace''Mubeenah dai wacce ka sani kʼanwarka dʼiyar babanka na kano wato Baddo...!ʼʼ
Dariya ya saki yana fadin''u canʼt juz be serious..! yarinyar da take masifar tsorona dai baza tabʼa gigin yin abunda wannan tayi ba,Hearthrob kibar rainawa kanki wayau da kuma bʼatawa kanki lokaci ki fito fili ki gayan ko wacce shegiyarce,idan kuma kinki toki tafi gidanku saina nemeki kamar yadda na fadʼa afarko...!ʼʼ
''Na rantse da girman Allah itace kuma ai gaskiya ta fadʼa ba kʼarya tayi ba,plss change for good...ʼʼ ta fadʼa ah kufule,
Afusace yake fadin''Yanzu Mubeenah ce har tayi kʼarfin halin gayamun waʼennan bakʼakʼen maganganun...?yar cikina..?don wallahi na isa haifen wannan yarinyar,kafin ta fito duniya na riga da na balaga kuma an tabbatar da cewa zan iya bawa wata ciki asannan aka haifeta,ammh wallahi ta debo ruwan dafa kanta da kanta,yanzu tana ina...?ʼʼ
Shiru ta mishi tana muzurai hakan yasa ya sake doka mata tsawa''Nace tana ina kin mun shiru...?
Dasauri tace''Ta wuce gida...!ʼʼ
Murmushin takaici ya saki kan yace''Aiko mahaifa ta koma na rantse da Allah saina kwakulota ayau,ki koma ciki tunda ki fadamun gaskiya...ʼʼ
Har zai shige part dʼinta sai yaji Hafsa tace''Tunda kace ta zauna toh wallahi nima dʼin zamana zanyi babu inda zani kuma saika janye sakin....ʼʼ shifa harga Allah yama manta da batunta sai yanzu ya tuna da ita data mishi magana,afusace yace''shikenan kita zama,kuma wallahi kika sake na fito na sameki saina kara miki saki dʼaya kuma Allah i mean it...ʼʼ
Dogon tsaki ta sakar tace''Nima dʼin ai da gaske nake ina nan wallahi bazan je koʼina ba ka dadʼe baka karamun sakin ba...!ʼʼ
''Fine Hafsa..! ni kuma Suleiman zan nuna miki ta yadda akai na banbanta da sauran mazan...ʼʼ yana gama fadar hakan ya shige part dʼin Jameelah,
Jameelah ta matsa tana nunawa Hafsa kuskurenta,amaimakon tayi ladab sai mikʼewa tayi tana jerowa Jameelar ashariya kala kala har dai Gidado ya fito cikin kananun kaya da makullin mota ya cimmata,kallon tsana ya shiga jifanta dashi tun kan ya karaso wajenta kuma ganinsa besa tabar zagin Jameela ba wacce ita tayi shiru kanta akasa,
Afusace ya daga murya yace _*''NI SULEIMAN ALASSANA GIDADO NA SAKI MATATA HAFSA BILYAMINU SAKI BIYU IDAN TA HANKALTA NAN GABA INA IYA MAIDATA,IDAN KUMA AʼAH HAKANAN ZATA CIGABA DA TAFIYAR DA RAYUWAR TATA BABU DAʼA GA MIJI TOH IDAN TA SAMU WANI TAYI AURENTA....!ʼʼ*_
Wani irin kukan kura tayi ta cakumo rigarsa tana kuka''I so much hate you suleiman kuma wallahi babu inda zani....ʼʼ
''I so much hate you too baby,now out of my house karki kuma mun taurin kai if not zan karashe sauke igiyar auranki dayayi saura akaina...ʼʼ ya fada yana sakar mata wani irin killer smile,kuka take mai daga hankali tamkʼar zata kashe kanta,Jameelah ma kukan take tana rokonsa kan ya maidata ammh ina idanunsa sun riga da sun rufe,ya umarci Jameelan data shige ciki kafin ta samu nata,dasauri tabi umarninsa gudun kar nata igiyar auran ya samu tangarda,
Har ya kusa da kofa zai fita ya daga murya yace''Hafsa idan kika bari na rigaki fita waje Allah saina karashe sauke igiya dayan...!ʼʼ yadai fada ne ammh harga Allah bekai zuci ba don kawai ya bata tsoro ne,dagudu ta kwashi hijabin da Jameelah ta ajje ta kwasa aguje har tana tureshi ta rigahi fita,awaje ta saka hijabin shi kuwa sai danne dariyarsa yake,ko pim bata kara ce mishi ba tabar gidan da saurinta gudun karya furta sakin karshen don ya tabbatar mata da cewa shi dʼin isasshe ne kuma zai iya aikatawa,securities na kokarin tsaida ita ammh ko takansu bata bi ta fice da kafa aguje tamkʼar mahaukaciya sabuwar kamu,fadawa motarsa yayi ya bata key,da sauri aka wangale masa gate,masu tsaron lafiyarsa suka matso kusa sukace mishi bazasu iya barinsa ya fita shi daya da goshin magrib dinnan ba,yace musu donʼt worry iʼll be fyn,atsiyace yabar gidan,ko meh kama da ita be hango ba hakan yasa straight ta dauki hanyar central area garki wato family house zashi kenan,
Koda ya isa ya cimma an ana kokarin tada iqamar sallar magrib ne,ah daidai kofar gidan yayi parking sannan ya nufi masallacin gidansu don sauke farali,yana lure da yadda Kasim keta kauda fuska don karsu hadʼa idanu,murmushi kawai ya saki ya kuma nuna kamar besan dashi awajen ba,ya gaisa da samarin gidan da kuma yabbaninsa waʼenda keta mamakin saurin dawowarshi,ce musu kawai yayi sun kammala abunda yakaisu da wurwuri ne,har aka idar da sallah Kasim be bari sun hadʼa idanu da Gidado ba don har sauri saurin saka takalmi yake yabar wajen,waigowar da zaiyi sai ganinshi yayi abayansa yana jiran fitowarshi,gabansa yayi wani irin tsalle kamar zai fado waje,jan hannunsa Gidado yayi suka koma gefe yasa hannunsa yana dan bugun kafadarshi yace''Clever boy kwantar da hankalinka ni bata naka nake ba yanzu ta budurwarka nake,wato ka koya mata rashin kunya sannan kuma kace tamun ko..?toh dafatar ka shirya cetonta don yau mai kubutar da ita ahannuna sai Allah...!ʼʼ
Ya fadʼa yana nannade hannun rigarsa tamkʼar wanda ke shirin dambe da saʼansa,ya kada kai ya shige cikin gida yabar Kasim tsaye anan da tsananin mamaki da takaicinsa,Part dʼin Yumminsa ya nufa straight ya tarar tana wanka hakan yasa ya nufi dakinsu Ramlah direct,suna can suna kallon wani india film ah system dʼin Hamma Aliyu wanda dʼa ne ga goggo Boddiya yakanzo ya yini agidan lokaci zuwa lokaci,Gidado be shaidashi awaje ba if not tare ma suka jera wajen sallah,Aliyu nada shekaru 35 aduniya kuma maʼaikacine awani industry na raw materials,daga shi har Gidado basa wani shiri don kowannensu naji da girman kai,shine jikan tsoho na biyu agidan amma ya kasance ta bʼangaren yʼa mace ne,tunda ya kyalla idanu akan Baddo yaji ta mishi kuma yanason ya aureta tunda dama can bashi da auran,be damu da kankantar shekarunta ba hankalinta ya yaba mawa,ammh sedai ko kadan be beri ya fallasa mata sirrin zuciyar tasa ba,zai samu tsoho ne da zancen,tunda su Ramlah suka dawo daga gidan Gidado suka cimmasa shine fa suka hanashi sukuni sai fira don tanan ne yadan banbanta da Gidado akwai sakin fuska ga kannensa ammh bandasu OA😅,dazai tafi sallah shine Ramlah suka kwace system dʼinsa dake su mayun kallo ne suka nufi daki dashi,aka baje saman gado ana kallo,ita dasu Hanifa da Baddo,su wajen biyar,suna tsaka da kallon sai ganinsa sukayi ya fadʼo dakin tamkʼar an jefoshi.............✍
_*Wayyo Allah Gidado meh kayi haka ne?😭 tofa ga wani Aliyun ya danno fa kuma wai shima din baddon yakeso😳koya zata kaya..?muje zuwa...*_
_*4 extra free pages remaining purchased by Nanarh Ayeesha buh mind you registration is still goin on😜*_
_ku nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._
*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...
07065481260..Ko kuma 09069067488
_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_
*🍃KISHIN MATA🍃*
🍃🍃🍃
_mai dauke da salo na daban🤙..!_
*♟
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT
WɾƖTҼɾ
ى
ASSɷ
*✍
*NA*
_*HAFNANCY LURF💕*_
_*[Hafseesee]*_
_*💍NANARH AYEESHAʼS PAGE..!😘*_
_*💫BABI NA SHA HUDU..💥*_
!...Ramlah ce tayi saurin shutting dʼin system dʼin jiki na rawa ta sakko kasa tana hawaye,sauran ma suka mara mata baya ammh banda Baddo wacce tayi kokarin danne tsoronsa taki sauka,koda taga yana kwance belt kin motsawa tayi ammh badon bata tsoron bane kawai kʼarfin hali da kuma kokarin nuna jarumta mutuniyar take,rinannun idanunsa kʼyam akanta yana mamakin sabon sauyin da aka samu atattare da wannan yarinyar wai kwata kwata ta dena tsoronsa,taya ma akai yayi sakacin da har hakan ya faru ne..?ammah ai babu damuwa yanzun nan kuwa zai maishe da tsoron nashi