Showing 93001 words to 96000 words out of 102125 words

Chapter 32 - KISHIN MATA part Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

5879

namu acikin barnar da kika aikata...?" Abbanta hadda cire hular kansa ya wurgeta dashi yana fadin"Don uwarki yi magana nace meye namu aciki...?" Mami tace Cike da jin haushin zagin daya gunduma mata"A"ah ubanta dai tunda da alamu kai tayo gado, ai Allah ne ya kamaka don ance duk wanda yay zina da ƴar wani sai anyi da nashi, gashi nan abun kunya da auranta ma ta aikata wannan abun tirrr ɗin……Muhammad wallahi abunda ka shuka shi kake girɓewa…abunda kayi shi za"ayi maka don wannan alkawarin Allah ne, ashekarun baya can shekaru kusan talatin da suka shuɗe ka taɓa yiwa wata ƴar aikinmu fyaɗe harka korata ko zaka iya tunawa…? Har tace maka insha Allahu sai an rama mata akan ƴar cikinka…?toh gashi nan Muhammadu Allah ya rama matan donshi baya barin azzalumi kamarka ya tafi hakanan har sai yaga sakayya........"

Ta barke da kuka mai tsuma zuciya, babu abunda kake ji na tashi sai kalmar innalillahi wa"inna ilaihi raji"un da kuma Allah wadai daga bakunan jama"a, kuka sosai Azeema ta sake fashewa dashi tana fadin"Innalillahi wa"inna ilaihi raji'un Abba ashe hukuncinka ne na karba ban sani ba...? Ya Allah meyasa baka bar abun ya tsaya ah iya kansa ba har sai daya shafeni...?

"Ai wannan alkawarin Allah ne don haka karki kuskura ki dora ayar tambaya akai, kiyi kuka da mahaifinki don shine ya shafa miki wannan masifar sannan kuma harda son zuciyarki aciki domin kuwa ki sani ba laifinsa ne kadai ba, tabbas kema kin taka naki rawar awannan kazamin tafiyar...." acewar Aliyu, shima ɗin jinjina aka miƙa masa,

Azeema tace tana jan majina"Tabbas da nawa laifin aciki ammh na iyayena yafi yawa, su suka matsa akan cewa lallai saina rabu da mijina tunda babu rabo atsakani, suka matsa mun lamba akan dole saina nemi saki awajen mijina in fito in auri wanda sukeso, hakan yasa na shiga cikin tsantsar tashin hankali mara misaltuwa domin kuwa ina masifar son mijina bana fatar yau mun wayi gari ace mun rabu don zuciyata tana iya yin bindiga, banyi gangancin sanar dashi ba don nasan yana iya yi musu abunda sukeso shiyasa kai tsaye ba tare da neman wata shawara gun kowa ba na nemi *KASIM* ƙanin mijina kasancewar kamanninsu da juna ya ɓaci, don haka idan har rabo ya ratsa atsakaninmu har kuma ɗan yayi kama dashi Kasim ɗin toh tamƙar Mustapha shine ubansa, don haka babu wanda zai dora ayar tambaya akai, da fari kasim ɗin bai yadda ba har shine yake ta nuna mun illar yin hakan da irin zunuban da zamu kwasa, ammh alokacin nayi nesa bana jin kira, idanuna sun riga sun rufe, matsin iyayena da kuma shaiɗanina sunci galaba akaina, burina kawai naga na samu rabo kona samu iyayena su banni na shaƙi iskar duniya, gashi banci nasara ba sai tarin zunuban dana kwasa da kuma kafirin kunya........" ta rushe da wani sabon kuka mai fidda sautin tausayi.......



"innalillahi wa"inna ilaihi raji"un wayyo! ni Hauwa'u ni nasan abunda nima na shuka ne ya komo kaina....na halaƙa zuri"ata da hannuna biyu, ina mai takaicin wannan rana da tazo agareni da baƙin fuska………" kukan baƙin ciki ya kubce mata,gabaki daya aka waigo aka zuba mata idanuwa cike da tsantsar mamakinta, kowa fuskarsa dauke da tambayar abunda ita kuma ya shafeta acikin wannan lamarin, hatta su kansu masu laifin dakatawa sukayi da kukansu suka zuba mata idanu baki buɗe.............…



Haj.karama matar Baba Alseny ce tayi karfin halin cewa"Tofa!… rikicin duniya da mai rai ake, ana wata ga wata, ana bikin duniya ake kuma na ƙiyama……………………✍"



_*Tofa! Jama"a wacece wannan Hauwar....?*_

_muje zuwa mutanena👭_

_*HAFFY MOUSTY💕*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

   _LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

   _*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

   _ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA TALATIN DA TAƘWAS...💥*_

……Kafeta da jikakkun idanu Kasim yayi wanda suka canza launi izuwa red danger tsabar tashin hankali, aɗaya ɓangaren kuma gabansa sai harbawa yake dasauri dasauri, shine yayi ƙarfin halin cewa"Momy bamu fahimceki ba…?meh kike nufi ne da abunda kika fada..?"  Tsoho ya kara da"Hauwa'u meh kika shuka da kike girɓewa ayanzu…?taya kika halaka zuri"arki da hannunki..?munaso mu sani..." fashewa tayi da kukan nadama tana fadin"Tsoho menene ban aikata ba..?nayi imani da Allah tashin hankalin da ahalina suka tsinci kansu aciki niche sila, kubar ganin laifin kowa ku dorashi akaina don ta dalilina ɗana Kasimu yake cikin wannan musifar, sabida na tabbata ishara ce Allah ya nunamun bisa ga babban kuskuren dana tafka, sa"annan ta dalilin tonuwar asirinsu duk da cewa alokacin ba"a kai ga cin nasara ba su Gidado suka samu mummunar hatsari har mijina ya rasa rayuwarsa...."

Sake fashewa tayi da matsanancin kuka tana fadin"Haƙiƙa duk aikin da son rai ya shiga cikinsa toh tabbas sai ya ɓatashi komin muhimmancinsa, haka kuma duk wanda yayi sakaci har son zuciya ya rinjayi haƙurinsa da kuma imaninsa toh ya sani zai halaƙa, mafi tsananin jihadi shine yaqi da bin son rai domin kuwa duk wanda ya hanawa zuciyarsa abunda take so na saɓon Allah, toh haƙiƙa wannan ɗin ya huta daga sharrin duniya da bala"in dake cikinta, kuma zai kasance an kiyayeshi an kuma tseratar dashi daga cututtukan cikinta, da dukkan alamu nikam bani da rabo domin kuwa na gama gogawa kaina baƙin fentin da har ya shafi gudan jinina…" kuka yaci mugun ƙarfinta, sai binta da kallon mamaki kawai ake tayi don babu wanda ya gano inda zancen nata ya dosa, Hanifa wacce ke zaune kusa da Ramlah take ta faman rusar kuka tunda uwar tasu ta soma magana ne tace"Momy don girman Allah stop beating around the bush....ki fito fili ki gaya mana abunda kika aikata don kowa anan kin barshi ne acikin duhu, ki taimaka ki ceto zuciyoyin dake cikin zullumi plssss.."

Ita kanta kuka ne yaci ƙarfinta, kusan tsawon mintina uku Momy bata ce kala ba hakan ya sake fusata wasu acikinsu, su Goggo Binta suka hayayyaƙo mata tamƙar zasu cinyeta ɗanye ba shiri ta danne kukanta ta soma bayani tana mai ciccije leɓuna"kuyi hakuri abun ne babu dadin ji ammh ya zama dole na fada, domin kuwa yau dubu ne ya cika, inason ku gafarceni don komai da zan fada *KISHINMU NA MATA*  ne ya janyo mun hakan, Ummerherny idan zaki natsu ki duba kakaf zuri"ar nan Tsoho yafi sonki da kuma ya"yanki, hakan ne ya doramun tsananin kishinki dana ya"yanki acikin zuciyata, bama kamar Gidado wanda bana burin na budi idanu na ganshi araye sabida irin tsanar da nake mishi har yakai girman na fir"auna da Musa, kasancewar acikin jikokin gidan nan Tsoho yafi qaunarsa, sa"annan kuma da takurawa ɗana kasim da yake yawan yi kan ya gyara rayuwarsa hakan ya kara hura wutar tsanarsa azuciyata, nasan tabbas sonsa yake shiyasa yakeson yaga ya daidaita rayuwarsa ammh dake bana qaunarsa shiyasa nake ganin laifinshi,

Tsoho bai wani damu akan ƴa"yan kowa ba saina Ummerherny, su dinne abun tinkahonsa hakan yasa naci alwashin kawo musu cikas arayuwa, naci burin rage musu farin ciki kota halin kaka ne, niche nan na shiga tsakanin ummerherny da Gidado, na sanya tsanarsa acikin zuciyarta har take ganin komai yayi arayuwarsa ba daidai bane, na cika mata zuciya da damuwar ya"yanta ta hanyar hana musu haihuwa.....zuciyata fari kwal ina mai jindadin ganin damuwarsu, haka zalika shima Tsoho yana cikin damuwar, hankalina bai taɓa dagawa kan wannan makircin dana haɗa ba sabida kowa yana yiwa abokiyar zamanta kallon itace keda sa hannu akomai kasancewar ita Allah bai bata rabo ba toh shiyasa take kishi har tayi shige shigenta ta hanawa ya"yan yar"uwarta samun haihuwar...ina nufin *HAJIYA HADIZA* wato *HAJJU*………azatonku wannan *WANKAN RUWAN KWARYAR DA KUMA SHANTA* shine yake hana musu haihuwa…?toh albishirunku nima ina da nawa *RUWAN KWARYOYIN* ɓoye adakina wanda ke dauke da sunayen *JAMILA* , *HAFSA* , *AZEEMA* ,da kuma *SURAYYAH* .....Na Baddo ne kawai babu don an gayamun cewa tafi ƙarfina shiyasa har ta samu rabo, ayanzu dinma bawai azaune nake ba ina yin duk wani shige shigena na ganin ɗan bai zo duniya ba…………"

kasa karashewa tayi kuka yaci mugun ƙarfinta, sai kalmar innalillahi kowa keta ambata yana mai zubar da ruwan hawaye masu radadi, wannan al"amari nata yafi tsinkar da zuciyoyin mutan katafaran falon don nata abun ta haɗa ne da shirka, tsawon lokaci aka kwashe ana cizgar kuka babu wanda ya iya ce da ita kala, can Gidado ya nunata da ƴar yatsa yana kuka"Hajiyar kasim kin cucemu! kin kuma zaluncemu daga ni har yan"uwana, saidai kuma ki sani dubunki ne ya cika shiyasa kika gurfana agabanmu ayau kike tona irin makircin da kika kulla, ki sani ba Mubeenah kadai ba hatta da dan cikinta sai sun zame miki dodanni masu tsananin firgitarwa wa"enda idan akace ko kallonsu ne kiyi bazaki iya ba balle har ta kaiki ga kusantar inda suke...." tsaigatawa yayi yana mai sakin murmushin ƙarfin hali kan yacigaba"Kuma kinsan mai...? Ni Suleiman Alassana Gidado bazan ja miki kalmar Allah ya isa ba domin kuwa Hakuri mabudi ne na fita daga kunci, kuma ana karfafa shi a lokacin aukuwar fitina da masifu, Kuma addu’a ce makami mafi karfi ta yakar abokan adawa. Mai tsira da amincin Allah ya ce: _*"Ka ji tsoron addu’ar  wanda aka zalunta, domin lallai ita babu hijabi a tsakaninta da Allah.”*_  don haka in ta nine kije na barki da Allah kuma matayen nawa suma sun barki da mahaliccinsu, Allah zai saka muku ko my Meelah da Hafsyna...?"

 

 

Ya ida yana duban inda Jamila da Hafsan ke zaune rungume da juna suna cizgar kukan zaluntarsu da akayi bayan duk sun yadda da wannan matar, bayan har girki take musu tana aikowa dashi acikin kwanakin amarcinsu, shiyasa akace lallai mutum ka basshi kawai, da rawar murya Jamilar ke fadin"Eh Sahibu mun yafe mata wallahi…! mun yafe mun yafe..." ta fada tana kai kokarin danne kukanta, alokaci guɗa kuma tasa hannu ta rufewa Hafsa baki wacce ga dukkan alamu so take taja mata Allah ya isa, da rawar murya Jamila tace"Hafsa kiyi shiru don Allah karki ce wani abun kuma, ki sani haihuwa da kuma rashinta duk yana ga Allah, ba wai wayau da dabarar mutum bane……"

  

  "Haba Jamila har sai yaushe ne ke zaki nuna tsantsar ɓacin ranki akan abu ne…?azatona adalilin wannan babban al"amarin ayau hakurinki zai ƙare musamman ma idan akayi duba da yadda kike neman haihuwa ido arufe, sa"annan kika ji wai ashe dasa hannun wata aciki toh sai inda karfinki ya kare...?ammh ji wai hakuri kike sake bawa kanki fa....." Gidado ya fada yana mai zirarar da hawaye, murmushi mai ciwo Jamila ta saki wanda yasa mutane suka ji tausayinta sosai kan tace"Toh in banda abunka Suleiman wani mataki zan dauka akai...?shin yin hakan ne zai bani haihuwar atake...?ka sani nina dauki hakan ne amatsayin jarabawata kuma dan girman Allah na rokeka karka ingizani ga aikata abunda bai dace ba, ka taimakeni in samu in cinye jarabawata, pls ko dangina banason asanar dasu komai, na rokeku kumin wannan alfarman...." ta fada tare da hada hannayenta tana rokonsu, sosai ta burge ba kadan ba har Hafsa ma saida taji kawai inama ace itace Jamilar mai ƙyakkyawar zuciya haka,

Mutane sai tirrr da Momy suke tayi, ya"yanta sai kuka suna Allah wadai dake, nayi danasanin kasancewata jininki, maganganu dai marasa dadi suke ta yayyaɓa mata, can suka ga Tsoho yasa hannu ƙarkashin kujerar da yake zaune akai ya zaro shibgegiyar bindigarsa, tuni kowa ya razana ya miƙe, daidai inda Momy take ya saita hannunsa na mugun rawa, ga hawaye na ziraro masa yake fadin"Hauwa'u kinga yadda dai na saita wannan bindigar akanki, toh kuwa da"ace dakwai alburushi aciki da babu abunda zai hanani fasa kanki domin daga ke har danki kun kafa kazamin tarihi mai baƙin fenti acikin zuri"ata, ayau da Munniru na raye da yayi tirrrr da macen da yake tunanin ta gari ce, kullum idan muna tare sai ya yabeki ba tare da sanin cewa ke ɗin kinma fi fir"auna mugun nufi ba...haka kuma kika sa kowa yake ta yiwa baiwar Allah Hadiza kallon watakila dasa hannunta agame da rashin haihuwar su Gidado ashe duk kece……munafuka! Azzaluma kawai Allah ya nuna mana bayanki....."

Kuka yaci mugun karfinsa, ya jefar da bindigar akasa, ya"yansa suka taimaka masa yakoma ya zauna kan kujerarsa, ran kowannensu na suya ganin ayau mahaifin nasu na rusar kuka akan wata banza can, tausarsa suka dunga yi har dai yayi shiru, su mustapha da sauran mutane wa"enda ada sunyi zargin dasa Hannun Hajjun sune suka koma kuma ayanzu suna neman gafararta, dama dama Gidado koda rana daya bai taɓa kawo tunanin hakan aranshi ba sai akan mahaifiyarsa wacce akaso shiga tsakaninsu,murmushi mai ciwo Hajju ta saki kan tace"Haba bayin Allah wallahi ku sani ko kadan ni Hadiza ban taɓa kullatan wani da mugun nufi ba, kowa da nake zaune dashi da zuciya ɗaya ne nake zaune dashin, mai zaisa nazo duniya sannan na koma gaban Allah da kwandon asara...?"

Murmushi mai wuyar fassaruwa ne ta sake saki kan tace"Rashin hakuri da kuma bin son rai shine abu na farko dake kaimu ga halaka, zanyi bayani akansu domin masu hali irinna Hauwa suyi kokarin yakicesa daga ransu, wato *SON ZUCIYA* cuta ce mai saurin hallakar da wanda ta kama, domin tana da wuyar sha’ani.Duk wanda Allah ya tsare shi daga bin son zuciyarsa to wannan shi ne wanda zai iya bin karantarwar wahayi (Alkur’ani da Sunna) cikin sauki ba tare da ya sha wata wahala ba har kuma Allah ya tseratar dashi daga musifu da fitintinun duniya, wanda kuwa ya kamu da cutar bin son zuciya to wannan ya yi hannun riga da shiriyar Allah kwatakwata. Domin son zuciya kishiya yake ga bin shiriyar Allah, duk wanda ya zabi dayansu to dole sai ya rabu da dayan.Bin Son zuciya shi ne ramin ɓata mafi zurfi. Duk wata fandara a duniya to hade take da bin son zuciya.Hanyoyin dai biyu ne kacal babu ta ukunsu; ko dai mutum ya bi tsantsar gaskiya ya miƙa wuya ya yi imani da Allah ko kuma ya yi jayayya ya ki gaskiya ya bi son zuciyarsa ya karyata wahayi, don haka Duk wanda ya zabi ya bi son zuciyarsa toh ya sani bai zalunci kowa ba kansa kawai ya zalunta, kuma ya sani cewa ya haramta wa kansa samun shiriyar Allah kenan har sai ranar da ya tsabtace zuciyarsa ya nufi Allah da ayyukansa, sabida haka Hauwa kiyi kuka da kanki domin kuwa basu kika zalunta ba kanki kika zalunta..."

Kuka ta fashe dashi tana fadin"Ai kuwa wallahi kaina na zalunta....." tsaki kowa yaja ammh banda Hajju wacce ta cigaba da jawabinta" inason kowa yayi hakuri abarsu da Allah domin kuwa yin hakuri ibada ne, hakuri dabi"ace daga cikin dabi"un fiyayyen halitta, ko kuwa bada shi kuke koyi ba…?" gabaki daya aka amsa mata da eh dashi ne, hakan ya bata damar cigabawa"Toh shin ko kunsan lada da kuma sakamakon da masu hakuri ke samu...?ko kuwa baka muradin ƙyakkyawar makoma ne…?ku sani Allah yana saukar mana da fitintinun rayuwa, don ya jarrabamu ya nuna waye yafi wani kyakkyawar aiki kamar yadda ya fada acikin suratul mulk aya ta 2, don haka dukkan kunci ko tawayar dukiya ko wani abun tashin hankali daya sameka kayi hakuri, don Allah madaukakin sarki yana cewa dukkan tsanani yana tare da waraka, bakasan abunda Allah ya nufi ko ya tanadar maka adalilin wannan hakurin naka ba, ta yiwuwa adalilin hakurin da kayi Allah ya musanya maka abunda ka rasa da maficicinsa, Jamila ki cigaba da hakuri don hakurinki da kauda kai akan abu yana masifar burgeni, ki cigaba da hakuri don na tabbata Allah yayi miki wani babban tanadi na alheri ne nan gaba kawai kiris ya rage………"

Ta jima tana nasihu masu ratsa zukatu, daga karshe aka tisa ƙeyar Momy zuwa dakinta don tace muddin ta kifar da wa"ennan ƙwaryoyin masu dauke da sunayen su Jamila tofa komai zai koma daidai ammh saidai ita zata ɗan tabu, babu wanda ya damu da haukacewar tata aka tilastata ta kifar da ƙwaryoyin, ammh saida aka jira mutanenta suka zo sa"annan ta kifar don anason suga komi da idanunsu ne, abu sai ace ah film ko ah littafin hausa wai shine ya faru dasu?😜 tana gama kifarwa ta cire dankwalinta ta jefar, zani ma ta kama zata kwance mutanenta suka riketa, haka suka sakata acikin mota suka tafi da ita suna Allah wadai da ita, ya"yanta sai kuka suke tayi suna mai nadamar kasancewarsu jininta hatta dashi kansa kasim ɗin, haka kuma sun rantse bazasu bita ba, bayan an dan natsu Mustapha ya rubutowa Azeema takaddar saki har biyu, yaso cika na ukun ammh kasancewar anyi hani da yinta shiyasa kawai ya bata biyu, tamkar zata haukace ammh babu wanda yabi ta kanta, iyayenta suka jata suka tafi da ita da niyyar washegari zaa je ah kwashi kayanta, kasim kasa zama yayi agidan ya fice zuwa gidan wani abokinsa ko zai dan samu sassauci aransa.....

_*kuna iya samun update zuwa yamma insha Allah*_

_*HAFFY MOUSTY🌷*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

   _LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

   _*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

   _ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA TALATIN DA TARA...💥*_

………Sau da yawa bawa kan rikice gami da samun kanshi cikin dimuwa alokacin da shafin kaddara mai muni ta rabi rayuwarshi, haka kuma zukata kan cika da zallar nishaɗi da jindadi mara misaltuwa alokacin da bigiren ƙyakkyawar kaddara ta waiwayosu, sai dai da dama na daga cikin mutane suna manta cewar mai ƙyawun da kuma mummunar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login