Showing 81001 words to 84000 words out of 102125 words

Chapter 28 - KISHIN MATA part Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

5876

mutum sai dai shi wanda ya sakan ya ƙare maka ƙyaƙƙyawan kallo,hannunsa duka biyun zuɓe acikin aljihun wandonsa,fuskan nan ahaɗe tamƙar bai taɓa sanin dariya ba,ko sake kallon inda Andrew yake bai yi ba yace cikin kakkausar murya"ku kawo mun shi ofishina..." yana gama fadar hakan ya shige ofishin nasa ayayin da suka rakashi da salute,cikin zafin nama suka hankaɗa ƙeyar Andrew zuwa ofishin,duk jikinsa ya mutu da ganin DCP Gidado don ga dukkan alamu bazai dauki raini koda na ƙwayar zarra bane,bayan sun kusa kai ciki suka hangoshi yana juyi akan kujerarsa hannunsa kuma riƙe da shade ɗin daya cire,cikin kasaita yadubisu Musa yace"uncuffed him and gerraway…"

Cikin sauri suka cire masa handcuffs ɗin sannan suka sake saluting ɗinsa kana suka fice kamar yadda ya umarta,bayan fitarsu Gidado yadubi Andrew wanda jikinsa yadau rawa sosai yace"Ga wuri nan Mr.Andrew have a sit and feel comfortable cuz i mean no harm...wasu tambayoyi kawai nakeson kadan amsa mun..." sosai ya sake tsinƙewa da al"amarin,ganin yaki motsawa yasa Gidado ya sake cewa"Am very sure you ain't deaf....i said plss have a sit and feel comfortable like very comfortable....."

Bai ci musu ba yaja kujera ya zauna,tsawon lokaci Gidado bai ce masa uffan ba sai nazarinsa yakeyi,ga namiji nan dai har namiji ammh kwata kwata babu hali na gari,shi azatonsa ma wani he-goat ɗinne zai gani as the Andrew Isaac,ammh sai yaga a well responsible man wanda idan ba gaya maka kazaman halayensa akai ba tofa zaiyi wuya ka masa kallon mutumin banza,ajiyar zuciya Gidado ya sauke kan yace"Mr.Andrew Isaac inason yadda na tarbeka amutunce haka nakeson kaima ka taimaka ka gayamun tsakaninka da Allah abunda ke tsakaninka da matata *HAFSA BILYAMINU*....."

Wani irin tsalle ne zuciyarsa tayi da jin kalmar data fito daga bakinsa,ashe mijin Hafsa ne zaune agabansa..?Nabila ta taɓa gaya mishi cewa mijin Hafsan ɗan sanda ne ammh kwata kwata yama manta,tuni idanunsa suka raina fata,Gidado ya lura da tsananin tsoron daya bayyana akan fuskarsa sai kuma duk yaji ya bashi tausayi,sam tashin hankali babu dadi,ga dan"uwanshi nan mustapha na shirin shigansa nan bada jimawa ba,tuni yaji wani sabon tausayinsa ya sake lulluɓe zuciyarsa,hakan yasa yashiga bin Andrew asannu yace dashi"look am not going to hurt you juz tell me the truth and go away...i promise bazan dau mataki ba kaji nace Allah...."

cikin rawar murya yace"Dan girman Allah kayi hakuri sharrin shaiɗan ne,her younger sister Nabila is my girlfriend ammh tsautsayi yasa kawai naji ina sha"awar matarka har na biyewa son zuciya na dauki lambar wayarta ah phone ɗin sister ɗinta shine na ƙira……"

cigaba yayi da neman gafararsa ammh kwata kwata hankali da kuma tunanin Gidado sam baya gareshi,don kifa kai yayi akan table yana kukan zuci,tsawon mintuna goma Andrew na abu daidaya har dai ya gaji da rokonsa yakai hannu ya taɓoshi,afirgice Gidado ya dago kai ya zuba mishi jajayen idanuwansa wanda suka matukar tsoratashi yace"whatt....?" sosai abun ya bawa Andrew mamaki da tsantsar tsoro don atunaninsa Gidadon zai dau mataki ne kawai wayau yayi masa don ya fada mishi gaskiya,

cike da tsoro yace"Nace kayi hakuri wallahi bazan sake ba..." ah fusace Gidado ya miƙe yana fadin"Ka tashi kaje kanka kayiwa bani ba,gaka dai mutumin kirki afuska ammh azuci kafi fir"auna iya aika aika,ya rage gareka ka tuba ko kuma ka cigaba da barna,ammh ka sani duk wanda yayi mai ƙyau don kansa haka zalika duk wanda yayi akasinta kansa yayiwa,ka tashi kaje bazan dau mataki ba ammh na barka da Allahna don shine zaiyi mana maganin azzalumai irinku,Mustapha Allah ya saka maka! Allah yayi maka sakayya....."

Kuka yaci mugun ƙarfinshi,hannu kawai yake nuni ma Andrew alamun ya tafi kawai ya bashi gu,dasauri Andrew yabar ofishin cike da mamakin wannan al"amari na Gidadon don da dukkan alamu akwai wani abu can daban wanda dama yake damunsa,sai kuma duk yaji ya bashi tausayi sosai ga kuma wani irin nadamar munanan halayensa daya shigesa lokaci guda..................✍

_*HAFFY MOUSTY🌷*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

_*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

_ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

_*💫BABI NA TALATIN DA UƘU...💥*_

.........Fitar Andrew keda wuya sai ga Inspector Kabir ya fado cikin ofishin hankali tashe yake faɗin"Ranka shi dade shin wai kai ne ka bashi izinin tafiya..?don gashi can yana kokarin wucewa shine muka tsareshi nace bari inzo inyi comfirming...." maganarshi ce ta yanke ah sa"ilin daya ga ogan nasa na running hot tears,sosai abun ya bashi mamaki har yana kokarin sake magana sai yaga ya daga masa hannu alamun ya tafi kawai bayason hayaniya,da mataccen jiki yafice da baya,yaje ya bawa Musa umarnin freeing Andrew ɗin…

Bayan tafiyarsa Ƙabir ya dubi Musa yace cike da damuwa"Anya baka tunanin ko wani laifi mai girman gaske ne wannan ɗan tahalikin ya yiwa yallabai…?" Musa yace cike da rashin fahimta"mai ka gani...?"

Saida ya sauke ajiyar zuciya kan yace"Samunsa nayi yana kuka abunda bamu taɓa kamashi yana yi ba kenan,shiyasa na shiga mamaki nake tunanin ko wani babban laifi ne mutumin yayi masa...?

  Akiɗime Musa yace"kai da gaske kake ko wasa...?kuka fa kace ka kamashi yana yi...?" ɗan siririn tsoki Kabir ya saki yana fadin"Toh malam ƙarya zan maka ne…?inga abu da idanuna bawai gayamun akai ba sannan ka nemi ƙaryatani…?

    cike da tsantsar mamaki Musa ya sake cewa"shine kuma ya bari muka sakeshi ya tafi..?anya kana ganin akansa yashiga wannan damuwar kuwa...?watakila dai dama can dakwai abunda ke damunsa ne...."

suna cikin kuskus ɗinsu ne sai gani sukai ya fito zai tafi gida,ƴan sanda su wajen shidda suka taso zasu mara mishi baya sai yayi saurin dakatar dasu yace Inspector kabir da Musa alone sun isheshi,

Tun kafin ya isa gida ya kawar da tsantsar damuwar dake shimfiɗe saman fuskarsa sannan yayi kokarin maye gurbinsa da annuri,sosai yaji dadin yadda iyalan nasa suka tarɓeshi,sun haɗa kawunansu wuri guda kuma hakan ba karamin farin ciki ya tsundumashi ba,sake haɗa kansu yayi ya musu nasiha mai ratsa zukata,daga ƙarshe aka shiga firar yadda za"a tarbi zuwan baby,shi dariya ma abun ya bashi yadda Jamila da Hafsa suka zage kai kace ko gobe ko jibi ne ɗan zai faɗo duniya,sosai suka sashi nishaɗi har ya ɗan manta da damuwarsa naɗan lokaci………

Bayan Andrew yakoma gida ya tarar babu babu Nabila haka kuma babu dalilinta,tsadadden wrist watch ɗinsa ma babu shi kuma ya tabbata itace ta dauka,bai wani damu ba don aganinsa ya wuce nan.



      *****AH GURGUJE PLS*****

Tun takwas na safe Mustapha ya diro garin Abuja,Gidado ya aika aka je dakkoshi daga airport don dama haka suka tsara,idan ya diro gidansa zai sauka direct,tun shekaranjiyar basu sake waya da Azeema ba,ita bata nemeshi ba haka zalika shi ɗinma yabi umarnin dan"uwan nasa bai nemeta ba,sai dai fa tun daga shekaranjiyan har zuwa lokacin nan hankalinsa ko kadan bai kwanta ba,ya tabbata akwai abunda ke faruwa,hakan yasa yaketa istigfari aransa,shi karan kansa mai girma Gwamna ya rasa gane kan mutumin nasa acikin ƴan kwanakin nan ammh sai bai matsa masa da tambayoyi ba har suka rabu kuwa,yana fitowa daga mota ya hango Gidado can atsaye ya harde hannayensa abaya,da alamu dama isowar Mustaphan yaketa jira,Musty na haɗa idanu dashi dasauri ya nufeshi har inda yake tsaye ya rungumeshi gami da rushewa da kuka mai tsuma zuciya yana mai fadin"Dan"uwa don Allah wai mai yake faruwa ne da ake ɓoyemun…?ka gayamun ko wani ne ya mutu...?"

Hannu yasa yashiga bubbuga bayansa yana mai kokarin danne hawayen dake neman shatato masa,murmushi ƙarfin hali ya kwakulo sannan yace"Hbaa musty meye haka ne sai kace wani karamin yaro..?ai da mutuwa wani yayi babu abunda zaisa na ɓoye maka don ko ba jima koba daɗe zaka jishi ne…kawai wani abu nakeson na nuna maka agidanka..." dasauri Mustapha ya cika dan"uwan nasa yana kallonsa ido cikin ido kan wani murmushin farin ciki ya suɓuce masa yace"Bro kar dai ace itama zeettyna ciki ne gareta shine kukeson kumin suprise...?"

   "kusan hakan ne…" Gidado ya furta gami da sakin murmushin ƙarfin hali don kawai ya kwantarwa dan"uwan nasa da hankali,Mustapha ya soma ja da baya baya face full of amazement yana fadin"Brother cant believe this....atlast mun kusa ganin guɗan jininmu,damuwar Yumma dasu Tsoho yakusa zuwa ƙarshe……dan"uwa anxiety yana neman yimun yawa plsss ka rikeni kar in fadi………"

       Taku ɗaya Gidado yayi ya cafko hannunsa don ƙiris ya rage yakai kasa,kallo guda zakayi mashi ka tabbatar da cewa tabbas farin ciki ne yayi masa yawa har ya haifar mishi da over anxiety,sosai tausayinsa ke dukan zuciyar shi Gidadon har yakeji aransa kamar ya fasa tona asiri don bazai iya juran ganin dan"uwan nashi acikin mayuwacin hali ba,ammh kuma ɓoye mishin zai zamo tamƙar cin amana ce,gara kawai ya fallasa asiri don haka shine kawai kwanciyar hankalinsu dukah,rungumo kafadarsa yayi suka soma takawa zuwa ciki Gidado yana fadin"mu shiga ciki kaci abinci sannan kasamu ka huta kafin mu kama hanya..." bai ci masa musu ba suka shiga ciki,sai barka yaketa yiwa su Jamila da karuwar da aka samu,ah ɓangare guda kuma yana mai cike da mamakin irin sauyin da aka samu daga Hafsa sai dai uffan bai ce ba don shi mutum ne wanda bai cika shiga sabgar da bata shi ba sai in har ta kama,bayan sun gama cin abinci,ba tare da sanin Mustapha ba Gidado ya aiki yaransa su dakko mishi Baba Haruna da kuma Baba Munniru don tun ajiya ya kirasu awaya ya nemi alfarma zaisa azo adaukesu ayau.

  Abakin titi suka tsaya jiransu,suna isowa Gidado ya ƙarbe makullin mota sannan ya sallami yaransa yace dasu shi zai tuƙa motar da kansa,dake wannan family issue ne don haka bazai zo ace wani ɓare yashigo cikin maganar ba,sannu ahankali ya juya akalar motar ya lula titin da zai fiddaka unguwarsu Mustaphan,kasancewar ma basu da wani nesa da juna,addu"ah kawai yake tayi aransa kan kar Allah yasa yayi fail,Allah yasa dai su cimma Kasim agidan,don wallahi idan ya kasance babu shi tofa bai san wani dabarar zai musu ba,shafa kasumbarsa yayi tare da kai dubansa kan agogon dake zagaye da tsinsiyar hannunsa yaga 11:25am,kara gudun motar yayi don gabaki ɗaya ya ruɗe,tsoronsa ɗaya ayanzu watakila babu kasim ɗinma agidan,cike da tashin hankali ya dubi Mustapha dake hakimce saman kujera mai zaman banza sai kalle kalle yake yana mai cike da mamkin abunda dan"uwan nasa keson nuna mishi agidan nasa...

    "Mustapha da fatar dai Azeema batasan muna tafe badai ko....?" yaji saukar amon maganar Gidadon acikin dodon kunnuwansa,gaban mustaphan ne ya yanke ya fadi yace arikice yana dubansa"A"ah wallahi ban fada mata ba....." Gidado yace duban hanya"ƙarya kake ni ban yadda dakai ba,dazu da kake breakfast nace maka ina zuwa,koda na dawo na tarar kana waya,ah sa'ilin daka ga haɗa idanu dani sai kawai naga kayi saurin datse call ɗin……for the very last tym dawa kayi waya...?" ya ida magana tare da bugan sitiyari wanda hakan ba karamin tada hankalinsu Baba Munniru yayi ba,Baba Haruna yace"kai mai sunan Tsoho wai mai yake faruwa ne haka...?wani abune ma akeson anuna mana ne ehh?

 

Hannu kawai ya daga masa alamun su ɗan dakata,da jajayen idanu ya sake waigawa yana duban mustapha,yace"dakai nake fa...nace dawa kayi waya dazu...?" da rawar murya yace"Da itace....don Allah kayi hakuri bakina ne ya suɓuce har nace mata dirowa ta gari kenan…" wani irin wawan burki ne yaja ya gangara gefen titi yana jin yadda zuciyarsa ke zillo akan allon ƙirjinsa,with running tears ya dubi mustapha al"amarin daya sanya gabansa mummunar faduwa na ganin dan"uwan nasa na zubda ruwan hawaye don kawai ya gayawa matarsa cewa yana gari..?atake kawai ya tabbatarwa kansa da cewa tabbas babu lafiya,don bai ga abunda zai iya saka jarumin namiji kamar DCP Gidado zubar da ƙwalla ba sai akan al"amarin da yayi tsamari...



Gidado ne ya katse mishi ɗan guntun tunaninsa"meyasa zaka ɓatamun shiri bayan mun tsara ni dakai cewa bazaka fada mata ba sai dai ta ganmu ƙwatsam…?mustapha why...?ashe dama zuciyarka bata da riƙo da amana...?ashe bazaka iya cika ordinary promise ba…?yuff spoilt my plan......juz get down na fasa zuwa gidan....." ya ida magana tare da grabbing kansa da karfi yana jin tamkar yayi hauka don gabaki ɗaya ya ɓata mishi duk wani shiri nashi,

Su Baba Haruna da suka gama ruɗewa da wannan al"amarin,sun rasa gano inda zance ya nufa,Baba munniru ne yayi ƙarfin halin cewa"Kai kunci gidanku dukah...mu sa"annin wasanninku ne dahar zaku dakko mu daga gida ku maida shashashai...?kun sakamu acikin duhu sai abunku ku kadai kuke tayi,hakanan ya dace..?toh meye amfanin tasomu agaba da kukai...?muzo muyi kallon wasan ƙwaiƙwayo ko mene…?

Baba Haruna ne yashiga tausarsar yana kwantar masa da hankali dakyar yadan sakko,Gidado kuwa kamar ya sani yace hadda Baba munnirun ya biyosu don kakaf acikin dangi shine mai ɗan karancin fahimta da kuma yadda da zance,yana daga cikin dalilan dayasa ya gwammace akamasu Azeema turmi da tabarya,ya samu shaidu in ba haka ba idan yaje da zancen abaki ba yadda za"ayi ba,kai Baba munnirun ma yana iya sa adda ya fille masa kai don kai tsaye zai ce sharri aka kullawa ɗan nasa…

Cikin tsantsar tashin hankali Mustapha ke fadin"Don girman Allah Hamma ka gaya mana abunda ke faruwa plsss..." azuciye Gidado yace"bayan ka ɓata mana shiri shine kake son na gaya maka komi……?ka gane mai aciki...?toh ka sani bana aiki ba tare da evidence ba,ka riga kayi spoiling komi so ka jira next time...ammh for now get down from my car kuma karka bari na sake maimaita kaina..."

cike da mutuwar jiki ya balle murfin motar ya sauka,ko jira ya rufe kofar Gidadon beyi ba ya fuzge motar aguje,su Baba sun cika mishi kunnuwa da uban tambayoyi ga lissafin kwalkwalwarsa dake neman hargitsewa tsabar tunani,da karfi yace"Yabba kuyi hakuri bana cikin mood din bayani don Mustapha ya riga ya ɓata komai, ku bari idan na samu lokaci zanzo in muku bayani har gida...."

Baba Munniru ya cigaba da fada wai akan meye zasu maida hankulansu ta yara?kaza da kaza,waya mutu waya tashi...afusace Gidado yace"Yabba don Allah my brain....nayi imani da Allah dakasan mai nake shirin nuna muku ne da wallahi zaka so ace da mun cigaba da tafiya aduhu kawai ba tare da kun san komi ba...?

Baba munniru dai ya matsa alan dole sai an gaya mishi abunda ke faruwa,yace"Karka damu kadai fadamun kawai koda kuwa hakan na nufin zan sadaukar da rayuwata ne akai...."sosai yake neman caza kwakwalwar Gidado don Baba akwai masifa,tuni Gidadon ya soma tunano zantukan Azeema da kasim,nan da nan hankalinsa ya tashi,ya nemi fita hayyacinsa don baya tunanin akwai cin amanar data kai wannan muni,wai kuma duk akan neman haihuwa yasa su Azeema kauce hanya...?

Kwata kwata yama manta cewa tuki yakeyi sam bai lura da bus ɗin dake tahowa ta gabansu ba sai ji kawai yayi su BABA na ihu suna fadin"Kai Gidado mai kake tunani ne kalli gabanka mota na zuwa...." alokacin daya farga daga tunane tunanensa tuni lokaci ya kure,duk kokarinsa nason ganin ya kaucewa katuwar motar ammh still saida suka jame.....

Babu abinda kake ji sai kalmar _innalillahi wa"inna ilaihi raji"un_ dake fitowa daga bakunan mutane don tuni sun ƙaryo titin Garki sabida dama sune zai sauke agida…

Gidado ihu yake yana ambatar kalmar _innalillahi wa"inna ilaihi raji"un_ yana fadin"Ya Allah karka dauki raina ba tare dana gayawa mustapha abunda bai sani ba.....kasim kaci ama......" maganarsa ce ta sarke ah sa"ilin da kallonsa ya sauka akan Baba munniru wanda yake cikin wani mayuwacin hali,yayi wani irin jina jina dashi,sai lumshe idanu yake tayi idanunsa akan Gidado da shima ɗin yake cikin wani halin amma saidai baikai nashi ba,dakyar yake fadin"Suleiman don girman Allah kafadamun mai ɗana kasim ya aikata…?karka bari in mutu ba tare da sanin abunda yayi ba......." ya ida magana tare da zubowar hawaye wanda ya cakuɗe da jinin fuskarsa,kafin Gidado yakai ga cewa wani abu sai jin hayaniyar mutane sukai,daga nan bai sake sanin inda yake ba.....

***

Bayan Azeema ta gama waya da Mustapha har yake ce mata yana gidan Hamma kuma suna shirin wutowa gidansu ne..! da rawar jiki ta latso kasim take fada masa kar yazo mustapha na gari…

Shi kuwa mustyn bayan ya sauka daga motar Gidadon,saida yadan taka kan ya samu abun hawa zuciyarsa atunƙushe sam ya rasa meke masa dadi acikin duniyarsa,agaban gidansa motar hayar ta saukeshi,tun acikin motar ya hango wani manyantaccen mutum zaune adakalin gidansa,bayan ya biya taxi man ya soma nufo mutumin wanda ayanzu dai ya shaidashi,wannan taxi man ɗinne wanda ya taɓa dakko Azeema har yace masa daga saloon ya dakkota……toh ko meke tafe dashi..?mai yake nema....?

**

Taimakon gaggawa shine aka baiwa su Gidado don acikinsu duka babu wanda yake motsi,wasu acikin mutanen sun sansu farin sani kuwa,nan da nan akayi rushing nasu zuwa gwagwalada hospital ayayin da wasu kuma suka nufi gidansu hankali tashe don isar da mummunar saƙo………

*ku biyoni.....✍*

*HAFFY MOUSTY🌷*

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

_*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

   _ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA TALATIN DA HUDU...💥*_

     ………Ayau kimanin sati ɗaya kenan dasu Gidado suka sami mummunar hatsari,Baba Haruna tun awashegarin ranar ya miƙe don bai wani jigata ba hasalima ƴan kananu kananun rauni ne ya samu,Baba Munniru kuwa tun kafin ah isa asibiti rai yayi halinsa, _Innalillahi wa"inna ilaihi raji"un_ gashi har ya koma ga mahaliccinsa bai san takamemmen abunda ɗan nasa ya aikata ba,yau ne yake cike kwanaki bakwai cif da rasuwa,Gidadon kam shi ba"a ma maganarshi don har izuwa yanzu bai farfaɗo ba kasancewar yaɗan samu buguwa ne ah kai,

Tun jiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login