Showing 60001 words to 63000 words out of 102125 words

Chapter 21 - KISHIN MATA part Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

5905

option illa bin bayansa.....

Baddo ita kadai zaune afalo sai gashi ya fito,kallo daya yayi mata sannan ya dauke kansa ya nufi dinning area zuciyarsa na cigaba da azalzala don bacin ransa ya karu ne akan Hafsa,haushinsa kenan da ita wato batasan tazo tayiwa miji barka da zuwa ba,kuma bawai batasan ya shigo gidan bane,a''ah tana ganin tafi karfin ta fito ta sameshi saidai shi yaje yasanar da ita cewa ya dawo,Baddo taga yana kokarin daukar jug ya tsiyayi ruwa ah cup,dasauri ta isa wajen har tana neman faduwa tace''kawo in zuba maka..'' wani uban tsawa ya doka mata yana fadin''step back karki zuba mun datti aruwa...'' adaidai lokacin Jamila ta iso wajen,sosai Baddo taji haushin wannan wulakancin da yayi mata sai taji tamkar ta aza hannu aka ta kurma uban ihu ko taji sanyi aranta,Jamila ta kura mata idanu cike da tausayinta ganin tasa hannu tana dauke guntun hawayen daya zubo mata,anci sa'a idanuwansu sun jame,Jamila ta girgiza mata kai alamun karta damu komi mai wucewa ne nan bada jimawa ba,Baddo ta sakar mata lallausan murmushi wanda yafi dacewa akirashi dana karfin hali,Jamila tayi serving nashi sannan tayi na Baddo,ta dauki hanya da nufin zuwa kiran uwar mulki,dasauri Gidado ya dakatar da ita har ya ƙware garin saurin tsaidatan,saida yakora ruwa sannan ya dubeta da red eyes yace''Ina zaki..?''

''Zan kira Hafsa ne tazo muci abinci..''

Azuciye yace''You see...?wallahi kece ke siyawa kanki raini awajen kananan yara,ita Hafsan 'yar baby ce da har sai anje an tuna mata cewa ta fito taci abinci...?ai tasan na dawo tayi zamanta aciki don haka komo ki zauna kici naki abincin babu inda zaki...!'' ya fada tare da nuna mata wajen zama akusa dashi,har ta bude baki zata sake magana ya doka mata tsawa''Juz obey...!!!!!''

Bata ci musu ba ta koma ta zauna akusa dashi,suna tsaka dacin abincin sai gata ta fito ayangance cikin damamman wando da black top,kai kace ko itace da girkin ma,sai taunar cingam take tana huro balam balam abunda kuma Gidado ya tsana kenan arayuwarsa,tun kan ta karaso wajensu yace afusace''karki kuskura kizo mun nan da karar abun nan akunne if not ranki zaiyi mugun 6aci..'' ta6e baki tayi sannan ta cire cingam din ta rike ahannu,ko data gaidashi ma ciki ciki ya amsa,abun mmaki itace da cewa su Jamila ina wuninku,Jamilar ce kawai ta amsa mata cikin sakin fuska ammh Baddo ta amsa ne fuska ba yabo ba fallasa,zama tayi awani empty chair ta shiga latse latsen wayarta tana jiran taji Gidado yace wai ke bazaki dibi abinci kici bane..?

har Jamila ta mike zatayi serving nata sai ya dubeta aƙaiƙaice yace''meh zakiyi...?''

''I wnt to serve her...''

Yace''koma ki zauna ki cigaba da cin abincinki ai tana da hannu...'' yana gama fadar hakan yakai lomar shinkafa baki,sosai hakan ya bawa Hafsa haushi don haka sai tayi maza tace da Jamila''No karki damu ni akoshe nake ma...'' babu wanda ya tankata har aka gama cin abincin,Baddo ta taya Jamila kwashe kayan da aka ɓata zuwa kicin sannan suka koma falon alokacin yana goge bakinsa da tissue,duban Baddo yayi yace''ki soma shiryawa nan da 3weeks zaki soma attending _*AMERICAN INTERNATIONAL SCHOOL*_ ...''

Batasan lokacin data daka wani irin tsalle ta rungumeshi ba tana murna tare da jero masa godiya,dasauri ya tureta yana fadin''ke miye haka are you mad..?ko bakisan kin girma bane...?''

Dariya ne yaso kufcewa Jamila aranta tace''Ai kadan ma ka gani,bazama kasan ta girman ba sai lokacin daka farga ka ganta dauke da babynka asannan ne zakasan she's a full grown woman..''

Baddo tace''Daddy thank you very much i love you Allah ya biyaka da gidan aljannah...'' lumshe idanu yayi bai ce komi ba,ta rungume Jamila tana kukan murna,Hafsa kuwa dogon tsaki taja sannan ta mike tana fadin''Ku kuma naku salon soyayyar kenan..?tou Allah ya kyauta..'' tana gama fadar hakan tasa kai ta wuce ayayin da suka bita da kallon Allah ya shiryeki......

Har zuwa lokacin bacci Baddo bata bar farin ciki ba don har mantawa tayi da tsoron kwanciya ita ɗaya,burinta ayanzu kawai bai wuci tayi waya da iyayenta ta gaya musu cewa Hamma zai batta ta cigaba da school ba,shi kuwa bayan ya gama shirin kwanciya sai ya tuna fa yau ita kadaice zata kwana ah part ɗinta,hakan yasa yace da Jamila yana zuwa sannan ya fice da sauri zuwa part ɗin Baddon..............✍

_*HAFFY MOUSTAFA🌷*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

   

_*KISHIN MATA…!*_

     _Na marubuciya Hafnancy…_

         _akan naira 200kacal👌_

_ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA ASHIRIN DA HUDU…💥*_

…………Duk wasu al"adun data saba gabatarwa kafin ta kwanta bacci duk tayi su,kamawa daga wanka,wanke baki kamar yadda Antinta ta koyar da ita yinsa kafin ta kwanta,daga ƙarshe ta dauro alwala tayi Nafila raka"a biyu don nuna godiyarta da kuma jindadinta ga ubangiji daya amshi addu"arta har yasa Hamma zai barta ta koma makaranta,Gidado yasha addu"a awajen wannan baiwar Allahn,ba ita ta nemi lafiyar gado ba sai misalin sha ɗaya saura na dare,wannan tsoron kuma duk babu shi ya ƙau don ta kudiri niyyar gara ta fara sabawa sabida yanzu ne ma zata soma kwana ita ɗaya har sai zuwa yadda zai kasance musu(wallahu ahlamu…Allah ne mafi sani),har ƙarfin hali tayi na kashe bulb light _don koyarwar manzonmu ne SAW na akashe wutar lantarki idan za"a kwanta sabida ba"a son mutum,aljan dadai sauran miyagun abubuwa susan position ɗin daka kwanta,addu"a itace kawai kariya agaremu ba wutar lanta ba,don haka masu barin wuta akunne idan zasu kwanta don Allah ku bari babu ƙyau (Wannan tunatarwa ce)_

ƙudundune kanta tayi acikin bargo har kai ta rufe kuwa,ta daga hannu kenan tana shirin soma karanto addu"ar bacci sai kawai taji buɗowar ƙofa,da sauri ta yaye blanket gabanta na dukan uku uku idanuwanta kuma ƙyam ah direction ɗin door,suffar kakkarfan namiji ne take hangowa ammh bazata iya tantance ko wanene ba sabida duhun daya karade dukkan ilahirin dakin,wani irin faint shout ta saki tana fadi atsorace"plsss wanene...?na haɗaka da girman Allah karka cutar dani…" ta ida magana tare da runtse idanu tana mai girgiza kai,dariya ne yaso kufce masa ammh sai ya cije yasa hannu ya kunna wuta,haske ya gauraye ko'ina....idanunsa suka sauka akan cute face ɗinta,pyjamas ne ke jikinta,duk da cewa bai ga yadda kayan ya zauna mata ajiki ba ammh ya tabbatar da cewa sosai zatayi looking dope acikinsa,aransa yace"whaoo…! small baby looks pretty tonight..." ya ida magana tare da jan wani breathe,atsorace ta buɗe idanuwan,karaf acikin nashi,ajiyar zuciya ta sauke tana fadin"owh daddy u scared me alot wallahi....plss daddy karkayi girman kai say sorry don kayi kuskure anan…" ta ida magana tare da kama kunnuwanta duka biyun tana kallonsa ammh zuciyarta wannan karon babu alamun tsoronsa atattare da ita,wani wawan ajiyar zuciya ya sauke ya soma tunkaro inda take still idanunsa akanta,yanayin fuskarsa not showing happines haka kuma baza kace yana cikin sadness ba ammh actually jikinsa asanyaye yake,ganin yana kusanto inda take yasa taji tsoronsa yaɗan tsirgu azuciyarta,cikin sanyin murya yace"meyasa zan bada haƙuri wannan ƙaron bayan banyi laifin komi ba…?or is it a crime in shigo dakin wacce take amsa sunan matata...?"

Ya ida magana tare da zama agefen gadon,wani sanyin dadi ne taji ya lulluɓe mata zuciya jin da tayi atleast yau yadan nuna mata cewa ita ɗin matarsa ce,ganin tayi shiru tana wasa da yatsun hannayenta yasa yace"small baby tambayarki nake...?ko mamaki kike da abunda na faɗa…?excuse me plss dont get me wrong,akwai banbanci tsakanin wacce take amsa sunan matata da kuma wanda na kira da matata okay...?so get dat into ur skullll...." wani irin ɗaci ne taji aranta da wannan baƙar maganar daya jefa mata,saurin kawar da kanta tayi gefe jin hawaye na shirin zubo mata,harga Allah ita dai bazata iya cewa ga yadda SO yake ba ammh kuma bazata iya fassara yadda take ji agame da dan"uwan nata ba,dan kwanakin da sukayi atare batasan meyasa ta daina ganin laifinsa akan duk wani abun takaicin dazai cusa mata ba,infact batasan meyasa take burin ya ambaceta da matarsa ba,sam bata ƙaunar wannan kalmar da yake yawan gaya mata wato _*'WACCE TAKE AMSA SUNAN MATATA'*_

katse mata tunani yayi ta hanyar tallafo haɓarta,forcing her to look straight into his eyes da jikakkun idanu,langwabar dakai yayi yace cike da tausayi"haba small baby kuka kuma...?meh daddy yayi miki…?okay fine nafadi ba daidai ba am sorry bazan sake hurting feelings ɗinki ba,dama zuwa nayi na duba ko zaki iya kwanciya ke kadai kuma alhamdulillah i can see u really want to try and do such...Allah ya karemu dukah gdnyt..." dasauri ya miƙe da nufin barin dakin jin yadda zuciyarsa ke masa zafi don bazai juri tsayawa yaga kukanta akanshi ba,da azama ta sakko daga kan gadon ta cafko hannunsa ta rushe da kukan mai tsuma zuciye tana fadin"Hamma for how long will diz continue...?meyasa kake yawan sakani kuka ne akanka..?tun kamani da kayi da Hamma Kasim ah lungun gida muna zantawa toh tun daga wannan ranar ban sake samun wani farin cikin azo agani ba arayuwata don fa muddin ina kusa dakai tofa bazan iya kirga iya adadin sau nawa zakasa na zubar da hawaye awannan lokacin ba...meyasa kakemun hakane sai kace ni ɗin ba jininka ba…?ka tuna fa babu dan"adam ɗin daya wuci kuskure balle ma fa ganinmu kawai kayi muna hira bawai abunda kake tunani bane akai wallahi…don Allah dan"uwana mu manta da komi mu rungumi kaddararmu da hannu bibbiyu na kasancewa mata da miji,am sorry i juz have to kip down my ego and talk to you don naga baka da niyya haka kuma bakada ranar zama kayi tunani kace anya abunda nakeyi daidai kuwa...?nasan ni ƙaramar yarinyace awajenka,bari in ari bakinka ah inda kake yawan cewa ni ɗin tamƙar ƴar cikinka nake sam bakamun kallon matarka,Hamma accept it or not 'ƴar cikin taka ce dai kuma ke neman ankarar dakai abunda ya shige maka duhu………Hamma pls i beg you ko bazaka soni ba kayi kokari ka amsheni amatsayi mata..i juz want us to live happily and dats allllll....wallahi tallahi bani ƙaunar ganinmu cikin ƙunci akodayaushe,ka ƙuntata mun sannan kuma ka ƙuntatawa kanka...yayana,ubana kuma mijina plssssss ka tausayawa ƙanwarka,'ƴarka kuma matarka…"

Ta ida magana tare da durƙushewa akasa ta kankame kafarsa daya daƙyau tana mai cizgar kuka,sosai jikinsa yayi mugun sanyi hakanan kawai yaji tausayinta ya tsirgu azuciyarsa,runtse idanu yayi yana mai jin zafin kukan da takeyi adalilinsa,sai yaji duk ya tsani kansa totally tare da yin nadamar kuntata mata dayake yawan yi akodayaushe,ba tare daya fuskanceta ba ya miƙa mata hannu ta baya yana fadin"Get up and stop crying...." dasauri ta daga kai tana kallon hannun daya miƙon,bata tsaya dogon tunani ba ta miƙa mishi nata hannun ya dagata sannan ya waigo ya rungumeta,ajiyar zuciya ya sauke ayayin da ita kuma ta sake rushewa da wani sabon kukan,hannu yasa ya shiga shafa blondy like hair ɗinta,alokaci ɗaya kuma yana mai hura mata iska akunne yace"Haba enmatan daddy kukan ya isa hakanan man...! yanzu dai gayamun sau nawa kika bari Ƙasim yayi taking advantage akanki…?

Dasauri ta tureshi zuciyarta na mata tukuki,ta fashe da wani silent cry tace"Haba Hamma yanzu duk rantsuwar dana maka akan babu abunda ya taɓa shiga tsakanina da Ƙasim,rantsuwar tawa ta tashi abanza kenan baka yadda ba...?don girman Allah set ur mind free karka kawo zargi acikin lamarin auranmu,karka haramta mana juna wallahi ni Kasim ko hannuna ban taɓa bari ya riƙe ba balle akai ga batun yasamu yadda yakeso awajena ba plsss trust me…........"saurin taran numfashinta yayi yace azuciye"Shut up....karki rainamun hankali man Mubeenah,nifa nasan ko waye kasim,he's an ass dope womanizer wanda idan yaci alwashin lasar zumar duk wata ƴa macen,tofa Allah yasa tafi giginya taurin kai ne wallahi sai ya sameta kuma yayi yadda yakeso da ita balle keda ido ɗaya kawai zai zaro miki kiyi mishi abunda yakeson…………" wani irin bugu takai masa ah kirji tana kuka tace"Suleiman wai ni mai ka daukeni ne...?kallon 'yar iska kakemun ko…? wacce ta gama tambaɗewa agari kamar yadda dai ka faɗa,toh ni bansan mai kuma zan fada maka dahar zaisa ka yadda cewa babu wani ɗa namijin daya taɓa kwantawa dani ba ammh mafita ɗayace kawai ya saura kuma shine ka kwanta dani next time idan kwana ya zagayo kaina,toh anan ne zaka samu amsar tambayarka sannan ni kuma zan wanku daga zargin da kakemun....."

cike da mamaki yace"whao! haba yanzu kika fito amutum ɗinki Mubeenah,tuntuni yakamata kice Suleiman i want to hav a taste of you inji yadda kai kuma naka dadin yake ammh bawai kita beating around the bush ba,bakiyi laifi ba don kin tambaya sabida haƙƙinki ne ammh naso ne ki nunamun jan"aji da kuma alkunya irin dai na asalin ɗiyoyin malam bahaushe......." ya fada yana mai zagayeta ransa na mugun suya,wani bakin ciki ne ya sake cika mata zuciya tace"wallahi am not begging you to sleep with me kawai so nake na wanke kaina daga zargin da kakemun..."

Saurin taran numfashinta yayi yace"Inso kike ki wanke kanki awajena toh ai dakwai hanyoyi dayawa da zaki bi har in gano gaskiya dakaina ammh bawai ki zubar da mutuncinki ba,karki manta har yanzu amsa sunan matata kawai kike ammh ban riga dana amsheki amatsayinta ba,zan iya daurewa in karbeki amatsayin mata ne aduk randa na gano gaskiyar zance dakaina,idan kuma kika kuskura na gano cewa Kasim ya taɓa kwantawa dake tofa ki sani zamanki agidan nan ya ƙare…" cike da rawar murya tace hawaye na ziraro mata"Ta wani hanyar ne zaka bi ka gano gaskiyar...?" Afusace yace"Babu ruwanki da hanyar dazan bi,ki zubamun idanu kawai kiga aiki da cikawa,zan tafi don na shiga haƙƙin matar kwarai,sannan kuma zanyi nazari akan bukatarki,zaki samu feedback ana gobe zagayowar kwanarki.....gudnite…" yasa kai ya fice bayan ya kashe mata wuta ya kuma ja mata kofar ya rufe,hannu tasa akai tana mai rushewa da wani sabon kukan tace"wayyo Allah ni Mubeenatu wai sai yaushe ne dan"uwan nan nawa zai bar sakani zubar da hawaye ne...?sai yaushe ne zai sakani cikin farin ciki..?"

kan gado ta zuɓe tana sake sakin wani shafin kukan tace"Mijina kana sakamun damuwa sam baka la"akari da irin kankanun shekarun da nake dasu,Hamma baka taɓa sakani dariya ba ammh ni nadau alƙawari watarana zan saka yin abu guda biyu at the same time,wato kuka da dariya kuma duk alokaci guɗa…bansan ko menene zanyi maka da zaisa ka shiga cikin wannan yanayin ba ammh ina ji ajikina cewa wannan ranar tana nan zuwa agareka..............."

Akifen bacci yakwasheta,shi kuma bayan ya koma daki ya tarar Jamila har tayi baccinta,shigewa blanket yayi ya rungumota jikinsa sannan ya maida bargon ya rufesu dashi,duk tana jinsa ammh ko motsi batayi ba sai kukan zuci takeyi idanuwanta aruntse,dakyar bacci ya kwasheshi don ya daɗe ne yana tunano hirarsu da Baddo,kukanta mai tsuma mishi zuciya da kuma jarumtar maganarta wanda suka girmi shekarunta,yasani sarai duk abunda yake mata baya ƙyautawa ammh zarginsa akansu ita da kasim ne yaki gogewa acikin zuciyarsa don kasim yakasance idan ya har ya ƙyalla idanu akan ƴa mace har kuma ta kwanta mishi arai tofa sai ya lasa zumarta,hakan yasa yaji sam bai yadda da zancen data gaya mishi ba ammh ya zama dole ya bincika don ya gano gaskiya…sai dai kuma ta wani hanya ne zaibi ya gano gaskiyar...?

     *********

Ayau ne Azeema ta wayi gari da masassara,jikinta yadau zafi sosai ga kuma wani irin aman da tayi ta zubawa adaren jiya,sai kuma kasalar jiki datake ji,mustapha duk yabi ya ruɗe dayake yana gari,tun bakwai na safe suka kama hanyar asibiti,yakaita wani tsadadden asibiti aka ɗibi fitsarin don gwaji,sosai hankalin mustapha ya tashi don Azeema bata taɓa yin makamancin wannan zazzabin ba,ita kuwa aranta dadi ne fal ya cikata don tasan bazai wuce ciki ne gareta ba,sai jerowa Kasim godiya take tayi aranta har Doc.Jude ya fito,itace ma ta riga mustapha tashiwa don cimma likitan wanda yake tunkaro inda suke,cike da mamaki Mustapha yace"Haba Zeettyna keda baki jindadi ki koma ki zauna in karbo mana sakamakon man..." noƙe masa kafada tayi sannan ta karasa da sauri wajen likitan wanda shi karan kansa mamakinta ne yakusan sumar dashi,hannu tasa ta fuzge takaddar hannunsa tana dubawa,idanunta ya sauka akan negative wato kenan babu ciki ajikinta,kara ta sanya ta raba takaddar gida biyu sannan tayi wani kukan kura ta cakumo kwalar rigarsa tana fadin"How can it be negative again bayan na tabbata am pregnant…?Doctor Jude am very sure dat bakasan aikinka ba kawai yi kakeyi and am gonna prove you wrong today,zanje wani asibitin kuma zan dawo maka da positive result..." ta ida magana tana cizgar kuka sosai,shi kuwa likitan kasa furta komi yayi sai kallon mamaki yake binta dashi baki sake,dakyar mustapha ya ɓanbare hannunta daga jikin likitan yana fadi cike da zafi"ke…!Azeema meye haka...?shin rashin haihuwa hauka ne..?wani irin cin mutunci kenan kika masa agaban idon mutane...?

Atsawace tace"mustapha i want a baby idan kai din ka cika namiji then ka bani ciki..." ta fada tana kai masa duka akirji tana rusar kuka,ganin zata tara mishi jama"a yasa kawai ya rungumota jikinsa yana lallahinta"am sorry Azeema Allah ne kawai zai baki haihuwa ammh ba mutum ba,ke kina ganin da"ace mutum ne ke bada haihuwa da kowa bai bawa kansa shi ba...?matata karkiyi sabo sannan kuma karmu gaji mu koma gida mu cigaba dakai kukanmu wajen ubangiji ina mai tabbatar miki da cewa next gwajin da zamuyi zai fito positive ne..." ya ida magana hawaye cike fal acikin kwarmin idanunsa kawai dauriya yake yi,haka dai suka bawa likitan hakuri sannan suka tafi,bata saduda ba saida ta sakashi yakaita wani asibitin aka sake tabbatar mata da cewa bata da shigar ciki,anan dinma taci kuka tamƙar ranta zai fita kai kace akanta ne aka soma samun rashin haihuwa,har ta bawa wasu tausayi anan,shi kansa mustapha mugun tausayin kansu yake duka,daga ƙarshe suka yada zango agidan Gidado kuma anci sa"a yana gida dake weekend ne bashi zuwa wajen aiki in baya kama dole

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login